Showing 69001 words to 72000 words out of 260204 words

Chapter 24 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt

ba zama, tun d'azu ka kasa zaune ka kasa tsaye sai faman zagayar d'aki kakeyi, halan tsoron zaunawa kakeyi gudun kada asake damqeka waje d'aya, koda yake gaskiya ka zaunu dole ka guji abunda zai sakesa ka zauna inba dole ba."
Wani irin dimmm...baffa yaji har jiri na neman d'ibarsa jin kalaman dake fitowa daga bakin d'an uwan nasa, badon yasan lokacin da mahaifiyarsu ta haifi baffa Ali ba da tabbas yace daqyar idan shi jinin sane, saboda gaba d'aya halayyarsa kwata kwata batada kyawo, Babu hankali da lissafi acikin kowane irin zance da zaiyi, amma babu yanda ya iya dole yayi haquri dashi tunda jinin sane, fatarsa d'aya ALLAH ya ganar dashi matsalolinsa ya gyara kafin wuri ya qule masa, murmushi yayi sannan yakoma inda yake zama lokacin da yake jinyar yana kallonsa sannan yace.

"Aliyu, ai ita jarabawar ALLAH takan zone ga bayinsa muminai, tabbas na zaunu anan wurin kuma nakanji na tawaya sosai, shiyasa yau da ALLAH ya yaye mun wannan lalurar nake ganin yakamata nayi farinciki na nuna masa cewa nagode da lafiyar daya bani, ba tsoro nakeji ALLAH yasake jarabtata ba domin shiyasan dalilinsa nayin hakan, nagode da irin naka farincikin daka nuna mun domin yasa nad'auki wani darasi aciki."

Girgiza kai baffa Usman yayi had'e da cewa. "Ashsha Ali Kai kam wane irin d'an uwane haka? Shin kana ganin abunda kayi burgewa ne ko kuma zai samaa maka nishad'ine shiyasa kayisa? To kasani kayi kuskure mai girma domin kayi izgilanci da al-amarin ALLAH wanda shi keyin yanda yaso alokacin da kuma yaso.
"juyowa yayi ya kalli baffa sannan yaci gaba da cewa.
"kayi hak'uri da kalamansa in sha ALLAH zaiyi nadamar yinsu ko yaushene."
Baffa Usman nagama fad'ar haka yabar d'akin dama tuni itama matarsa Inna Bilkisu takoma cikin gida don cigaba da aikinta saboda marecen dake gabatowa, nan take baffa Ali yaji jikinsa yayi sanyi kuma yafahimci bai kyauta ba.

"Yi hak'uri Yaya." Yafad'a tare da miqewa shima yabar d'akin, Inna ruqayya nabiye dashi a baya...







*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___33πŸ’Ž

Ranar kam baffa kasa kwana yayi saboda abubawan da suka tarar masa azuciya, tsantsar farincikin samun lafiyarsa da irin kalaman da d'an uwansa ya jefesa dasu, Abu mafi cimasa rai shine yanda matarsa uwar d'ansa tayi biris da al-amarinsa, duk masoyansa na nesa dana kusa sunzo tayasa murnar samun lafiyarsa amma ita da take matarsa mallakinsa da tafi kowa ribantuwa da ita takasa zuwa ta dubasa balle tanuna masa farincikin da tayi, wasu zafafan hawayene suka zubo masa yana mai nadamar zab'enta a matsayin abokiyar rayuwarsa kuma uwar 'ya'yansa, ganin zai sake jawowa kansa wani b'acin rai da damuwa yasa yashiga bayi yayo arwala yatada sallah yana mai miqa godiyarsa ga ALLAH daya fitar dashi cikin jarabawar da take ciki batare da anrabasa da imanin saba,

