Showing 54001 words to 57000 words out of 260204 words

Chapter 19 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt

ta kawo masa abinci yaci, hakn kuwa ba qaramin tai maka masa yayi ba don daka kallesa zaka fahimci yasamu sauyi arayuwarsa,

Wannan dalilin yanqara haifar mata da tsana mai qarfi azuciyar Yaya hawwa fiye da wacce take yimata ada, hakan yasa tasake d'aura d'amarar ganin tafidda ita gidan tako wane hali, duk ranakun da Nuraddeen yake gida Yaya hawwa batada wajen zama imba shiyarsu ba, haka zata ararrashe akan kujera tace akunna mata kallo adafa mata wannan a soya mata wancan, duk wani motsi da zasuyi akan idonta basuda wani shaqat, ga Nuraddeen mayen soyayyane yanaso akoda yaushe yadinga rab'ar jikin matarsa Amma bayada wannan damar saboda yanda tayi masu kane kane, tun Rashida Bata damuwa har taso ma jin daban saboda tun hutun sati biyun daya d'auka yagama sangartata da kuma lalatata da kalolin soyayyarsa, sun koma saidai suyi soyayyar a kitchen idan tace ta d'ago mata wani abun sai yayi kamar zai fita shi kuma anan yake samu ya lallab'a sushige suyita soyayyarsu kamar wasu munafukai, randa Yaya hawwa tagani kusan Tara masu jama'a ta tashiyi saboda masifa sai kace ba miji da mata ba, wai sun maida ita 'yar iska sun barta a d'aki ita kad'ai,

A ranar baffa yakirata yayi mata fad'a sosai akan taqyale yaran nan tadena shiga shiyarsu inbada qoqqwaran daliliba kada mutuncinta yazube, ai kuwa tayi masa tas tace bazata Dena ba in ya isa ya taso ya riqe mata qafafuwa ta hanata shiga, tsananin b'acin rai ranar daqyar yayi bacci saboda ciwon daya nemi taso masa kamar zai kashesa.

Haka aka d'aukesa akayi asibiti dashi da safe aka duddubasa had'e da yimasa allurai sannan suka dawo,

Aranar data tashi shiga shiyar duk saida tasa aka kirawo mata yaran gidan tace su ahigo suyi kallo suma su d'ebe qeyar ido, adako korarsu takeyi tana hantararsu muneera ba kunya itama tabisu sukaje suka cika d'akin tab ko masokar tsintsiya babu banda hamami babu abunda ketashi aciki, da yake lokacin har tagama girki kawai ta d'auki na baffa tanufi qofar fita riqe dashi zata kaimasa bayan tasa takunna masu kallon, tana wucewa Yaya hawwa tayi tsaki had'e da cewa "yarinya indai wannan gidanne sai nasa kinficesa da kaifin qafafuwanki."

Nuraddeen kuwa dama yana uwar d'aki kwance yana bacci sai dai kawai yajiyo yayar yara afalo da sauri yafito don ganin ko lafiya,

Tsaye yayi cak yana kallon ikon ALLAH sake da baki tare da kallon mahaifiyar tasa data ashisahire saman kujera, tsabar b'acin rai baisan sadda yayi kukan kura ba yafara fatattakar yaran daga d'akin, aguje duk suka fita in banda muneera da tayi tsaye tana kallonsa had'e da susar kanta, wani irin zazzafan mari ya d'auketa had'e da cewa.

"Uban me kikeyi anan."

Kallon yaya hawwa data miqe tsaye tana gyara zanenta tayi dafe da kunci tana kuka tace,

"Inna ce.." tare da nunata,

"Buhun uba!, yaushe nace kishigo ba yara nakira ba kika taso da wud'annan gwalmammin qafafuwa naki kika biyosu don kina sakarai, Kai kuma akan me zaka koresu suna kallonsu."

Shiru yayi hannunsa riqe da kunkuru ya sa d'ayan ya shafo kansa sannan cikin b'acin rai ya sake d'auke muneera mari yana fad'in, "maza kibar d'akinnan kafin naji maki" b'are baki tayi tare da fad'uwa zaune wajen tasa wata irin muguwar qarar da saida Yaya hawwa dake shirin komawarta tazauna akan kujerar tazabura tana fad'in.

"Ke munafukar ALLAH tashi kifita kafin nima naqara maki."

