Showing 213001 words to 216000 words out of 260204 words
Chapter 72 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt
ba aduniya don haka dole ta haqura da ra'ayinta tabi umurnin mahaifiyarta, haka taci taci gaba da renon cikinta yau ciwo gobe lafiya har watan haihuwarta ya kama,
Ranar tana zaune taga little yashigo kai tsaye yawuce d'aki yaje ya harhad'o mata kayanta cikin akwatuna biyu ya fiddosu falo sannan yakoma ya d'auko mata mayafinta yana fad'in.
"Gimbiya tashi muje.."
Binshi tayi da wani irin kallo dake cike da tarin tambayoyi kala kala da take buqatar ya amsa mata kafin sutafi yayi murmushi had'e da cewa.
"Easy madam! Bafa Saida ki zanyi ba, wannan irin kallo haka ai sai kisa 'yan kayan cikina zubikkewa."
Saida tayi dariya sannan yace. "Ahh.. to! Ba dole ba naga notice tsakar rana bazato ba tsammani."
'Dan matse fuska yayi kamar mai shirin kuka had'e da cewa. "Yana iya gimbiya! Gwaggo tace nakawo mata 'yarta yau d'innan ba sai gobe ba tunda watan haihuwarki yakama bazai yuyu kizauna ke kad'ai agida ba, nace zan ajiye aikina mu zauna gidan tare tace a'a, nace aturo maki Shahida shima tace bata amince ba, kinga kuwa dole na cika umurninta."
"Aw! Akan wannan abun d'an abun kake b'ata rai?, Lallei Abu sumayya kice kashagwab'e da yawa yanzu, Ina can d'in ba baqonka bane tunda bawani waje za'a kaini ba, ni danaso komawa kano gaba d'aya nahaihu can da sai kayi qaqa?"
"Tab inbiki mana!"
"Da kuwa katabbata bita zaizai gaskiya."
Taqare maganar had'e da tuntsirewa da dariya can kawai yaga hawaye na zubo mata dariyar takoma kuka, da sauri yaqarasa kusa gareta ya zauna tare da jawota ajiki yana fad'in.
"Gimbiya menene?" Ta d'ora kanta aqirjinsa had'e da cewa.
"Abbana, Ina son naga Abbana ko sau d'ayane, bana son namutu ban ganesa ba."
"Yaa salaam! Gimbiya meya kawo zancen mutuwa kuma, bazaki mutuba har sai muntarawa Abba jikoki da yawa da zaiyi alfahari dasu, kinsan ko jiya saida likita yafad'a maki cewa kirage damuwarnan da yawa tana tab'a lafiyar babynmu, shine kike kuka yanzu bakya son yafito very healthy ne?"
"Ina so mana, Amma bazn iya dena damuwa akan Abbana ba, Ina so naji muryarsa pls Abu sumayya ko a'ane."
Ganin yanda duk tabi tarikice masa yasa yaciro wayarsa had'e da kallonta yace.
"Idan kikaji muryarsa kinyimun alqawarin zaki dena wannan kukan?"
Da sauri ta d'aga masa kai yayi murmushi had'e da shafo kanta dake saman qirjinsa sannan yakira Abba da d'ayan layinsa na (data) da yake using dashi, don tunda ya gwada kiransa bayan auren sau d'aya suka gaisa yagano shine yadena samunsa daga baya idan yakira, may be ya kulle masa layine ta yanda bazai iya samun saba. Bugu d'aya Abba ya d'aga yana fad'in.
"Hello, hello assalamu alaikum." Can yayi tsaki jin ba'a amsa shiba had'e da kashe kiran, d'ago kai tayi ta kallesa hakan yasa yasake kiran lambar yana murmushi.
"Assalamu alaikum." Abba yafad'a awannan karon tare dayin shiru yana jiran a amsa masa a d'aya b'angaren, jin ba'a amsashi ba yasa ya sake tsinke kiran little yasake kira akaro na ukku.
A hasale abba ya d'aga kiran yana fad'in.
"Wai wayene halan? Idan ba'ada abuncewa kar asake kira, shashancin banza da wofi."
Amai makon ya katse kiran saiya ajiye wayar yaci gaba da fad'ansa yana fad'in.
"Wannan ai shashancine akira waya akasa magana, mutane sun d'auka yanda basada abunyi kowama baya dashi, saika rufesu da fad'a akama srry is wrong nomba."
