Showing 102001 words to 105000 words out of 260204 words
Chapter 35 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt
so yakeyi ya shiga jikin bokan amma ji yake Sam bazai iya rayuwa ajikin saba, hakan yasa ya quduri zaman jiran dakon biladama nafarko da zaya fara takowa cikin jejin zuwa inda suke don ya d'auki fansa tahanyar shiga jikinsa..
*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*ππ
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πΆββοΈπΆπ»ββοΈ *SANNU SANNU*πΆπ»ββοΈπΆββοΈ
π _Bata hana zuwa..._π
_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπ*
_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*π
_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*π
*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*π
*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*β€οΈ
Page___48π
Jiniyar motocin 'yan sanda kawai ketashi aguje saman titi kusan mota uku, gaba d'aya cike suke da zaratan 'yan sanda majiya qarfin da babu alamar tausayi atattare dasu ko misk'ala zarratin, yanayin fuskokinsu kad'ai idan ka kalla zai tabbatar maka da ashirye suke dasu fuskanci kowane irin qalubale ne indai akan aikin da suka fitoyine, motar su inspector najida itace agaba, sai wacce aka d'auko Yaya hawwa tare da wasu 'yan sanda su biyar tana biye dasu a tsakiya sannan ta ukun data biyo bayansu wacce ke d'auke dasu blessing da wasu 'yan sanda su uku abaya, tafe suke yaya hawwa najin wani irin tashin hankali na ziyartota saboda tunawa da yanda takwashe da boka bargaji a wancan karon, Babu babban tashin hankalinta irin kar suje bokan yaqi bayyana tunda b'acewa yakeyi bala'i yaganta a hannun 'yan sandan nan data tabbatar basuda sauran Imani azuciyarsu, idan ko har haka tafaru ta tabbata a wannan karon wannan arniyar mai qirar samudawa kasheta zatayi, tana wannan tunaninne taji ankai mata wani mugun naushi abaki, kufron Jamil ne da ahalin yanzu babu d'igon tausayinta ko kad'an a ransa yana kallonta cike da tsana, Wanda yayi mata hakanne dama don jin motar su inspector najida dake gabansu data tsaya had'e da cewa.
"You stupid maza kifita anzo wajen."
Juyawa tayi cike da fargaba tana kallon bakin titin da suka tsaya tare da waigawa gefe gefe tana kallon cikin dajin, jitayi gabanta yaqire yafad'i da sauri tadafe qirji tana fad'in. "Wayyo ni ALLAH."
Cike da hasala wata 'yar sanda dake cikin motar tare da ita ta izo qeyarta suka fito tana fad'in
"Idiot, bakiyi wayyo ba, yanzune zaki fara, tana fitowa sauran 'yan sandan suma suka firfito bayan motocin nasu sun tsaya suka zagayeta hannunta na d'aure da ankwa, cikin jarumta inspector najida tafara azo qafarta wajen motar kafin ta ida fitowa gaba d'aya fuskarnan tata a d'aure, d'aga kai tayi tana qarewa dajin kallo tun daga farkonsa har zuwa qarshe sannan tajuyo ta maido kallonta ga Yaya hawwa da kanta ke nad'e da bandeji, hakama hannunta and'aure matashi tare da sagalo bandejen da aka d'auresa ga wuyanta, sai qafarta itama duk an nad'e mata yatun da bandeji ga fuskarta da blessing ta bubbuge mata itama duk ta kumbure, gaba d'aya halittarta ta canza kai bazakace Yaya hawwarnan bace mai shegiyar isa da rashin mutunci, ajiyar zuciya tayi sannan tafara takowa zuwa inda suke tsaitsaye har lokacin idanuwanta nakan Yaya hawwa, tana isa da sauri duk suka qame had'e da buga qafa suka sara mata, sunansu tashiga kira d'aya bayan d'aya suna amsawa da qarfi yayinda Yaya hawwa ta sinne kai qasa tana Dana sanin wannan halin data jefa kanta, musamman yanda taga 'yan sanda zagaye da ita, da qarfi taji inspector najida tace.
"Kowa ya shirya acikinku?"
"Yes sir." Suka fad'a atare.
"Duk kankanku a shirye kuke daku bada rayukanku ga yiwa qasarku aiki?"
"Yes sir." Suka sake fad'a atare.
"Ok ina buqatar kowanenku yacire tsoro ya fuskanci wannan aiki da zamuyi mai suna operation ss, ba gudu baja da baya, duk rintsi duk wuya kada wanda yagudu har sai mun kama wannan azzalumin da duk wani dake tare dashi a wannan jejin kunaji ko?"