Rashida, Rashida, Rashida, Nuraddeen yashiga k'wala mata kira ransa ab'ace, dama gashi cikin b'acin rai ya wuni saboda halin da mahaifinsa ke ciki, basu jima da dawowa daga asibiti bane yasamu ya kishin gid'a sai ga wani b'acin ran mahaifiyarsa na neman qara masa....






*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___26πŸ’Ž

Rashida kuwa dake can d'akin baffa takai masa abinci bata san wainar da ake toyawa anan ba saida Aysha yarinyar Inna Bilkisu ta iskota aguje tafad'a mata, murmushi kawai tayi batare data nuna abun yadameta ko kad'an ba taci gaba da yiwa baffa yankan farcen da take yimasa don koda tashigo ta iskosa yagama cire na hannuwa yana dubarun yanda zai duqo ya cire ta qafafun shine takarb'i rezar tana qarasa masa suna d'an fira jefi jefi.

Muryar Aysha dake a tsaye har lokacin ta tsinkayo daga dogon tunanin da take akan ynayin rayuwar da take ciki dangane da matsalolin uwar mijinnata na yau da kullum tana fad'in, "Aunty fa Yaya nakiranki."
Adai dai lokacinne tariqe farcen qarshe da zata qarasa cirewa baffa akaifar, saida tacire sannan ta d'ago kai tana kallonta had'e da cewa.
"Jiki ganinan tafe kinji." Kallonta baffayayi lokacin tana mik'ewa daga zaunen da take bayan ta d'auki k'yallen data aza qasan qafafuwan nasa qumbar da take yankewa na zuba akai ta kakkab'ik kesa awaje tadawo ta lunkesa ta mayar a inda yasa tad'aukosa d'azu. "A gaida Rashida ALLAH yayi maki albarka, sai nakeji gaba d'aya jikina yayimun sayau tamkar an d'auke mun wani abu akai."
Baffa yafad'a yana jujjuya yatsun hannuwansa, dariya tayi had'e da cewa. "Kasan dattice idan ta tararwa mutum shiyasa wanda suka saba yankawa idan tataru basajin dad'in zama da ita ajiki, baffa bara naje nadawo nazuba maka abincinka kaci sai kasha magani."
Yana kallon qafafuwansa yanda faracen sukayi masa tas saboda shi mutumne mai tsananin zafta da son gyara jiki yace. "To jeki, ALLAH yasa kigama lafiya, yakawo maki rabo Mai albarka."
Akunyace tabar d'akin batare data amsaba tana murmushi tanufi qofar shiga part d'insu, tana kawowa Inna ruqayya nakawowa itama saboda qarar 'yarta data jiyo, qoqarin kaucewa Rashida tayi ta bata hanya tawuce amma saboda rashin imani irin na Inna ruqayya tasa kafad'a da qarfi ta mangajeta tafad'a ajikin ginin shiyar tasu kanta kuma yabugi gambun qofar tayi baya baya tafad'awa sauran buloluwan da akayi aikin sashensu dake ajiye gefen jikin ginin.
Cike da azaba zafin buguwar da tayi tasaki wata irin qarar da saida Nuraddeen dake falo zaune ya dafe kansa zabura, da sauri yafito sukaci karo da Inna ruqayya da babunko d'igon imani da tausyi atattare da ita tabaro Rashida can kwance ta tahowarta tana masifar waya tab'a mata 'ya, ko kallonta beyi ba shima ya wucikke warsa tare da tsayawa bakin qofar ya leqo don ganin ta Ina yaji muryar qarar Rashida, daidai lokacinne yaga Inna Bilkisu tarugo aguje tare da 'yarta fadeela tana fad'in. "Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun Kai ruqayya wannan wane irin rashin imanine haka ki bangaje yarinyar mutane tafad'i kuma duk da kinji qararta bazaki tsaya kiduba halin da take ciki ba."
Har ta aza qafarta tashiga d'akin tajuyo cike da maseefa tadawo don dama jiraye take da inna Bilkisu, bangaje nura tayi dake tsaye bakin qofar kamar an dasa yana kallon ikon ALLAH, gaba d'aya saboda yanda gaskiya tayi masa yawa kasa cewa komai yayi sai bin Inna Bilkisu data tallabota tana d'an bubbuga gefen uncinta had'e da kiran sunanta yakeyi.
"To munafuka algunguma, sarkin ashibanci da son yabo, fad'i ba atambayeki ba tsabar kicifi da iyayi ina ruwanki, meya shafeki no aciki ko dake akeyine da zakizo kisamun baki, kinsan me tayi manine da zakizo kisamun baki, Ina yanzu kika jiyo qarar muneera acikin d'akin nan Amma tsabar mugunta Ina kallonki ko ajikinki tunda ba 'yarki bace, sai yanzu don antab'a bare Zaki taso mana da wani migun bakinki kisa mani baki, to wallhi ahir d'inki Bilki da shiga sabgata ko inyi maki rashin mutunci, ni uban waye nasakawa baki da aka tab'amun tawa 'yar." Inna ruqayyace tafad'i haka tare da fitowa tayi tsaye akansu batare data damu da ganin halin da Rashida keciki ba. "Fadeela jeki d'ebo mun ruwa ki kawo inaga yarinyarnan suma tayi."
Da sauri fadeela tabar wajen taje ta d'ebo ruwan takawo Inna Bilkisu ta karb'a ta yayyafawa Rashida. "Mtssssss.. ALLAH ma yasa tamutu idan taso ba abunda yashamun kai iyayenta keda asara bani ba." 'dago kai Inna Bilkisu tayi had'e da kallonta hawaye cike da idanuwanta, kasa magana tayi ta maido kanta had'e da sake zuba ruwa a hannunta tashafawa Rashida, wata irin doguwar ajiyar zuciya Rashida tayi tare da dafe goshinta dake mata rad'ad'i tana fad'in. "Wash.."
"Sannu Rashida." Inna Bilkisu tafad'a tana kallon inda ta dafe goshin nata ya kumburo, sai alokacin nurah ya qaraso wajen idanuwansa sun kad'a sunyi jawur kamar an watsa masa barkono aciki, wani irin zugi da rad'ad'i yakeji kallon halin da matarsa keciki amma yakasa tab'uka komai saboda jin nauyin Inna Bilkisu dake wajen tana kula da ita, had'a idanuwa yayi da ita ta sakar masa murmushin daya tabbata cikin qarfin hali tayisa don takwantar masa da hankali,
"Nura d'auki matarka kushiga ciki, kaga goshinnan nata yabugu kad'an lullunda matashi koya saki, ALLAH yasawaqe kuma yaqara maku hak'uri."

