Showing 189001 words to 192000 words out of 260204 words
Chapter 64 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt
'yata yake neman lalatata izuwa tahanyar da aka samosa, meye dalilin kirana?, meyasa bazaki jawa yaronki kunnuwaba daya nisanta kansa da 'yatah?, meyasa bazaki lusar dashi cewa wutsiyar raqomi tayiwa qasa nisa?, meyasa amatsayinki na uwa bazaki zaunar dashi kinuna masa banbancin aya da tsakuwa ba?, oh! Wato kinaso yaronki ya zama kiyashi ja abunda yafi qarfinsa saboda son zuciya da sakarci irin naki, me kike so akiraki uwa ko kuma uwar kawai tunda kin kasa banbancewa d'anki tsakanin fari da baqi?, To bari nafad'a maki yayi kuskuren neman aure a inda bai dace da shiba kuma da sannu zan nusar dashi wannan kuskuren da yayi tunda ke kin kasa."
Tunda yafara magana Rashida batace dashi komai ba har saida ya dasa aya sannan tashare qwallan da suka zo mata, aduk lokacin da aka aibanta mata yaro sai taji wani qululu yataso azuciyarta ya tokare mata wuya, zafi da zugin da zuciyarta keyimata kuwa suke saka hawaye saurin kwaranya daga idanuwanta, murmushin qarfin hali tayi wanda saida ta tabbatar yaji sautinsa akunne sannan tace.
"Alhamdulillah daka fad'amun kowane irin mahifine kai batare dana b'ata lokacina wajen fahimtar dakai abunda nake da tabbaci ayanzu cewa bazaka tab'a fahimtarsa ba, sanin kima da darajar mutuntaka yasa nayi yunqurin kiranka don tunatar dakai girman qudura ta ubangiji akan abunda shi yake da iko akansa, amma yanzu nafahimci baka buqatar hakan!, Naji yarona bayada uban kmar yanda kace ko, bayada asali shima, yarona bayada nagarta da kima a idanun duniya musamman ga irinku to duka naji kuma nayarda da hakan, Amma Ina so kasani ayanzu yarona, shine rayuwar 'yarka!, shine kimar gidanka!, shine abun so ga dukkanin nakusa gareka!, yarona shine zab'in fatincikinka da kafi so aranka! Kuma shine wanda take alfahari dashi data jingina wanzuwar rayuwarta bisa samunsa!, Bana buqatar sanin abunda ke faruwa acikin gidanka domin 'yar taka da kake cewa yarona na bibiya tana tare damu, zuciyarta takasa amince mata ta zauna atare dakai saboda gazawarka wajen sama mata farinciki, hakan yasa tazo garemu cike da so da qauna kuma mun karb'eta hannu biyu dommu nuna mata yanda rashin uba ke iya samar da gata fiye da masu uba."
"Ka kwantar da hankalinka babu abunda zai sami 'yarka don nafahimci karazana da jin hakan, izuwa yanzu 'yarka na gab da isowa wajenka domin nasa yarona ya maido maka da ita, koba komai wannan inganci nasa da nagartarsa da duniya takasa ganewa kai ka ganota, sannan kasa aranka kausasan kalamanka basu isa susa infad'a maka waye ubansa idan har baka sani ba ko in rabasa da 'yarka domin nasan ko banyi hakan ba ina da tabbacin soyayyar da 'yarka keyi masa kawai ta isa tasa d'ana yayi nasara akanka wajen aure 'yarka, yawwa! Sannan naji kamar kace zaka nusar dashi kuskurensa ko? To Ina jiran hakan domin idan ka kuskura kayiwa d'ana wani abun ko kuma yadawo naga qwarzane ajikinsa to tabbas zan manta da cewa ni uwace in d'auko tsofaffin kayan da suka dad'e ajiye nasa don bimasa haqqinsa, Kuma Ina tabbata maka cewa idan nafara shari'a dakai bazan bari ba har sai na tabbatar da nima na nuna maka kuskurenka natab'a mun d'a da kayi, saboda haka kada kafasa ga fili ga mai doki, ni na barka lafiya."
Takashe wayarta tun kafin yayi qoqarin cewa wani abun zuciyarta fal cike da farincikin ta mayar masa da baqaqen maganganun daya yimata daidai shi.
Wani irin qugi Abba yayi tare da ture dispenser d'in dake gefensa a kan fridge yana mai jin d'acin kowace kalma d'aya da Rashida ta mayar masa, wanda ya ta'allaqa hakan da walaqanci da kuma cin zarafi da 'yarsa ta cikinsa tajawo masa takowane b'angare.
