Showing 177001 words to 180000 words out of 260204 words
Chapter 60 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt
tad'an saki fuskarta tare da d'aga hannu kamar zata maresa sannan ta ajiye tana fad'in.
"Bakayi laifi ba amatsayinka nad'a don ka ambaci mahaifinka, nakan ji ba dad'i kawaine aduk lokacin da aka tuna mani dashi, amma taya kake tunanin zan manta da muryarsa bayan a kullum inajin muryarka?, Hakan zai kasancene kawai idan rouhina yarabu da gangar jikina, tashi katafi, ALLAH yasa kaci galaba a soyayyarka kuma yabaka ikon shiga gaban duk wani Abu da zai shiga tsakaninka da ita, ya hanaka zubar da qwalla acikin soyayyarka kamar yanda nayi."
"Amin ya rabbi gwaggo, Amma nafasa tafiyar sai gobe in Sha ALLAH, bazan iya tafiya nabarki da b'acin ran da nine silar sakaki acikinsa ba koda da qwarar zarra ne."
Wani farinciki taji ya dirar mata azuciya saboda jin kalamansa, tabbas tasan yana iya qoqarinsa wajen faranta mata, don haka itama dole taso duk abunda zai faranta masa, ko kad'an bata tab'a sa tsammanin biyayyarsa tayi girman da zai datse duk wata alaqa da abunda yake matuqar so ba musamman waya da baza'a iya yiwa kowane mutum shamaki akanta ba, murmushin daya fassara masa irin farincikin dake zuciyarta ta sakar masa had'e da cewa.
"Tashi kaje marece nayi Abu sumayya, ALLAH ya tsare hanya, kuma kagaishemun da ita sosai kaji ko.?"
Cikin qwarin guiwa yamiqe yanajin farinciki shima aransa tare da yimata sallama sannan yabar d'akin, part d'in Fatima yanufa itama yayi mata sallama had'e da kama hanya yana mai fatar samun masoyansa cikin qoshin lafiya.
Bashi ya isa kano ba sai zuwa qarfe takwas da rabi na dare, kai tsaye ya nufi anguwar su batool batare daya biya ko Ina ba don ko baba balarabe da baffa bai sanar dasu zancen zuwansa ba saida ya iso sunata mamakin abunda ya dawo dashi bayan sunsan yau yakoma,
A anguwar sharad'a phase 1 little yasa Mai mashin d'in daya d'aukosa ya ajiyesa kamar yanda batool ta tab'a fad'a masa.
Bayan ya sallami mai mashin d'in yanufi qofar wani gida daya hango mai gadin gidan awaje shida wani mutum saman kujeru, hannu yamiqa masu duk suka gaisa sannan yashiga tambayarsu don ALLAH a ina ne gidan Alhaji umar fari,
Tasowa d'aya daga cikinsu yayi ya d'an matso kusa dashi tare da nuna masa wani gida can gaba kad'an da yatsa yana fad'in.
"Kaga wacan gidan mai gate kalar ruwan qwai?, to ka matsa gaba canne gidansa?"
"Alhaji umar fari nake tambayarka fa?"
"Eh! Kaje mana canne gidan, halan kai baqone agarin?"
"A'a! kawai dai bansan gidan bane."
Little yabashi amsa had'e da miqa masa hannu yayi masa godiya sosai sannan yawuce.
Bakin gate ya tsaya lokacin daya isa qidan yana qarewa girmansa da had'uwarsa kallo, gabansa ne ya soma fad'uwa da sauri ya dafe qirjinsa tare da isa jikin gate d'in ya d'an qwanqwasa mai gadin ya leqo had'e da cewa.
"Waye?"
"Amm..nine?"
"Kaine wa?"
"Baqon batool ne."
Bud'e masa yayi tare da cewa ya shigo, bayan yashiga ciki maigidan yadinga qare masa kallo tun daga sama har qasa sannan yace.
"Jira, Bari afad'o mata."
