Showing 18001 words to 21000 words out of 260204 words
Chapter 7 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt
akan batun Rashida 'yarka"
"Tofah injin malan bawani shashancin ta aikata ba?." Mahaifin nata yafad'a tare da muskutawa ya gyara zamansa, "ko kad'an baba, kawai yanayin yanda take karatune yasa nace bari na bincika ko akwai wata matsala da kukasan tana fama da ita don asan wane irin taimako yakamata a matsayinmu na malamai mubata awannan gab'ar, saboda idan kalura awud'annan shekarun nata kamata yayi ace yanzu tana makarantar gaba da primary wato secondary amma ace gatanan har yanzu a primary kuma bata fahimtar komai kaga wannan matsalace da yakamata ace anbinciki dalilin da yasa takeyin haka." jinjina kai mahaifin nata yayi tare da fitar da wani iska abakinsa sannan yace, "Hmmm! Malan karabu da wannan yarinyar, babu wata matsalar dake damunta in banda daqiqanci da kuma shashanci, ko kad'an bata son karatu tuntana 'yar qanqanuwarta, haka mukayita fama da ita har takai wud'annan shekarun, hatta aji shiddan da kagata saida nabiya kud'i masuyawa sannan nasamu akaturata saboda tasamu takardar shedar qare primary don insamu inkaita tagaba da ita wato secondary, alokacin tana qarama na d'auka quruciya ce sai yanzune data girma na fahimci cewa abun nata iskancine da rashin maida hankali wajen karatu, ko kad'an ba tason karatun shiyasa takeyin hakan."
"Amma baba ai wannan babbar matsalace da yakamata ace kazaunar da ita katambayeta saboda ataimakawa rayuwarta, duk yaron da kake gani anhaifesa da baseera, kawai rashin samun daidaituwar layin d'aya kamata su haune kansa kaganesu haka, inada yaqini akan da za'a fara magance mata matsalar da kesa ta kasa maida hankali ga karatu to da tabbas za'asha mamakin ganin baiwar da ALLAH yayi mata,"
"Taya zan iya magance mata matsalarta malan bayan bazata yuyu ba?, Shekarunta duka sha biyar aduniya yanzu tashigo shekara ta sha shida, taya zan iya aurar da ita awannan lokacin? Yarinyar da batasan komai ba aduniya ga kuma rashin ilimi da yake d'awainiya da ita, wakake tunanin zai iya karb'ar amanarta idan na damk'a masa?"
"ALLAH shine masani baba, tunda wannan itace matsalarta zaifi kyau ace anyi mata auren da ace anbarta ga tutar babu, ba ilimin kuma babu auren daga qarshema inba ALLAH yakare ba abunda ba'aso yabiyo baya, ni Ina ganin da zakayi hak'uri kayi mata auren da yafi, shekarunta basuda illar da zasu hanata aure saboda ada iyayenmu da shekaru goma sha biyu ake aurar dasu kuma su zauna lafiya har su haifemu ba tare da sunyi wani karatu ba."
Rai b'ace mahaifinnata ya mik'e had'e da cewa, "ni bazanyi hakan ba, domin wancan zamanin daban wannan ma daban saboda haka idan wannan yakawoka tashi katafi don wlh ko bataso dole sai tayi karatu, wayasani ko kune kuke b'ata mana yara kuna juya masu ra'ayi saboda son kanku."
"Subhanallahi, gyara kayanka baba ai bazai zamo sauke muraba ba, a matsayina na malami don na bibiyi matsalar dake jawowa d'alibina rashin fahimtar karatu bazai zama illa ba, kuma wannan ai shawarace nabaka saboda kasamawa 'yarka maslahar rayuwa da kuma kai kanka, idan kana ra'ayi saika d'auka idan Kuma baka ra'ayi kanada damar da zaka ajiyeta, meye abun b'acin rai da har zaikai ga wud'annan kalamai haka!."
"Naji kuma nagode kama hanya katafi."
