Showing 33001 words to 36000 words out of 260204 words
Chapter 12 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt
ta sake fiddo da wasu bugaggin shaddodi irin wud'anda akeyiwa rini har guda biyu ta sake miqa masa tace, "Nima ga tawa gudun mawar aqarawa 'yata dasu, ALLAH ya sanya alkhairi kuma yakauda idon maqiya." Tana gama fad'a tajuya tayi tafiyarta don gurinta ya gama cika, damuwar da takeso tagani a fuskar Yaya hawwa da takaicin da take son tusa mata arai tagansu qarara kuma taji dad'i,
Godiya ya dinga yimata yana fad'in ALLAH yabar zumunci kafin yajuyo wajen mahaifiyar tasa amma ga mamakinsa sai yaga tayi fuuuu..tabar wajen ranta ab'ace, kwashe kayan yayi yanufi wajen baffa dasu yana mai yabawa qoqarin 'yan uwan nasa, sunyi masa abunda kaf dangi babu wanda yayi tunanin yimasa kuma yaji dad'i sosai, haka shima baffa cike da jin dad'i yayita sanya masu albarka,
Yaya hawwa taci alwashin cewa koda ansa kayan alefen d'anta saita ciresu a gaban bilkisu tasa masu kalanzir ta qyasta ashana ta qonesu, ita ba ayi mahaluk'in daya isa ya nuna mata cewa ita da d'anta gajiyayyu bane balle ace za'a wani taimako masu har ayimata gori agabanta, ALLAH ALLAH ta dingayi gobe tayi kayan sudawo hannunta don tagwadawa inna bilkisu ita bata isa amma kash koda k'arfe 10 na safe yayi har baffa yasa ankira masa wani mak'wabcinsa dake da mota gwab irin ta haya d'innan yace da baffa Usman da kuma baffa Ali suje sukai kayan babu buqatar sai ankwashi ayarin mata guda anje kai lefe don d'ai d'orawa mutane hidima, duk yanda baffa Ali yaso zagayawa yazo ya sanar da yaya hawwa abun yacutara don baffa zaunar dashi yayi cikin d'akin yace karya kuru yatashi har sai angama kammala komai, baffa Usman shiya kwashe kayan yana kaiwa cikin mota yana dariyar yanda yaga baffa Ali na faman mutsu mutsu da qafafauwa yana son tashi amma baffa ya hanashi, bayan angama kaf baffa yaciro dubu goma aqarqashin katifar da yake kwance yaba baffa Ali yace idan sunkai lefen subayar asayi kayan wanka da ake kaiwa a al'adance.
Kallon baffa Ali yayi had'e da cewa "tashi kutafi kuma wlh karka sake inga kanufi cikin gidannan ina kallonka babban kwabo kawai"
Baice komai ba yamiqe yafita yana waiwayen cikin gida, ji yakeyi har wani cizonsa maganar keyi amma baffa ya kasa ya tsare ga kuma baffa Usman biye dashi yana gimtse dariyar dake cinsa, kamar yaro haka ya dinga kumbure fuska har suka bar qofar gidan,
Hamdala baffa yayi kafin nan yatura yusufa daya hango zai shiga cikin gida yace yakirawo masa Yaya hawwa, da qunquni tashigo cikin d'akin tare dayin tsaye bakin qofa fuskarnan ba annuri ko kad'an saboda fushin da takeyi dashi akan abunda yayi mata tace "gani lafiya?" Shikam dariya ma tabashi ganin yanda take cika tana batsewa akan d'an qaramin abunda yafaru tun kwana biyu da suka wuce, to inata da wannan baisan mezai faruba shiyasa yace qara yafad'a mata da kansa da ace taji ga wani, wannan dalilinne ma yasa yahana baffa Ali komawa cikin gidan don yasan halinsa tsab zai iya qarawa wutar fetur, cikin tsokana yace,
"Haba hawwa wannan irin cika da batsewa da kikeyi haka sai kace ba uwar ango ba, yihaquri zo muyi magana fushi ba naki bane kinji."
"Malan nifa inada aiki cikin gida inzaka fad'amun abunda zaka fad'a to kafad'a sauri nakeyi."