A daidai bakin qofar shiga falon part d'insu batool ya tsaya tare dayin sallama,
Cikin sa'a kuwa yaji muryarta ta amsa lokacin ita kad'aice a falon kwance tana faman karanta wasiqar jaki, gaba d'aya tashin hankalin da take ciki akan mazajen da mahaifinta ke kawo mata ta aura tana bijirewa yasa ta manta cewa shekarar da take zaman jira ta shigo har taqare batare data sani ba, gaba d'aya tarame ta lalace saboda matsi da takurar mahaifinta, Babu wani farinciki da take samu awajensa yanzu saboda gazawar da tayi wajen yimasa biyayya, gashi bai saba mata da hakan ba sai abun ya kashe mata biyu, agefe d'aya tunanin masoyinta da d'imbin soyayyarsa dake qara cika tana timbatsa acikin zuciyarta ad'aya gefen kuma takura da kuma damuwar da take cikine sai sukabi suka tasota agaba tabi duk taqare, Yauma saida mahaifin nata yayi mata duka saboda b'acin ran da tasashi aciki na walaqanta d'an amininsa da yazo wajenta bisa umurnin mahaifinsa akan zasu had'asu aure kuma yaganta yace yana so, zaune suke a Paris hutun da aka samu yadawo dasu nageria, ai kuwa tayi masa tas, tabuga masa warning akan ya nesanta kansa daga mafarkin dake nuna masa cewa yanemi soyayyarsa domin itad'in mallakin wani ce, gaba d'aya rouhinta, da kuma gangar jikinta na masoyinta ne kuma koda zai shekara d'ari yana bibiyarta bazata tab'a amince masa ba balle yasa ran zata auresa, da taga yanace yana son takurata harda riqe mata mayafi ta zabga masa mari had'e da cemasa yayi kuskuren aikata mata hakan domin hatta abubuwan da suke mallakinta mutum d'aya ne keda hurumin tab'asu, shine masoyinta, cikin gida tashiga ta d'auko ashana tare da kalanzir ta canzo wani mayafi tazo da wanda tacire ta jefasa agabansa tasa masa kalanzir ta cinna masa ashana yaqone, Saida yagama qonewa sannan ta d'ago kanta had'e da cemasa, "kamar yanda kaga na qona wannan mayafin haka zan qona duk wata zuciya da tayi qoqarin tunkarata da kalmar so, zaifi sauqi agareka ka manta da wannan kalmar agareni acikin rayuwarka ni kuma nayi maka alqawarin zanci gaba da kallonka a matsayin Yaya Kuma nabaka girma a matsayinka nad'an aminin mahaifina, ai kuwa tana rufe baki taji an d'auketa zazzafan marin da saida taga wuta, ashe duk abunda yafaru mahaifinta nacan daga gefen corridorn bayan d'akinsa yana hangota, shinefa har ya iso bata sani ba ya d'auketa mari, da gudu tayi cikin gida yabita yayi mata shegen duka, da Kuma yasanarwa da mahaifiyarta shine itama tayimata fad'a sosai kuma ta d'auki fushi da ita.
Tana tunanin wud'annan abubuwanne taji mai gadin yace.
"Wai anayiwa batool sallama."
"Je kace bata nan." Tabashi amsa ataqaice cike dajin haushi.
Bayan mintuna biyu ya sake dawowa yace.
"Wai yace don ALLAH kizo ba dad'ewa zaiyi ba kawai yanaso yagane kine."
"Kaje kace masa bana buqatar hakan koshi waye."
A hasale ta taso lokacin da taji yadawo tana fad'in.
"Idan kasake dawowa nan wlh saina tabbatar abakin aikinka."
Cikin rawar murya mai gadin yace.
"ALLAH yabaki haquri ranki shi dad'e ai har ya tafi, Amma yace afad'a maki Abu sumayya ne daga borno.."
Ai kafin yarufe baki da gudu tafito cikin falon har tana turesa gefe da kad'an ya fad'i tanufo bakin gate tana fad'in...