Bayan sati d'aya da samun lafiyar baffa duk masu zuwa dubasa sun gama zuwa ciki har da iyayen Rashida, baba da umma da malan balarabe da matansa sai yayarsu hajia maryama da kuma aunty marwiyya, haka sukayo mota guda sukazo dubasa wanda ranarce tafarko da umma tazo gidan, duk da tanajin 'yan wasu matsaloli da 'yarta ke ciki tayi farinciki sosai ayanayin da taganta, don ba qaramar kulawa take samu daga wajen Nuraddeen ba, lokacin ne cikinta yacika wata biyar dam, tayi haske ta murje ko Ina na jikinta ya cika fam sai sheqi da kyalli takeyi abunta, ga d'an cikin daya fito ya zauna mata d'agwas ajiki gwanin sha'awa, duk wani motsi nata na akan idanuwan Nuraddeen da baffa, duk abunda take so taci suna bid'o mata batada wata matsala saboda yanzu komai tanaci kuma tadena yawan aman da takeyi si can baka rasa ba.
Rashida tayi farincikin ganinsu sosai har tanaji kamar takoma ciki, da zasu tafi baffa yahad'a masu sha tara ta alkhairi shida baffa Usman suka rakasu har bkin mota, haka kurum Rashida ta tsinci kanta da fashewa da kuka tanaji kamar karsu tafi subarta tariqe ummanta sosai, saida Nuraddeen yayi da gaske yasamu ya lallab'ata suka koma cikin gida sannan su kuma suka wuce cike dajin kewar 'yar tasu.
Duk wasu abubawa da baffa yasan nashine a d'akin da yayi jinya yana cika satin nan guda da warkewa ya kwashesu yamayar asalin shiyarsu wato d'akin Yaya hawwa dama jinya ce takaisa can shiyasa yanzu da ALLAH yabashi lafiya ya dawowarsa saboda yasamu damar tsawatar mata, sosai hakan da yayi ya matuqar b'atawa Yaya hawwa rai har tana cewa ita ya komawarsa can d'akin kar yazo ya takurata, yi yayi kamar bai jitaba yaci gaba da kwaso kayansa yana maidowa nan cike da burin dakatar da ita ga dukkanin mugun nufinta.

Hakan kuwa da yayi ya matuqar yiwa Nuraddeen dad'i ya sake maida hankalinsa wajen renon cikinsu, wata irin mahaukaciyar soyayya yake nunawa Rashida wadda ko alittafan novel bata tab'a jin irinta ba balle a finafinan zamani, kusan ko yaushe yana gida idan yataso makaranta, tare sukeyin komai kuma yanaci gaba da koya mata karatunta, ba laifi tana fahimta sosai don yanzu karatun hausa kowane irine zata iya karantawa, haka shima na bokon don su ( _come, go, sit-down, walk, run, stop, shoutup, ask_) duk ta iya, haka ma fannin had'a jimloli da turanci irinsu, ( _I will be there soon, stop crying, don't worry, why do you ask, tell them e.t.c_) duk ta iya saboda yanda ya d'aukesu da muhimmanci shiyasa yafara koya mata ire irensu saboda yanda zai samu sauqin mu'amala da ita cikin sauqi idan suna cikin mutane, haka shima duk wasu addu'o'in da be iyaba yana koya daga wajenta, rayuwarsu cike take da burgewa gwanin ban sha'awa saboda yanda suke son junansu, qauna da kuma kulawa abun ba'a magana, kallo d'aya zakayi masu kafahimci yanda kowanensu ke shirye da sadaukar da farincikinsa akan d'an uwansa, furuci da kalamansu d'ai idan ka saurara zaka fahimci cewa shirya suke da su mutu wa junansu, daidai da qwarar zarra basa ba baqinciki damar da zai shigo masu cikin rayuwa, sun yarda da juna kuma sun amince akan zasuyi rayuwa tare kuma zasu mutu atare shiyasa sukeda tsananin fahimtar juna, cikin Rashida na tsufa qwaqwalwarta na dad'a bud'ewa wajen d'aukar karatun da Nuraddeen ke koya mata, Wanda si yanzu ne tafahimci cewa Babu wata wahala cikin karatun kamar yanda take tunani kawai rashin so da maida hankali yasa takasa natsuwa tayisa.