"Yes sir."
"Kun shirya?."
"Yes sir." Suka sake fad'a atare cikin d'aga murya har lokacin suna a qaqqame, kallonta tayi had'e da yimasu umurni da hannu data shiga gaba su bita abaya. Nan take blessing kamar jira takeyi ta tasa qeyar Yaya hawwa zuwa cikin jejen, tafe yaya hawwa take tana d'ingishi suna biye da ita abaya, Saida sukayi tafiya mai nisa sannan suka soma shiga ainahin cikin dajin da boka bargaji yake, wata irin qara suka jiyo da kururuwar da tasa nan take Yaya hawwa ta d'iba da nakare wani gefen zata koma baya, taqa biyu blessing tayi ta damqota tare da buga mata qasan kututun bindigar dake hannunta tafad'i qasa, rufeta sukayi da duka, da sauri inspector najida ta dakatar dasu.
"Ku kqyaleta, kada wanda ya sake dukanta nace, dolene duk abunda zatayi a qyaleta saboda musamu takaimu wajen idan ba haka ba tabbas zatayi yunqurin aikata abunda zai b'ata mana aiki, don haka ku d'agota muje" tana gama fad'ar haka tajuya suka d'ago Yaya hawwa suka sake tasa qeyarta, ganin zata iya sake barazanar guduwa yasa blessing da wasu 'yan sandan suka shiga gaba, ita kuma Yaya hawwa tana bayansu, sukuma sauran 'yan sandan wasu nagefenta na dama dana hagu, wasu kuma bayanta ansata tsakiya tako ina, haka sukaci gaba da kutsawa cikin dajin cikin dakewa duk da irin kalolin sautin da sukeji masu tsananin firgitarwa,
Suna kaiwa cikin dajin daidai inda rumfar boka bargaji take wata irin guguwa maicike da wata muguwar qara mara dad'i ya taso had'e da dumfarosu, da sauri inspector najida taduqe tana fad'in.
"Kuyi qasa." kafin tarufe baki gaba d'aya sun duqe kowane nakaranta abun daya sani a bakinsa, yaya hawwa kad'aice tarage a tsaye sai blessing data rufe idanuwanta tana watsi da hannuwanta tana fad'in
"In Jesus name." 'yan uwanta Christian dake duqe suka amsa mata da "emeeen."
"our father, who is in heaven, olobidani danki danka,..." Tafara karanto addu'arsu ta christoci tana qara watsa hannuwa da jijjiga jiki, su kuma suna amsa mata.
Kimanin kusan minti uku guguwar tayi acikinsu tana yawo kafin can suji ankece da wata irin muguwar dariya ta shaqiyanci sannan iskan ya lafa.
A hankali suka fara tasowa suna kallon yanda iskan ke nad'id'iya yana komawa inda yafito, suna juyowa ga mamakinsu sukaga wayam ba Yaya hawwa ba mafarinta, hakan yasa inspector najida tabasu umurnin fitar da bindigogin hannunsu tare da tunkarar inda iskan yafito cikin taku mai cike da sand'a har suka isa wajen, nan take tafara rarrabasu da hannu suka zagaye bukkar da suka hango a tsakiyar wurin, ita tafara tunkarar bukkar tafarayi sukuma suka taqe bindigogin dake hannunsu suna jiran kota kwana, tana isa bakin bukkar wata wuta da basusan ta inda tafitoba tafara cin bukkar daga sama had'e da zagayeta, da sauri inspector najida tajawo baya suna kallon ikon ALLAH, yayin da sukaga boka dake can ciki kwanci jikinsa duk yayi borarrai yafito aguje yana ihu, tashin hankalin dake shimfid'e a fuskarsa yasake bayyana ne a lokacin da yaga yanda 'yansanda sukayiwa wajen qawanya, a tsorace ya tattaro d'an sauran qarfin daya rage masaya arta dana kare 'yan sanda suka tarosa, ya juya ta d'aya b'angaren nanma suka sake tarosa suna nufo inda yake, waige waige ya shigayi yana jujjuyawa ko zai samu hanyar guduwa amma hakan tacutara sanadiyar yanda duk suka zagayesa, juyawa yayi zai koma cikin rumfar dake ci da wuta don ya qwammacewa mutuwarsa akan yashiga hannun hukuma su walaqantasa,
"Kana qara taku d'aya zan harbeka." Inspector najida tafad'a tana matsowa inda yake.