*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*ππ
[11/14, 22:52] Billy S Fari: πΆββοΈπΆπ»ββοΈ *SANNU SANNU*πΆπ»ββοΈπΆββοΈ
π _Bata hana zuwa..._π
_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπ*
_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*π
_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*π
*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*π
*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*β€οΈ
Page___81π
Duk iya qoqarin da baffa Usman zaiyi awajen don ya gamsar da baffa cewa Nuraddeen ba'a bisa hankalin kansa yaqi dawowa qasarsa ba qinyarda yayi daga qarshema ya shashantar da maganar tahanyar yiwa baba balarabe da shima yake had'a baki da da baffa Usman wajen qoqarin lurar dashi nuni da kwanon furar dake gabansa yana fad'in.
"Bisimillah malan balarabe kasamu ko furar ce kasha maqoshinka yabud'e sannan kaci abinci tunda naga nema kake ka ida dallashesa bayan kukan da kasha." Yaqare maganar cikin zolaya gaba d'aya sukasa dariya.
'Daukar kwanon furar yayi yasha sosai har saida yakusa shanyewa sannan ya ajiye baffa yace.
"Yawwa ko kaifa, yanzu fad'amun ya labarin 'yatah Rashida da mahaifiyarta?, Suma suna fushi damu ko?"
"Gaskiya banace haka ba, Amma dai ita mahaifiyarta taji ba dad'i sosai musamman da yarinyar taqi amincewa da hukuncin da shi mijin mahaifiyarta yayi yunqurin d'auka naganin yazo in akwai hanyar da za'abi don samun maslaha abi idan kuma babu sai aje kotu taraba auren, acewarsa bazai yuyu ta zauna da aurensa ba kuma bayanan."
"ALLAH sarki, dole zataji hakan ai, abubuwanne sunyimata yawa akai, Kuma bai kamata abiyewa ra'ayin yarinyar ba tunda ko musulunci bai yarda da hakan ba, kaga dai har yau babu wanda aka cutar acikin wannan al'amarin kamar ita Rashida, mtsss kwata kwata wannan abun beyi dad'i ba, wlh da anje kotun anraba auren da duk sai yafi akan wannan zaman da tayi tab'ata quruciyarta gaba d'aya ga wanda baisan darajar aure ba."
Baffa yaqare maganar cike da damuwa d'auke a fuskarsa, bashar (Abba) ne yashigo shida yayunsa asiya da Bilkisu riqe da jikunkunan littafansu na leda zasuje islamiya baba nusaiba tabakkasu abinci ga kwano sukawowa Yaya hawwa, kasancewar shine agaba yana hango baffa yarugo yafad'a ajikinsa, nan take duk damuwar dake tattare afuskar baffa ta b'ace ya d'agosa cike da fara'a yana fad'in.
"A'a aminina har anfito zuwa makarantar?"
"Eh baffa, Ina wuni?"
"Lafiya klw aminina, injin babarku tabaka abinci kaci ka qoshi." Yaqarasa maganar yana dariya tare da d'an mammatsa cikinsa.
Dariyar shima yayi sannan ya juya yaje wajen baffa Usman yabashi hannu suka kashe don shine gaisuwar tasu yana fad'in "Ina wuni baffanmu?."
"Lafiya klw malan bashar, za'a makarantar ko?"
"Eh.."
"To madallah, Allah yabada ilimi mai albarka."
"Amin." Yaron yafad'a tare da juyawa wajen baba balarabe daya hangosu asiya duqe agabansa suna gaishesa shima yaje yamiqa masa hannu sukayi sallama sannan ya gaishesa, dariya sosai yabawa baba balarabe ganin yanda yamiqo masa hannu suka gaisa batare da tsoro ba kamar yanda sauran yara keyi, yace
"Agaida yayana aminin baffansa, ALLAH yayi maku albarka." Ya amsa da amin mungode sannan yabi bayan 'yan uwansa da suka nufi cikin gida yana tsalle tsalle.