Tuggu da makirci kuwa har yau Yaya hawwa takasa dena shiryawa Rashida shi, idan tayi wannan tayi wancan ta binne nan ta binne can amma duk wanda tayi sai ALLAH ya kubutar da Rashida, sau da yawa tasha zuwa tayi binne binnenta a bayan d'akin Rashida sai ALLAH yatura yara garin wasa su tonosa, musamman ta karb'o maganin da zai sawa Rashida baqin jini agun Nuraddeen ta zauna ta dama matashi cikin fura da nono saboda sanin yanda take matuqar son furar ta ajiye gefe da zimmar idan Rashida tashigo gaishesu zata bata tasha, malan bakada imani ya tabbatar mata da cewa matuqar ta shata Nuraddeen zai tsaneta da ita har abunda ke cikin cikinta kuma bazai qara ko awa d'aya da ita ba a matsayin matarsa zai saketa da kansa, kuskuren da tayi ta manta cewa da bakinta tasha fad'a agaban kowa cewa ba tason Rashida da ita har abunda ke cikinta, shiyasa lokacin da taba Rashida furar da tazo gaishesu baffa dake zaune yana karyawa yafahimci akwai wani abu ciki, har Rashida tamik'e cike dajin dad'i tana yimata godiya baffa yakirata, wata baqar leda yajawo agefensa dake d'auke da fura da nono da ba'a dama ba masu yawa ya miqa mata yace taje da ita tadama masu ita da mijinta sai tabashi ta hannunta yasha, yanda taga furar tayi kyau yasa taji tabiyo mata arai amma bazata iya musawa baffa ba tunda yace yana so, miqa masa furar tayi tana binta da kallo kafin takarb'i wacce ya miqo mata aleda tabar d'akin, tana fita Yaya hawwa tafara masifa akan ya za'ayi tabata abu ya karb'ar mata, murmushi kawai yayi tare da girgiza kai yace "hawwa kiji tsoron ALLAH, yarinyar nan da bakinki kike iqirarin baki sonta akan me zaki bata wani abu yanzu, shiyasa nafahimci akai wata badaqalar da kike shiryawa aqasa ni kuma na karb'e furar."

"To amma ai badonta zanyi ba saboda abunda ke cikinta kuma naga tana sonta sosai." Saida ya mere baki sannan yace, "saboda abunda ke cikinta? Kin manta shima kince bakya sonsa bakya qaunarsa? Taya za'ayi yanzu kiyiwa mahaifiyarsa abu donsa baya baki sonsa."

"Nifa malan kadena jifata da sharri ba abunda nasawa furar nan, kyautatawa ce kawai amma kana bid'a kamaida cibi yazama qari."

"To fad'awa wani hawwa, Amma dai bani ba, kinfi kowa sanin nasan halinki kar babu abunda bazaki iya iyaw yarinyar nan ba tunda baki sonta baki qaunarta, idan kuma kince ba haka bane ungo furar kisha ke." Yafad'a yana miqa mata furar a hannunta. "Ungo riqa kisha nace." Yasake fad'a akaro na biyu yana kallonta.

Ganin ta had'e rai tare da juyar dakai gefe yasa yayi murmushi cike da takaici yace.

"Hmm! ALLAH yaganar dake hawwa, bakida gaskiya ko kad'an acikin alamurranki, zan so ace kin daure kin zibar da makaman yaqinki akan yarinyar nan tunda har rabo yariga yashiga tsakani, kiyaqi zuciyarki kiyarda da qaddarowar ALLAH acikin aurennan idan ba haka ba zakiyi babban dana sani da Kuma nadama lokacin da basa da amfani, yanzu haka hawwa zuciyata cike take da nadamar zab'arki da nayi amatsayina uwar d'ana gashi nadamar batada amfani tunda har rabo ya gitto a tsakaninmu, lokaci yariga yaqure mani da zan iya maida hannun agogo baya badon haka ba wallahi bazan zab'awa d'ana mahaifiyar da Bata tsoron ALLAH kuma take shirka dashi."
Baffa nagama fad'in haka ya d'auki furar yaje toilet da ita yazuba da yake na qasane ya jefar har da kofin aciki sannan yafita yana mai neman sauqi da sassaucin jarabawar da ALLAH yayi masa da ita.

Ita kuwa kamar ta k'walla ihu haka taji don izuwa yanzu tafara fara kaiwa maqura bisa tufk'ar da takeyi baffa nayi mata walwala, gaba d'aya ya kasa ya tsare akan al-amarin yarinyar ko shine mahaifinta ai hakan ya isa, miqewa tayi had'e da riqe qugu tana hurar hanta tace, "Shikenan! Yanzu kam wasan yazo qarshe, zanyi amfani da dukkanin abunda na mallaka a duniya don cikar burina da nuna maka cewa baka isa ka dakatar dani ba." A fusace tajuyo ta d'auki mayafinta da sauri da sauri tabar gidan ta nufi jejen wani mugun boka da tuni taso zuwa rashin kud'i ya hanata ana cemasa boka mai abun mamaki wato (bargaji) kamar yanda kowa yasanshi dashi yau taquduri komai yakeso zata bashi matuqar zai fitar mata da waccan matsiyaciyar acikin zuri'a.