Dariya batool takamayi ita da little tana goge hawayen da suka zubo mata, azahirin gaskiya taji dad'in jin muryar mahaifinta sosai amma aqarqashin zuciyarta wata irin kewarsa ce ta sake rufeta, tana matuqar son mahaifinta fiye da tsammani saboda tsananin shaquwar dake tsakaninsu abunma ba'a magana, qaddarowar son dake tsakaninta da little tajawo mata rabuwa dashi badon ranta yaso ba, cikin dubaru had'e da so da qauna little ya dinga fad'a mata kalamai masu sanyi da zasu kwantar mata da zuciya har saida yaga damuwar dake fuskarta ta gushe daga nan kuma ya karkata akalarsa izuwa muradinsa har saida suka farantawa juna rai sannan ya taimaka mata tayo wanka tashirya, akwatunan tajawo tasake gyara duk abunda take da buqata sannan yafito dasu yasa cikin mota, tana qoqarin fitowa yaja hannunta suka koma cikin d'aki shima ya d'auko wata jikka ya dinga jidar kayansa yana zubawa.
Turo idanuwanta tayi awaje tana dariya tace.
"Abu sumayya ya haka!, Ina zuwa da wannan uwar jikka haka kake ta loda kaya."
"Tab..ai wlh qafarki qafata bazan zauna ba, mezanyi agidan nima can zan koma ai inada nawa d'akin."
Dariya ta dinga yimasa har tana riqe ciki had'e da cewa.
"Ashe ko kaida gwaggo."
"Eh naji dai, amma bazan zauna anan ba ke kina acan sai kace wani mara gata." Yaqarasa maganar yana kulle zip d'in jikkar suka fice tare yanaci gaba da jinini tana dariya.
Satinta uku da komawa gidan Dr wajen Rashida wanda gaba d'aya duk kulawar daya kamata tasamu Rashida nabata wand idan kagani kai karantse kace 'yartace ba suruka ba, yauma kwance take saman gadon bayan sallar magrib Rashida na gefe tana jan carbinta sai kawai taga ta zabura, da sauri ta katse lazumin had'e da miqewa tanu wajenta ganin tariqe kunkuru,
"Batool lafiya?."
"Wash..gwaggo bayana."
"Subhanallahi sannu ko haihuwarce?" Bata tsay jin amsar da zata bata ba da sauri tajawo wayarta takira little sannan tayi cikin gida ta sanar da fatima."
Kan kace me gaba d'ayansu hankalinsu yatashi suka nufi d'akin da sauri, dur qushe suka iskota gefen gado tana yarfi da hannuwa tana cizon baki, ga wani zufa daya tartso mata alokaci d'aya saboda tsananin azabar naquda, ganin haihuwarce zangu zangu yasa Rashida ta d'auko wata qatuwar leda ta shimfid'a mata tare da zane sabo sannan suka kamata ita da fatima suka maida wajen, tun batool na juriya har azabar zafin ciwon naquda tasa tafara kiran abbanta tana fitar da wani iska abaki,
Wani irin tausayinta yarufe Rashida tunawa da irin yanda azabar haihuwa take da tayi, safa da marwa ta shigayi tana karanto addu'o'in da tasani abaki tare da nema mata sauqin rad'ad'in da take ji, bini bini tajuyo tayi mata sannu fatima kuwa tuni tafita taje takirawo Dr, yana zuwa yasa suka riqota suka kaita a mota daidai lokacin little shima ya iso hankalinsa atashe Dr yace yashiga motar ya shiga sannan yaja suka nufi asibiti bayan Rashida takoma ciki ta d'auka kayan da za'a iya buqata.
Ko mintuna ashirin basuyi da Isa ba batool ta samb'alo qatuwar 'yarta kyakkyawa jawur da ita, ho ho zo kaga murna a wajen little ba'a magana don gaba d'aya bakinsa kasa rufuwa yayi musamman da aka fiddo yarinyar daga d'akin haihuwa Dr yamiqa mashi ita, gaba d'aya kamarta sak da batool d'insa babu ta inda tabarota tun daga kan hasken fata har zuwa kamannin fuska.
Kallon Rashida yayi yana dariya yace.
"Gwaggo kinga yarinyar nan gaba d'aya mamanta ta d'auko ko tayimun 'yar kara nima tayi kama dani."
Murmushi kawai Rashida tayi batare data tanka saba tanajin wani irin farinciki marar misaltuwa na mamaye mata zuciya, soqo Fatima tayi masa akai had'e da cewa.
"Lallai little ashe rashin kunyarka har takai haka ban sani ba, bazaka bamu 'yar ba kakame kariqe sai kace wanda za'a qwace mawa sai kamanninta kake fad'a mana."