Batare daya saurareta ba yaci gaba da tafiyarsa hakan yasa ta sakar masa albashori aqafa yasaki wata irin qara had'e da durqushewa wajen saboda zafin harbin daya ratsa jikin,
"daga hannuwanka sama."
Zafin rad'ad'in da yakeji yasa baisan lokacin daya d'ora hannayensa a bayan qeyar kansaba, nan take taba blessing umurnin tasa masa ankwa tare da mayarda bindigarta a bayan wandonta, qafa blessing tasa ta shurasa tabaya ya fad'a kwance a kife sannan tajawo hannuwansa tabaya zata saka masa ankwa tana fad'in "shegiya wari takeyi." ta d'ad'a masa duka abaya, cikin zafin rai boka bargaji ya juyo da qarfi afusace tare da riqo wuyan blessing data duqo da niyar samasa ankwa daga kwancen da yake, gaba d'aya 'yan sandan sukayo kansa suka nunasa da bindiga suna fad'in ya saketa.
Blessing kuwa da tsabar warin jikinsa tasa takasa attaka wani abun hakan yasa yayi nasarar shaqe mata wuya da kyau har tana fidda wani kakari,
"Kuja baya, kuja baya nace ko in kasheta." Yafad'a yana qara cusata cikin jikinsa, Wanda hakan d'ai ya isa yasa tafita hayyacinta. Ja da baya 'yan sandan suka farayi yayinda inspector najida taciro bindigarta a fusace kafin ya ankara ta sakar masa ita ga hannu yasaki wata irin qara had'e da sakinta yana riqe hannu, da sauri sukazo sukazo suka jayeta tana fad'in
"Yeh Jesus." tana fidda lumfashi daqyar.
Nan fa 'yan sandan suka rufar masa da duka tako ina, kan kace me sunyi masa jina jina ko motsi bayayi, take suka saka masa ankwa had'e da tallabarsas suka tafi, yayinda inspector najida da sauran 'yan sandan suka sake bazama cikin jejen wajen nemo inda Yaya hawwa tashige don atunaninsu guduwa tayi, abunda basu sani ba tuni baqin aljani yayi nasarar shiga jikinta had'e da birkita mata qwaqwalwa, duk iya dube dubensu sunyi acikin jejen amma basu gane taba sai akan hanyarsu ta fitowa sukaci karo da ita tana hizge hizgen hakukuwa tare sabbatun da basuda basuda Kai balle gindi, tana ganinsu ta d'iba dana kare suma suka rufamata baya suna qoqarin kamota.
β’β’β’ β’β’β’ β’β’β’
Al-amirin little Nuraddeen kuwa abun alhamdulillah don ana ganin haske sosai, gaba d'aya kuzarinsa da lafiyarsa sunfara dawowa, jikinsa yayi kyau sosai daidai irin na jarirai sa'annin sa, bayada wani naqasu ko wani ciwo da yayi saura atattare dashi, yana samun lafiya yanda yakamata saboda yanda iyayen nasa uku suka jajirce wajen kula dashi, soyayya kuwa tsakanin Fatima da Dr nura sai k'arasa wanda yafi nuna masa ita, haka Rashida wani irin so takeyi masa marar misaltuwa wanda takan b'oyene kawai saboda nuna kara ga mutanen da sukayi mata halacci marar misaltuwa, kulawarsu kad'ai agareta da yaronta ya isa yasa ta iya sadaukar da duk wani farinciki nata agaresu,
Zaune suke a falo su uku ita da fatima sai Dr. nura dake can gefe kwance saman 3sitter riqe da little Nuraddeen yana yimasa wasa shikuma yana b'angalar dariya,
Kalaba ce Rashida keyiwa Fatima akai wacce kallo d'aya zaka yiwa kalabar kasan wadda keyinta bata gwane ba,
"Wlh aunty ko kad'an kalabar nan batayi kyau ba, don ALLAH kibari na tsefeta uncle ya kaiki inda aka sabayi maki." Hannu fatima tasa tashafo kalabar da gaba d'aya tsorayen sukayo mata gaban kai suna yimata reto had'e da kwashewa da dariya tace.
"Kai ka kai! Maman baby meye haka kika yimani tsoraye agaba suna yimani reto, nashiga uku ni inno, niba yarinya ba da tsoraye agaba." Juyowa dr.nura yayi had'e dayin dariya yace.
