Showing 66001 words to 69000 words out of 260204 words

Chapter 23 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt

acikin barci, kasa cewa uffan yayi har saida Inna Bilkisu dake tsaye cikin rumfarta tana sauraronsu ta matso wajen ganin yanayin daya shiga ta dafashi tana fad'in. "Karka kuskura ka amince da wannan soki burutsun na muneera kasan halinta da shirme, idan kuma har gaskiya take fad'a to kada ka tsorata domin da wannan tsoron naka za'ayi amfani wajen cutar da kai da kuma matarka kayarda ba mai yimaka sai ALLAH kuma Babu wanda ya isa ya cutar da kai sai abunda alqalamin qaddara ya rubuto akanka, maza kawuce kaje wajen iyalinka ba abunda zai sameku in sha ALLAH tunda kun riqe ALLAH, sharri shi Kuma d'an aikene duk inda kaje zai dawo ya sanar maka."

Taqare maganar tana kallon Inna ruqayya da tsabar kunya tasa tayi wuri wuri da idanuwa tana faman susar wuyanta.
Wasu zafafan hawaye yaji son zubo masa wai ace qiyayyar da mahaifiyarsa keyima matarsa har takai ga za'a iya had'a baki da ita acutar mashi da ita don d'ai cikar burin wasu, cikin zafin rai ya dubi Inna Bilkisu yace. "Inna Bilkisu me yarinyar nan tayi masu da suke nema su cutar da ita, nine fa d'ansu duk wani abu na mataki daya kamata su d'auka akaina ya dace ba itaba." Girgiza kai Inna Bilkisu tayi had'e da cewa.

"ALLAH dai ya kyauta, kawai kashiga ciki in sha ALLAH babu abunda zai sameta."

"Munafuka! aikin kenan ko yaushe sa ido, to Ina ruwanki tunda duk abunda akayi d'in da sanin mahaifiyarsa ita data haifesa, meye naki nasa baki, ke kuma shegiya mai baqin baki kamar aku da yaushe akayi haka? wato ke uwar soyayya zaki qaqaba mana sharri tsakar rana, tashi muje yau sai kin gane kurenki" irin borin kunyar nan Inna ruqayya tafara wud'annan suruttan had'e da rufe muneera da duka tana janta,

"Dakata Inna ruqayya! ku gaggauta zuwa kusa a kwance qullin da akayi maku akan matata idan ba haka ba duk abunda yafaru da ita to sai nayi shari'a daku.." kafin yarufe baki yaji saukar wasu zafafan marora har biyu a fuskarsa, Yaya hawwa ce da tun d'azu da taji muneera ta sako baki tana zuba tafito tayi tsaye tana qare masu kallo ta sakar masa wud'annan marora bazato ba tsammani, cikin d'aure fuska da rashin tsoron duk abunda zaije yadawo tace
"Don buhun ubanka dake kwance anyi qullin kuma baza'a kwance ba kayi duk abunda ka iya, inkaga dama kaje koton duniya ni hawwa bana tsoron uban kowa akan wannan tsigalalliyar yarinya bare daka auro mani, Kai nifa nagaya maka natsani matarnan tun wuri ka rabu da ita ko agaban idanuwanka insa ta walaqanta, shashashan banza da wofi har kace zakayi shari'a damu akan bare." tunda Nuraddeen ya soke kai qasa bai d'ago ba sai hawaye dake faman kwarara daga idanuwansa, yarasa wannan wace irin qiyayya ce mahaifiyarsa keyi ma Rashida da har Bata shakkun kowa akan zata iya illatata.

'Dago kansa yayi yana kallon Yaya hawwa yace. "Innar mu kiyi hak'uri, aurena da Rashida muqaddirine daga ALLAH, Ina sonta sosai shiyasa nakasa haqura da ita tun farko, don ALLAH ko donni ki daure kisawa zuciyarki soyayyarta, inada yaqini akan zakiyi alfaharin samunta a matsayin suruka, kigujewa wannan mummunar al'adar da kike tunanin daidace kada ta jefaki cikin fushin ALLAH."

"To saketa idan kana so kada nashiga cikin fushin ALLAH, idan bahaka ba nayi maka baki ka lalace." Taqarasa maganar tana gyara tsayuwarta da d'aurin zanenta,

"Haba Yaya hawwa meyayi zafi haka keda d'anki, ai idan kikayi kuskuren yimasa baki damuwar akanki zata fad'a, don ALLAH da girmansa kiyi hak'uri kibar yaronnan tunda yana son matarsa, yaran zamani da kike gani bad'ai suke dana da ba zaifi kibarsu suyi rayuwarsu yanda sukesu ke Kuma iya naki kibisu da addu'a," Inna Bilkisu tafad'a tana kallon Yaya hawwa cike da girmamawa.