"To yihakuri kishigo mana." Badon taso ba haka taqaraso cikin d'akin tayi masa tsaye qiqam akai, murmushi yayi sannan yace,
"Dama zancen lefennan ne.." bai qarasa ba tace,
"Sai akayi me, ai jiya munriga mungama magana da yarona baza'a kaishi yauba sai gobe don haka nima inada hakk'i da d'ana yau nakira 'yan uwana abamu lefe suma sugani daga nan zamu fidda wud'anda zasuje kai kayan gobe in ALLAH yakaimu don wlh baza'aje da kowace shegiya acikin gidannan ba naji kana kawomun wasu kalan dangi ehe." Baki bud'e baffa ke kallonta har ta dasa aya kafin yace, "ikon ALLAH, waike kam hawwa har yaushe zakiyi hankaline?, Meye amfanin maido da hannun agogo baya da kikeyi yanzu bayan da yardar ALLAH nasan lefennan da kike magana har yakusa isa inda yakamata, don ALLAH kidinga tunani kirege fitina domin in mune aduniya gobe bamu bane, mutuwa na tare damu akoda yaushe saboda haka muzama masu hak'uri.." bai rufe bakiba yaga tajuya da qarfi tana kallon inda aka ajiye akwatunan had'e da lailayo asshar ta tule saboda ganin wurin da tayi wayam shiya tabbatar mata da abunda yake fad'i gaskiya ne, dole yariga da yasan hakan saita faru don haka ya gyara qafafuwansa had'e da mik'esu yayi kwanciyarsa,
Masifa tadinga zazzaga masa had'e da miyagun kalamai tana bubbuge abubuwan dake cikin d'akin tamkar wata mahaukaciya yayi tamakar baisan tanayi ba har tagaji don kanta tabari, amma yinin ranar mutanen gidan sunsha zagi manya da yara acewarta duka sunsan da zancen suka munafucceta, shi kuwa Nuraddeen da mahaifinsa sunsha tsiga da miyagun kalamai kala kala, Kai inkaji kace ba d'anta da mijinta take yiwa suba, yayi mata ranstuwa yana magiya akan baisan da baffa zaisa su baffa Usman suje kai lefen ba yafi aqirga amma fir taqi yarda, saboda tsoron fushinta har kuka yadinga yi yana roqonta Amma tace yafice mata daga d'aki Bata son ganinsa, itama saboda takaici da baqincikin rashin cikar muradinta har da k'walla tayi tana tsinewa yarinyar albarka.π€π€£
β’β’β’ β’β’β’ β’β’β’
A can garin yarimawa kuwa tarba tamusamman baba da qanensa malan balarabe suka yiwa su baffa Usman, sosai sunji dad'in karramawar da aka yimasu don musamman baba balarabe yasa aka gyara masu kaji ga fura da nono mai sanyi sannan aka yimasu abinci da abunsha musamman, ko kad'an baffa Usman baiso tsayawaba bayan sun bada kayan amma malan balarabe yayita roqonsu dole ganin girmansa yasa suka haqura suka tsaya, sunci sun sha sunyi nak sannan su baba sukayi masu godiya, musamman baffa Ali da har saida yayo guzurin nama a aljihunsa don yaji dad'in bawa yaya hawwa labari, dubu uku malan balarabe yabasu yace susha mai ahanya angode sosai baffa Usman yace bazasu karb'a ba hakan kuwa ba qaramin b'atawa baffa Ali rai yayi ba don har yafara hango lalurorin da zaiyi da nasa kud'in idan anbashi, haka aka rabu cikin farinciki da murna tsakaninsu baffa Usman da iyayen Rashida kowanensu na yabawa karamcin da suke dashi.
Duk da ba wasu kayane masu yawa ba ayanda ake qaryar lefe azamaninnan duk wanda yaga lefen sai ya yaba kyansu tare da qoqarinsaa matsayinsa na malami kuma mai matsakaicin k'arfi,
*A gurguje*
Acikin kwanakin da suka rage a d'aura auren Rashida da malan Idris abubuwa da dama sun faru musamman ta b'angarensa don kusan Yaya hawwa fidda hannuwantatayi a sha'anin auren Saida 'yan uwa da abokanan arziqi aka had'u akayita bata haquri sannan ta haqura gaba d'aya gidan bata magana da kowa duk gaba takeyi dasu akan haka har lokacin da auren ya matso ana saura kwana biyu, babu wani shagali da akayi inba walima ba wacce itama ab'angarensu Rashida aka shiryata don sukam suna cikin farinciki sosai musamman iyayen Rashida da ita kanta, shima Nuraddeen ba'a barsa abaya ba amma idan yatunada matsalolin mahaifiyarsa duk sai yaji auren ya fice masa arai saboda tsoron abunda masoyiyar tasa zata fuskanta acikin gidan musamman wajen mahaifiyarsa da kuma baffa Ali, ko ranar da akazo jere yana jin irin walaqancin dasu muneera da baffa Ali sukayi masu banda inna balkisu da tazo ta jajirce wajen da ba qaramin kunya tasu akayi ba hakan yasa baffa yakirata ya damqa mata ragamar kula da mutanen amaryar da zasu zo har zuwa lokacin da za'a kammala shagalin,
