Showing 6001 words to 9000 words out of 260204 words

Chapter 3 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt

fatan tabbatuwa cikin amincin ALLAH da yardarsa akoda yaushe Kuma cikin kowane hali shine addu'ata agareku, tabbas naga karamci, halacci, yarda da kuma zallar soyayya agareku, nayi farinciki da kuma murna ganin irin kyakkyawar tarba dana samu daga wajenku akowane group wanda hakan yatabbatar mani da cewa nid'in takuce akoda yaushe, ngd ngd ngd sosai ALLAH yadubi zuciyar kowanenku yabiya masa da buqatunsa na alkhairi👏🏻 Ina farinciki da kuka nuna mani cewa yanda nake ikirarin cewa ina sonku FILLAH kuma kuna so na FILLAH😍 in sha ALLAH zan zage damtse wajen ganin kun ilmantu kuma kun nishad'antu da wannan littafi,😅fatana shine ku juri bina daki daki tare da qarfafamun guiwa, ni kuma in sha ALLAH nayi maku alqawarin da *SANNU SANNU* Zaku samu tarin fad'akarwa da kuma farinciki marar misaltuwa acikin wannan labarin🥰MUCH LUV FILLAH na wajena😘❤️_

Page___2💎

Aguje matashin saurayin ke tafiya saboda yanda Abba ke faman reren kuka tare da azazzalarsa akan yayi sauri, kusan minti ishirin da biyar suka d'auka kafin su isa cikin garin kano,

Hanyar asibitin suka nufa zuciyoyinsu cike da fargabar abunda zasu riska, suna isa ko daidaita parking basuyi ba Abba yafara kiciniyar bud'e gambun motar da sauri saurayin ya danna lock d'in motar had'e da cewa,

"Haba Abba! Me kake shirin yi hakanne, karka manta babu abunda muke iya canzawa daga qaddarar da ALLAH yatsaro agaremu da kuma sauran bayinsa, kabi ahankali in Sha ALLAH babu abunda ya samesu." ko jin abunda yake fad'a Abba ba yayi sai faman kica niyar bud'e motar yafita kawai yakeyi amma yakasa saboda lock d'in daya saka mata, ganin haka yasa wanda d'azu Abba yakira da hussaini ya dafa kafad'ar matashin had'e da cewa,

"Shurahbil bud'e masa kaji ko!."

"Amma uncle h...." Bai qarasa ba yayi saurin d'aga masa hannu da sauri shurahbil yacire lock d'in ba tare daya sake cewa komai ba suka fito tare da bud'ewa Abba da tuni yakai maqurar b'acin rai da hasala kawai yanayin da yake jin kansa acikine yasa bai tsaya bi takan saba, fitowa yayi har yana neman fad'uwa sukayi saurin riqesa ba tare da sunce dashi komai ba suka nufi emergency ward, girgiza kai shurahbil yayi tare da bin bayansu hannunsa na riqe da 'yan biyun da tunda sukaji tsayawar motar suka tashi daga baccin da sukeyi atare,

Har sun kusa shiga emergency d'an uwan uncle hussain wanda shine hassan Kuma mahaifin shurahbil ya juyo yace, "katsaya daga waje kafin muji halin da suke ciki, idan zai yuyu ma ka koma cikin mota da yaran nan, idan akwai buqatar kazo zamu nemeka."

Babu musu yakoma cikin motar shida yaran tare da ciro wayarsa yajawo game d'in race na motoci yanayi, dama aikinsa kenan aduk lokacin daya kad'aita shi kad'ai, yaran na ganin haka duk suka dawo daga inda suke zaune baya zuwa gaba inda yake zaune suka haye masa jiki suna kallo shi kuma mahaifinsa ya ida qarasawa can cikin emergency ward d'in tare dasu Abba suna tambayar mutanen da sukazo daga k'auyen da accident d'in yafaru, sunfi minti goma shabiyar kafin su samu su had'u da d'aya daga cikin wud'anda suka kawo su Abu sumayya d'in wanda shikad'aine ya tsaya awajen, sauran kuwa tuni suka wuce bayan sunga likitocin sun karb'esu, shima d'in saida wannan bawan ALLAHn yaje yakirawo police tukuna suka amshesu.