"Ai kuwa kinga sunyi matuqar yimaki kyau dole nabawa maman baby tukuici." Fillon kujerar dake gefenta tajawo ta cilla masa tana harararsa yayi saurin cab'ewa yana dariya, itama Rashidar dariya tayi tana mai yaba kyawon irin rayuwar da suka tsarawa kansu acikin gidan ta farinciki duk da kuwa matsalar da suke ciki hakan bai hanasu yin rayuwarsu cike da burgewa ba, tunowa tayi da habibynta da ace suna tare yanzu ta tabbatata itama haka zasu gudanar da tasu rayuwar da d'ansu cikin so da qaunar juna, muryar Fatima tajiyo tana fad'in "wato dariya ma zaku samun ko!, to ALLAH bazan tsefa kalabar nan ba, a haka zan zauna da ita sai kuci gaba dayin dariyar har sai ta isheku."
"A'a'ah aunty kiyi haquri mana, ai tun farko saaida nafad'a maki ban iya kalba ba kikace kina so a haka, Bari intsefe maki kinga sai uncle yadena yimaki dariya, qyalesa tukuicinma bana so nayafe masa." Rashida tafad'a tan gumtse dariyar data zo mata had'e da qoqarin fara tsefe kan, kuka little Nuraddeen yafarayi alamun yagaji da wasar Dr nura yataso tare da miqama Rashida shi yana fad'in "karb'arshi kibashi abincinsa, ni bari natsefe mata tunda bata so."
Karb'ar little Nuraddeen tayi tawuce d'akinta, shi kuma ya zauna tare da d'aukar tsinken data ajiye yana fad'in "yawwa matar Bari na tsefe maki ko."
"Bana so, bari kawai nasa ribon nakamesa ahaka, zuwa jibi sai ka kimu nida ita inda akayomun ayo mana ko kuwa?"
"Eh, haka ne?."
"Duk yanda kika ce matar."
Murmushi tayi tare da jawo hular dake gefenta ta saka, sannan takira dattijuwar dake yimata aiki tace ta gyara wajen, acan gefe suka koma suna tataunawa akan maganar mayarda Rashida da zasuyi kamar yanda sukayi mata alqawari tunda yaronta ya soma samun sauqi sai gata tafito goye dashi bayan ta tabbatar data bashi nono ya sha ya qoshi, tare suka d'ago kai had'e da cewa.
"Har yagama sha?."
"Eh, yamayi bacci, shiyasa nagoyasa" tafad'a kanta na qasa tana wasa da 'yan yatsun hannunta,
"to qaraso mana." suka sake fad'a kusan atare, kallon juna sukayi shida ita had'e dayin dariya sannan Rashida taqaraso itama tasamu waje ta zauna,
"Dama akan maganar komawata gidane uncle, shine nace bari inyi maka tuni." tafad'a har lokacin knta na kallon qasa, murmushi Nuraddeen yayi don yasan dama haquri kawai takeyi amma tuni ta damu takoma wajen iyayenta.
"Rashida kenan! Zancen da mukeyi kenan yanzu, dama Ina tunin gobe idan naje zan sake komawa naduba ko an sallamosu, inyaso wani sati idan zan koma sai muje tare gaba d'aya ko?, Inaga kamar hakn yayi tunda kinga bki shirya komai ba balle ince goben muwuce tare, inafatar hakan yayi?"
"Eh uncle" tafad'a cike da farinciki, Fatima tayi dariya tana fad'in
"Amma maman baby acikin labarin da kika bamu, babu inda kika kawo mana matsalar mijinki wato mahaifin little, Kuma ga dukkan alamu akoda yaushe zuciyarki bata rasa tunaninsa, me zai hana kibada address d'insa sweety yaje ya snar masa koda ba'a isko iyayen naki ba qilan shi zaisan asibitin da aka kwantar dasu kuma shima hakan zai sama masa natsuwa aransa idan yaji inda kike. Ko kindena sonsa ne saboda abunda mahaifiyarsa tayi maki."
Ajiyar zuciya Rashida tayi kafin tace..
"Ko kad'an aunty, asali ma kullum da tunaninsa nake kwana kuma dashi nake tashi, daidai da rana d'aya ban tab'a jin natsanesa araina ba saima d'inbin qaunarsa dake qara lunkuwa azuciyata, kawai inajin tsorone kada asanar dashi mahaifiyarsa tasamu labari ta sake aikata abunda yafi haka agareni da kuma jaririna, nafison idan munje nakoma hannun iyayena asanar dashi, nasan in sha ALLAH idan yaji zasu san matakin daya kamata su d'auka akai kafin wani abun yasake faruwa, wannan dalilin ne yasa banyi tunanin aje asanar dashi ba ko kad'an duk da gangar jikina da kuma rouhina na fad'amun baya cikin kwanciyar hankali da kuma qoshin lafiya."