Anyi walima taji da gani don su baba balarabe sun taka rawar gani sosai kuma sunyi duk abunda yakamata ayi tun daga kan abubuwan ciye ciye dana lashe lashe, musamman aka yanka rago ranar walimar saboda had'ewa akayi haddata saukarta ta alqur'ani, malamai da dama sun halarci walimar sunyi nasihohi kalakala akan zamantakewar aure da kuma biyayya ga ALLAH da manzon tsira, baqar abayace mai kyau da tasha duwatsu ta ko ina jikinta da Kuma farar alkibba ta saka gashi tasha kwalliya had'e da lalle tayi kyau sosai kamar ba itaba, wani abu da zai qara burgeka ga walimar shine yanda malan Idris da abokanansa da sukayi zuwan bazata awajen walimar Jim kad'an da farawa yasha shaddarasa fara qal d'unkin riga da wando kaftani, nan take aka halarto masa da kujera kusa da inda Rashida ke zaune, wani irin farincikine ya lullub'eta a hankali tad'ago kai takallesa tayi murmushi shima yayi mata sannan tamaida kanta qasa, sosai iyayenta sukaji dad'in halartarsa wajen domin hakan yanuna masu irin muhimmancin da take dashi awajensa, nan aka cigaba da gabatar da nasihohin amarya da ango na saurare wasa wasa Rashida tafara jin gabanta nafad'uwa kafin can kuka ya kubce mata wanda ba sau d'aya aka saba ganin amare nayin hakan ba, anyi komai lafiya anqare batare da wata matsalaba kuma anyiwa amarya da ango fatan alkhairi tare da zaman lafiya da zuria masu albarka sannan kowa ya watse, yanda Rashida ke kuka sosai ba qaramin tab'awa malan Idris zuciya yayi ba don har saida yaso ya keb'e da ita don ya lallasheta amma kunya ta hanashi saidai akan hanyarsu ta komawa gida yakirata awaya ya lallasheta, Saida yaji tayi shiru tadena kukan sannan yakashe yana fad'in,
"Sai gobe habibty idan nazo d'aurin aurenmu.." bai qarasa ba takashe wayar tana dariya don tasan wannan tsokanar da biyu yayita, dariyar shima yayi sannan yakashe wayar yanajin wani irin farinciki marar misaltuwa aransa...
*_ALLAH KAJIK'AN IYAYENMUππ_*
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πΆββοΈπΆπ»ββοΈ *SANNU SANNU*πΆπ»ββοΈπΆββοΈ
π _Bata hana zuwa..._π
_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπ*
_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*π
_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*π
*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*π
*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*β€οΈ
Page___16π
Tun daga qofar gida da mashin ya ajiyesa yaga alamar cewa aiki akeyi agidan nasu saboda tarin yashi daya gani da masu aiki da sai faman shige da fice sukeyi da kayan aikinsu, yaran gidansu dake gefe suna buga k'wallone suka hangosa da gudu suka nufo inda yake suna fad'in "oyoyo yaya nura, ya nura oyoyo" suka qaraso wajen su kusan bakwai suna ruguguwar d'aukar kayan, cikin tsawa ganin yanda suke jan jikkunan akwatayyen suna ruguguwar d'auka yace "ha'a kai kunada hankali kuwa! Ji iskanci zaku lalata kayan mutane, maza ku ajiye kubani waje." Dariya suka aza masa ganin yanda ya zazzare masu idanuwa, kansu yayo ahasale kamar zai dokesu suka bar wajen aguje sunaci gaba da dariya, d'aya daga cikin sune daya d'arasu hankali ya tsaya yana had'e da cewa "yi hak'uri yaya nura" kwafa yayi kafin ya d'auki d'ayar jikkar da tafi girma da qarami yacewa yaron, "yusuf d'auko mun wannan d'ayar." Cikin jin dad'i yaron ya tallabo jikkar ahankali tamkar wanda ya d'auko k'wai yabi bayansa, Kai tsaye shigifar da baffa ke kwance yanufa da kayan yaron nabiye dashi sukayi sallama suka shiga, baffa na ganinsa ya washe baki had'e da cewa, "Kai agaida mutanen yarimawa, sannu da zuwa sannu da zuwa."