Rashida kuwa na komawa sashenta ta kwab'e hijab d'in dake jikinta zuciyarta cike da farincikin tafara samun karb'uwa a wajen uwar mijinta ganin alkhairin data yimata, ALLAH sarki baiwar ALLAH bata san cewa yanzu haka tana can kan hanyar illatata ba da kuma tabbatar mata da tsanar da take yimata ba, kitchen ta nufa da tulalen cikinta daya shigo wata na tara, nan da kwana ashirin ko yaushe ana tsammanin haihuwarta, wani d'an madaidaicin bokiti ta d'auko taje ta dama furar da baffa yabata tasha sosai sannan taje toilet ta watso ruwa tadawo falon taqara shan furar sannan takai kitchen ta ajiye, tana fitowa saiga Nuraddeen ya dawo daga makarantar can yarimawa da yake koyarwa, don tunda cikinta ya tsufa yadena zuwa yayo kwanaki acan sai dai kullum yaje ya dawo, cike da yanga tanufo inda yake don ta tarbosa tana fad'in, "oyoyo habibynah welcome back my love my everything."
Bud'e da baki yabita da kallo yana kafeta da idanuwansa maau matuqar d'auke mata hankali, murmushi tayi ganin yanda yake kallon takowarta izuwa garesa da d'an cikinta daya yimata kui, dama saye take da wata doguwar riga data d'ame mata jiki ko ina cikin yafito sosai ya matauqar qara mata kyau kamar ba ita ba, rufe idanuwansa yayi had'e da bud'ewa sannan ya bud'e mata hannayensa kafin taqaraso yana fad'in "thank you habibtynah kece haka kuwa?" tana qarasowa tarungesa ya mayar da hannuwansa yana shafa bayanta yana dariya, tace

"Ni d'ince kuwa donma babynka ya b'atamun tsari."

"Kai habibtyn habiby! ba ruwan baby na kyau ma naga ya qara maki sosai." Yafad'a yana janta zuwa d'aki, cuno baki tayi had'e da cewa.

"Ba wani nan habiby wayau dai zaka yimun, Amma kabari nahaife maka babyn nan naka zakaga yanda zanyi fresh in koma 'yar gayu, baran ma idan nafara zuwa school d'in da kace zaka kaini, hmmm sai kasha mamakin ganin yanda habibtyn nan taka zata canza." Tak'are maganar tana aza kanta saman kafad'arsa riqe da hannusa, "ALLAH habibty nah?.." Nuraddeen yafad'a daidai lokacin da yake qoqarin zaunawa saman kujera had'e da turo idanuwa waje. turo nata itama tayi tana kad'a masa kai alamar tabbatar da zancenta had'e da cewa "serious habiby".

Jawota yayi ya zaunar da ita saman cinyarsa yana shafa cikinta ahankali sannan ya d'ago kansa yana kallonta yace "you're serious ko? to nafasa babu inda zakije." Saida tayi dariya sannan tarungumosa ta aza kansa saman breast d'inta tace, "haba dai habiby!, kaima dai kasan wasa kakeyi, kaga! Mudai bar wannan maganar ka tashi muje na tayaka kawatso ruwa sai kaci abinci, duk da yau dai ba abunda kake so nadafa maka ba, Eba ce da miyar shuwaka nayi maka."

Saida yayi kissing d'in cikin nata sannan ya d'ago kai ya lakuci hancinta sannan yace, "anything habibty indai daga wajen kine I luv it koda kuwa bana son sa."
Yafad'a yana kashe mata ido d'aya. Jan hannunsa suka nufi uwar d'aka tana fad'in "you different habiby."