Hannu yabasu suka gaisa kafin yace, "kune iyayen bayin ALLAHn da mukazo dasu?." Cikin rawar murya Abba ya amsa masa da "eh bawan ALLAH mune, Ina zamu ganesu ne, suna ina?." Shiru mutumen yayi kafin ya d'an nisa fuskarsa cike da damuwa yace, "likitoci nakan duba su amma suna buqatar addu'ah sosai, shi namijin sun wuce da shi ICU (internatal care unit) ita kuma macen suntafi da ita gyni emergency." Shiru yayi tare da ciro gilashin idanuwansa yasa gefen babbar rigarsa ya goge k'wallan da suka zubo masa sannan yaci gaba da cewa, "dukkaninsu suna cikin wani mawuyacin halin da addu'armu kawai suke buqata, amma har yanzu ina kallon yanayin da naga baiwar ALLAHn nan aciki kafin suwuce da ita, abun gwanin ban tausayi yanda abun dake cikinta ke faman motsi Yana neman taimako yayin da ita d'in takasa d'aga ko d'an yatsanta da zaya iya bashi koda k'warin guiwa ne na second d'aya, Ina addu'a ubangiji yadubi karamci da tausayi irin na uwa alokacin da rauni yasa takasa bawa d'an dake cikinta taimako da yakawo masu tallafi da kuma agajinsa domin ceto duka rayuwarsu."

Wani irin jirine ya d'ibi su uncle hussain jin yanayin da 'yar d'an uwan nasu ke ciki daya sasu ja da baya tare da fad'awa zaune saman kujerun dake bayansu saboda tsananin tashin hankali suna furta kalmar, "innalillahi wainna ilaihirrajiun." dama shi Abba tunda sukazo suka samu suka lallab'asa ya zauna saboda bawata lafiyar qafafune keda shiba balle yajuri iya tsayuwa na tsawon lokaci, lokacin da yaji wannan labarin sai kawai ya sake fashewa da wani sabon kukan da dama tun d'azu yake yin abunsa saboda rashin sanin awane hali gudan jinin tasa take ciki, kalmar shahadar shima ya Fara maimaitawa had'e da cewa, "Amantu billahi, qadarallahu wama sha'a fa'ala." cikin tausayawa mutumen ke kallonsu kafin yace, "hak'uri zakuyi tare da addu'a kuma kusamu ku matsa inda suke nasan gab ake da anemi 'yan uwansu, ni ina kan hanya tane ta zuwana garin minna, dama tsammanin jiran isowarku anan kamar yanda d'an uwana ya sanar mun awaya shine dalilin daya tsaidani anan saboda nasan kuna isowa dole direct nan (emergency) zaku zo, don haka ni zan wuce, ga wud'annan takardun acikin aljihun namijin aka tsincesu" yaqarasa maganar tare da miqawa Uncle Hassan takardun, har zai tafi saiga wani Dr da shine suka karb'i case d'in anan emergency ya iso wajen had'e da kallonsa yace

"Ahhhh, ranka ya dad'e baka wuce bane?"

"Eh Dr sadeeq Amma yanzunnan zan tafi in Sha ALLAH, wud'annan sune patient relatives na mutanen da muka kawo" yabashi amsa tare da nuna masa su Abba dake zaune kamar ruwa yacisu.

"Masha Allah, ranka ya dad'e to ALLAH ya kiyaye ya kuma saka da alkhairi"

"Amin ya rabbhi" yafad'a tare da bashi hannu sukayi musa baha, kallon su uncle h yayi tare da cewa "duk wani abu daya kamata wannan Dr zai taimaka maku insha ALLAH, aminina ne sosai don haka ku kwantar da hankalinku, pls Dr you should consider..." har lokacin suna riqe da hannuwan juna.

"I will in sha ALLAH" yabashi amsa sannan suka yimasa godiya ya wuce, Dr yace sutashi yayi masu jagora zuwa can ICU d'in sannan suje gyni emergency, juyowar da zasuyi wajen Abba sukaga wayam babu kowa a mazauninsa, hankalinsu tashe saboda sanin yanayin da yake ciki suka fara duddu basa acikin wajen basu ganesa ba, cikin tashin hankali suka yiwa Dr bayanin ko wayeshi da matsayinsa ga patient d'in yace, "karku damu, inaga yakasa jurewane yanufi can, kuzo mutafi can d'in."