"Yawwa baffa, munsameku lafiya" Nuraddeen yafad'a yana ajiye kayan had'e da komawa kusa da mahaifinnasa ya zauna, shima yaron ya ajiye ta hannunsa inda yaga ya ajiye sauran sannan yafita, binsa da kallo baffa yayi kafin yajuyo ya maido kallonsa ga Nuraddeen yace "lafiya klw Nuraddeen yaron can nake kallo kaf cikin yaranmu shi kad'ai ALLAH yayiwa natsuwa sak irin taka, shiyasa yake matuqar burgeni, gaba d'aya halinsa ba irin na sauran yaran bane da kuma mahaifinsa, kaga ikon ALLAH bazaka tab'a ganinsa kace yaron Aliyu bane don gaba d'aya tun daga kamarsa da halin kai hatta tafiyarsa duk irin na Usman ne kai kace shiya haifesa" murmushi yayi had'e da cewa "ALLAH sarki baffa, ao dama zumunka ka haifa maka, ni kaina jinina yafi had'uwa da nasa akan sauran yaran, yanzu nagamo dasu abakin gida gaba d'ayansu basajin magana baffa saidai addu'ar ALLAH ya shirya."
"Amin fatanmu kenan!, Kai dai ka kula kuma dikkaninsu ka rik'esu gaba d'aya da zuciya guda saboda abu d'aya like kuma duk lalacewarsu bakada wud'anda suka fimaka su aduniya don haka kayi haquri da yanda halinsu yake ka sosu ka qaunacesu don bazaka iya canzasu ba, ubangiji ALLAH yayi maku albarka ku duka"
"Amin baffa, insha ALLAH zan kula da hakan har qarshen rayuwata."
"Masha ALLAH da kuwa naji dad'i sosai." Juyawa gefe yayi tare da jawo ledar magungunansa yana duddubawa sannan yace
"Baffa ya qarfin jikin naka?"
"Alhamdulillah ina samun sauqi sosai."
"Amma baffa jikinka ya gagara nuna haka har yanzu, kodai canza maka maganukkan nan za'ayi?."
"A'a nace maka nasamu sauqi sosai, yakabaro can wajensu 'yar tawa, suna lafiya?"
"Duk lafiya klw baffa"
"Madalla kasamu kaje kawatsa ruwa daga nan sai kashiga kagani komai yakusa kammala."
"To baffa, dama cewa nayi ga kayannan nagama had'awa sai 'yan abubuwan da baka rasa ba."
"Ahhh to masha ALLAH, ai wannan Bari kakeyi har saika huta sai ka kirawo ita mahaifiyar taka da sauran dangi abud'a agani, agaisheka ALLAH yayi albark."
"Amin baffa." Yafad'a tare da miqewa ya nufi sashen da mahaifiyarsa take, har ya aza qafa zaishiga cikin rumfar d'akin nata ya hangota wajen da dabbobi suke tana dama masu qasari, juyowa yayi tare da nufo inda take yana fad'in,
"Ahhh..innarmu ashe kina nan." Dayake kanta aduqe yake batama lura da shigowarsa ba sai yanzu da taji maganarsa ta d'ago kai da sauri had'e da cewa.
"A'a oyoyo oyoyo, d'an baffansa shigowar yaushe?" Takwankwahe hannun rigarsa yayi had'e da saka hannunsa cikin bahon da take had'awa dabbobin qasari yayi yana murmushi yace, "banjima da isowaba innarmu, ai nazata yarannan sunshigo sun fad'a maki, wajen baffa kawai nafara isa na duboshi da jiki."
"Rabu da ja'iran banza, yanzu haka wasa ta d'auke masu hankali basu shigo suka fad'a munba aida tuni na isa wajen kafin ka zazzagewa mahaifin naka aljihunka, gashi yanzu sun jamun tsiyar da k'ilan ko sisi bazan samu ahannun kaba."
"Kai innarmu! Ai kinsan yanzu ba'ayi albashi ba ko sisi banzo dashi ba balle baffa klya karb'a."
"Kai ni rufemun baki, kai da baffan naka ai ba'a gane kanku, Ina dai lafiya naga yau ka iso kafin a hau masallaci kai da baka isowa gidannan sai bayan sallar juma'ah wani lokacin ma har ana gab da sallar la'asar.?"
"Lafiya klw innarmu kinsan yanayin yanda rayuwar take, balle yanzu da abubuwa suka shigo gabana."
"ALLAH yakyauta, tashi kaje ka watso ruwa kaci abinci kafin afara kiraye kirayen sallah."
"To innarmu, wai kije baffa na nemanki."
"Kai nifa akwai aikace aikacen da nakeyi bana so inje yafara mani suruttannan da basuda gaira balle dalili." Kasa cewa uffan yayi ya girgiza kai cikin ransa yana mai addu'ar ALLAH ya shirya masa mahaifiyarsa.