"Kema dai kyafad'a, bana fad'a maki baida kunya ko kad'an ba kikace a'a, to ai gashi yau kingani da idanuwanki."
Saida yayi mata hud'uba ya rad'a mata sunanta da tunkafin tazo duniya mamanta ta rad'a mata wato (sumayya) sannan yamiqawa Fatima ita yana fad'in.
"ALLAH yaraya mana sumayya." Had'e da gyara mata d'an bargon da aka nad'ota dashi aciki daya d'an rufe mata fuska.
Baki bud'e Rashida ke kallonsa tare da mamakin rashin ta idonsa kafin taji Fatima tace
"Aikam little kabushe fitilarka, ALLAH dai ya shiryaka, in dai wannan narkakkarce badon kar in saketa tafad'i ba ace kishine nakeyi ai dana sakar maka abukka qasa."
"Mama kice dai kinga zata anshe maki Abba shiyasa kikace haka, dama tunda yafito da ita naga yanata kallonta da alama yagama qyasawa."
Taji muryar abbaty daya biyo bayansu yafad'a yana wasar baki shima, hannu yaba little suka tafe had'e da cewa.
"Congrat real Abu sumayya, ubangiji ALLAH yaraya mana."
"Amin" duk suka fad'a kafin dady yasake dawowa ya fad'a masu cewa batool na buqatar jini sai an qara mata don jininta yayi qasa, nan take suka nufi lab shi dasu abbaty da little cikin sa'a kuwa ana auna na little yazo daidai da nata aka d'ibi leda d'aya aka qara mata,
Sosai batool tasamu sauqi don anata fira da ita 'yan uwa da abokanan arziqi dake zuwa dubata, murna awajensu uncle h ba'a magana suda hajia mama da sauran mutanen gida, abbanta ma da aka sanar dashi saida wani annuri ya bayyana a fuskarsa har zaiyi magana sai kuma yayi saurin d'aure fuska yaci gaba da duba jaridarsa batare daya tanka ba, baiso tankawa ba azancen sai kuma yaji ya tsinci kansa da cewa,
"ALLAH yara itama yabata lafiyar shayarwa."
Wannan addu'ar da yayi tasa kowa jin cewa tabbas nan kusa bada jimawa ba zai daina fushi da 'yar tasa kuma yadawo da ita cikin rayuwarsa kamar yanda take ada.
Bayan kwana biyu su uncle h zasuje dubo batool bayan an sallameta daga asibiti hajia mama tacire kunya agefe tabisu taje tadubo 'yarta da kuma baby sumayya, taji dad'i matuqa ayanda taje ta isko 'yartata cikin kulawa da walwala da kuma soyayyar uwar miji da sauran ahalinsa, kusan yini sukayi acan kafin sufara yunqurin juyowa su dawo gida bayan sun ajiye mata kayayyakin da suka jemata dasu masu uban yawa kama daga kan suturarta data baby, kayayyakin abinci da kayan qarin jini da kud'i masu yawa sukace taqara tayi hidima dasu kafin suna, kuma sauran 'yan uwanta da iyayenta nanan tafe ranar suna sannan suka yiwa Rashida dasu Dr da iyayensa godiya sosai suna masu nuna masu farincikin da sukaji na had'a zuri'a dasu da kuma yabawa qoqarinsu wajen kulawar da sukaba 'yarsu wanda hakan baqaramin dad'i yayi masu dady da dr ba suma, koba komai sun samu natsuwar cewa sun kula da amanar batool da suka basu d'ari bisa d'ari tunda har suka yaba ayanda suka ganta.
Ranar suna kuwa batool tasha mamaki don taga gata kala kala kama daga wajen 'yan uwanta har zuwa 'yan uwan mijinta da nasu Dr abun saidai tace alhamdulillah, anyi taron suna lafiya an watse lafiya na kusa sun koma gidajensu na nesama sun kama hanya saidai fatan ALLAH ya saukesu gida lafiya.
