Showing 222001 words to 225000 words out of 260204 words

Chapter 75 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt

wajenne zai cimma maganin da yardar ALLAH.

Firgigit sai ya farka daga baccin da yakeyi yaga ashe mafarkine yakeyi amma aransa yatabbatar da wannan wajen da akace ya tone shine inda suka binne maganin, bako shakka isharace akeyi masa kuma da yardar ALLAH kome zai faru yau sai ya tone wajen, goge zufan da yabi duk ya jiqe masa jiki ya shigayi yana karanto addu'o'i a bakinsa don mafarkin yamatuqar tayar masa da hankali, gashi lokacin qarfe uku nadare balle yaje ya sanar da d'an uwansa, dole ya haqura yakoma ya kwanta yanata istigfari da hailala da kuma tasbihi daga kwancen da yake har aka kira sallar asuba, yana jin baffa Usman ya qwanqwasa masa qofa ya amsa tare da jawo iccensa (crutch) wanda yake dogarawa yamiqe yanufi bakin qofar yabud'e yafitoa.

Bayan angama sallar asuba ya zauna masallaci yayita tasbihinsa har rana tafito sannan yanufi gida, yana kaiwa bakin qofar gida ya tarar da baffa Usman shida baffa suna magana wacce akan d'an uwannasu ne baffa Usman yake roqon yayi haquri ya yafe masa, nan yafad'a masa cewa tun ranar da abun yafaru ya yafe masa amma baya buqatar alaqar komai tahad'asa dashi ko shekara nawa za'ayi har sai sun warware qullin da sukayiwa Nuraddeen.

Baffa Ali na kawowa baffa ya miqama baffa Usman hannu sukayi sallama yabar wajen tun kafin ya ida qarasowa, binsa kawai yayi da kallo sannan ya qaraso wajen ya miqawa baffa Usman hannu suka gaisa fuskarsa cike da damuwa, ganin haka ya shiga kwantar masa da hankali har yake sheda masa cewa ai d'an uwan nasa ya yafe masa dama yafad'a masa b'acin raine yasa yayan nasu fushi dashi har ya d'au matakin daya d'auka akansa, gashi yanzu ya sauko abunda kawai yarage sukoma su rarashi Inna ruqayya tahaqura hakan shine zai ida daidaitawa tsakaninsa dashi.

Baffa Ali yajima yana zubarda qwalla kafin ya d'ago kai ya sanarda baffa Usman labarin mafarkin da yayi jiya had'e da cewa.

"Na tabbata wajenne Usman kuma zanje na tono wajen in Sha ALLAH, roqona d'aya agareka idan nura da Rashida sun dawo kace su yafemun, suyafemun abunda nayi masu, nayi nadama sosai, bansan abunda zai faru ba, zan dawo koko ta ALLAH zata kasance akaina."

Duk inda jikin baffa Usman yake yau saida yayi sanyi sosai, yamatuqar ji tausayin d'an uwan nasa domin gaba d'aya ya sare ma rayuwarnan ta duniya, yayi tuba taubatan nasuha tare da miqa wuyansa gaba d'aya,

Qarfafa masa yayi tayi sannan yace sushiga cikin gida su, bayan sun gama karyawa sukayi arwala tare sannan suka nufi wajen tono inda maganin yake,

Gaba d'aya zuciyar baffa Ali ta dake haka ya dinga shiga cikin juji har suka isa bayan shagunan, runtse idanuwansa yayi don yatuno daidai wajen kamar yanda ya gani a mafarki sannan yabud'e a hankali yanaci gaba da taku har ya isa wajen, kallon baffa Usman yayi had'e da cewa.

"Kaga wajen nan in Sha ALLAH.."