Mik'ewa malan Idris yayi ransa duk babu dad'i had'e da gyara tsayuwarsa sannan yace
"Zan tafi kayi hak'uri don ALLAH bisa shiga rayuwarka data ahalinka da nayi amma karka manta annabi yace _kullukum ra'in wa kullukum mas'ulun an ra'iyatihi_ damu malamai da kuma ku iyaye dukkaninmu makiyayane kuma dukkaninmu abun tambayane akan abubuwan da aka bamu kiwo, kayiwa ALLAH godiya daya baka 'yar da zata iya fad'a maka gaskiyar abunda ke ranta sab'anin wasu 'ya'yan da saidai iyaye suganesu da abun kunyar da son ransu ne ya jawo hakan." Yana gama fad'a yabar wajen cike da mamakin iyayen dake tafka kuskure irin haka da zai kaisu ga dana sani....
*_ALLAH KAJIK'AN IYAYEN MU_*ππ
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πΆββοΈπΆπ»ββοΈ *SANNU SANNU*πΆπ»ββοΈπΆββοΈ
π _Bata hana zuwa..._π
_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπ*
_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*π
_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*π
*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*π
*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*β€οΈ
Page___10π
Misalin qarfe goma na safe baba yanufi makarantar su Rashida yasa aka aka kirawo masa malan Idris, cikin girmamawa yayi masa sallama tare dasa wata d'aliba ta d'auko masu kujeru guda biyu ta aje masu a k'ark'ashin inuwar wata bishiya dake a tsakiyar compound d'in makarantar, hannu ya basa suka gaisa had'e da cewa "bisimilah baba" yana nuna masa kujerun, tare suka jero har suka iso wajen, saida ya zauna sannan shima yazauna yana nazarin abunda yakawoshi bayan jiya sun rabu baran baran dashi, shiru yabiyo bayan gaisawar tasu kafin can baba ya nisa yace "Ina fatar kaganeni malan?, nine bashar mai takalma wato mahaifin Rashida wanda jiya kaje wurinsa" murmushi malan Idris yayi kafin yace "naganeka baba, ya gida? Ya iyalin?, Injin dai ko lafiya naganka yanzu?"
"Eh lafiya klw alhamdulillah, dama nazone inbaka hak'uri bisa abunda yafaru jiya, sai daga baya dana zauna nayi nazari nafahimci nayi kuskure akan abunda nayi maka, saboda shi gyara kayanka bazai zama sauke muraba ba, zuciyata ta gamsu kuma ta amince da shawararka don haka nazo inbaka hak'uri, don ALLAH kayi hak'uri bisa kausasan kalaman da nayi agareka, kasan duka mai rai ajizine" kansa na aqasa yana murza 'yan yatsun hannunsa ya d'ago yana kallon baba sannan yace
"Karka damu baba, wlh babu komai ai haka rayuwar tagada, wasu mutane nada saurin fahimta da kuma yarda wasu kuma akasin haka, koma dai meye ni babu komai araina nayafe maka, saboda haka kamanta da komai babu wata damuwa, mukan yiwa ALLAH laifi ya yafe mana balle mudaya halitta." Jinjina kai baba yayi yana qara yaba hali irin nasa tare da tunanin ta inda zai b'ara b'ullo masa da d'ayan zancen daya kawoshi, cikin dakewa yayi gyaran murya had'e da cewa "madalla malan naji dad'i sosai kuma nagode, Allah yayi albarka yasa agama lafiya, hak'ik'a samun mutum irinka awannan duniyar da za'ayiwa laifi kuma adawo arok'esa yafuwa kai tsaye yayafe nada wahala, nagode sosai"
"Babu komai ba ai yawuce"
"To bari natashi natafi nasan bazaka rasa ajin da zaka shiga koyarwa ba yanzu"
"Ai yau aji d'ayane agareni baba kuma tun safe nagama dasu saboda first period ne, Bari dai akirawo maka Rashida ko?"
"A'a kyaleta kasan yau juma'a bawani dogon lokaci bane gashi lokacin zuwa masallaci na gabatowa" mik'a masa hannu yayi suka sake gaisawa sannan yajuya zai tafi, har yayi taku biyu sai kuma ya tsaya had'e da juyowa yace
"Emm nace bakaji ba?." Juyowa malan Idris da har yafara tafiya shima yayi had'e da cewa
"Na'am baba, magana kakeyi?."