A 'bangaren hajia nafeesa kuwa har lokacin bata saduda ba don tanada abunda zata iya kula da kanta koda babu abunda za'a bata agidansu, Shakur nazuwa akai akai wajenta ya gaisheta tare da abun kyautatawa da ALLAH ya hore masa, yayita qoqari wajen lurar da ita kuskuren da tayi tare da nuna mata cewa yanda take d'aukar umma ba haka suke ba mutanene masu karamci da dad'in zama amma taqi fahimta saima masifar da take rufesa da ita wai shima ambashi ya canye kamar yanda aka yiwa mahaifinsa, hakan yasa ya haqura dayi mata nasihar saidai addu'a da kullum yake yimata akan ALLAH ya ganar da ita, wasa wasa tun ana qidayar watannin da tayi batanan yanzu har takusa shekara amma taqi ta hankalta hakan yasa 'yan uwa da abokanan arziqi aka shiga ba Abba haquri akan yabari tadawo d'akinta tunda ba sakinta yayi ba shima yabuga kai ga qasa yace bazai bari ba har sai tayi hankali, kawai aqyaleta taci gaba da abunda takeyi ai SANNU SANNU bata hana zuwa...lokaci zaiyi wanda idan taji wutar gashinta da kanta zata gano kuskuren da tayi kuma tanemi gyarawa.
_BAYAN SHEKARU BIYAR_
Abubuwa da dama sun faru ciki har da rasuwar 'yarsu Abu sumayya da gimbiyarsa lokacin tanada shekara d'aya aduniya wanda hakan ya matuqar tayar masu da hankali, musamman Rashida da little da suka d'auki son duniya suka azawa yarinyar don little kam har da zazzab'i yayi na tsawon sati d'aya, batool kuwa gaba d'aya ta dangana tabarwa ALLAH ikonsa acewarta shikad'ai yasan dalilin amsar yarinyar, yarinyar nada matuqar kwarjini da kuma shiga ran mutane sosai wanda hakan yasa mutuwarta tagirgiza mutane da yawa, ciki kuwa harda hajia nafeesa da tuni tayi nadamar abubuwan data aikata saboda ba kad'an tasha wahalar zaman gida da tayiba sanadiyar gobarar da sukayi gidansu yaqone qurmus da mahaifiyarta aciki saidai aka tattara tokarta data cinye aka sallaceta aka rufeta, ita kuma gaba d'aya jikinta yaqone fuskarta kawaice bata qone ba itama gefe yafara qonewa aka kaita asibiti da taimakon dady inda daqyar likitoci suka ceto rayuwarta don babu wandama yayi tsammanin cewa zata rayu, sai gashi cikin iyawar ALLAH da yardarsa da take kwana basu qare ba tasamu sauqi bayan takwashe watanni kusan uku tana jinya a asibiti, alokacinne tagane cewa duniya ba abakin komai take ba kuma idan mutum yasan farkonsa da qarshensa to baisan tsakiyarsa ba don kusan duk jinyar tata batool dasu ammie ne sukayi, tayi kuka sosai akan abubuwan data yimasu daga qarshe ta roqesu gafara kuma suka yafe mata umma kawaice bata fiye shiga harkar taba don har ga ALLAH bata son abunda zai jawo mata wani walaqancin awajenta, abunda bata sani ba kuwa shine hajia nafeesa tayi nadama sosai har cikin zuciyarta don har little da Rashida saida tanema gafara kuma takira abban batool tafad'a masa cewa duk abunda tafad'a akan little ba gaskiya bane, tayine saboda kwad'ayin d'anta shakur ya auri batool da kuma tsanarsa saboda soyayyar da mijinta ke nuna masu shida kakarsa da mahaifiyarsa kuma tayi nadamar hakan don ALLAH ya yafeta, alokacin Abba yayi nadamar d'aukar maganar hajia nafeesa da yayi sosai amma sai zuciyarsa ta nuna masa cewa koma meye ai bai kamata duk irin d'imbin soyayyar daya nunawa 'yar tasa ba ace tagujesa ta bijirewa umurninsa da zab'insa ba saboda son zuciyarta, tazab'i ta b'ata masa don tafarantawa kanta da masoyinta don haka baiga dalilin da zai koma bata wata soyayyar tasa abanza ba, kuma yayiwa ita hajia nafeesar kaca kaca had'e da cewa shi yanzu bayada case da wannan maganar don haka da ita da batool d'in da mijinta suje can suqarasa,
Wannan dalilin yasa hajia nafeesa ta qudiri riqe 'yar uwarta batool hannu biyu tare da kyautata mata tana yimata addu'ar samun daidaituwa tsakaninta da mahaifinta kota rage alhakinta data d'auka kuma ta dinga jan sumayya ajikinta sosai tana kula da ita had'e da cewa adinga kawo mata ita tana tayata reno, kusan ko yaushe cikin sayen 'yan kayayyakin yara take tana aika mata dasu tare da kayan wasa da sauran abubuwa wanda nan take Abu sumayya da gimbiyarsa suka manta da abunda tayi masu, dama ita uwa samnace da zaran kaso d'anta to shikenan ka gama da ita, duk girman laifinka zata iya mantawa dashi adalilin soyayyar daka nunawa d'anta kamar dai yanda suka manta da laifin da hajia nafeesa tayi masu suka saki jiki da ita suna kaimata baby sumayya da zuciya d'aya wanda hakan yajawo shaquwa mai tsanani tsakaninta da yarinyar shiyasa lokacin da yarinyar tarasu tana cikin wud'anda mutuwar ta jigata sosai.
