Showing 45001 words to 48000 words out of 260204 words
Chapter 16 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt
muce."
Sosai su aunty marwiyya sukaji dad'in kalamanta kuma sun samu 'yar natsuwa akan d'azu, mik'ewa sukayi da zimmar fita don tuni sauran mutane da yaran sunfita sukad'ai ake jira Rashida tarik'esu tanata kuka, duk qarfin zukatansu suma saida suka zubar da kwallah saboda tausayinta, so suke sutafi amma tariqesu gam saida su kareema sukazo suka b'anb'areta ajikinsu sannan, riqeta sukayi suna lallashinta su kuma suka wuce inna bilkisu na biye dasu kowacensu na k'walla,
Suna fitowa matar baffa Ali ta toshe hanci had'e da rangad'a uwar gud'a tana fad'in, "wayyo duniya budurwar wawa, wai iyayen amarya da kuka wannan ai anyi abun kunya, koda yake qila amaryar tasu ta gagara yi abunka da yaran zamani shine su suka yimata." Wucewarsu sukayi suna tir da halin fitinanniyar mat irinta inna balkisu nata basu hak'uri har bakin k'ofar gida, sunaji tana fad'in.
"Munafucci dodo akan wasu yake qarewa" Wanda bako shakka sunsan da inna balkisun take...
*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*ππ
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πΆββοΈπΆπ»ββοΈ *SANNU SANNU*πΆπ»ββοΈπΆββοΈ
π _Bata hana zuwa..._π
_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπ*
_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*π
_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*π
*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*π
*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*β€οΈ
Page___21π
Murmushi yayi don yakula da kallon da take yimasa saboda hasken wutar lantarki data haskesu lokacin da suke qoqarin shiga toilet d'in, seda yashiga sannan ya sake mik'a mata hannusa tariqo ya shigo da ita cikin toilet d'in, alama yayi mata data iso gaban fanfon dake tsaye ciki irin na qarfe d'innan da xaka gani a tsakiyar gida ko anguwanni ana d'ib'ar ruwa, ahankali tafara takowo kanta na sunkuye a qasa, cikin takun da baiwuce biyu zuwa uku ba ta isa gaban fanfon had'e da duqawa wajen, d'ayan hannunta ta d'ora saman kan fanfo zata kunna taji shima ya d'ora nasa akai da niyar kunna mata, d'ago kai tayi ta kallesa suka had'a ido ya sakar mata murmushi, da sauri ta sinne kanta qasa itama tana mayar masa da murmushin, ahankali yafara juya kan fanfo har lokacin hannusa na saman nata, ganin ruwan sunfara zubowa yasa ta tara d'ayan hannunta tana d'ibar ruwan tana kuskure bakinta had'e da wanke fuskarta, qoqarin jaye hannunta tayi yariqesa gam tamkar wanda za'a kwacewa hakan yasa ta kasa tashi tayi duqenta awurin, tanaji yana wasa da hannunsa akan nata kafin yacirosu akan fanfon bayan yasa d'ayan hannun nasa ya kashe batare da yasaki hannunsa sake riqe da nata ba,
Bayan sun fito toilet yanufi falo da ita ya zaunar da ita qasan center carpet d'in dake shimfid'e ya d'an tura center table d'in dake tsakiyar don sud'an samu isashhen fili da bazasu matsuba, ledar daya shigo da ita yaje ya d'auko tare da shiga kitchen ya d'auko wani d'an k'aramin tray da cup d'aya ya d'aurayosu ya kawo agabanta yana fad'in.
"Washh amarya bakya laifi." yana kallon yanda ta noce kanta qasa tana wasa da 'yan yatsun hannunt, riqo hannun yayi yanabin 'yan yatsun da kallo had'e da cewa.
"Habibty lallen nan yayi kyau sosai gashi garin wannan wasar taki kina nema ki gogemunshi da wuri haka."
Tana qoqarin janye hannun yayi 'yar dariya tare da yimasa kiss wanda yasa Rashida jin wani yanayi atattare da ita, ja baya tayi kad'an kafin ya saki hannun yana mai basawa kamar baisan me tayi ba, naman ya zube masu a plate had'e da ciro gorar fresh youghout d'in acikin leda ya tsiyaya a cup,
"Habibty matso kici abinci nasan bazaki rasa jin yunwa ba." Yafad'a tare da nufo bakinta da yankan naman daya d'auko, kauda kanta gefe tayi alamun bazata ciba shima yasake maida hannunsa a gefen yana fad'in.