"Bilki."

"Na'am Yaya hawwa."

"Bilki." Yaya hawwa ta sake fad'a akaro nabiyu tana kallonta, itama ta sake amsa mata kamar d'azu.

"Ya isheki haka babu ruwanki da d'ana, kifidda bakinki a wannan maganar saboda ba huruminki bane, ni nahaifi d'ana baruwanki ko yankasa zanyi shishshigin naki ya isa haka kina jina, idan kuwa ba haka ba zan zageki tass awurinnan nayaga maki rigir mutunci ba abunda yadameni, ke kike da abun fad'i agari bani ba don haka bar wajen nan tun wuri kinaji na ko?"

"ALLAH yabaki haquri." Inna Bilkisu tafad'a tare da barin wajen zuciyarta cike da tausayin Nuraddeen, wata irin gud'a Inna ruqayya tasaki had'e da cewa, "su uwar gulma andaiji kunya idan ansanta, sai aja tsomakaran qafafuwa asani inda akayi yau shishshigi baiyi rana ba." Bata tankata ba tawuce abunta Yaya hawwa tajuyo tana kallon gefen da Inna ruqayyace take tace.

"Ai kece babbar uwar gulmar kuma zan dawo ta kanki."
"Kai nadawo gareka zaka saketa ko kafiso sai naga walaqantata agidannan."

"Innar mu don ALLAH kada kirabani da Rashida Ina matuqar sonta."

"Maida son akan waccan mai idanuwa kamar na mujiya koba komai 'yar uwarka ce" Yaya hawwa tafad'a tana nuna muneera dake jingine ajikin k'arfen rumfa ta takure waje d'aya, wani irin shu'umin murmushi Inna ruqayya ta saki tana ayyana abubuwa aranta, cikin katsa tsawa taji tace masa.

"Ka saketa nace.." duqewa yayi agabanta yana fad'in "innar mu kiyi hak'uri bakina bazai iya furta wud'annan kalaman agareta ba."

"Bazaka sake tab'a saina tsine maka?." Tafad'a tana qoqarin bud'e baki ta tsine masa, da gudu Rashida dake lab'e tafito ta durqushe agabanta itama tana hawaye.

"Don ALLAH kada ki rabamu innarmu, kifad'i duk abunda kike so zamuyi amma kada kirabamu ko don albarkacin abunda ke cikina."

Rashida tafad'a tana kuka, wani irin mugun kallo yaya hawwa tabita dashi tana kallon yanayinta da d'an cikin daya taso kad'an ajikinta kafin tace....





*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___32πŸ’Ž

Buhun uba mezan gani haka?, Munafukan ALLAH dama cikine dake ake yimani rufa rufa agidan nan? tirqashi to idan tunaninki yabaki cewa wai cikin dake jikinki nada wata kima ko daraja awajena da har zai iya dakatar dani daga qudurina to kinsha qarya, dake har wannan abun dake cikinki bana sonku bana qaunar ganinku, don haka kai kasaketa kaji nafad'a maka kafin raina yab'aci" Yaya hawwa tafad'a cikin zaro idanuwa tana kallon Nuraddeen da izuwa yanzu gaba d'aya qasusuwan jikinsa sunyi sanyi, ga wani irin zazzab'i daya ji yana shirin taso masa, a hankali ya d'ago kai bakinsa na rawa yace. "Innar mu kidubi girman ALLAH kada kirabani da Rashida, wlh zan iya mutu idan kika rabani da ita, nayarda bakya son Rashida amma abunda ke cikinta bai kamata ki k'isa ba saboda jinin kine kuma jinina."
Tana bud'e baki tayi magana taji muryar baffa da tun d'azu yake yaqar zuciyarsa dake Shirin mutuwa ta sanadiyar raunin daya samu tamaidasa marar amfani aduniya, bayan da rayuwarsa ba mutuwa yayi ba cikin qarfin hali da jajircewa da kuma miqa dukkanin yaqininsa ga ALLAH akan zai iya abunda yasawa ransa yafara qoqarin rarrafawa yana dafa bango, addu'a yake maimaitawa azuciyar yana ambaton dukkanin sunayen ALLAH abakinsa yashiga bin bango yana fad'uwa yana tashi, wani azababben ciwo yakeji na qara taso masa tun daga kan qugunsa har zuwa tsakiyar qasan tafin qafafuwansa amma haka yaci gaba da takawa saboda rad'ad'in da yakeji da ciwo azuciyarsa yafi ciwon da yakeji yanzu atattare dashi har ALLAH ya kawosa inda zasu iya ganinsa, fad'uwa yayi zaune zufa na tartsikke masa tako ina ajikinsa yana fitar da lumfashinsa sama sama, ji sukayi cikin d'aga murya baffa yace.