"Eh, dama nace baka fad'amun sunan kaba da kuma inda kake don da alama bautar qasa takawoka nan!." Saida yayi murmushi sannan yace,
"Sunana Nura idris aliyu, Amma anfi sanina da Idris aliyu saboda da haka abokanan karatuna suke kirana a makaranta shiyasa sunan yabini, ni d'an garin nanne a qauyen bebeji."
"Ikon ALLAH, inada aboki acan kuwa, sunansa malan idi ko kasanshi, muna had'uwane idan munje cin kasuwanne dashi."
Dariya yayi had'e da cewa, "in dai malan idi mai awaki kake nufi toshi d'in ai mahaifina ne."
"Allahu akabar malan dawo mu zauna." Baba yafad'a yana maijin cewa in sha ALLAHU haqarsa zata cimma ruwa, dama shi kuma malan idris kamar yanda yafad'a bayada wani ajin yanzu don haka ya sake dawowa suka zauna, "Aikuwa aminina ne sosai, sharabona dashi tun watanni biyar da suka wuce yacemun zaiyi tafiya to har yanzu kuma bamu sake had'uwa ba, ko har yanzu bai dawo bane?"
"A'a baba yadawo amma a hanyarsa tadawowa yasamu had'ari yanzu haka yananan gida zaune ana jinya yau sauqi gobe ciwo, wannan watansa na hud'u kenan baya zuwa ko ina"
"Subhanallahi, gaske mukajisa shiru kuma gashi ALLAH baisa mukabi bayansa ba muji ko lafiya? Sai satinnan daya wuce muka fara shawarar zuwa nemansa don munzata tafiyar tasa mai dad'ewa ce shiyasa muka jisa shiru, ubangiji ALLAH yabashi lafiya yasa kaffarane, insha ALLAH ranar lahadi munanan tafe mudubashi, bawan ALLAH! malan idi ai mutumen kirkine."
"Amin baba ALLAH ya yarda." Wannan zancen da baba yaji shine yahana yayiwa malan Idris zancen Rashida alokacin amma sosai yasake samun natsuwar mik'a aurenta a hannunsa kodon nagartar mahaifinsa da kuma tasa, sun d'an jima suna hira anan yake sanar dashi yau d'innan in ALLAH yaso zaije can qauyen yadubo mahaifin nasa kuma insha ALLAH zai fad'a masa cewa yana gaisheshi sannan baba yawuce bayan yakarb'i address d'insa.
Bayan yawuce malan Idris yayi dariya tare da cewa "ALLAH mai iko!haka rayuwa take shiyasa akeson kazauna da kowa lafiya, da ace jiya bayyita tausar zuciyarsa ba akan abunda baba yayi masa daba qaramar kunya yau yajiba kasancewarsa abokin mahaifinsa." Sake murmushi yayi sannan yakoma cikin office d'insa
Rashida kuwa tuni cikinta yad'uri ruwa ganin mahaifinta a makarantar, atunaninta yazone saboda abunda yafaru jiya, tsoronta d'aya kada yauma idan takoma gida ya doketa idan malan idi yafad'a masa sauran abunda tace, jikinta har rawa yakeyi atashi taje wajen malan Idris taji abunda yakawo mahaifinta don gaba d'aya ta manta da zancen da tayi dashi da safe akan yazab'a mata duk mijin da yaga dama kuma tunaninta bai kawo mata baba zai iya nema mata malan Idris ba, ana tashi tanufi office d'insa har suna cin karo dashi yana qoqarin rufe office d'in batare data damu ba cikin turo idanuwan dake nuna tsoro qarara a fuskarta tace "don ALLAH malan meya kawo baba makarantar nan!? Wlh inajin tsoron kar ace ka koma cemasa wani abun akaina ya sake dukana, ko ranar da kaje gidanmu saida yazaneni sosai da tsintsiyar shara" qura mata idanuwa yayi yana kallon yanda bakinta ke motsawa da yanda idanuwanta suka firfito saboda tsoro, ji yayi kamar ma bai tab'a ganinta ba sai yau saboda yanda yanayin tsoron nata ya bada wani fasionable atattare da ita, yanda take game hannu tana tambayarsa yasa jikkar hannunta fad'uwa da sauri ya duqa zai d'auko mata itama alokacin taduqo sukayi karo da juna,
"Yi hak'uri malan." tafad'a had'e da d'aukar jikkar ta rataya akafad'a, girgiza kai yayi kamar wani soko sannan yafara tafiya yana murmushi had'e dajin wani abu akanta, da gudu ta cimmasa tace, "malan baka fad'amun kome mahaifina yazoyi anan ba."
