Showing 117001 words to 120000 words out of 260204 words

Chapter 40 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt

gida."

Shiru tayi na tsawon daqiqa d'aya dake nuna damuwarta akan maganar, har ga ALLAH tanajin rad'ad'i aranta idan ta tuna halin da Rashida zataje ta riska na rashin iyayenta, ba wani dogon shiri yayi ba face doguwar riga jalabiya daya zura ajikinsa sannan ya karb'i little a hannunta yana fad'in.

"Kidena bana son irin wannan dogon tunanin zai iya sakaki cikin damuwar da zata iya ankarar da ita halin da ake ciki."

"Shikenan Dr, Amma kana ganin bazamu bari sai gobe muje kaita ba? Ni sai nake ganin kamar dare yayi yanzu.

"Noo...hakan zaisa tayi kuka damu idan mukace mubari sai gobe, amma in mukaje yanzu mun kaucewa duk wani zargi daga gareta akan cewa rashin zuwanmu ne akan lokaci ya haifar da hakan kin gane?."

'Daga masa kai tayi sannan tashiga toilet, batafi mintuna biyar ba itama tafito tawuce falo tajawo akwatin kayanta dama tun d'azu Mai gadi ya shigo masu dasu ciki tawuce itama tashirya cikin doguwar rigar wani yadi marar nauyi, karb'arsa tayi takoma d'akin da Rashida ke ciki ta isko ita har tagama shiryawa tana ranka sallolin kanta tunda qasaru ne, tad'an jima zaune kafin taqarasa tamiqa matashi had'e da cewa.

"Ungoshi kiwatsa masa ruwa kifito falo muna jiranki."

Karb'arshi tayi tana fad'in "sannu aunty yaron nan nabaku wahala, shikenan shi baza'a ajiyesa shi kad'ai ba sai an tsaresa?"

"Ikon ALLAH! kin jiki da wata magana mmn boy, ai lalura ce takawo hakan, Amma badon haka ba mezaisa yana baccinsa ayita reto dashi hakan?"

Fatima taqarasa maganar tana murmushi sannan tamiqe tafice daga d'akin, a falo taci karo da Dr nura yadawo daga wajen ba maigadi saqo ya sawo masu abinci a wani restaurant dake kusa dasu a can bakin titi.

Hijab d'inta ta d'auko tadawo falon yana zaune ya miqe had'e da kabbarta sallah har suka gama ranka sallolin atare, suna zaune Rashida tafito d'auke da little ta gyarashi sai qamshi yake saye da hijab d'inta har qasa, duqawa tayi ta gaishesu suka amsa kowanensu fuskarsa d'auka da murmushi kafin Dr nura yamiqe had'e da karb'ar little d'in a hannunta ya zauna d'aya daga cikin kujerun dake falon, ita kuma ta zauna kusa da Fatima da har lokacin bata tashi daga inda sukayi sallar ba tana addu'a, sai da tagama suka shafa tare Rashida nafad'in. "Amin ya Allah masu albarka auntynah."

Zaro idanuwa wje Fatima tayi had'e da cewa.

"Nashiga uku ni batulu, yaushe kika fara shiga zuciyar mutane mmn boy kina gano sirrin addu'o'in da sukeyi."

Dariya Rashida tayi sannan tace. "Ba shiga zuciya bane auntyna, abunda ya tsaya mani araine har yakai yasa bana iya gama duk wata ibada tawa ba tare dana roqi ALLAH daya kawo mana qarshen saba, balle ke da nasan duk yanda nakai ga jin zafinsa kinfini shiyasa natabbatar idan ni ina yin addu'ar samun yayewar wannan abun toke zaki fini yin hakan sosai, ubangiji ALLAH yanda kuke bawa yaron nan kulawa kuma ALLAH yakula daku yabaku zuri'a masu albarka."

Tare duk suka had'a baki ita da Dr.nura suka amsa da Amin.