Bai jira amsar da zai bashi ba yafara saran wajen yana, wasu irin sautukka ya soma ji kala kala Wanda azahirin gaskiya d'aya d'ago kai ya kalli d'an uwan nasa shi bayajin komai, hakan yasa yaqara cire tsoro aransa shima yayi kamar baiji komai ba, sannu ahankali yafara cin karo da wasu abubuwa masu kama da mutane aciki suna yimasa gizo a fuska cikin ramen wani irin hayaqi ya turnik'e wajen had'e da wari Mai mugun d'oyi, jiri ne yafara d'ibarsa amma cikin qarfin hali yaci gaba da tono wajen har yakai ga qullin maganin, ji yayi kansa ya wani sarawa duniyar najuya masa yafara karanto addu'o'in faya sani ga baki, wata irin dariya yaji ansaki mai qarar gaske had'e da amsar addu'ar da yakeyi anaci gaba da karantawa. "Muma musulmi ne kamarka, muna sallah muna addu'o'i don haka baza kaci galaba akanmu ba har sai ka amshi saka makonka daidai da laifinka, bazamu barku ba kamar yanda kuka nememu to tabbas sai alqawarin ALLAH ya tabbata akanku kamar yanda mummunar makomarsa zata tabbata akanmu." Yaji an fad'a cikin kunnuwansa tare da kecewa da wata irin muguwar dariya, kan yace wani abu yaga wata baqar mummunar halitta cikin sigar wani baqin hayaqi tana fitowa daga cikin ramen tare da nufatosa daga zaunen daya fad'i tun d'azu dafe da kansa, da sauri yasa hauyar dake hannunsa ya ida ciro maganin wanda kusan tare suka fito da wannan halittar ta lullub'esa sai dai baffa Usman dake gefe yaga iska Mai kamar guguwa tana nad'ed'e niya cikin jikin baffa Ali dako ganinsa bayayi sai dai muryarsa da yajiyo cikin wahalalliyar qara yana fad'in "Usman ka fiddo ashana ka qona wannan qullin maganin kuma kafasa tukunyar dake cikin ramin nan."

Cike da tsoro jikin baffa narawa yafiddo ashana dama sunzo da ita ya cinnawa maganin sannan yasa hauyar yaje cikin ramin ya faffasa tukunyar dake ciki bakinsa d'auke da addu'a yanayi yana kallon iskar data nad'id'iye baffa Ali, Yana gama fasa tukunyar yaga iskan yawani cure waje d'aya tare da duddun qulewa yayi can gefen daji yana gudu da qarfi shi kuma baffa Ali yashe awajen ko motsi bayayi wasu quraje duk sun feshikke masa tun daga fuska har zuwa tafin qafa, da sauri ya jefar da hauyar agefe ya qarasa wajensa jikinsa na rawa ya tallabosa yana jijjigarsa yana kiran sunansa amma ko yatsansa baya motsi, cikin qarar murya yace.

"Ataimakeni..."

Ko baki bai rufe ba sai ga mutane sun iso wajen, ganin yanayin da suke ciki yasama wasu shakku akan meya kawosu wajen, qilama wani abun zasuyi ALLAH ya mayar masu da abunsu don haka suka tafiyarsu, mutum biyu kad'aine suka tsaya suka riqowa baffa Usman baffa Ali aka tallabosa zuwa titi sannan suka tari napep aka sashi ciki baffa yayi masu sannan mai napep d'in yaja suka nufi asibiti dashi, tun kafin ya qarasa isa yakira baffa ya sanar dashi komai.

Baffa na tsaye gefen gado yayi saurin zaunawa saboda wani irin jiri da yaji ya d'ebesa.

Istigfari ya shigayi ALLAH yasa son kansa baisa asanadiyar rayuwa d'aya ba surasa har rayuka biyu, a wani gefe na zuciyarsa kuwa hamdala yayiwa ALLAH da akaci nasarar tono maganin yasan koba komai in Sha ALLAH d'ansa zai dawo hankalinsa kuma ya tuna dasu.

Kamar antsikaresa yayi saurin miqewa yabar gidan ya nufi asibitin da baffa yafad'a masa cewa can suka nufa.

Yana isa ana fitowa da baffa zuwa d'akin da zanyi jinya na 'bangaren maza wato (male medical ward) don har angama dubashi babu abunda ke damunsa, 'yar doguwar sumace kawai yayi sai qurajen da suka feshikke masa a jiki kuma Alhamdulillah ya farfad'o daga sumar har ansa masa drip bacci ya d'aukesa.

Zuba masa idanuwa sukayi suna kallo cike da tausayinsa, tabbas duk bawan da ALLAH keso yakan nufesa da tubamawa kura kuransa kuma yaqara masa da jarrabawa don tabbatar da imaninsa, fatansu d'aya shine ALLAH ya yafi kura kuransa albarkacin tubar da yayi kuma taubatan nasu da tasashi sadaukar da rayuwarsa don jadda tubarsa ga ubangijinsa.

Sudai likitoci sunyi masu bayanin babu wata matsala kuma in sha ALLAH kurajen dake jikinsa ma zasu b'ace saboda na infection ne acewarsu, amma kallo d'aya zakayi masa kasan yana jin zafin wud'annan quraje lura da yanda yake fitar da lumfashi.