"Haa mana." Kamar yanda akeyiwa yara harda d'an bud'e bakinsa murmushi tayi tare da girgiza masa kai tace.
"Naqoshi malamina."
Harararta yayi da wasa kafin yace,
"Ai baki isa ba.maza kibud'e bakinki bana son musu Kuma."
Ganin ya d'aure fuska yasa tabud'e bakin ya tura mata naman ciki yana fad'in "gud gel" haka yayita bata tanaci har naman yakusa qarewa, riqe masa hannu tayi lokacin da yasake d'auko wani yankan cikin marairaice fuska kamar zatayi kuka tace.
"Kayi hak'uri malamina naqoshi tun d'azu ci kawai nakeyi saboda kace baka son musu amma ALLAH idan naqara wani akai yanzu zan iya yin amai."
"Kin tabbata."
"Sosai malamina"
"Ok bari nima na tabbatar idan har da gaske kikeyi" noce kanta qasa tayi ganin yasake matsowa kusa da ita gabanta na dukan uku uku taji ya d'ora hannunsa saman cikinta da saurin ta rintse idanuwa yanda yake shafa cikin ahankali yasa dariya ta soma zomata da sauri tariqe hannun tana fad'in.
"Don ALLAH kadena, ALLAH kayar da Dani na qoshi sosai" tana 'yar dariyar da saida haqoranta suka bayyana.
"Eh to na amince amma har yanzu da akwai inda bai ida cika ba, ungo wannan ki shanye saiki cike wajen kinji ko d'alibata."
Yafad'a tare da mik'a mata cup d'in daya tsiyaya fresh youghout d'in, ba musu takarb'a tunda yariga yafad'a mata cewa baya son musu shi kuma yafara cin sauran naman daya rage yanayi yana kallon yanda take kurb'arsa ahankali, murmushi yayi don gaba d'aya komai na yarinyar na burgesa musamman yanda take motsa bakinta, nad'e takardar naman yayi bayan ya cinye ya ture ta a gefe tare da jawo sauran da kecikin gorar yafara sha shima, saida ya kusa shanye sa sannan ya ajiye gorar da sauran da ke ciki ko rabin gora beyi ba a lokacin itama ko rabin nata bata sha ba, miqewa yayi ya d'auke late d'in tare da ledar naman da kuma gorar youghout d'in daya rage ya nufi kitchen dasu, ledar ya kad'a a dosbin ya d'auraye plate d'in ita Kuma gorar ya ajiye a gefe don har lokacin ba'a cire fridge d'inta acikin kwali ba balle a jona,
A inda ya barta anan ya sake iskota zaune tana jujjuya cup d'in da sauran youghout d'in dake ciki, kallonta yayi had'e da cewa.
"Habibty dare fa yayi ko bakyajin bacci ne?"
Miqewa tayi taje ta d'auraye cup d'in tare da wanko bakinta shi kuma yawuce toilet don ya watso ruwa, koda tadawo falon tajiyo motsin ruwa a toilet komawarta inda take tayi ta zauna tana kallon tsarinfalon nata da kayan da iyayenta suka zuba mata, sosai ta jinjina masu sabo kyan kayan da kuma yanda aka qawatashi da frem masu kyau kalar coppy colour, kujerunta da labulayenta duka suma kalarne sai 'yar madai daiciyar tv dake ajiye saman tv stand da qatuwar flower acan gefen falon daga kudu tana wannan tunaninne taji ya shigo falon saye da doguwar jallabiya yace
"Habibty je kiyo arwala muyiwa ALLAH godiya daya nuna mana wannan ranar."
Bayan tafito ya jasu sallar raka'a hud'u sannan ya sallame, addu'o'i yayita kwararo masu na samun zama lafiya da kuma zuri'a masu albarka, bayan yagama yajuyo yayi mata tambayoyi akan abunda ya shafi tsarki da kuma wanka, yasha mamaki sosai yanda yaji tabashi amasarsu yanda ya kamata hakan yasa baiyi zurfi ba wajen yimata tambayoyin saboda kusan qarfe sha biyu harda rabi tayi, miqewa yayi ya nufi tsakar gidan ya kashe fitila sannan yadawo cikin falo itama ya kashe har lokacin tana nan zaune gabanta na fad'uwa duk da dai bata san gaskiyar abunda zai biyo baya ba Amma keb'antarta daga ita sai namiji awake d'aya abune da Bata tab'a yiba don haka dole tsoro da fad'uwar gaba su kamata, tana jinsa yana kiran sunanta tamakure a gefen kujera jikta na rawa.