Maigadi ne yayi sallama Fatima taje ta karb'o saqon ta kawo falo ta ajiye sannan taje ta d'auko plates guda uku da cokulla da wani tray babba da yuqa ta ajiye bayan ta d'aurayosu, zuzzuba abincin tayi dake cikin robobin take away sannan taje ta wanko fruit d'in Rashida takarb'a ta gyara masu, miqewa tayi taje ta d'auko little a saman jikin Dr nura dae kwance saman kujera tana fad'in.

"Bisimillah yallab'ai."

Saida sukaci suka qoshi Dr ya d'auki makullin motarsa tare da d'aukar little dake saman kujera yana 'yan wasanninsa da hannuwa sannan ya fice yana fad'in.

"Ina jiranku a waje."

Kwashe kayan suka farayi suka wawwanke komai had'e da gyara wajen sannan suka bi bayansa, dama kayan Rashida nacikin mota ba'a fiddo komai ba inba 'yar jikkar baby bag d'in little dake sagale a hannunta ba, shiyasa shikad'ai ta gyara ta sauyawa kaya ita kuma tamaida wud'anda ta cire ajikinta.

Kasancewar akwai 'yar jayawa sosai tsakaninsu yasa koda suka isa anguwar tasu Rashida qarfe tara da rabi nadare har yayi, duk d'okin da Rashida keyi nason zuwa taga iyayen nata suna nufo anguwar taji gabanta yafara fad'uwa, a hankali tafara kirawo sunayen ALLAH tana mai neman tsarinsa daga dukkanin sharrin dake iya cutar da ita ko d'anta.

A daidai bakin qofar gidan ya tsaya da yake akwai wutar nepa da d'aid'aikun mutane dake kai da kawo cikin anguwar, ko gyara tsayuwar motar beyi ba ta b'alle marfinta ta ruga aguje tanufi qofar gidan tana kiran "umma, ummaa."

Turus ta tsaya ganin qofar rufe da kwad'o gabanta na tsananta fad'uwa, juyowa tayi jiki ba k'wari tace.

"Uncle ya naga gidan arufe?." Tana qarasowa inda suke a firgice.

Maqwabcinsu ne taga yazo wucewa zai shiga gidansa kafin dr yace wani abun tabi bayansa da sauri tana fad'in. "Baba, baba na kande!."

Da sauri ya juyo yana kallonta cike da mamaki yaja da baya, ya matuqar tsoratar ganinta awannan lokacin ba zato ba tsammani, matsawa ta sakeyi kusa dashi jikinta na rawa tace, "baba nakande nice fa Rashida, nice Rashidar umma fa, don ALLAH baba kada ka gujeni ka tsaya kafad'amun Ina su umma da baba sukaje, Ina son nagansu baba nakande, Ina matuqar kewarsu, kafad'amun ina ne suka tafi don ALLAH."

Wata irin ajiyar zuciya ya sauke cike da ta'ajibi yace. "Rashida!"

"Na'am baba nakande."

"Rashida ke ce?"

"Eh baba, Ina su ummata suka tafi?"

Jinjina kai baba nakande ya farayi kafin yafashe da kuka yana fad'in. "Wayyo ALLAH na Rashida sai dai kiyi haquri..."

Bata qarasa jin abunda zai fad'a ba tsabar fargaba da tsoron abunda take tunanin zai fad'a yasata fad'uwa wajen, da gudu su Dr. Suka qaraso wajen Fatima taduqa ta tallabota tana kiran sunanta, Dr nura dake riqe da little ya miqama baba nakande hannu dake kuka yace.

"Assalamu alaikum, baba meye kafad'a mata halama haka?."

"Yaro kaine?" Baba nakande yafad'a yana share hawaye don ya wayesa,

"Eh baba."

"Dama tana hannunka?"

"Eh baba,"

"To meyasa bak sanar da ita komai ba?, Gashi yanzu tun kafin infad'i abunda zan fad'a tasome."