A b'angaren Abba kuwa kamar yanda Dr yafad'a kasa jure zama awajen yayi hakan yasa yamiqe lokacin da suke magana ba tare da sun lura ba yakamo hanyar gyni emergency jikinsa na rawa sai faman had'a hanya yakeyi, babu abunda yake buqata alokacin irin yaga 'yarsa kuma yasan ko awane hali take ciki, kasancewar dole sai yafito tacikin emergency ward d'in zai iya isa gyani emergency dake can gefe dasu yasa shurahbil ya hangosa yana harhad'a hanya tare da neman fad'uwa, da gudu yafita cikin motar ba tare da ya tsaya kula yaran dake tare dashi ba yanufi inda yake, da sauri ya qarasa wajen tare dasa duka hannayensa biyu ya rungu mosa yana fad'in,

"Abba ina kuma zakaje haka kai kad'ai, Ina su uncle ne?." 'Dago kai yayi ya kallesa ba tare daya iya furta masa komai ba sai dai ya nuna masa gefen da gyni emergency take da yake ana iya hangota daga nan inda suke, jujjuyawa shurahbil yayi yana kallon ta gefe gefensu ko zai hango su uncle h amma ko alamarsu babu, hakan yasa yariqasa suka nufi wajen, sukuwa 'yan biyun ganin yabar gambun motar abud'e yasa suka fito suma suna 'yan dube dube ta gefen, dai dai lokacin mutumen daya biyo bayansu Abba da mota shima yayi parking motarsa wajen tare da fitowa da sauri, cike da mamaki ya nufo wajensu tare da kamo hannun d'ayar yace,

"Ina zakuje ne?"

"Baba zamuje yabamu game." Tafad'a tana tsalle tsalle, tashi yayi ya leqa cikin motar yaga babu kowa aciki gashi kuma anbarta abud'e, gefe da gefe yakalla kuma baiga su uncle ba, hakan yasa ya rufe motar tare da ce masu, "to ina baban naku yaje?." hanyar da shurahbil yabi suka nuna masa. Kallonsu yayi yaga yanda suka jigata yace

"Zakuci abinci?"

"Eh zamuci dama yunwa mukeji" suka fad'a atare

"To kuzo muje" yafad'a tare da riqo hannuwansu, d'ayar ce ta wafce hannunta had'e da cewa, "ni bazan jeba." Itama d'ayar ta wafce hannunta had'e da cewa "nima bazan jeba" haddasu maqale kafad'a, tsaye yayi yana kallon su cike da burgewa kafin yace,

"To zaku zauna anan inje inkawo maku abinci?."

"Mu baba zamu bi."

"Haba yaran baba ai bakusan inda zaku ganesa ba tunda yayi nisa, ku zauna anan karkuje ko ina bari naje nakawo maku abinci kuci kunji ko?"

"A'a sai dai ka kaimu wajen dady da ummie zasu bamu abinci muci ko hassana!" d'ayar tafad'a tana kallon 'yar uwarta,

"Eh, ke ummie ke baki ni kuma dadynah take bani abaki ko"

Tsayawa yayi yana kallonsu cike da jin wani farinciki aransa wanda baisan dalilin saba, yanayin surutunsu na matuqar burgesa wanda yanzune ya gano wacce taqi karb'ar ruwa a hannunsa d'azu itace hassana kuma itace tafara cewa baza take ba, d'ayar kuma itace hussaina wacce ta d'an karce a gefen kuncinta na dama, wani irin tausayinsu ne yaji ya rufesa tunawo da halin da iyayen nasu keciki yayi tare da addu'ar ALLAH yatashe masu da kafad'unsu, juyawa bayansa yayi ya hango d'aya daga cikin security d'in asibitin yamik'e tare da isa wajensa yabashi hannu suka gaisa sannan yace

"Don ALLAH ko zaka iya kula mani da yaran can kafin inje indawo?."

Ganinsa babban mutum yasa yayi saurin cewa, "Babu damuwa Alhaji indai zasu zauna." Don yasan dole za'a shafa masa wani abun, komawa wajensu yayi yariqo hannunsu yace,

"Yawwa yaran baba, kuzauna anan kafin babanku yadawo zanje nakawo maku abinci kunji ko?." Da sauri yabar wajen yanufi wani waje da ake saida abinci cikin asibitin aransa yana addua'ar yana saqa wasu abubuwa.

Cikin mintuna biyar yaje ya siyo abincin ya dawo ya taddasu tare da security d'in sai faman surutu suke yimasa tamkar sun sanshi, murmushi yayi sannan ya bud'e bayan motarsa ya d'auko wata carpet mai girma ya shinfid'a cikin inuwar tare da aje abincin hannunsa sannan ya jawosu ya zaunar dasu ya bud'e masu abincin ya tura masu a gabansu, d'aya daga cikin take away d'in da yayo ya sake d'auka ya miqawa security d'in dama donsa ya siya tare da gorar ruwa d'aya da kuma lemu yanata godiya.