Ya tsinkayo muryar Inna Bilkisu nafad'a cike da damuwa, duqawa yayi da niyar riqota, Inna ruqayya tariqo wuyan rigarsa had'e da cewa. "Ai wallahi baaka isa ba, mutum befi mutum ba balle ka dakarmun 'ya na qyaleka, wuce muje naga ubanme kayiwa 'yar tawa take wancan reren kukan." Ta jasa suka nufi cikin sashensa yana biye da ita, wani irin tuquqi yakeji aransa da badon matar qanen mahaifinsa bace ko wace yau sai ya koya mata hankali, qoqarin miqewa tsaye Rashida tayi hawaye na zubo mata daga cikin idanuwanta Inna ruqayya tayi saurin d'agata had'e da riqota sosai tanufi cikin shiyar tata. "A'a Inna Bilki bana son ganin abunda zai faru tunda tsakninsa ne da 'yan uwansa, kawai ki kaini shiyarki" Rashida tafad'a tana sake goge hawayen dake faman kaida kawo saman fuskarta akaro na ba adadi,
Kiyi hak'uri Rashida in sha ALLAH komai zai wuce." Sashenta tanufa da ita suna kai bakin dangaramar da zaka taka su ahiga cikin d'akin jiri ya sake d'ibarta da kad'an tafad'i, da sauri fadeela tariqota ita da Inna Bilkisu tana dafe da kanta sukaqarasa shiga da ita.