"Kashi yace abaki." Shine amsar daya Bata atakaice yanaci gaba da tafiyarsa, tsaye tayi kamar andasata awurin kafin tasake rugawa ta cimmasa, "malan, malan kashi fa kace!, to ni menayi kuma.?"
"Saboda bakyason karatu."
"Amma ai d'azu shiyace ya amince tunda aure nakeso zai yimun!" Tsaye malan yayi zuciyarsa nabugawar da baisan dalilinsa ba kafin yajuyo yana kallonta had'e da cewa, "waza'a aura makine?" gyara jikkarta tayi had'e da ware hannuwanta tana fad'in, "Ban sani ba, da akwai wani Rabe dake sona amma baba yace beyi masa ba, don haka shizai zab'ani miji da kansa" ajiyar zuciya ya sauke had'e da cigaba da tafiya tana biye dashi agefensa yaci gaba da cewa "Kuma ke kin amince?"
"Eh, ni nace ya zab'amun duk wanda take so"
"Kuma duk wanda aka zab'a makin zaki yarda ki auresa?."
"Eh mana zan yarda tunda ni nace na amince."
"Ko waye shi?."
"Eh, kowaye shi"
"Koda ace nine? zaki yarda"
"Eh, zanyarda man.." Bata ida fad'aba tayi saurin rufe baki tare da zaro idanuwanta tana kallonsa jin abunda yafad'a, juyowa yayi shima yana kallon cikin idanuwanta d'aya bayan d'aya sannan jinjina mata kai tare da sakar mata murmushi yace "ina sonki! Zaki aureni!" Yaqarasa maganar yana dariya tare da barin wajen batare daya jira jin amsar da zata bashi ba yana jin wani shauqi da kuma farinciki atattare dashi,
Ita kuwa Rashida gaban tane yayi mugun fad'uwa tare da sakin jikkar dake sagale a kafad'arta tafad'i k'asa, kallonsa takeyi har ya qurewa ganinta kalmar Ina sonki d'aya fad'a nayi mata yawo a k'wak'walwa, tafi mintuna biyar awajen tsaye kafin tad'auki jikkarta tanufi hanyar gida jikinta kamar wacce aka zarewa lakka,
A ranar yini tayi data motsa fuskarsa take tunanowa da kalamansa tayita murmushi, ganinta cikin wannan yanayin yasa umma ta sake tsorata da al-amarinta, don atunaninta tsabar farincikin amincewar da mahaifinta yayine akan zaiyi mata auren kesata wannan nishad'in, d'azu garin kallonta har k'walewa tayi ajikin bangon qofar shiga d'aki,
Haka ab'angarensa daya rufe idanuwa babu abunda yake gani sai yanda bakinta ke motsawa da idanuwanta, ahankali yakejin sonta nashiga acikin zuciyarsa da kuma sauran sassan jikinsa,
Rashida kyakkyawar yarinya ce irin black beauty d'innan, tanada tsayi sosai don takusa kaimasa a kafad'a, tanada manyan idanuwa da zarazaran gashin ido hancinta bayada wani tsayi sosai amma saboda ramin idanuwa da take dashi zaka d'auka dogon hanci ne da ita hakama bakinta d'an madaidaicine ciccif fuskarta, bai tab'a lura da hakan ba sai yau daya qura mata idanuwa,
Daga shi har ita matsuwa sukayi weekend taqare saboda mararin son ganin juna sai dai ab'an garenta takan shiga damuwa idan tatuna da cewa tariga da taba mahaifinta damar zab'a mata mijin da zata aura, gashi ba zato ba tsammani malaminta ya dasa mata soyayyarsa azuciyarta, duk wani motsi da zatayi tsananin sonsa ke sake shiga ranta, kuma ayanda tasan halinsa tunda har tafurta da bakinta kuma ya tambayeta ta amince da duk zab'in da zaimata to bata isa yanzu taje masa da wani sauyin magana ba,