"Aminina kenan!, ALLAH yasa kagado mai sunanka da dukkanin nagartarsa."
Su baffa Usman suka amsa da Amin, aranar baba balarabe yaga irin tsantsar soyayyar da baffa keyiwa d'an uwansa don gaba d'aya firar tasa komawa tayi akan rayuwar da sukayi da abokin nasa alokacin da yake raye, wani wuri yana basu labari yana dariya wani wuri Kuma saidai ya girgiza kai ya goge qwalla had'e da cewa ALLAH yajiqansa.
Suna zaune bayan sun dawo daga masallaci sallar la'asar saiga kiran little ya shigo awayar baba balarabe, yana dubawa yaga kusan 21missed call daga mabanbantan lambobin daban daban saboda a silent wayar take, yana d'agawa little yafara fad'a dashi yana fadin.
"Haba d'an tsohona, a Ina ka shigane yau tun safe aketa nemanka ba'a ganka ba kuma anata faman kiran lambar wayarka kaki d'agawa sai yanzu?, ga wannan rigimammiyar tsohuwar nan yayarka tazo dubaka da jiki ta tadda baka nan, a maimakon tajira kadawo sai masifa takeyi da tsofaffin mutane wai ansan bakada lafiya akabarka kafita, duk inda ya kamata nadubaka na dubaka amma ban sameka ba, yanzu haka ganinan kasuwa nazo shima baka nan su uncle hassan kawai na isko, har a rumfar kaka naje nanma baka nan, Ina kajene gaba d'aya duk kabi ka tada mana da hankali?"
Maganar yakeyi batare da yabashi damar da zai amsa masa tambayoyin da take yimasa ba, hakan yasa baba balarabe yayi murmushi had'e da katse wayar, ko ajiyeta beyi ba yasake kira awannan karon cikin girmamawa yace.
"Yihaquri d'an tsohona, hankalinmune yatashi kasan bazamu iya jurar wani abun ya sameka ba, kana inane ranka yadad'e baban gwaggonah."
"Canake ko inbari harka gama fad'an tukuna sai na amsa maka tambayarka ko kuwa."
"A'a d'an tsohona Yihaquri natuba fad'amun inda kake inzo in d'aukeke."
Rage murya baba balarabe yayi kamar mai tsoron wani abu yace.
"Kana inane kai yanzu."
"Ina nan kasuwa,"
"To I akwai kud'i a hannunka kaje tasha inda kake rakiyar dattijon nan abokina kashiga mota kazo ina nan qauyen nasu, Idan kazo sai kakirani, kuma kada kafad'awa kowa kaji?"
Gaban little ne yafad'i cikin sarqewar murya yace "e.e.eh naji, amma meyake faruwane?, me kajeyi acan? lafiya d'an tsohona?"
"Lafiya klw lele, kaidai kazo, Idan kazo zaka samu dukkanin tambayoyinka acan, maza ina jiranka, kaga marece kenemanyi"
Bai bari yasake jefo masa wata tambayar ba ya kashe wayar tare da sauke wata it ajiyar zuciya.
Little naji ya kashe wayar da sauri yakoma shagonsu ya karb'i dubu d'aya a hannun uncle hassan don d'ari uku kacalce a aljihunsa ya nufi tashar da ake shiga motar bebeji, yana zuwa shine naqarshe ya shige sukabar tashar gabansa kuwa sai faman fad'uwa yakeyi shi kuma yana cigaba da karanto addu'o'in daya sani abakinsa.