"Karka kuskura kasaki matarka Nuraddeen ko bana raye aduniya, ke kuma d'anki ne bazan hanaki kiyi duk yanda kike so dashi ba amma Ina so kisani aduk lokacin da kikayi nasarar sa Nuraddeen yasaki matarsa to kisani ranar nima babu aure tsakaninmu kije kema na sakeki." Afirgice yaya hawwa ta d'ago kai tana kallonsa jin kalaman dake fitowa daga bakinsa cike da mamaki, shikuwa Nuraddeen duk da babu wani qarfi ajikinsa da gudu yataso yayo wajen mahaifin nasa da shed'arsa kefita sama sama batare daya tsaya fahimtar maganganun dake fita daga bakin saba, fuuuu.. Yaya hawwa tayi tawuce sashenta ranta ab'ace, ko kad'an bata damu da yanayin data gansa ba balle tayi tunanin taya akayi yazo wajen, amma gaba d'aya yara da manya dake gidan sunyi mamakin ganin baffa a wurin batare da kowa ya riqosa ba, kansa suka taru hadda muneera dasu Inna ruqayya ana yimasa sannu duk da Inna ruqayya bakad'an taji zafin bayyanarsa awajen ba saboda yanda ya b'ata mata masu tsarin, Rashida kuwa tunda tajuyo takalli baffa daga durqushen da take shima yana kallonta tayi murmushi lokaci d'aya kuma hawaye na yimata kara kaina a fuska kasa tashi tayi har saida Inna Bilkisu tazo ta riqata ta tashi tana mai godiya ga ALLAH daya hana faruwar abunda Yaya hawwa taso faruwarsa.

Wajen suka nufa lokacin Nuraddeen ya rungume Baffa yana kuka cike da tagwayen farin ciki da suka lullub'e masa zuciya, na farko ganin akaro na biyu ALLAH yasake bawa mahaifinsa damar sake taka qasa da qafafuwansa na biyu kuma yanda ALLAH yakawo masa ginshik'in daya shiga tsakanin hana faruwar rabuwarsa da masoyiyarsa, shi kansa baffan kuka yakeyi Amma nasa na takaici da baqincikin irin matar da ALLAH ya jarabcesa da ita, d'ago kansa yayi yana shafa kan Nuraddeen yace.

"Kayi hak'uri dukkani tsanani yana tare da sauqi, Alhamdulillah wama sha'a fa'ala."

'Dago kai Nuraddeen yayi yana jin wani sanyi azuciyarsa ya kalli Rashida da har lokacin kuka takeyi ya girgiza mata kai alamun tayi shiru tare da sakar mata murmushi, hannu tasa tagoge hawayenta itama tana mayar masa da nata sannan tajuya tashiga sashensu ta d'ebo ruwa a joke, duqowa tayi tana karanta addu'o'in data iya had'e da tofawa tabawa baffa, murmushi yayi yakarb'a ruwan yana saka mata albarka yasha sannan ya miqawa Nuraddeen sauran yace ya shafa masa a qafafuwansa, bayan mintuna kad'an baffa ya gwada qoqarin tashi da sauri Nuraddeen ya miqa hannuwa zai riqosa ya dakatar dashi, su dai mutanen gida duk suna nan tsaye cirko cirko suna kallon ikon ALLAH, duk da baffa najin zugi da zafi atattare dashi hakan bai hanasa gwada miqewar da kansa ba yana cije baki saboda zugi da rad'ad'in da yakeji har ALLAH ya taimakesa ya miqe da kansa, rufe idanuwa Rashida tayi hawayen dake cikin idanuwanta suka samu damar zubowa sannan tabud'e tana fad'in "Alhamdulillahillazi bini'imatihi ta timmusswalihat, ya mujibudda'awat, Alhamdulillah kathiran."

Ihu yaran gidan suka fara suna tsalle ganin yanda baffa yafara tafiya ahankali yana dafa bango batare da anriqasa ba, juyowa Nuraddeen yayi ya rungume Rashida agaban kowa yana fad'in.