Ganin halin da take ciki yasa Fatima takoma cikin mota ta d'auko gorar ruwan swan d'in dake ciki ta yayyafa mata had'e da shafa matasu ga fuska,

Ahankali Rashida tabud'e idanuwa tare da fashewa da kuka tana fad'in. "Nashiga uku aunty don ALLAH kada kucemun iyayena sun mutu sun barni.."

"Haba Rashida, waya fad'a maki cewa iyayenki sun mutu?, Iyayenki na raye amma bamusan inda suka dosa ba, sun bar garinnan kwata kwata saboda b'atanki.."

Kan baba nakande yarufe baki tuni sukaga Rashida tafara fizge fizge idanuwanta sun kakkafe."

Da sauri Dr yace Fatima takarb'i little da sai faman kuka yakeyi ya tallabi Rashida yasa cikin mota, "baba don ALLAH idan ka amince kazo muje asibiti dakai, nasan bazaka rasa sanin wasu daga cikin dangin taba."

Duk da baba nakande najin tsoron halin mutunen duniya tausayin Rashida yasa bai tsaya tunanin komai ba yashiga motar ya bisu, da gudu Dr nura ke taka motar har suka isa asibiti, cikin gaggawa aka karb'i Rashida kasancewar wajen aikinsa ne ba tare da antsaya wani b'ata lokaci ba, ba'a jima ba likitan daya shiga dubata yafito had'e da tambayar Dr nura cewa dama tanada hawan jini (hypertension)?.

Nan yabashi amsar cewa tana dashi lokacin data haihu amma yayi tsammanin cewa wannan is normal yariga ya wuce,

"Noo..gaskiya ba haka bane, yanzu hakan shine ya tsar mata, sai dai baiyi mata worst sosai ba za'a iya shawo kansa da yardar ALLAH, inaga ko yanzu saboda bata jima da haihuwa bane hakn tafaru, amma in sha ALLAH komai zai dai daita don Babu wata matsala bayan shi, yanzu haka anyi mata allur bacci ne saboda tasamu isashhen hutu"

"Alhamdulillah Dr. Ngd sosai."

"Ba damuwa dr.nura, ALLAH yabata lafiya."

"Amin Dr"

Nuraddeen yafad'a yana kallon baba nakande dake zaune yayi tagumi.....



















*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[11/14, 22:52] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

_ASSALAMU ALAIKUM, GAISUWA DA FATAR ALKHAIRAN ALLAH AGAREKU MASIYANA, INA BAKU HAQURU AKAN RASHIN AMSA MAKU IDAN KUNYI COMMENTπŸ˜… KUYI HAQURI IN SHA ALLAH DAGA YAU ZAN GYARA, KUNA QORAFI AKAN HAKA ASHE ABUN SON KAINE WATO WANZAM BAKA SO GA KANKA,🀣 YO IDAN HAKAN NA BATA MAKU RAI ME KUKE TUNANI AGARENI NIDA NAZAUNA NAYIMAKU TYPING DON KU NISHA'DU SAI ACE ANWAYI GARI KO THANKS BAZAN SAMU AWAJENKU BA BALLE COMMENT, DUK DA DAI NI NASA KAINA AI KUNSAN BABU DADI DON NA TABBATA KUNA KARANTAWA, SHIYASA NIMA NA SHAREKU DON KUJI IDAN ABUN KWAI DA'DIπŸ˜‚ BUT TUNDA KUN QARA, TO ZAN GYARA KAMAR YANDA NAKEYI ADA, INA FATAR KUMA ZANGA CHANJI AWAJENKU TA HANYAR DA'DA'DAN COMMENT 'DINKUπŸ‘ NGD SSAI_

Page___55πŸ’Ž

Tuni baba balarabe da Yaya maryam dasu aunty marwiyya suka isa asibitin cikin daren sanadiyar wayar da baba nakande yayiwa baba balarabe ya sanar dashi zancen dawowar 'yar d'an uwan nasa shi kuma yakira Yaya maryam takira aunty marwiyya ta sanar da ita, kowanensu cike da farinciki yake a zuciyarsa naganin 'yar tasu duk da dai a yanayin da take ciki na nema ya gusar masu da farincikin,