Shiru sukayi suna nazarin kalmanta, tabbas abun duba wane awani b'angaren amma kuma yakamata tayi tunani akan halin da yake ciki, ace matarka da tsohon ciki ta b'ata kuma bakasan inda take ba kimanin watanni uku kenan yanzu cikin na hud'u, wud'anda sune suka kasance watannin haihuwar little Nuraddeen...
*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*ππ
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πΆββοΈπΆπ»ββοΈ *SANNU SANNU*πΆπ»ββοΈπΆββοΈ
π _Bata hana zuwa..._π
_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπ*
_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*π
_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*π
*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*π
*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*β€οΈ
Page___49π
Daqyar 'yan sandan suka samu sa'ar kamo Yaya hawwa, wacce kallo d'aya zakayi mata kafahimci zallar haukan daya sameta tuburan, Saida sukayi da gaske sukayi nasarar sanyata cikin bayan mota tanayi tanaa buge buge da fisgar kayan dake jikinta, wata uwar cacuma takaiwa boka bargaji dake zube qasan motar batare daya san inda kanshi yake ba tana fad'in.
"Kaine, kaine boka bargaji, kaine?, Mun halaka, Munb'ace, mun halaka, Munb'ace......" Wannan kalmar kad'ai take maimaitawa abakinta tanaci gaba da fizgar kayan jikinta, sudai 'yan sanda Imani da tsoron ALLAH rufesu yayi suka zuba mata idanuwa suna kallo, gaba d'aya takusa yaga kayan jikinta saboda yanda take fizgarsu, gani sunkayi tafashe da wata irin muguwar dariya tana ja da baya cikin motar had'e da dukan qirjinta kan suyi yunqurin riqeta aguje ta dirqo daga cikin motar tafad'o k'asa, kasancewar motarsu ce a tsakiya yasa tana fad'owa ta bayansu ta taka burki da qarfi 'yan sandan suka dirqo daga cikin bayan kantar suka rirriqeta tana sakin wata qara Mai tsananin firgitarwa wacce ko ba'a fad'a maka ba kasan bayin kanta bane, kusan su takwas suka taru saman kanta suna qoqarin maida ita cikin bayan motar, inta d'aki wannan ta daki wancan ta yakushi wancan har aka kwashe kusan mintuna ashirin suna abu guda kafin su samu da qarfin tsiya suturata ciki bayan sunyi mata d'an banzan duka sun jijji mata, Amma duk da haka bata saduda ba abunka ga marar hankali, daqyar da sud'in goshi suka samu suka isa da ita policetation suka jefata cell suka rufe, nan ma buge buge tadingayi tanayin wata qara mai tsananin sauti irin na halittu kala kala wanda hakan yamatuqar razana 'yan sandan da inspector najida, shi kuwa boka asibiti suka nufa dashi saboda acire harsashen dake hannunsa da qafarsa sannan suka dawo policetation d'in bayan anbaro 'yan sanda uku da zasu tsaresa acan asibitin.
Kasancewar koda sunka dawo daga asibitin har ankira sallar azahar yasa musulman cikinsu sukayi harmar zuwa wajen sallah, yayinda da akabar su blessing da sauran Christians d'in dake cikinsu su kula da Yaya hawwa da gaba d'aya hargaginta ya karad'e Police station d'in.
Bayan sun dawo inspector najida ta d'aga wayarta takirawo lambar baffa dake can kwance tun jiya da suka dawo yarimawa zazzab'i yarufesa, Nuraddeen na zaune agefensa sai kuma baffa Usman dake zaune ad'ayan gefen nasa ya rafka wani uban tagumi, da alama yana cikin damuwar ganin halin da d'an uwan nasa ke ciki, har wayar tayi ringing tagama babu wanda ya lura acikinsu shida Nuraddeen don kowanensu yashiga duniyar tunani saida sukaga baffa na qoqarin tashi don wayar nacan gefe ansata charji, da sauri Nuraddeen yariqasa ya tashi zaune daidai yana tambayarsa me yakeso, nuna masa wayarsa dake fidda sauti kad'an tana haske yayi ya ciro masa had'e da d'aga kiran dake qoqarin sake yankewa akaro na ukku, Saida ya kalli sunan