"Habibty taso muje mu kwanta." Yafad'a yana qoqarin had'iye dariyarsa ganin yanda ta sake shigewa can bayan kujera,
"Habibty, habibty..." yaci gaba da fad'a ahankali yana qoqarin isa inda take, a hankali hannunsa yakai saman kafad'arta tazabura tana shirin yin qara ya jawota ta fad'o jikinsa, "meye haka habibty? Nifa mijinkine da ALLAH ya halatta maki kiyi duk yanda kikeso dani da kuma gangar jikina haka kema ya halasta mani ke da duk wani abunda ke tattare dake, Ina sonki kina sona, menene abun tsorata da juna, karki manta nayi maki alqawarin zan kula dake Kuma zan baki farinci mai d'orewa matuqar Ina raye, zan soki soyayya mafi girma aduniya, irin soyayyar da zatasa harna mutu bazaki manta dani ba, Rashida kece duk wani bugun lumfashina don haka kiyarda dani bazan tab'a bari kicutuba aduniya, Ina so matuqar zuciyarki ta amince da kalaman dake fitowa daga qarqashin zuciyata ki kwantar da hankalinki muje mu kwanta abunmu kinji ko?."
Ahankali ta d'aga masa kai jikinta narawa jin yanda nasa jikin ke gugar nata tana qoqarin zamewa, riqeta yayi sosai sannan ya d'agata cak ya d'auketa yawuce uwar d'aka da ita, bai direta ko ina ba sai tsakiyar gadon ya zagaya ta gefe yacire jalabiyar dake jikinsa had'e da kashe fitilar ya hau saman gadon shima, jawota yayi ajikinsa yaji ko Ina rawa take na jikinta, ahankali ya sake mannata aqirjinsa sosai cikin kwantar da murya ya rad'a mata a kunne.
"Don ALLAH kinatsu habibty? Nayi maki alqawarin bazan cutar dake ba ko kad'an, kinga gidan yawa muke kada muyi abunda zaisa aganomu kinji ko?"
A hankali ta d'aga masa kai cike da tsoro hawaye na zubo mata,
"Kin amince?."
Nanma d'aga masa kai yasakeyi, cike da jin dad'i yakai bakinsa a goshinta yayi mata kiss, don aransa ya raya matuqar Bata amince ba bazai tab'a yimata dole ba saboda yanayin inda suke ciki zai iya zame mata abun gori idan har wajen tilastata yasa tayi abunda zaisa ajiyosu, ita kuma ta amsa masa ta amincene atunaninta na yakwana d'akin da ita badon tasan meye ainahin abunda yake roqon amincewarta aciki ba. ( _Karku manta Rashida yarinya ce, ba lallai bane don ta furta kalmar aure takeso kuma tasan me ake aikatawa acikin aurenba, batada wasu cikakkin abokanai inba meenah ba kuma a qauye ta tashi ba dolene ace tanada wayewar sanin ko meye ba don haka kada kuyi mamakin jin nace batasan me yake shirin yimata ba da har yake neman amincewarta ba da Kuma yanda ta tsorata har dasu rawar jiki saboda abune da bata tab'a yiba arayuwarta balle ace tasaba, tanada ilimi akan aure amma batada ilimin auren a aikace ko zahirance, sab'anin 'yan matanmu na yanzu da tun kafin akai yarinya tasan meza'a aikata_).
Bakinsa ya d'ora akan idonta d'aya yayi mata kiss haka ma ga d'ayar kafin ya gangaro ga abu mafi burgesa atattare da ita shine bakinta ya d'ora nasa akai da sauri tajaye tana hawaye,
"Don ALLAH kadena bana so?"
"Kiyi haquri habibty wannan shine fa auren." Bil haqqi ta wangame baki zata saka masa kuka yayi saurin rufesa da nasa yana tsutsa ahankali, tun tana qoqarin kwacewa har ta gaji tafara lumshe idanuwa tana karb'ar saqon yanda ya kamata, jinta tayi awani baqon yanayi tare da kasa attaka komai saboda yanda jikinta ya mutu had'e da yin sanyi, hakan yabasa damar cigaba da aika zafafan sak'onnin da zuka dad'e yana son isarwa azuciyarta hannayensa kuwa nak'ara taimaka masa akan dukkanin muradansa naganin ya maida ita cikakkiyar mace a wannan daren, sosai take amsar saqwanninsa tana fitar da lumfashi a hankali, cikin tausayi da nuna jinqai yafara qoqarin sarrafata had'e da karanto addu'ar saduwa har ya cimma burinsa.