A b'an garen inna ruqayya kuwa safiya na wayewa aka ganeta a sheme inda take kwana jikinta duk jini, ashe daren jiya 'yan iskan dake dakonta cikin tashar su kusan bakwai sunyo shaye shayensu suka farmata, saida suka qwace duk 'yan kud'ad'enta sannan d'aya bayan d'aya suka dinga amfani da ita ko tsufanta da qazantarta basaji, mutum d'ayane ya ganesu a tashar yana qoqarin fitowa sai gashi ya hango wata baqar mota qatuwa tayi parking wajen wanda ganin motar yasa samarin guduwa na qarshen dake kanta ma riqe da wandonsa yabar wajen, anfi mintuna uku kafin yaga wasu qatti su biyu sun fito cikin motar suna kallon gefe da gefensu, har bakin shigowa tashar da can gefen da samarin suka arta dana kare saida suka dibo suka tabbatar ba kowa sannan suka sunkuci Inna ruqayya dake kwance a sheme wajen sukasa cikin motar kamar yanda mutumen ke bayani, tsoro da fargabar abunda ke iya faruwa dashi tasa yakasa fitowa har motar tabar wajen, can gabanin asuba sai gashi yaga motar tadawo su sake fitowa da ita da sauri sun ajiyeta inda suka d'auketa farko, shine bayan sallar asuba gari yafara wayewa mutane suka ganeta a inda tasaba kwanci yashe jikinta duk jini, babban abunda yafi d'aga masu hankali shine, ancire mata ijiya d'aya sannan anfasa gefen cikinta da alama wani Abu aka cira daga ciki anka mayar anka d'unke don har filista akwai wajen, ga qasanta sai jini kefaman fita wanda basusan dalili ba, gaba d'aya ancire yatsunta na hannun hagu dana qafar dama amma duk da haka fata mutu ba lumfashi nafita ajikinta, hakan yasa nan take shugaban tashar nazuwa yayi gaggawar kiran 'yan sanda, ba'afi mintuna ashirin ba suka iso, yanda suka ganeta suma hankalinsu ya matuqar tashi, nan take yakira assibiti tunda da ranta bata mutu ba, tuni 'yan sanda suka zagaye wajen da wannan d'oruwan zare da suke sawa idan wani abu yafaru da suke rubutawa (don't across the line...) sukaci gaba da sauran bincike bincikensu kafin motar asibitin ta iso,

Mintuna shabiyar suma suka d'auka kafin su iso 'yan sandan suka basu damar isa wajen su d'auketa saboda subata taimakon gaggawa tunda da ranta bata mutu ba, amma kai kana kallonta ko ba'a fad'a maka ba kasan cikin azaba da bala'in rayuwa take, malaman asibitin na d'agota zanen dake rufe da jikinta daga qasa yafad'i, tsananin tashin hankalin abunda idanuwansu suka gane masu suda mutanen wajen yasasu sakinta, gaba d'aya abunda ya shafi al'aurarta daga qasa tsakankanin cinyoyinta anciresa wajen yayi jawur babu komai sai jan naman dake wajen, mutane kuwa ihu duk sukayi had'e daja da baya suna rufe bakinsa da qwalalo idanuwa, hatta 'yan sandan duk saida sukayi baya saboda firgita, abunda rayuwarsu Basu tab'a gani ba azahiri ko a finafinan hausa ko littafai sai gashi yau agabansu sun gani da idanuwansu, tabbas ko ba'a fad'a ba kasan wannan aikin masu sihirce sihircene da tsafi suka yayyanke mata sassan jiki,

Kan kace me tuni labari ya soma biye gari mutane sai rutatowa sukeyi cikin tashar don su tabbatarwa idanuwansu abunda sukaji ana fad'a, babu abunda yafi tsorata mutane irin yanda duk irin miyaku da cuwurwutar dake jikinta rad'ad'in baisa ta mutu ba, cikin qarfin hali da tausayawa d'aya daga cikin jami'an lafiyan da sukazo ta d'auki zanen ta nufi inda take da zimmar rufeta saiga wata irin guguwa daga sama tanad'o baqa qirin da ita ta turnuqe Inna ruqayya dake sheme wajen tana fidda lumfashi d'aya bayan d'aya,

Banda qarar sautinta da kururuwa tana ihu babu abunda suke iya ji ko gani, wani irin ihu takeyi tana qarar da duk Mai sauraro zai tabbatar da cewa inba rahamar ALLAH ba babu abunda zaisa halittar dake fiddashi ta dace balle asa ran zata rayu, mutane kuwa duk wanda ka kalla yayi jugum yana kallon ikon ALLAH, wasu Kuma da qarfin hali suna vedioting ga wayoyinsu,


Saida aka kwashe fiye da mintuna goma wannan iskan na juyi da wani qugi akanta ita kuma tana qara sannan ya b'ace.