Kallonsa sukeyi sana kallon abincin batare da kowacensu tasa hannu ba yace, "kuci mana." Girgiza masa kai sukayi alamun bazasu ciba yace

"Meyasa" atare sukace "dady yake bani idan zanci" itama d'ayar tace, "ummie take bani abaki." Shiru yayi kafin yajawo gorar ruwan d'aya ya wanke hannunsa tare da d'ibar abincin yafara basu abaki ahankali, idan yaba wannan yaba wannan yana jin wani irin farinciki ya mamaye masa zuciya.

Shurahbil kuwa suna isa gyani emergency sukaga wasu nurses aguje sun wuce da oxygen cikin theater room d'in dake laqe da wajen, bayan kamar mintuna bayar suka wasu sun sake wucewa da wani aguje, tsaye sukayi tare da rashin sanin abunyi data inda zasu fara, sunyi minti uku a tsaye kafin suga wata docter tafito daga cikin wani office dake kallon d'akin theater d'in da sauri shurahbil ya tareta had'e da cewa,

"Assalamu alaikum, don ALLAH Dr ko nanne aka kawo wata patient da suka samu accident mai juna biyu?" Don kallo d'aya zakayiwa matar katabbatar da cewa ita d'in cikakkiyar likita ce,

"Eh nanne, yanzu haka ita aka gama yiwa tiyata, ko kune relatives nata?." Ta tambayesa atak'aice

"Eh mune Dr yafad'a tare da gyara tsayuwarsa da alama yana son jin qarin bayanine daga bakinta, amma ga mamakinsa sai yaga tawuce cikin d'akin ba tare data sake cewa komai ba,

Dr sadeeq kuwa koda sukaje ICU d'in yashiga d'akin da ake duba Abu sumayya ya tarar ana k'ok'arin gyarasa saboda mai kowa mai komai ya amshi abunsa wato dai ALLAH yayi masa rasuwa, rufe idanuwa yayi cikin jimami tare da girgiza kai sannan yanufi wajen wani dr dake tsaye akan gawarsa yana qoqarin had'a bayanan tabbatar da mutuwarsa bayan dogon bincike da suka gudanar akanta, kallonsa yayi yace
"Ahh..Dr sadeeq kadawo? Kadai ga yanda ALLAH yayi ikonsa akan wannan bawa nasa ko, ya samu internal injury ne cikin k'wak'walwarsa haka kuma zuciyarsa tabuga a sanadiyar tsoro da kuma fargabar daya ziyarcesa a lokaci d'aya Kuma sai akaci sa'a yana d'auke da hawan jini wanda shine ya qara tasiri wajen bugawar zuciyar tasa har tafashe" girgiza kai Dr sadeeq yayi had'e da cewa,

"ALLAH sarki, ALLAH yajiqansa yayi Masa rahama, dama relatives d'insa ne suka iso"

"Ok zaka iya sanar dasu."

"Nooo..bazan iya ba Dr naseer i feel their pain."

"Ba damuwa, bari naqarasa had'e bayanan sai naje na sanar dasu, hak'uri zasuyi don dukkaninmu ita muke jira"

Sai bayan kusan mintuna biyar sannan suka fito tare da Dr naseer d'in suka nufi wajen da su uncle h suke tsaye, gaisawa suka farayi dashi sannan yayi masu bayanin ALLAH yayiwa patient d'insu wato Abu sumayya rasuwa...salati suka farayi tare da jinjina al'amarin, tabbas sunji ba dad'i rasa nagartaccen mutum irin Abu sumayya adaidai wannan lokacin da suke tunanin shine cikar burinsa da kuma farincikinsa don uncle hussain ahadda hawayensa, haquri suka basu sosai tare da addu'ar ALLAH ya gafarta masa sannan Dr sadeeq yace suwuce gyni saboda ga alama Abba baizo nan ba,

Jikinsu a sanyaye suka bar wajen suna tuna irin muqabalar daya fuskanta kafin su bashi auren 'yar tasu.

Suna isa Dr da d'azu suka magantu da shurahbil nafitowa wasu nurses su biyu na biye da ita abaya d'auke da jarirai guda biyu a hannunsu, kallonsu tayi tace

"A'ah Dr sadeeq barka da Rana, yau kaine a ward d'inmu?"

"Barka Dr imaan, ya zamuyi nabiyo patient d'inmu da muka kawo anan wacce tasamu accident, so dama d'azu da mukazo ake fad'amun kece on duty keda su Dr odugun da Dr na'eem hop anyi nasara wajen aiki"

"Yeah upcouse, Ashe kaine Dr na'eem ke kwatantamun, ya aiki?"