Little kuwa yayi kuka har ya gaji saboda tsabar yunwar da yakeji, goyashi fatima tayi bacci ya d'aukesa shi kuma Dr nura ya koma gida don ya d'auko masu abunda zasu iya buqata kafin gobe don yasan bazasu wuce gobe ba shiyasa koda su baba balarabe suka iso asibitin Fatima kad'ai suka tarar sai baba nakande, ita tawuce dasu d'akin da Rashida take kwance tare da yimasu bayani ataqaice kafin Dr ya iso.

Jugum jugum ya tarar dasu kamar wud'anda k'wai ya fashewa cikin ciki ya wuce ciki ya ajiye kayan dayazo dasu yana kallon gefen da Rashida ke kwance hannunta laqe da drip sun kusa qarewa sannan yajuyo yanufi inda baba balarabe ke zaune shida mijin Yaya maryam,

"Assalamu alaikum." Yafad'a yana miqa masu hannu suka gaggaisa kafin baba nakande yayi masu bayanin cewa shine mutumen da yazo da Rashida, cike da girmamawa suka sake gaishesa kafin ya nemi waje yazauna yana fuskantarsu, matsowa su aunty marwiyya sukayi wajen suma suka gaisa sannan Dr nura yagabatar masu da kanshi ataqaice yaqare maganar yana nuna masu Fatima.

"Waccan kuma iyalina ce."

"Masha ALLAH." Baba balarabe yafad'a sannan yace.

"Ni sunana malan balarabe, qane ga mahaifin ita waccan yarinyar Rashida, ita Kuma wannan sunanta Maryam wato Yaya agaremu nida mahaifin Rashida, wannan qanwar mahaifiyar tace sunanta marwiyya sai kuma shi wannan mijine ga ita yayar tamu wato alhaji ubale."

"Dukkaninmu da kake gani abu d'aya muke babu banbanci, Kuma mukad'aine iyayen Rashida acikin wannan garin, munyi baqin ciki sosai alokacin da muka rasata wanda sanadiyar hakanne ya haifar mana da shiga matsanancin damuwa kala kala har yakai ga su iyayenta da suka haifeta sun kasa jurewa rashinta sunbar garin bayan doguwar jinyar da sukayi a asibiti."

A yanayin bayanin da baba balarabe keyi yasa Dr nura gamsuwa akan cewa su d'in shaiqanta ne na jini don haka yasaki jiki sosai dasu had'e da yimasu bayanin yanda suka tsinceta dalla dallah da irin wahalar da yaronta yasha wanda shine sanadiyar da yasa basu nemesu ba tun wuri, duk da dai yayi qoqarin ganin yasamu iyayenta alokacin Amma ALLAH bai yarda ba, gaba d'ayan su kuka da tausayin halin da Rashida tashiga ita da yaronta suka shigayi suna Mai godewa ALLAH daya miqata ga hannun mutane nagari masu d'imbin karamci da halacci, a daidai lokacin little dake goye a bayan Fatima ya tashi yafara mutsu mutsu yana neman yin kuka Nuraddeen yamiqa mata hannu ta sancikke masa shi, miqasa yayi hannun malan balarabe had'e da cewa.

"Wannan shine abunda ALLAH ya albarkaceta dashi wanda muka rad'a masa suna Nuraddeen bisa yardarta da kuma amincewarta."

Hannun baba balarabe na rawa ya karb'esa yana qare masa kallo don wajen d'auke yake da hasken wutar lantarki kamar rana, tabbas ko ba'a fad'a ba wannan yaron jinin sune don kamarsa sak da d'an uwansa wanda itama mahaifiyar tasa wato Rashida dashi take Kama, wasu zafafan hawayene suka zubo masa yana maijin inama d'an uwansa bai tafi ba yaga irin kyautar da ALLAH yayi masa ta hanyar dawo masa da 'yarsa da kuma jikansa a hannunsa.