Qarar motar daya jiyo daga wajen gate ya sashi saurin fita tsakar harabar gidan yana huci ya d'auka su d'inne suka iso kamar yanda Rashida tafad'a, sai gashi ashe su uncle h ne suka dawo daga wajen nemanta agajiye rayukkansu duk ba dad'i saboda babu wani labari da suka samo akanta, har hajia nafeesa sun kirawo acan borno suji ko batool d'in taje can amma saboda batada wata masaniya akan zuwan nata yasa tace masu bata ganeta ba.
Har ya juya zai komawa ciki ya hango mota na kunno kai cikin gidan da sauri yadawo yanufi wajen motar tamkar wani zararre, hannu batool ta shiga yarfawa hawaye nazubo mata a fuska hango mahaifin nata da tayi ya tunkaro wajen motar tasu, sudai su Uncle h zura idanuwa sukayi suna jiran fitowar wanda ke cikin motar, qafar macce da suka gani tafara azowa lokacin da suka bud'e gambunan motar yasasu saurin qarasowa wajen motar suma, batool na ganinsu da sauri taqarasa fitowa jikinta narawa tanufi inda suke tana fad'in.
"Nashiga uku, uncle don ALLAH kuyi haquri ku yafemun kada kubari Abbana ya dukeni, wlh Abba natuba bazan qara guduwa ba..bayansu ta b'uya tana kallon idanuwa abban nata da sukankad'a sukayi jawur kamar an watsa masa barkono, cikin fushi yanufi wajen da little yake tsaye yariqe gambun mota shi bai qarasa fitowa ba shi baikoma ciki ba yana kallonsu uncle h da suka juya suna kallonta cike da mamaki.
Wata irin cakuma Abba yayiwa little had'e da shaqo wuyan rigarsa ya had'asa da jikin motar tasa yana fad'in.
"Kai d'an gidan uban waye da zaka d'aukemun 'yah?, ubanme kaje kayimata ana saura kwanaki a d'aura mata aure?, Kafad'amun uban me kaje ka aikata mata?"
Yanda yake kakari yasa batool rugowa tariqe masa qafa tana fadin.
"Abba ka qyalesa, don ALLAH aba karabu dashi, ba abunda yayi mani asalima ninaje na iskosa har gidansu, Abba naroqeka kabarshi kada kacutar dashi don ALLAH."
Ko kad'an little baiyi yunqurin kwatar kansa ahannun abba ba saboda kada yace yayi kokuwa dashi duk kuwa da azabar da yakeji Kuma bawai bayada qarfin bane kawai ya shiraya rayuwa ko mutuwane akan masoyiyarsa.
Yanda batool takoma qoqarin cire hannunsa ga wuyan little tana kuka yasa Abba sakinsa tare da riqo hannunta ya d'auketa wani irin zazzafan marin da saida takife wajen asume, da gudu little yayi kanta yana kiran sunanta had'e da cewa.
"Kada ki karaya batool, wannan shine qalubalen da soyayyarmu tazo mana da ita, don ALLAH kitashi kada kibari wani abun ya sameki, bazan juri hakan ba, batool batool tun yana qeqqegar tab'ata har yasoma aza hannunsa akafad'arta yana jijjigata, a fusace Abba yasake yowa takansa ya shuresa gefe amma hakan bai hana little tasowa ba yana kuka yana kiran sunanta, qafa Abba ya d'aga zai sake shuresa uncle Hussain yazo ya jayesa yana fad'in.
"Ta b'angaren sa ya isa haka domin idan ma laifi yayi na d'aukarta kacire wannan rad'ad'in azuciyarka, ayanzu bakada hurumin sake tab'asa sai dai ko 'yar taka gatanan agabanka zaka iya qarasata idan kana buqata,"
Yana gama fad'ar haka ya juyawarsa riqe da hannun little ya shige part d'insa dashi, shi kuma sai waiwayen batool daya hango uncle Hassan na yayyafa mata ruwa yakeyi yana sharar hawaye,
Tana farfad'owa tafara waige waige tare da nufar art d'insu tana kuka ahankali tana kiran sunansa,
Karki kuskura qafafuwanki sutaka mani cikin gida domin ya haramta daga gareki, yanda kika fita kika barsa Ina so ki kama qafafuwanki kifice daga cikin gidannan kafin nacireki daga cikin 'ya'yana, tunda har kikasa aka ci mutuncina kika zubarmun da kima a idanuwan duniya kikasa 'yan uwana suka juyamani baya to nima daga yau babuni babu ke, kije can kinemi wasu iyayen da suka fimu Amma mu bama buqatarki,
"Madalla daka fad'i hakan, idan har kai baka buqatarta to mu muna buqatarta, gida kuwa tanada ikon ta zauna tunda tana damu, batool share hawayenki in Sha ALLAH daga yau sun dena zubowa, idan har shi yayi maki gata kina qaramarki to mu zamuyi maki ita ayanzu da kike da girmanki tahanyar aura maki wanda kike so"
Uncle Hassan yafad'i hakan tare da riqo hannun batool yawuce part d'in uncle Hussain da ita shi kuma Abba yawuce fuuuuu..zuwa nasa part d'in....