"Ke alkhairice arayuwata da kuma ta mahaifina, ya ALLAH kada kabani damar shaqar lumfashi a inda babu habibty d'ina."

Cike da jin kunya Rashida ta notar da kanta qasa tana murmushi tare da d'an turesa daga rungumar daya yimata ta juya tabar wajen cike da farinciki azuciyarta."
Juyawa yayi shima yabi bayan yaran dake biye da baffa suna tafi da ihun murnar ganin ya samu lafiya,

Suna barin wajen inna ruqayya taja wani irin dogon tsaki cike da takaicin Rashidar babu babban baqin cikinta yanzu kamar cikin da tagani ajikinta wanda tamada yaqinin shizai qara zamowa shamaki kuma katangar da zata rugujewa 'yarta samuwar nata farincikin, cike da son muzanta Rashida daidai lokacin da ta aza k'afarta zata shiga sashenta tace "Aikin banza da wofi, zuri'ar 'yan tsibbu da mayu da gani anyo gadon buge bugen qasa."

Tsaye cak Rashida tayi tana sauraren kalaman da take jifarta dasu kafin tashigewarta batare da tajuyo ba balle ta tankata zuciyarta fad'a mata kada ta tab'a damar da kanta don tace mata haka, dama shi d'an adam haka yake duk abunda yake aikatawa sai yayi tsammanin kowama yana yinsa, konkad'an baici ta damar da kanta ba tunda tasan sunan da tayi mata da ita yafi dacewa ba itaba.

Da gudu muneera tabiyo bayan Rashida har zata aza qafarta ta shiga sai tatuno jan kunnen da ya nura yayi mata.

"Rashida" muneera takira sunanta cikin sanyin murya, juyowa tayi tana kallonta, ganin tana son yimata magana amma takasa shigowa tace. "Aunty muneera shigo mana."

"A'a bazan shigo ba ya nura na iskoni sai ya maidani tamkar jaki yasha Kara."

Murmushi Rashida tayi tare da dawowa bakin qofar inda take tsaye tace, "to gani aunty muneera" susar kanta tashigayi kafin tace, "naji Inna tana cemaki wai zuri'ar 'yan tsibbu saboda kinyi wani abu aruwa kinba baffa yasha yawarke har yana tafiya, don ALLAH da gaskene shi kikeyi?" Murmushin da bai kai cikiba Rashida tayi tare da gyara tsayuwarta sannan tace "A'a muneera ba gaskiya bane, ni bana tsibbu kamar yanda Inna ruqayya tafad'a maki balle iyayena ko zuriarmu, Amma muna roqon ALLAHn daya halicci cuta kuma yayi maganinta cike da yaqini kuma ya karb'a mana, adduace nayiwa baffa d'azu don yasamu sauqin rad'ad'in ciwon da yakeji sai aka dace da ijaba ta sauka bayan jimawarsa azaune yana shan magani da kuma amfani da addu'o'i Wanda inada tabbaci akan tasirinsu ne yanzu yazamo silar samun sauqinsa bayan natofa masa addu'a aruwa yasha."

"Laaa ashe Inna qarya takeyi, don Allah Nima zakiyiwa ya nura aruwan yasha sai ya aureni." Muneera tafad'a had'e da matsowa kusa ga Rashidar bayan ta d'an sassauta murya,

Saida Rashida tayi dariyar da duka haqoranta suka bayyana sannan tace, "a'a aunty muneera bazan yimaki ba domin duk son da kike yimasa baikai adadin wanda nake yimasa ba, saidai Ina baki shawara akan kema kije kiroqawa kanki ALLAH daya baki shi, amma nidai bazanyi ba." Taqare zancen cike da mamakin sakarci irin na Rashida,
Ture lab'b'a muneera tayi cike dajin haushinta tajuya tabar wajen tana fad'in "'yar baqin ciki, ALLAH ko bakyaso saina auri ya nura, bazaki zauna ke kad'ai ashiyar nan ba tundanima Ina qaunarsa, shegeyw mai tsawo kamar na iccen rama" dariya Rashida tayi sannan tawuce abunta had'e da turo qofar.

Na'ima da Aisha ma yaran Inna Bilkisu dake zaune dawowarsu daga wajen niqa kenan don duk abunda yafaru basa nan akayi suma suka sawa muneera dariya jin abunda yafaru tsakaninta da Rashida, kansu tayo tana susar kai suka tashi suka ruga aguje tabisu tana zunduma masu zagi dama Inna Bilkisu nacan d'akin baffa ana murnar samun lafiyarsa.