Rungume yaron yayi yanaji tamkar d'an uwan nasa ne kafin yaji hannun Yaya maryam data kasa dangana tana qoqarin karb'arsa.

Murmushi tasaki alokaci d'aya hawaye nasake suko mata saman fuska itama lokacin data karb'i yaron tana fad'in.

"ALLAH mun gode maka daka dawo mana da Rashida lafiya daga hannun bayinka salihai masu kyakkyawar zuciya, ya ALLAH ka lullub'esu da tarin ni'imominka tare da yalwataccen farinciki marar yankewa acikin zukatansu da kuma fuskokinsu,"

Taqarsa maganar had'e da d'ago yaron tana sumbatarsa.

"ALLAH ka isarwa mahaifiyarka Nuraddeen ita da iyayenka, yayi maka sakayya kaida mahaifinka ga muguwar kakarka data nemi salwantar maku da rayuwa kida mahaifiyarka, ALLAH..."

Katseta mijin nata malan ubale yayi tahanyar cewa.

"Haba Maryam, menene haka? Keda yakamta kigodewa ALLAH sai ki koma kinayiwa bayinsa mummunar addu'ah? Shin ashe hakan ya kamatan ceki kiyi bayan kinsan ALLAH maiyin sakayyane ga bayinsa wud'anda aka zalunta?."

Shiru tayi had'e da miqawa aunty marwiyya little itama takarb'esa, shafa kansa ta shigayi cike da qaunarsa tana yaba kyawon da ALLAH yayi masa da yanayin jikinsa mai cike da ban sha'awa.

Ganin gaba d'ayansu sun shagala yasa Fatima komawa cikin d'akin da Rashida ke kwance, tana zuwa ta isko tafarka daga allurar baccin da akayi mata lokacin kusan qarfe d'aya saura mintota nadare, da sauri Fatima ta matsa kusa gareta tana jero mata sannu, qoqarin tashi zaune tayi ta dakatar da ita tana fad'in "a'a komawarki ki kwanta maman boy."

Tana dafa kafad'arta had'e da qoqarin maida ita kwance,

"Aunty da gaske su ummata sun tafiyarsu?, Da gaske ba'asan inda suka tafi ba?, Shikenan bazan sake ganinsu ba?" Rashida tafad'a had'e da riqe hannuwanta tana kuka, cikin dakewa Fatima da tuni zuciyarta tayi rauni hawaye sun soma kaida kawo a fuskarta tace.

"A'a maman boy, Zaki ga su ummanki komai daren dad'ewa, hakan bayana nufin kun rabu bane Rashida sai dai kawai ubangijinki na auna imaninkine ta hanyar yimaki jarabawa wata bayan wata Kuma dama haka rayuwar mumini take, idan anyi masa jarabawa ya canye ta sai asake yimasa wata jarabawar wacce tafi tafarkon da akayi masa don kawai a d'aukaka darajarsa da kuma imaninsa idan ya canyesu, kiyarda cewa zasu dawo agareki nan kusa bada jimawa ba in Sha ALLAH." Cikin kuka tace

"Yaushe? Awane lokaci kuma aunty? Bayan zukatansu sunriga sunyi imanin cewa sun rasani kenan har abada."

"Kisa aranki cewa kusa zasu dawo, haba maman boy karki manta ALLAH subhanahu wata'ala yana cewa."

_"Laa taqnad'u min rahmatllah (kada mu kuskura muyanke qauna ga rahamar ALLAH)_"

"Don haka kada kicire tsammanin cewa rahamar ALLAH zatasa iyayenki sudawo matuqar kika miqa dukanin al'amurranki agaresa kamar yanda kikayi abaya, haqiqa wawa, lusari, Wanda baisan kanshi kad'aine ke rabka hannuwa yana tsammanin cewa ALLAH bazai jarabcesa ba bayan kuma yace yayi Imani, walh Rashida ALLAH da kansa ke cewa matuqar kukace kunyi Imani to."