*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*ππ
[11/14, 22:52] Billy S Fari: πΆββοΈπΆπ»ββοΈ *SANNU SANNU*πΆπ»ββοΈπΆββοΈ
π _Bata hana zuwa..._π
_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπ*
_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*π
_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*π
*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*π
*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*β€οΈ
Page___85π
Duk iya qoqarin su uncle h wajen ganin sun fahimtar dashi hakan ya cutara don gaba d'aya ida birkice masu ma yayi tamkar wata birkitacciyar kaca, shiru duk sukayi suna sauraren yanda take masifa yana qarawa har yayi mai isarsa yagama sannan suka miqe rayukkansu a 'bace sukabar wajen.
β’β’β’ β’β’β’ β’β’β’
Dady kuwa tunda suka koma shima ya canzawa hajia nafeesa, gaba d'aya baya shiga al-amurranta saboda yanda ransa yab'aci, ya tabbatar babu wanda ya shiryawa mahaifin batool wannan qullalliyar ta cewa little bayada uba sai ita wanda hakan baiyi masa dad'i ba ko kad'an, shiyasa ya d'auki fushi da ita don ya nuna mata kuskurenta, amaimakon ta fahimta sai itama ta sharesa tafita batunsa kamar yanda yake yimata, Saida taji tagaji don kanta sannan yau daya shigo part d'inta da daddare don ya duba yaransa saboda a part d'in ammie yake ta tsaresa akan lallai sai yafad'a mata dalilin da yasa yake fushi da ita har na tsawon sati biyu.
Waje yanema ya zauna fuskarsa a d'aure babu alamun walwala atattare da ita sannan yace
"Meye dalilinki na shegantawa Rashida d'ah da kuma shiga rayuwarsu?, meye yadameki da zuwam mu nemawa yaronsu auren da kikaje kika fad'i maganganun da zasu iya lalata komai?"
Wani irin sheqeqe ta d'ago takallesa had'e da cewa.
"Au dama akan wannan kake fushi dani?, Tirqashi! Ai wallahi da nasan akan wannanne dalilinka da ko kallonka bazanyi ba balle har indamu da fushin da kakeyi, Kuma da kake zancen shiga rayuwa dani dasu waya shiga rayuwar wani?, meye alaqarsu dakai da har zaka tambayeni zance sheganta yaronsu, yo ina uban nasa yakene da har don na shegantasa zakaga laifina?, Ina ganinsu kawai mukyi dashi tsakar rana shida da uwarsa da suka gudo ita da kakannisa batare da munga ubansa ba?, To don me an tambayeni bazan fad'i gaskiya ba?, Kama ajiye duk wannan agefe, kai kasan dolene ma nab'ata wannan auren tunda aka munafucceni akan za'a nemowa d'ana yarinyar sai akaje aka nemawa wanda ba'asan asalin saba saboda bid'ar suna, kaga kuwa koba komai yanda natsani kakarsa wlh in akwai abunda yafi lalata aure zan iyayi masu don bazan bari muhad'a jini dasu ba balle ace sunyi nasara akaina?."
"Haka kikace!?"
"Eh haka nace, nafad'a kuma naqara fad'a, indai ina raye wlh bazan bari wannan yaron ya auri 'yar uwata ba!."
"To shikenan, bari naqyaleki tukuna kafin hukuncin da zanyi maki akan wud'annan maganganun da kikayi tsaye kina fad'amun da abunda kika aikata yabiyo baya mugani idan zaki iya dakatar da abunda ALLAH ya tsaro, mugani idan kinada girman shaqiyancin da zaki iya ja da ikon ALLAH, ni dai natabbata wud'annan bayin ALLAH da kike gani ALLAH ne garkuwarsu kuma babu wani abu da zai samesu face yazamo alkhairi agunsu, sunyarda da Allah kuma shi suka riqa acikin al-amurransu, don haka nasan shine zai tayasu wannan fad'an da basuma san kinayi ba, kije ki binciki qarshen wacce tafiki fitsara da tanemi yimasu kaidi yanda ALLAH ya mayar mata dashi akanta!"