Acan cikin d'akin Rashida kuwa yaya hawwa na can hakince saman kujera tana kallonta, ita kuma muneera na zaune sai faman reren kuka takeyi tana susar kai sai kace wata sabuwar amaryar da akayiwa auren dole, duk abunda akeyi tana jiyosu daga tsakar gidan amma tayi kamar batasan anayi ba, bini bini take juyowa tana kallon muneera dake kuka can kuma sai tayi shiru ta qurawa tv ido tana susar kai tace. "Au munafuka dama kukan na qaryane! Wato anga abunda sai gidan masu kud'i ake gani d'an ba'a saba ba kin baza idanuwa sai kallo kike yi, ja'ira kawai." Ta kaimata dunguri a qeyar kai, sake fashewa da kuka tayi tana cije gefen d'an kwalinta had'e da sosa qeyar kan nata data daka, Inna ruqayya ce tashigo d'akin har lokacin tana riqe da kwalar rigar Nuraddeen tana fad'in. "Wato kasan matar taka bata cikin d'akin shine ka kamamun 'ya ka zalunta to wlh bazan yarda ba, ai kana ganinta ka zame kaje ka auro wata shine yanzu kake nema ka cuceta don baka samu yanda kake soba, wuce muje naga abunda kayimata" muneera naganinta ta taso tanufo inda take tana sake tab'e baki. "Buhun uba me zan gani haka ruqayya, d'an nawa kika shaqowa wuya haka sai kace wanda yayi sata! Uban me yayi maki."
Cikasa Inna ruqayya tayi kafin tariqo mueera tana fad'in. "Aiho dama kina cikin d'akin Yaya hawwa?, Kukan muneera najiyo nazata shikad'aine aciki shine na tasosa agaba yazo ya fad'amun abunda yayi mata gabanta har take wannan reren kukan saboda nasan duk abunda yasata kuka to ba kad'an bane"

Tafa hannuwa Yaya hawwa tashigayi tana sallalami had'e da gyara d'aurin zanenta kafin tace,

"Ke ruqayya sharri zakiyiwa yaron nawa don kinga bayyi magana ba?, shi dake da matan mezaiyi da 'yarki yarinya kamar an tsoma kaza acikin ruwan zafi anfiddata, tsigalalliyar yarinya munafuka kawai da ita, mai yagaggen baki zakuyi masa sharri, to maza kufita kafinna karya mata wud'annan gwalmad'ad'd'in qafafuwan nata."
"Dakata yaya hawwa gaskiya nagaji da wannan cin kashin naki, aci zalin yarinya agabanki bazakiyi magana ba kuma sai kiqara mata da kushe mata halitta, gaskiya nagaji kidena don nima ina son abuta a haka, shikenan daga zuwa tambayar meyayi mata sai kidinga cab'a mani magana..." Bata rufe baki ba ta Nuraddeen yafito a fusace riqe da belt a hannunsa dama tuni tsananin b'acin rai yasa ya shige uwar d'aki yayi zaune bakin gado yana tunanin ko meyi zai yimata ya rage rad'ad'in abunda tayiwa habibty d'insa, babban takaici ma wai shi Inna ruqayya ke zargi akan muneera ko mezaiyi da ita, meye ma zai tsinta ajikinta da zatayi masa wannan sharrin, yana zuwa ya finciko muneera daga jikinta idanuwansa jajir ya jefar da ita a qasa had'e da nuna Inna ruqayya yace. "So kikeyi nafad'a maki abunda nayi mata ko, to bari kigani na nuna maki, bari kiga kome nayi mata yanzun nan."

Jibgar muneera yafarayi da belt d'in yana watsa mata tako ina tana ihu, sheqeqe Yaya hawwa takalli Inna ruqayya data turo idanuwa waje tana kallonsa tace "yawwa qarawa shegiyar, yimata lilis munafukar yarinya kawai, daga mari sai uwarki tabisa da mugun sharri, yita jibgarta sai tagane shayi ruwane?"

Tafad'a tare da rab'awa ta gefensu tayi tafiyarta, qoqarin riqesa Inna ruqayya ta shigayi tana tsigarsa amma da yake zuciyarsa tariga tarufe a fusace ya d'ago kai yana cewa. "Wlh kibar ganin ke matar qanen mahaifinace duk kika matso wajennan saina had'a dake."
Ganin yanda fuskarsa ta sauya yasa tayi gum da bakinta tayi waje tana haragagon neman taimako, duka kam ranar muneera tashashi tun tana ihu har takasa shi kuma yace bazai dena dukan taba har sai lokacin data bar d'akin da qafafuwanta yanda gobe koda wasa akace tashigo shiyarsa bazata shigoba, Inna ruqayya kuwa tayi ihun neman taimakon har tagaji babu wanda yazo ai kuwa tana ta zundumawa mutanen gida zagi wai duk munafukaine sunaji za'a kashe mata 'ya kowa ya qyale,