_"wala nabluwannakum bi shai'in minal haufi wal ju'i wa naqsin min amfusi wassamarat, wabasshirisubirin, allazina iza asabathum musibatun qalu innalillahi wa Inna ilaihirrajiuun, ma'ana idan kunyi Imani dani to (zamu jarabceku da abubuwan tsoro, da yunwa da rashin rayuka daga kawunanku da kuma tsirrai, muna yima masu haquri bushara wud'anda idan musiba tasamesu sai suce ga ALLAH mukazo Kuma agareshi zamu koma)"_

"Saboda haka ki daure ki zamo cikin bayinsa masu haquri da yake yiwa bushara kinji ko!"

Cikin kuka dake cike da sauti Rashida tafad'a jikinta tana fad'in.

"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, allahummah thabbit aqadami wa haqqiq Imani,.."

Qarar kukan nata yajanyo hankalin su baba balarabe dake waje da sauri suka shigo cikin d'akin har suna rige rigen qarasowa bakin gadonta, tana ganinsu taqara fashewa da wani kukan had'e da rungume aunty marwiyya tana fad'in.

"Wayyo ummana.."

Babu yanda suka iya domin rasa iyaye tako wace irin fuska ce yanada matuqar rad'ad'i arai wanda dole ko ana so ko ba'aso awannan gab'ar dole abarta tayi kukan domin ko anhanata yinsa rad'ad'in da takeji azuciyarta bazai barta tahanu ba, sai da tayi mai isarta tayi shiru sannan tajaye daga riqon da tayiwa aunty marwiyya takwanta akan gado tana ajiyar zuciya har lokacin hawayen basu dena fita daga idanuwanta ba, sannu suka dinga yimata d'aya bayan d'aya tana amsawa had'e da binsu da kallo hawayen naci gaba da zubo mata.

Rarrashinta suka taru sunayi had'e da ban magana da dad'ad'an kalamai Amma gaba d'aya ita ba abunda take gani sai hoton fuskokin iyayen nata da batasan ranar da zata koma had'uwa dasu ba.

Gaba d'aya takasa tsaida zubar hawayenta wanda hakan yasa Dr nura yaje yakira Dr daya dubata yazo ya sake yimata allurar bacci bayan aunty marwiyya ta aza mata little daya fara qananun kuka tabashi nono yasha,

Bacci mai nauyi sosai ya d'auketa sannan baba balarabe yace da aunty marwiyya taje gida tunda dare yayi sosai lokacin qarfe d'aya da rabi,

Atafau tabuga kai ga qasa akan babu inda zataje anan zata kwana, don gani take za'a iya sake d'auketa idan taje gida kafin tadawo gobe da safe. Adole aka qyaleta tunda ta nace akan haka, Kiran mijinta tayi tasanar dashi anan zata kwana Kuma cikin sa'a ya amince mata don mutumne da baida matsala kuma ko bayan hka su biyu suke ga mijin nata shiyasa Bata damu da sai takoma gida ba.

Yaya maryam ma daqyar baba balarabe ya samu tabi mijinta sannna yajuyo yana kallon Fatima dake riqe da little yace.

"Fatima dake da Dr. Yakamata ku koma gida saboda akwai gajiyar tafiyar da kukayo kuna buqatar hutawa sosai, inyaso nida qanwar mahaifiyar ta zamu kwana anan idan Babu damuwa koda za'a buqaci sawo wani abu kunga ni Ina nan babu matsala."

Ji Fatima tayi kamar ta k'walla ihu don har ga ALLAH bataso barin asibitin ba amma saboda dr.nura ya amsa yasa dole babu yanda zatayi ta haqura ta miqawa aunty marwiyya little kamar zatayi kuka ta karb'esa sannan sukayi saida safe suka tafi sai tunzurar baki takeyi, kallonta yayi yana tuqi yayi murmushi had'e da cewa.

"Fatima meye abun b'acin rai naga kina turar baki haka?" Saida ta kallesa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login