Yana gama fad'ar hakan yafice abunsa ya barta da tarin tambayoyin da batada mai amsa mata su.
Bayan sati uku da faruwar hakan dady ya kirawo Dr da qanensa faruq sai shakur don sune manyan 'ya'yansa maza ya kuma aika aka kirawo masa little, bayan duk sun hallara ya d'auko takardun wasu gidaje guda biyu d'aya takardun gidan dake laqe dana faruk ne, d'aya kuma takardun gidansa ne dake can laqe da shagonsa wanda marigayi baba yayi tsare masa kafin yarasu, kallon Dr yayi yace.
"Nura kaine babban d'ana, kuma kasani cewa dukkaninku ni nabaku gidajen da zaku zauna lokacin da zakuyi aure, don haka yanzuma Ina so inbawa d'an uwanku shakur nasa saboda sati nasama nakeso da yardar ALLAH muje muyo maganar aurensa asamana rana da kuma sadaki."
Ciro takardun gidan dake kusa dana faruk yayi yamiqa masa had'e da cewa.
"A matsayina na mahaifinka nabaka wannan gidan dake kusa dana faruk halak malak kamar yanda nabawa sauran 'yan uwanka alokacin da zasuyi aure, saboda haka daga yanzu zaka iya zuwa kayi 'yan gyare gyaren da kake buqata kafin lokaci yayi, Kai koma saidashi kake da ra'ayin yi kasai wanda kake so zaka iyayin hakan nakane babu wanda zai hanaka."
Godiya Shakur yashiga yiwa mahaifin nasa yana wasar baki tare da kallon 'yan uwansa yace.
"Broth's kutayani yiwa dady godiya ALLAH yaqara bud'i."
Duk suka amsa da Amin har da little dake gefe zaune yana kallonsu, saida suka gama yimawa dady godiya gaba d'ayansu sannan ya ajiye takardun d'ayan gidan dake hannunsa agabansu had'e da cewa.
"Wud'annan takardun kuwa na gidan dake laqe da shagon da marigayi bashar kakan little yayi tsare mani ne, ALLAH shine sheda tun ranar da kai Dr inbaka manta ba kazo kasanar damu cewa matarka Fatima tasamu juna biyu yana tsaye araina naqudurta cewa zan bashi wannan gidan ya d'auki iyalinsa sukoma can saboda yiwa ALLAH godiya akan ni'imar da yayi mana takarb'uwar addu'o'inmu da yayi kaima ya nuna maka naka jinin aduniya, sai gashi kuma ALLAH yayi nashi ikon akansa, ganin hakan yasa naquduri cika wannan niyar tawa ga iyalinsa, nan ma ALLAH bainufi hakan tafaru ba dalilin kasantuwarsu aqarqashin inuwarmu, don haka yau Ina son ALLAH da mala'ikunsa da kuma ku 'ya'yana kuzama sheda ko bana raye na mallaka wannan gidan halak malak ga jikansa don cika wannan alqawarin dana d'aukarwa kakansa cewa zan bashi wannan gidan tun farko,"
"Dady mun sheda hakan uabangiji ALLAH ya saka maka da alkhairi ya lullunka maka da gidan aljannah," Shakur yafad'a yana dariya tare da jujjuya nasa takardun gidan dake hannunsa, duk da dai faruk bai tanka ba da zaran ka kallesa yanayin fuskarsa zai tabbatar maka da cewa baiji dad'in hakan da mahaifinsa yayi ba.
Takarda da biro dady yaciro yayi rubutu akai sannan yafara ba Dr yace yasa hannu shida 'yan uwansa, bayan sun sa ya amshi takardun yamiqawa little dake zaune tamkar andasa shi, banda hawaye babu abunda ke zubo masa saboda ganin irin gatar da dady yayi masa tamkar yanda yayiwa 'ya'yansa, wannan bawan ALLAH wane irin mutunne shi da kokad'an babu qyashi da hasada acikin al'amurransa, yana karb'a yafashe da kuka hannunsa na kakkarwa,
"A'a Dady ban cancanci haka ba daga wajenka, abubuwan da kukayi mana nida mahaifiyata da kakannina kawai sun wadatar don ALLAH kabar takardun gidannan."