Kasancewar drivern motar na gudu yasa suka isa cikin qanqanin lokaci ya kirasa had'e da sanar dashi cewa sun iso, kallon baffa usman yayi tare tambayarsa Ina zai cemasa akawosa ya fad'a masa sannan ya sanar dashi, saida yanemi mashin ya hau ya fad'a masa sunan inda zai kaishi yaji yafad'a daidai sannan yakashe wayarsa,
Kallonsa baffa keyi yanajin wani farinciki marar misaltuwa aransa, wai yau jikansane da aka fita da cikinsa acikin gidannan zai sake tako da qafafuwansa bayan tsawon wasu shekaru, tabbas ALLAH mabuwayine acikin al'amurransa don in bashi ba babu wanda ya isa yayi hakan, shikad'aine ya isa yanuna ikonsa ga yanda take buqatar wanzuwar abubuwa alokacin da yakeso kuma alokacin da yaga dama, bini bini baffa yakai kallonsa ga abakin qofar zaure yana jiran isowarsa, gaba d'aya ya matsu sai mutsinniya yakeyi tamkar wani yaro kai kace yauce rana tafarko da zai fara had'uwa da little d'in, murmushi baffa usman yayi yana kallon yanda fuskar baba balarabe kefidda annuri, shima sai kallon baffa yakeyi da alama yasamu farinciki sosai da gamsuwa akan abunda ya aikata yau.
Tsayawar Mai mashin aqofar gida yasa baffa Usman saurin fita ya samu yana sallamar mai mashin d'in, har little yaciro wayarsa zai kiran baba balarabe sai yaga baffa Usman ya nunasa da hannu had'e da cemasa.
"Abu sumayya?" Kamar yanda yaji baffa nakiransa dashi.
Murmushi little yayi tare da d'an russunar da kansa qasa yace.
"Eh, Ina wuni?" Fad'ad'a murmushin sa baffa Usman yayi tare da qarasowa wajensa yayi saurin miqa masa hannu tare da yimasa sallama, cike da yaqinin cewa tabbas wannan jinin d'an d'an d'an uwansane baffa Usman ya amsa masa sallamar yana qare masa kallo tare da tunano kammannin Rashida acikin fuskarsa.
Kusan secod biyar suka kwashe ahaka kafin can baffa Usman yayi firgigit kaman wanda yafarka daga bacci yajawo hannnunsa su shiga ciki, tunda suka shigo baffa ke kallonsa har suka qarasa, shidai little sai bin ko ina nagidan yakeyi da kallo kafin can ya ajiye idanuwansa akan baba balarabe, ajiyar zuciya ya sauke yana fad'in.
"Kai wlh ALLAH tsohonnan yau ka wahalsheni da yawa, gaba d'aya ka tada mani da hankali gabana sai fad'uwa yakeyi."
"To ai seyadena yanzu tunda gani kagani cikin qoshin lafiya."
Matsawa yayi inda baffa yake had'e da zaunawa kusa dashi yasa hannu ya dafo kafad'unsa, "sannu kaka, anwuni lafiya?"
"Lafiya klw Abu sumayya, ya kake?"
"Ina lafiya kaka, yanaga kamar jikinka a sanyaye.."
Muryarsa na rawa ya juyo duka jikinsa yana fuskantar little tare dasa hannayensa yariqo fuskarsa dasu yace,
"Farincikine yahaifar da haka jikana tare da samun kyakkyawan albishir daga bakin da bazai tab'ayimun qarya ba akan cewa kai d'in jinina ne, katuna nasha fad'a maka inada wani d'a tafiyarka da maganarka sak irin nasa, har kake tambayata yana ina? Kana so kasanshi katuna,"
Kasa amsa masa yayi saboda yanda yaji gaba d'aya jikinsa ya mutu yana kallonsa, juyowa yayi yana kallon baba balarabe ya jinjina masa kai alamun tabbatar mas da zancen baffan.
"Hakane Nuraddeen, wannan shine kakanka wanda yahaifi babanka, nazab'i nahad'aka da sune batare da sanin mahaifiyarka ba da kuma 'yan uwana saboda gudun lalacewar zumunci tsakanina da 'yar uwata, koba komai ni kaina na sauke wani nauyi da d'an uwana yamutu yabarni dashi aransa,
Little baisan lokacin da wasu hawayen da zai iya kira dana dad'i ba suka zubo masa da sauri yataso ya rungume baba balarabe yana fad'in.