Sunji damuwa matuqa akan rashin yarinyar amma daga qarshe suka fawwalawa ALLAH komai kamar yanda mahaifiyarta batool tayi, bayan watanni bakwai da rasuwarta ALLAH yasake bawa batool wani ciki, murna awajen little kam ba'a magana kai ka rantse kace shine cikinta nafarko, don farincikin daya nuna fiyema da wanda yayi ne alokacin da tasamu cikin sumayya tana tayi masa dariya, tun cikin na qarami idan yafita sai yakira fiye da sau bakwai kafin ya dawo yana tambayar ya unborn d'insa yake har ya tsufa ko gajiya bayayi, musamman da taje scanning d'inta na farko aka tabbatar mata tana d'auke da cikin 'yan biyu duka mata, ai sai kulawar ta sake lunkuwa har zuwa lokacin da zata haihu,.....
*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*ππ
[11/14, 22:52] Billy S Fari: πΆββοΈπΆπ»ββοΈ *SANNU SANNU*πΆπ»ββοΈπΆββοΈ
π _Bata hana zuwa..._π
_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπ*
_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*π
_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*π
*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*π
*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*β€οΈ
Page___95π
Da lokacin haihuwarta yayi ta matuqar shan wahala don kusan kwana tayi tana naquda a asibiti amma ba haihuwa ba mafarinta, hakan yasa likitocin suka yanke shawarar yimata operation, koda aka fad'a mata kowa yayi tsammanin zata tada hankalinta amma saita nuna babu wata damu don yanzu batada babban burin daya wuce taga an rabata da cikin dake jikinta lafiya, damuwarta d'aya shine mahaifinta, tana kuka takira hajia mama ta sanar da ita taje itama tafad'a masa, kamar dai wancan karon haka yayi yace ALLAH yasa ayi cikin nasara kuma ya sauketa lafiya, hajia mama taso ya amshi wayar yayi magana da ita kota samu natsuwa amma sanin halinsa yasa batayi hakan ba saidai tace mata tariqe wayar kada ta tsinke har taje tafad'a masa yace hakan, wasu zafafan hawayene suka zubowa batool jin muryar mahaifinta da tayi da kuma addu'ar da yayi mata ahankali tace.
"Alhamdulillah!, Ya ALLAH kaci gaba da sanyaya zuciyar mahaifina har sai yaji yayi na'am dani kafin ka amshi rayuwata."
Godiya tayiwa mahaifiyarta tare da roqonta gafara sannan tace koda ba'a fito da ita ba ALLAH ya amshi ranta taroqa mata gafarar mahaifinta kuma tafad'a masa duk tsawon shekaru shidan data d'auka ba tare dashi ba tana rayuwane da tarin d'imbin qaunarsa acikin zuciyarta, wud'annna kalaman nata sun matuqar kashewa mahaifiyarta jiki har saida suka sa tazubar da qwalla amma bata bari ta fahimci hakan ba taqarfaf mata guiwa sosai tare da yimata addu'a ALLAH yasa ashiga lafiya kuma a fito lafiya, cikin jin dad'i batool ta amsa da amin tana maijin wata irin natsuwa atattare da ita.
Cikin iyawar ALLAH ana shiga da batool ko mintuna talatin ba'ayi ba aka fiddo mata da kyawawan yaranta 'yanmata biyu masu matuqar kama da junansu wato (identical twins), both doctors da nurses d'in da suka amshi haihuwar sai ihu sukeyi cike da farinciki ganin girman da yaran ke dasu cikin qoshin lafiya, duk wanda ya kallesu da abinda zakaji yana fad'a,
"Wowww...fine baby's, wow...the baby's are so cute, woooo..so beautiful." Haka sukayita santin kyawon yaran har aka gama shiryasu.
Da aka fito dasu hajia nafeesa ce tayi saurin amsar d'aya, imaan matar Shakur da itama lokacin ke d'auke da tsohon cikinta na farin ta amshi d'aya don wannan karon Rashida bata zoba Fatima