Inna Bilkisu kuwa ji tayi kamar ta taka tsabar farinciki don koda baiyi komai akai ba ta d'au alwashi akan sai tayi mashi fad'a daya tashi tsaye ya qwatowa matarsa 'yancinta a gidan matuqar shi ba lusarin namiji bane, sai gashi da kanshi yayima kansa fad'a.
Yaya hawwa kuwa dama sashenta tawuce tashige d'aki had'e da haye gadonta ta soma bacci batare data sakebi ta kansu ba, su baffa Ali da baffa Usman su kuma basa gida balle su kawo mata d'auki ,

Sai da jikin muneera yayi tib'is tukuna tafara qoqarin k'watar kanta daga hannunsa ganin babu sarki sai Allah, da jan gindi tafito shiyar Inna ruqayya na tsaye bakin qofar takasa komawa sai faman zunduma masa zagi takeyi, da sauri ta riqota had'e da ida jawota tafito sukayi shiyarsu tana kuka yace.

"Wannan shine abunda nayi mata, kuma kad'an tagani, idan nakoma ganin qafarta cikin shiyata saina maida ita gurguwar qarfi da yaji." Sannan ya juya yakoma ciki,

Toilet ya fad'a had'e da d'ibar ruwa acikin durom d'in dake ciki yafara sakarwa kansa yana sakin wata irin ajiyar zuciya. Yajima aciki kafin yafito ya hau gyaran falon had'e da sharesa tass, feffesa room freshener yayi soboda tsamin da yaji d'akin nayi sannan yanemi kujera mai zaman mutum uku ya kwanta rigingine kansa na kallon silin zuciyarsa cike da matsananciyar damuwa

Acan shiyar Inna Bilkisu kuwa saman gadonta suka kwantar da Rashida, hannuwanta da idanuwanta tashiga duddubawa tana son gaskata abunda zuciyarta ke rayamata akanta tun kwanaki biyu da suka wuce saboda yanda ta canza, murmushi tayi had'e da cewa,
"Alhamdulillah ALLAH kaine abun godiya." har lokacin takasa Dena murmushin da takeyi, kallonta fadeela tayi had'e da cewa, "Inna menene?."

Bata tanka taba saidai kallon Rashidar data koma yi tana qoqarin rufe idanuwanta saboda baccin da take ji, baccinta mai isarta tayi kafin nan tafarko tana jin wata irin matsananciyar yunwa dama d'azun data gama abinci bata samu taci ba saboda tare sukeci dashi shikuma alokacin bacci yakeyi,

Kasancewar koda ta tashi bakowa ad'akin yasa tasauko saman gadon had'e da fitowa bakin qofar d'akin ta saki wata uwar hamma dake nuna ba qaramar yunwa take jiba.
"A'a Rashida har kin tashi?." Inna Bilkisu dake sharar cikin rumfar tasu tafad'a tare da d'agowa tana kallonta.

"Eh inna barka da marece, shara kikeyi?."

"Eh wallahi wajenne ya d'anyi datti ga baffanku yana kan hanyar dawowa ke sanshi baya son datti ko kad'an, ya qarfin jikin naki?"

"Alhamdulillah da sauqi Inna bari na riqa maki."

"A'a ki barshi ai nakusa qarasawa, maza jeki tun d'azu mijinki na ciki nasan ran nan nasa a cunkushe uake yanzu, kuyita haquri har ALLAH yakawo qarshen wannan al-amarin kinji ko."

Duqar da kanta qasa tayi tana wasa da 'yan yatsun hannunta tana murmushi sannan tabar wajen, har takusa shigewa Inna Bilkisu tace,

"Au Rashida." Juyowa tayi tana kallonta taci gaba da cewa "dama nace ki kula da kanki saboda yanzu bake.." Bata qarasa ba saboda hango Inna ruqayya da tayi nafitowa daga cikin d'akinta sai tayi shiru had'e da cewa

"Jeki rashida maya magana dake anjima"

"Mtssss...munafucci kunun kanwa!."

Inna ruqayya tafad'a tana jefo wata tasar Inna Bilkisun data gani cikin rumfarta.

Batace mata qanzil ba taci gaba da shararta ita kuma tawuce shiyarta batare data fahimci kome Inna Bilkisun ke nufi ba.










*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___27πŸ’Ž

Tana shiga Kai tsaye kitchen tashiga ta d'ebo abincin a plate, tun kafin taqaraso cikin d'akin tasomaci saboda azabar yunwar da takeji, kwance ta iskosa idanuwansa arufe amma babu alamun bacci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login