"Nagode d'an tsoho da kazamo nafarko wajen cika mani muradai na da kuma mafarkaina, kayi mani abunda duk duniya Babu Wanda zai iya yimani, ka haska mani rayuwata alokacin da take cikin duhun rashin sanin makomarta anan gaba, ba shakka kakana yafi kowa sa'ar samun d'an uwa aduniya, yayi saurin tafiyane saboda yanada yaqinin cewa goben ahalinsa zatayi kyau a hannun d'an uwansa, nagode maka nagode maka sosai d'an tsohona mai ran qarfe, ka dad'e kayi qarko har zuwa qarshen ahalinmu."
Yasake rungumesa sosai kamar zai tsaga jikinsa ya sakasa,
"Kai meye haka? Meye haka kakeyi lele? Cikani mana kasan ba qwarine da qashina ba yanzu, wannan abu haqqine akaina duk da nasan hakan zai iya haifarmun da matsala, amma nayi farinciki sosai, wannan addu'ar taka bana fatar karb'uwarta domin banaso qarkona yawuce lokacin da zanga jininka, don haka kama dena fatar hakan kaji ko?"
Yaqarasa maganar qwalla nazubo masa a fuska, d'agowa little yayi daga jikinsa yasa hannuwa yagoge masa hawayen fuskarsa yana fad'in.
"Kadena kuka mana d'an tsohona, kayi Abu mai kyau, ka sada yaron da akeyiwa kallon shege da danginsa na uba, ka gyara zumuncina don me da ALLAH zai tsaida rayuwarka ga iya ganin jinina bayan shi yafad'awa manzonsa cewa duk wanda ya kiyaye game da sha'anin zumunta zaiyi masa tsawon rai tare da gyara gobensa?, Natabbata koda baka kai lokacin da nakeyi maka fata ba in Sha ALLAH zaka wuce lokacin da kai kake fata, na dad'e da dason sanin dangin mahaifina, amma yanayin da mahaifiyata keshiga da alqawarin dana d'aukar mata akan bazan sake tambayarta abunda zai sakata cikin damuwa ba shi suka hanani tsaurara son sanin hakan saboda gudun na kaucewa umurninta duk kuwa da shegantani d'in da akeyi"
Miqewa yayi yakoma wajen baffa da duk wata kalma da yake ajewa ke dad'a tunkud'o da fitar hawayenta saboda tausayinsa da yakeji da kuma rad'ad'in kalmar da yaji ana jifarsa da ita, kamo hannuwansa yayi yana murzawa ahankali tare dayin murmushi alokaci d'aya kuma hawaye na zubo masa yace.
"Kakana kaima kuka kakeyi?, Kaida zakayi farincikin bayyanar jikanka agaresa mezai saka kuka Kuma?" Sa hannuwansa yayi akan fuskarsa shima yagoge masa hawayen dake zubowa sannan yaci gaba da cewa.
"Kana kewar mahaifina kamar yanda nima nake matuqar kewarsa ko?."
Girgiza masa kai yayi had'e da saurin rungumesa yana cewa.
"Ko kad'an jikana, kai kad'ai nake kewa da kuma mahaifiyarka, ka manta dashi tunda bayada buqatarmu na tabbata zaka maye mani gurbinsa."
"A'a kakana, zaiyi matuqar yimani wahaka na iya maye maka gurbinsa, kayi haquri kada kayi fushi dashi, duk da Ina son jin muryarsa, Ina son ganinsa, Ina son na rab'i jikinsa nayi fira dashi na fad'a masa damuwata nayi kuka ya sharemun hawayena amma nakasa samun haka saboda yayi nesa damu banyi fushi dashi ba, natabbata SANNU SANNU bata hana zuwa..kamar yanda bamuyi tsammanin zamu had'u da juna ba sai gashi ahankali ba zato ba tsammani ALLAH yahad'a fuskokinmu shima in Sha ALLAH da sannu zai dawo garemu, da kanshi zai cike gurbinsa da kake tunanin zan maye maka da yardar ALLAH."
Wani irin sanyi baffa yaji