Koda likitocin suka dubata tuni rai yayi halinsa ta cika a bainar jama'a cikin wani mummunan hali tayi mummunar cikawa a idanuwan duniya bisa laifukka da zunubbai data aikata arayuwarta. _(wal iya zubillah, ALLAH kakaremu da mummunar cikawa kuma kasa sanya mu muyi kyakkyawar qarshe, dama haka rayuwa take, duk bawan dake aikata zunubi adoron qasa yaga ubangijinsa ya tona asirinsa to alamar yana qaunar sane sai ya hanzarta yin kyakkyawar tuba kafin lokaci yaqure masa, idan kuma kaga kanata sab'awa ALLAH ya qyaleka yana cigaba da baka nasara acikin alamurranka to kaiconka, wallahi talalace yayi maka, cikar wa'adi kawai yake jira yayi maka mummunar damqar da bazaka iya kuccewa ba, alokacin babu batun bud'ad'd'iyar qofar tuba agareka domin wuri ya qure maka, tabbatuwar alqawarin ALLAH akan kane kawai zai wanzu agareka, shikenan kazamo cikin tab'ab'b'u bayinsa kuma kayi asara, ya ALLAH ka aminta damu kabamu ikon tuba wa dukkanin laifukanmu da zunubbaban da muka aikata makaπŸ‘)_

Haka likitoci suka d'auki gawarta akaje akayi binciki akai, inda su baffa Usman na asibiti wannan labari yazo masu wanda dama sun san hakan zata faru kamar yanda d'an uwansu yayi masu bayani, ALLAH kenan! Wato duk abunda mutum ya aikata arayuwa da sannu zai dawo ya riskesa, batare da sun damar da kansu akan maganganun da sukaji nata yawo agari akanta da mutuwarta ba sukaje police station sukayi bayanin cewa sune 'yan uwanta aka basu hannu sukasa sannan sukaje asibiti aka basu gawarta, bayan likitoci sun basu qwaqqwaran bayani akan binciken da sukayi suka gano cewa mutum bakwai sunyi amfani da ita har sau bakwai kafin tamutu, haka kuma cikin bincikensu sun gano ancire mata sassan jiki da dama kafin tamutu kama daga ijiyarta d'aya, dukkanin yatsun hannunta na dama da kuma qafarta ta hagu, haka kuma an yanke mata al'aura, ancir mata qoda d'aya da kuma mahaifarta wanda suna tsammanin aikin masu anfani da sassan jikine wato (secret society) amma sun miqa dukkanin bayanan daya dace ga jami'an tsaro Kuma in Sha ALLAH zasuyi qwaqqwaran bincike akai, baffa kam kuka yafashe dashi saboda tsananin tausayin irin azabar da ya kafin ALLAH ya amshi ranta, nan ma saida sukasa hannu ga wasu takardun sannan aka basu gawarta suaka tafi da ita gida don suyi mata wanka a sallaceta....

β€’β€’β€’ β€’β€’β€’ β€’β€’β€’
A qasar malesia kuwa Dr nura na kwance akan gadonsa sai faman juyi yakeyi saboda tun kwanakin baya da suka shud'e ya soma jin kamar akwai wani Abu daya rasa acikin rayuwarsa amma meye? shine abunda qwaqwalwarsa takasa tuna masa, kwana biyu ma da suka wuce yaji wani d'aya daga cikin abokanan aikinsa ya ambaci zaije qasar Nigeria har yake tambayarsa wace qasa ce haka, yayi masa bayani, tun alokacin yake nanata sunan a qwaqwalwarsa kuma yake son ya tuno wani abun yakasa, kusan kullum haka yake don musamman yake shiga google ta laptop d'insa yayi searching akan qasar don kwata kwata tun lokacin da baffa yakirasa awaya yaji muryarsa har abun ya nemi zame masa tab'in hankali idan yana tunano muryar tasa ya dena amfani da waya, telephone kawaine dake ajiye d'akinsa yake amfani dashi kuma shima saboda idan za'a nemesa emergency ne a asibiti shiyasa ya ajiyesa, ayanzu kuwa ji yakeyi tabbass ya rasa wani abun awannan qasar da yakeji ana ambata, tun daren jiya yake jinsa ba daidaiba har zuwa wayewar safiyar yau hakan yasa yakasa bacci in banda aikin juye juye akan gadon nasa babu abunda yakeyi, can yaji wani irin abu ya tsirgo masa cikin kai tamkar an soka masa wani irin qarfe mai zafi aciki, addu'o'i yafara karantowa yana fad'in.