Dariyar da saida haqoransa suka bayyana yayi had'e da jawota tafad'o masa ajiki ya jingina jikin wardrobe d'in dake cikin d'akin yana k'arewa kyakkyawar fuskarta kallo suna shaqar lumfashin juna yace "you're different zakice habibty ba you different ba kinji ko?."
'Dan turo baki tayi sannan yace, "koma yane ai kaine ka koyamun shi ahaka" tafad'a a shagwab'e tana b'alle masa mab'allin rigarsa, da haka Nuraddeen ya shiga zolayarta yana aika mata da wasu zafafan saqonni masu wuyar fassarawa har yasamu ya lallabata cikin azanci yabiya buqatarsa.

Tare suka shig wankan bayan sun fito ta kimtsa agurguje had'e da zuwa ta kawo masu abinci sukaci suka qoshi sannan yace ta taso suje tamotso jikinta don yaga qafafuwanta sun fara kumburi,
Kitchen tafara shiga tasha ruwan farin zob'on da umma tabata satin daya wuce da sukaje dubosu tace tadinga sha zai taimaka mata wajen kakkatse tsak'in dake fita yayin haihuwa da wani wanda Inna Bilkisu tabata shi kuma tace maganin tsinkau tsinkau yakeye, Sha takeyi tan wani b'ab'b'ata rai yana tsaye yana kallonta har tagama sannan tafito.








*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___34πŸ’Ž

Habiby wai har ina zamuje ne motsa jikinnan haka naga duk kabi ka kasa ka tsare." Rashida tafad'a tana cuno baki ba, jawo hannunta yayi had'e da cewa,

"Idan mukaje ai kya gani, nalura bakya son kina motsa jikinki kuma kinsan ko awonmu na qarshe da mukaje saida likita ya jamana kunne akan kirinqa yawan motsa jiki zai taimaka maki wajen aihuwa, don haka dole yanxu kiyi hak'uri muje ko don chu luv d'inmu, mud'an zazzagayo"

Zaro idanuwa tayi waje had'e da rufe baki tace, "don ALLAH karufan asiri habiby, wlh bazan iya ba, ka kuwa san halin mutanen garin nan naku kuwa?, Kawai kayi haquri zan motsa anan cikin gida karka jawowa kanka zagi." Zai sake magana ta aza yatsanta akan leb'ensa had'e da cewa.

"Pls.. habibyyyyy." Tare da Jan k'arshen sunan cikin shagwab'a.

Bayanda ya iya da ita dole ya hak'ura don aduk lokacin data yimasa irin wannan kiran ji yake baya iya musa mata akan komai,

"To yanzu fad'amun ya kike so ayi, motsa jikinnan dai kinsan dole kiyisa ko saboda lafiyarki Kuma ina so ki haifomun my chubby luv very strong!" Yafad'a yana kallon cikin idanuwanta.

"Muje ka rik'amun k'afa fuwana zanyi set back (wani salon motsa jikine da mutum zai kwanta ko kuma zaunawa yana yin gaba yayi baya na tsawon wasu sekonni sannan yadawo gaba, haka zai dingayi har na tsawon mintunan da yaji zai iya.)"

"Anya zaki iya habibty." Ya tambayeta cike da tsoro, "o'oh zan iya mana, ai masu ciki nayi kuma babu abunda ke samunsu."

Haka kuwa akayi suka koma falo ya taimaka mata sosai tayi set back d'inta fiye dana mintuna ashirin har tagaji ta dena saboda mararta da taji tad'an amsa mata, sake taimaka mata yayi ta watso ruwa saboda yanda zufa kefita jikinta sannan yariqota suka dawo falo ta zauna tare da miqe qafafuwanta ya shiga yimata tausa har bacci ya d'auketa.

β€’β€’β€’ β€’β€’β€’ β€’β€’β€’
Tafiya mai nisa Yaya hawwa tayi kafin takai cikin dajin boka mai abun mamaki (bargaji), tana kaiwa ana kiran sallar la'asar tayi tsaye abakin wani beji tana dube duben ta inda zata hango bukkar bokan da aka fad'a mata cewa daidai wajen yake zama sai gashi ta isko wanen wayam Babu alamar wata bukka awajen, tafi minti biyar kafin tajuya zata bar wajen cikin wani irin sauti marar dad'in ji taji ance.

"Maraba dake hawwaaa.., maraba da zuwa gidan miyagun aljanu, gidan biyan buqatun shed'anu da bau tsoron ALLAH, gidan rashin tausayi da imani, gidan da babu kunya balle mutunci, gidan cin amana da mugunta, gidan da babu jin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login