"A'a! Little meye haka?, Wannan kyautar tun asali cancantar kakan kace shiyasa tazo hannunka, shi kuma alkhairi danqone idan kayishi watarana zai dawo maka, bamusan me gobe zata haifar ba, abunda muka bayar shine namu wanda Kuma mukayi amfana dashi sharar banzane, rabon bawa kuwa duk inda yake bai wucesa don haka kawai ka amsa kayiwa ALLAH godiya domin shine yabaka ni kawai nazamo silane sai kayi mani addu'ah"
Godiya yayita zuba masa tare da sake miqawa Dr takardun ya amsa ya sanya masu albarka tare da miqo masa yana fad'in.
"Karb'a amma kafin nan bari nima amatsayina na uba agareka infad'a maka irin abunda dady yafad'awa Shakur d'insa, wannan gida nakane halak malak kaje idan akwai gyare gyaren da zakayi kayi kafin lokaci yayi, idanma bakada ra'ayinsa zaka iya sayar dashi kasai wanda kake buqata babu wanda zaice kayi laifi."
Gaba d'aya dady dasu shakur sukasa dariya, sun d'an jima awajen suna tattaunawa akan maganar auren kafin dady yasallami kowanensu yana maijin farincikin sauke wannan nauyin alqawarin daya dad'e dashi acikin zuciya har na tsawon shekaru, faruq baiji dad'i ba ko kad'an amma da yaje wajen ammie yana qunquni ya sanar da ita fad'a tayi masa sosai tare da nuna masa cewa idan mutum ya tallafi bayan wani to shima ALLAH zai tallafi bayansa, alkhairi kuwa danqone baya fad'uwa qasa banza, sucire qyashi da son duniya suyi koyi da mahaifinsu wajen taimakon wanda bayada, musamman shi faruq d'in don ta tabbatar Dr yariga daya gama hawa kyakkyawar turbar mahaifinsa shi kad'aine yamzu kansa ke rawa wani lokacin don haka yatsaya yayiwa kansa fad'a domin duniya ba wajen zama bace, Dole ya sauka daga dokin naqin daya hau ya bata haquri tare da tabbatar mata da cewa zai kiyaye.
Rashida kuwa har gida ta isko dady da guntayen hawayenta tayi masa gdy bisa kyautar da yayiwa little, umma kuwa ba'a magana don haka ta tashi cikin dare tayita zuba masa addu'a bayan tayi masa godiya, gawata kulawa ta musamman da riritasa data qarayi tamakar qwai a faranti.
β’β’β’ β’β’β’ β’β’β’
Acikin sati ukun da aka kwashe kuwa banda qara cikakken bincike akan bayanin dasu baffa suka basu uncle h babu abunda sukayi saboda maganar da yayan nasu yazo da ita cewa wai hayar mutanen da sukazo amatsayin iyayen little akayi, sunyi hakanne don qara tabbatar da zancensu baffa akan hukuncin da suka gama yanke shawarar d'auka akan yayan nasu, kafin sukai ga zartar da hakan kwatsam saiga wani Abba yakawowa batul akan shi zata aura nan da sati biyu kuma ba gudu ba ja da baya, wayyo ranar batul qaramin hauka kawaine batayi ba, tayiwa mahaifinta kuka tayi masa magiya kamar ranta zai fita amma yaqi saurararta, kwana d'aya da zancen aka kawo lefe set d'in akwati uku, duk inda ran su uncle h yake ya b'aci don gaba d'aya bai bid'esu ba shi kad'ai ke sha'aninsa.
Haka batul ta dinga kuka tare da isko su uncle h tana riqon qafafuwansu akan kada subari abbanta ya aura mata wanda bata so amma saboda b'acin rai akan abunda yayi masu suka kauda kai akanta, ganin yanda sukayi biris da ita yasa ta iske iyayenta mata tana roqonsu akan su dakatar da mahaifinta kada yayi mata auren dole nan ma suma suka qyaleta, matar uncle Hassan ce da bazata iya jurewa kukan nataba tana hawaye tariqo hannuntata nufi d'akin Abba da ita, yana zaune falo tayi sallama suka shiga lokacin yana waya har dasu qyaqyatawa da alama yanajin dad'in firar wanda suke waya dashi, yana gamawa ya d'ago kai yana kallon matar uncle hassan d'in da hawaye ke kwance a fuskarta yace.
"Lafiya hajia Naga kamar hawaye afuskarki? Meyake faruwa?"
Nuna batool data durqusar