"Wash..wash.wash!" Tun yana fad'a ahankali har ya soma sakin wata irin qarar da tasa abokinsa da suke gida guda amma kowane da part d'insa rugowa aguje, yana shigowa ya samesa kwance qasa a zube yariqe kansa, fita yayi waje ya kirawo mai gadin gidan nasu ya taimaka masa suka maidashi kan gado, saboda kusan yasan da matsalar Dr nura yasa baiyi wahalar kaishi asibiti ba ya bubbud'a wadrobe d'insa dake jikin bango ya ciro first-aid d'insa ya d'auko wasu allurai yayi masa don a tsammaninsa waccan matsalarce ta matsanancin ciwon kai da yake fama da ita idan ya matsawa kansa da tunani, kafin kace me, tuni wani irin nauyayyan bacci ya d'aukesa, bai farka ba sai kusan qarfe sha biyu da rabi, yana farkowa bakinsa d'auke da baffa cikin wata irin murya mai qarfi da zata tabbatar da cewa yadawoma tunaninsa yana bin ko ina da kallo.....





*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[11/14, 22:52] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___98πŸ’Ž

Da sauri abokin nasa dake zaune cikin d'akin gefe yana daddanna laptop d'insa ya tureta gefe yayo kansa tare da dafa kafad'arsa, cikin harshen turanci ya shiga tambayarsa lafiya?, Meke faruwa dashi ne?, meye baffa da yaji yafad'a?, dama shi d'an qasar Thailand ne babu yaren daya iya inba nasa ba sai kuma yaren turanci.

Wani irin kallo Dr Nuraddeen yabishi dashi had'e da cewa.

"Baffa mean dady, dt's my father."

"oh! You mean father?, So why have you calling him?, what happened to your father!?"

"Nothing.." yabashi amsa ataqaice
kafin yafara qoqarin tunano abubuwan da suka faru ashekarun baya kafin zuwanshi qasar, a hankali yafara tunano fuskar mahaifinsa da mahaifiyarsa ranar da yaje police station ya iskota awani yanayi har zuwa abunda yafaru ranar da zai baro qasar da maganganun da yayi da baffansa kafin yatafi, anan tunanin matarsa Rashida data b'ata ya fad'o masa arai da sauri ya miqe kamar wanda aka tsikara yanufi inda wardrobe d'in kayansa suke, watso kayan qasa ya dingayi yana dube dube da alama wani abu yake bid'a, a hankali yake kiran sunanta yana fad'in.

"Rasheedah!πŸ’” Habibty!... habibty!!..habibty!!!."

A daidai wannan lokacin Rashida na kwance ita da 'yan jikokin nata hassana da hussaina, gama karyawarsu kenan ta watso masu ruwa suna faman yimata rashin ji shine tasakasu agaba tace sukoma bacci itama baccin takeji, dama tuntuni aka dawo dasu wajenta saboda cikin da batool ke dashi tsufo kuma rigingimunsu na damunta sosai ko kad'an basa bari tahuta shiyasa little ya tarkatosu ya maido wajenta itama gimbiyar tasa tasamu tad'an huta kona wata d'aya ne kafin ALLAH ya sauketa lafiya, taji tsikar jikinta na tashi da wani irin fad'uwar gaba da bata tab'a jin irin saba, kwatsam taji habibinta gaba d'aya yau ya dawo mata arai, cikin wata irin rud'ewa da rashin kuzari ta tashi zaune tana fad'in,

"habiby!, habiby!!..meyake faruwa da kaine?, hasbunallahu waniimal wakeel, tabbas akwai abunda ke shirin faruwa dakai, jikina nafad'amun haka innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun."

Muryar yaran da dama basu koma baccin ba tajiyo ta bayanta suna tafi da hannuwa suna zagayata had'e da cewa.

"Habiby!.habiby meyeke faruwa da kaineee." Sun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login