"Alhamdulilah Dr." Tafad'a tare da kallonsu uncle h dasu Abba dake tsaye suka gaisa sannan tace

"Ok Dr wud'annan sune relatives d'in patient d'inka"

"Eh Dr imaan"

"Ok congratulation Alhaji anyi nasarar ciro mata 'yan biyu macce da namiji amma.." kafin ta iyar Abba yafashe da kuka yace,

"Shikenan dama nasan hakan zata faru, ya ALLAH kayafemun, yau gashi nayi sanadiyar jefa kaina cikin huznu dalilin nisanta kaina da ita da nayi, ta tafi tabarni da mikin da har lokacin da za'a karb'i tawa rayuwar bazai warkemun ba." Dafa kafad'arsa Dr imaan tayi had'e da cewa

"Haba baba! Waya fad'a maka 'yarka tarasu, 'yarka na a raye saidai ba wannan kukan naka take buqata ba, kayi hak'uri addu'arka ita take so yanzu kaji" wani irin sanyi yaji azuciyarsa wanda saida hakan ya bayyana qarara a fuskarsa ya juya gabas yayi sujudush shukur had'e da kallonsu uncle h da fuskokinsu suka kasa bayyana farinciki ko kuma damuwar da suke ciki yace,

"Alhamdulilah, Hassan hussaini 'yarku naraye bata mutu ba, kuzo kuyiwa ALLAH godiya kunji ko." ganin yanda fuskokinsu suke yasa hankalinshi ya koma akan mijinnata da sauri ya qarasa inda Dr sadeeq yake yace,

"Dr ya jikin mai gidan nata?"

"Sai hak'uri Alhaji shikam ALLAH yayi masa cikawa"

"Innalillahi wainna ilaihirrajiun" Abba yafad'a da k'arfi tare da fad'uwa zaune, duk wanda ke wajwn jikinsa yayi sanyi jin cewa Abu sumayya ya rasu, hatta Dr imaan saida taji shock atare da ita saboda tunowa da halin da matar ke ciki, "ALLAH yajiqansa tafurta tare da juyawa ta koma cikin d'akin tiyata"

Su uncle h suka karb'i yaran suna kallo tubarkallah masha ALLAH dasu, kyawawa dasu sak kamar mahaifiyarsu gasu da girma sosai, hud'uba suka yimasu sannan sukaba nurses d'in su aka koma dasu ciki saboda ga alama basuda lafiya don gaba d'aya hannuwansu saye suke da calular irinta qarin ruwa,

Shurahbil kuwa jiyayi tamkar kar arabashi da jaririyar dake hannunsa wacce itace hussaina d'an namijin kuma shine hassan yana ta kallonsu har suka shige dasu ciki, hakan ne yasa
ya tuno da yabaro 'yan uwansu a mota d'azu kuma bai rufeba, ai da sauri ya juya yamik'i hanyar inda suka ajiye motar,

Yana zuwa ya tarar basu cikin motar, nan take duk hankalinsa yatashi yafara dube dube harda qarqashin mota, kamar ance ya juyo ya hangosu cikin motar mutumen ya kunna masu laptop suna kallo hankali kwance, zaro idanuwa shurahbil yayi tare da qarasowa wajen yafara bubbuga glass d'in motar saboda duka a kukkulle suke saboda a.c da aka kunna, a hankali mutumen yafara sauke glass d'in motar tare da juyowa yana kallon shurahbil...







*_ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*
[8/17, 10:18] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___5💎

A yanayin da barrister kamal yashiga wajen iyalinsa dake zaune a babban falon dake tsakiyar d'akunansu suna fira ya tabbatar masu da cewa akwai matsala, hakan yasa amaryarsa meenatu dake d'auke da tsohon ciki wata takwas miqewa da nufin barin wajen saboda 'yar uwar tata sajida da yake d'akinta tasamu damar rarrashinsa da kuma kwantar masa da hankali, kirawota yayi cikin sanyin murya yace

"Ina kuma zakije?."

"Zanje na kwanta dama muna jiran dawowar kane munji shiru."

"Shine kuma zaki tafi baki jira jin dalilin daya dad'ar dani ba?."

"Kayi hak'uri, baccin ne yariga yazo kuma kasan yanayin jikin nawa" tak'arasa maganar tana faman lumshe idanuwa irin na masujin baccinnan, hannunta yariqa tare da rakata har cikin d'akinta yasa taje tayo arwalar bacci sannan ta kwanta ya lullub'amata bargo tare da kashe mata fitala sannan yafito.

Zaune


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login