Kasancewar bai zomata cikin tashin hankali ba yasa yayi nasarar rabata da budurcinta duk dai shima kansa saida ya wahala wajen qoqarin samun hanya, Rashida kam tasha kuka sosai, tayi dana sanin furta kalmar aure takeso don har seda taroqesa a maidata makaranta zatayi karatu sosai, wannan abun ba kad'an yabashi dariya ba hakan yasa yahaqura duk da bawani jimawa yayi ba balle gamsuwa, saboda duk duniya bayada burin daya wuce Rashida ta samu cikakken ilimin boko kamar yanda take dana arabiya,
Wannan dalilin yasa yanaji yana gani ya haqura tare da komawa rarrashinta, da qyar yasamu taui shiru bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita, amma kallo d'aya zaka yimata kasan baccin bana dad'i bane,
Jin alamun gari yayi sanyi da iskan da ake kad'awa sosai yasa yafahimci ruwa za'ayi don haka ya gyara kwanciyarsa tare da jawota ajikinsa yanajin wata sabuwar sha'awarta na taso masa, murmushi yayi cikin farinciki da jin dad'in yanda yasameta sannan ya ja masu bargo suka lullub'a.
β’β’β’ β’β’β’ β’β’β’
Yaya hawwa kuwa yana fita ta tashi zaune had'e da jawo ledojin guda biyu tafara bud'e tafarkon, ganin naman ragone yasa ta turesa gefe tajawo dayar tabud'e, wahe baki tayi had'e da cewa
"d'an kwal uba ga naman kaza zaka bani na rago, duk da dai naga irin wanda nake so ne Mai kitse kasiyo."
Zaunawa daidai tayi tabud'e qafafuwanta tasa naman a tsakiya tayago naman kaza taci sannan ta d'auko yankan na ragon Mai kitse bayan ta birkid'eshi da yaji taci, haka tayitayi har ta canye naman ragon da kaza d'aya sannan tajawo gorar youghout d'in ta aza asama, wata uwar gyatsa tayi had'e da cewa
"d'an buhun uba, wato inana kwance turus kashige d'aka da mata kusha wannan uwar dad'in ni kuma ka had'ani da mai kitse kad'ai, yo waya fad'a maka shikad'ai nake so bana son ita wannan abar mai fika fikai.
Nad'e d'ayar kazar tayi ta tura aqarqashin filo tare da gorar youghout d'in d'aya, shi kuma sauran takoma ta kwanta tana sha tana suruttanta har bacci ya soma d'aukarta, can cikin bacci taji kamar ana Kiran sallar asuba da sauri tamiqe tanufi sashensu Nuraddeen tafara bubbuga qofar, kasancewar baaccin ya soma yimasa nauyi sosai shiyasa baiji ba saidai baffa Usman ne yaji qarar ana dukan qofa daga wajen sashen Nuraddeen da sauri yafito don ya zata shine, ganin Yaya hawwa tsaye bakin qofar yasa yaqarasa wajen yana murzar idanuwa cikin rage murya yace
"Lafiya Yaya hawwa kike buga masu qofa awannan lokaci?."
"Aiho Usman ashe kaima kafito, ja'irin yaro kaji har ankira sallar asuba bai fitoba shine nace Bari na tadashi don Karya makara" kallon sararin samaniya baffa Usman yayi kafin yace.
"Ikon ALLAH! To aike yaya ba'a isa kiran sallar asuba ba, qarfe uku da rabi yanzu ko baki duba agogo bane."
"Kace wlh, Niko naji kiran sallah yanzu shiyasa nataso." dariya yayi don ya fahimci zallar damuwane yasa kunnuwanta ke hakaito mata kiran sallah awannan lokacin, dariya suka jiyo shiyarsu baffa Ali wanda har da zai fito Inna ruqayya tariqesa ta hanasa fitowa.
"Wlh waccan yayar tashiga uku, mace baqin hali sekace gareta farau suruka, shiyasa naso muneera ta auresa don ta gyara mata zama wannan takurawa har Ina, fita batunsu baban yusufa koma ka kwanta." Tafad'a tana dariya had'e da kashe wutar d'akin,
Girgiza kai baffa Usman yayi had'e da cewa "ki koma ki kwanta Yaya hawwa idan asuba tayi zan tashesu."