Har yayo wankansa ya sauya kaya tana nan zaunenta ita da wata mata da tazo wajenta suna fira, wannan karonma girgiza kai kawai yayi yawuce abunsa, har yad'anyi nisata k'wala masa kira yazo,
"Kashiga kitchen akwai sauran d'imame ka kad'auka kaida mahaifinka don namanta bansamu tun d'azu nasa ankai masa ba." agogon hannunsa ya duba yaga sha biyu saura amma ace har lokacin mahaifinsa bai karyaba wannan wace irin rayuwace mahaifiyarsa keda ita bayan tasan ko cikakkiyar lafiya bayada, kamar zaiyi kuka yace.
"Innarmu badai sai yanzu baffa zai karyawa ba?"
"Eh mana, ai kaji nafad'a maka mantawa nayi, kaje ka d'auka katafi in kuma so kakeyi saika gama tuhumata to bisimillah."
"Bahaka nake nufi ba innarmu, kinsan ba cikakkiyar lafiya yake da ita ba ko kad'an bai dace ace yakai wannan lokacin bai karya ba domin hakan zai iya shafar 'yar sauran lafiyar data rage masa," mik'ewa tsaye tayi had'e da dukan qirji tana zaro idanuwa tace
"Nashiga uku ni kuluwa, yanzu yaronnan nizaka qarewa magana akan mahaifinka, eh lallai ta tabbata za'a rabani da d'ana tun ba'aje ko Ina ba, to tunda nabar ubanka da yunwa zoka dokeni kaji ko nura?."
"A'a innarmu ai batakai can ba ALLAH yabaki hak'uri." Yafad'a tare da shiga kitchen ya d'oko abincin sannan yawuce, yanaji matar dake zaune tare da ita tana fad'in.
"Kai hawwa! Haka nura yakoma maki marar kunya daga jin zancen aurensa?, To wlh sai kintashi tsaye inba haka ba da ankawo yarinyarnan yasan yanda lamarin yake shikenan kashinki yabushe, dubi wannan rashin kunya daya zuba maki daga ganin zaiyi aure to inata da anyi auren, gaskiya akwai aiki babba e'ehhhmmm nura kam ya lalace" cike da takaici ya qarasa barin wajen ba tare da yaji amsar da zata fitowa daga bakin mahaifiyar tasa ba, yana kaiwa bakin qofar shiga d'akin da baffa yake yaci karo da baffa Ali shi kuma zai fitowa, yana gaishesa amma kota kansa baibi ba jikinsa har rawa yakeyi ya isa wajen yaya hawwa ya kwarmato mata duk da dai baffa yace yaje ya kirawota, binsa da kallo yayi sannan yawuce cikin d'akin ransa a dagule, baffa isman daya gani zaune ya sashi sakin murmushi had'e da duqawa har qasa ya gaisheta bayan ya ajiye kwanon tuwon agaban baffa,
Baffa Usman na murmushi ya amsa masa cikin fara'a had'e da cewa,
"Agaida ango d'an gidan baffa, sannu da qoqari, ashe da tsiminka ab'oye kasa yayana yanata wahala." Cike da kunya ya noce kai qasa yana murmushi baffa Usman yaci gaba da cewa,
"Madalla to ai ka kyauta, ALLAH yayi albarka yaqara bud'i."
"Amin baffa Usman." Ya amsa masa a kunyace, jiyayi baffansa yace,
"Meye nan ka ajiye nura."
"Tuwone innarmu tace akawo maka."
"Kai kaci naka.?"
"A'a baffa alhamdulillah naqoshi.?"
"To Nima dai Alhamdulillah don qanena ya sawo mani abunda na samu na karya kuma har nasha magani, ubangiji Kuma ALLAH ya shirya yaganar." Dashi har baffa Usman sun fahimci yanayin damuwar da yashiga yanzu amma saboda shi mutumne mai haquri da rashin son aibata babba gaban qarami a maimakon yayi fad'a sai ya sauya maganar ta hanyar addu'a."
Kamar iska haka sukaga yaya hawwa tashigo d'akin rai ab'ace tana dube dube ALLAH kad'ai yasan abunda baffa Ali yafad'a mata wanda shi ya haifar da shigowar tata ahaka, tsaye tayi cak ganin akwatunan tana cika tana wani batsewa kafin ta kalli Nuraddeen tace,
"Amma kai wannan yaro munafuki ne, yanzu kasan da wud'annan kayan kazo a matsayina na mahaifiyarka a maimakon ka kaisu can saika tsaya anan dasu ka ajiye don d'ai munafucci, to meye alaqar uwaye maza da kayan lefe indai ba k'ulle k'ulle ake son