Ita ko Inna ruqayya sashen Yaya hawwa tanufa ta iskota cikin d'aki in tayi nan tayi can tana daddagar hannu had'e da cizon baki tana girgiza kai, "hmmm yanxu fa shikenan bakida abunyi yariga d'aya jawo maki reni ga yarinya, ya zubar maki girma agaban idanuwan d'anki sai yanda sukaga dama zasuyi acikin gidannan." Ina ruqayya tafad'a tana watsa hannuwanta baya tariqesu tana jiran amsar da zata fitowa daga bakin Yaya hawwa don tasan yanda zata sake tunzurata idan ta zubar da maka manta a fusace Yaya hawwa tajuyo had'e da cewa "inaaa wallahi qarya ne, bai isa ba matuqar Ina raye, ai fad'a da aljani sai anshirya kuma duk lalacewar bushiya tafi qarfin a takata da qafa koda kuwa da takalmi ne, ni hawwa ban tab'a sawa raina abuba nakasa, atarihin zuriarmu ba'a tab'a sakin mace ba don haka baza'a fara akaina ba, badai ya hana nura ya saki matar saba, to ni kuma zansa matar nurah tabar nura nahar abada koda hakan na nufin zan mutu wlh sai tabar cikin gidan nan ita d'in banza da wofi." Murmushi Inna ruqayya tayi kafin yace, "ahh to Nima dai shi nagani, wallahi idan bakiyi da gaske ba saita rabakinda d'anki da mijinki, yanzu haka fa Ina kallon wasu surqulle da tayi da wasu sabbatu ta tofa masa aruwa yasha sai gashi ya tashi da qafarsa, ke wannan yarinyar itama Ina ganin da nata shirin take don ko yayan Bata barsa ba tunda kikaga kimanin watanni goma sha yana zaune duk rigima da fitintinun da akeyi agidannan bai tab'a tasowa ba sai yau don yaji ance a saketa, aikam kema kinsan sedai ALLAH ya kayauta Amma tagama da Yaya balle nura."

Takai qarshen zancen had'e da fashewa da wani kukan munafucci,

"Ke ruqayya fita, fita kibarni inji da abunda ke damuna don yau dole in koma wajen malan bakada imani, wannan shegen cikin dake jikinta dole adakatar da zuwansa duniya da ransa kafin ita Kuma musn nayi da ita."

"Gaskiya kam Yaya hawwa, ai yarinyar nan wlhi tagama tona mana asiri."

"Mtss..zan zageki ruqayya kitafi nace, akwai mai tona maku asiri kamar hasararriyar yarinyar dake gabanku, ai bakiga tonon asiri ba sai ranar data bud'e baki tafad'a duniya cewa iyayenta shashashune da basu san ciwon kansu ba tukuna, ni nafara tunanin bazan iya had'a zuria da itaba a haifo mun jika sak aku kuturu da gwalmammin qafafuwa."
Yaya hawwa taqare zancen tana turo Inna ruqayya waje had'e da rufo qofar d'akinta. Tsaye Inna ruqayya tayi tana ayyana kalar abunda zata yimata duk ranar da burinta yacika akan wannan walaqancin da take yimasu ita da 'yarta sannan tawuce ranta ab'ace, d'akin da baffa yake tanufa fuskarta sake don kar afahimci yanayin da take ciki, lokacin mutane sun taru sai shigowa sukeyi suna fita ana yimasa barka da arziqi, baffa Ali da baffa Usman suma na zaune gefe fuskokinsu d'auke da farinciki duk da shi baffa Ali bahaka yaso aransa ba, yaso sai sungam shirinsu tsaf Mai faruwa tafaru koda zai samu lafiya gudun kada ya dakatar masu da shiri, yaqe kawai yakeyi amma haushi da takaicin taahin d'an uwan nasa yayi masa katutu azuciya, shi kam baffa yana tsaye yana gaggaisawa da mutanen dake shigowa,
Kallo d'aya Nuraddeen yayiwa Inna ruqayya ya d'auke kai had'e da barin d'akin don yanzu shi ko ganinta baya son yi, bayan an watse yarage su kad'aine mutanen gida zaune baffa sai faman zagaya falo yakeyi yana yiwa ALLAH godiya, kallo d'aya zakayi masa ka fahimci tsantsar farincikin da yake ciki saboda ynda ya bayyana a fuskarsa.

Wata irin muguwar dariya sukaji baffa Ali ya kwashe da ita harda tuntsirawa yana nuna baffa cike da isgilanci sannan yace.

"Ho.ho.ho Yaya kace yau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login