"Asubar batayi ba kenan!"
"Eh" yafad'a tare da juyawarsa yakoma d'aki, Daren ranar kam kasa komawa bacci tayi in banda saqawa da kuma warwarewa azuciyarta babu abunda takeyi,
Baffa shima kansa abun dariya yabashi don duk abun dake faruwa akunnensa yanaji saboda alokacin shima ba bacci yake yiba, zaune take abunsa yana karatun al-qur'ani kafin yafara sallolinsa daga zaunen yajiyo bugun qofarta, rashin qafafuwa ya hanasa tasowa da sai ya riga baffa Usman fitowa, sosai matar tasa tabashi dariya ya d'aga hannuwa sama yana addu'a ALLAH ya shirya masa ita yaganar da ita kura kuranta tun wuri bai qure mata ba sannan yaci gaba da ibadunsa tare da roqawa d'an nasa samun dukkanin bud'i na duniya da zaman lafiya had'e da 'ya'ya nagari...
*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*ππ
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πΆββοΈπΆπ»ββοΈ *SANNU SANNU*πΆπ»ββοΈπΆββοΈ
π _Bata hana zuwa..._π
_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπ*
_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*π
_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*π
*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*π
*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*β€οΈ
Page___22π
Yaya hawwa kuwa har akayi kiran sallar asuba na farko idanuwanta biyu tanaji anfara kiraye kirayein sallar tamik'e had'e da azo qafarta bakin qofar d'aki kawai taji saukar ruwan sama ya kuccike ba zato ba tsammani don tun wurairan biyu da hadarin ya kankama iska ya taso ta ko Ina sai kuma daga baya ya kwanta hadarin kuma ya wargaje cikin ikon ALLAH nan take kuma da asubar ya sake had'uwa saiga ruwa, tsaye Yaya hawwa tayi kamar tafashe da kuka tana kallon sama, wata irin walk'iya akayo da tsawa alokaci d'aya da gudu takoma cikin d'akin tanemi waje ta zauna gefen gado idanuwa sunyi mata qululu, yau take jiran ad'auke ruwa gobe take jira amma sai sake sauka sukeyi kamar da bakin k'warya, hakan yasa kosu baffa Usman basu samu fita masallaci ba balle malan Nuraddeen ango sai dai kowanensu yayi sallarsa a d'aki tare da iyalinsa,
Nuraddeen kuwa saboda sanyi da qyar yasamu yayi wankan tsalki ba tare daya tayar da Rashida ba da sai faman yatsine fuska takeyi cikin baccin saboda babu ruwan zafi, sallarsa yayi sannan ya shiga cikin kicin d'inta ko zaiga inda aka ajiye rishow d'inta, cikin sa'a ya hango kwalin electric stove ya jawo had'e da cirosa daga ciki ya jona ga socket d'in kitchen d'in sannan ya ciro tukunya cikin kwalinta itama ya d'ora bayan ya d'an kara hannunsa saitin electric d'in yaji yafara zafi ya d'ebo ruwa ya zuba sannan yakoma cikin d'akin, gefen gadon ya zauna tare dasa yatsansa yana d'an shafa lab'b'anta, ahankali yaga tafara bud'e idanuwanta suka sauka akan nasa daya qura mata, suna had'a ido tayi saurin rufewa had'e da cuno d'an k'aramin bakinta ta kauda kanta gefe, dariya yayi kafin yace "haba ta malan nura fad'amun waya tab'amun ke kike juyamun kai haka." Shiru tayi batare data amsa masa idanuwanta na arufe, hannunta ya cire daga saman qirji da yake ta riqe bargon yana shafa lallen dake jiki a hankali tare da yimasa kiss, jaye abunta tayi da sauri tana fad'in "kadena bana so.."
Kafin tarufe baki taji ya had'e bakinsa da nata ya sakar mata wani irin sihirtaccen kiss. Idanuwanta ta lumshe tanajin tamkar na'urar jikinta ta d'auke ta had'e da dawowa.
"Morning habibty kin tashi lafiya?" Kad'a masa kai tayi tana tunani abubuwan da suka faru jiya tsakaninta dashi kawai saita tsinci kanta cikin matsananciyar jin kunyarsa, "taso muje kiyi wanka yafad'a had'e da miqewa, har zai