Shikam malan idris safiya na wayewa ranar asabar ya isko mahaifinsa ya sanar dashi komai ba tare daya b'oye masa ba akan aminin nashi da suka had'u da kuma zancen 'yarsa d'aya gani yana so wacce ayanzu yake da nufin aurarwa, sosai mahaifinsa yaji dad'i kuma yayi murna ya tabbatar masa da cewa idan ALLAH yabashi lafiya nan da sati mai zuwa zaije suyi zancen ko yatura qannensa suyo masa maganar, anan yake sanar dashi cewa ai yasan halin aminin nasa yanada matuqar kirki amma akwaisa da zuciya da kuma kafiya, shiru malan idris yayi tuna yanda suka fara kwashewa dashi shekaran jiya wanda yatabbatar zuciyace tasa yayi hakan, nisawa yayi kafin yace
"To baffa don ALLAH kayi masa magana dawuri saboda ko yaushe zai iya bada aurenta ga wani, gashi kuma kace yacika kafiya da yawa" dariya baffa yayi tare da bubbuga kafad'arsa yace
"To Nuraddeen, ka kwantar da hankalinka in Sha ALLAH bazan bari haka tafaru ba, bari idan sunzo gobe d'in sai nafara b'ulguta masa maganar sai muji me zaice kaji ko?." haka sukaci gaba da tattaunawa akan matsalar ciwonsa har yake cemasa shi dai yaso ace cikin 'ya'yansa wani yayi karatun kiwon lafiya kodon taimakon gida da waje, gashi yanzu sai faman kashe kud'i akeyi akan matsalar ciwonsa kuma sunk'i fad'a masu gaskiyar abunda ke damunsa balle a tsammani waraka nan kusa ko kuma nesa.
Ranar lahadi misalin karfe sha biyu na rana, baba da wasu abokanan kasuwancinsa su uku da kuma qanensa da shima duk tare ake akasuwa suka kama hanyar bebeji don gano malan idi, basu kaiba sai misalin k'arfe biyu na rana saboda yanayin injinin motar da sukaje da ita Bata cika kyauba sai an lallab'a, qannen malan idi su biyune suka tarbesu tare da shigowa dasu cikin gida inda yake zaune saboda hatta qugunsa yasamu matsala be iya tafiya.
Sosai farincikin ganinsu ya bayyana a fuskarsa kamar yatashi sama don murna, haka suma saidai su nasu farincikin ya surku da tausayinsa ga yanda fuskokinsu suka nuna, saboda malan idi mutumne mai dad'in sha'ani da kuma hak'uri, kusan ma halin sane malan Idris ya gado, murmushi ya dinga yimasu yana fad'in "karku damu alhamdulillah Ina samun sauqi, muyiwa ALLAH godiya da yasa fuskokinmu suka sake had'uwa badon haka ba ai shikenan rabuwarmu kenan tun ranar."
Abinci aka kawo masu yasa malan Idris daya shigo gaishesu ya zuzzuba masu abincin, bayan sunci sun sai gashi yasake shigowa da gorunan lemu da ruwa yakawo masu hadda mahaifin nasa da qannensa, har zai fita baffa ya kallesa had'e da cewa,
"Dawo nan kazauna" yana nuna masa gefen da baba take zaune, gaban sane yafad'i tare da sadda kai qasa sannan ya qaraso ciki ya zauna amma acan d'an nesa dasu, gyaran murya baffa yayi sannan yace....
_Tofah baffa zai fasa kwai agaban kowaπ€£ Bari in gudu kafin kaina yayi girma saboda kunyar da zan tayasa jiπ
don son jin abunda baffa zai fad'a yau to inji ruwan comment idan ko ba haka ba kuda new update sai upper weekπ_
*_ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU_*ππ
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πΆββοΈπΆπ»ββοΈ *SANNU SANNU*πΆπ»ββοΈπΆββοΈ
π _Bata hana zuwa..._π
_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπ*
_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*π
_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*π
*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*π
*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*β€οΈ
Page___11π
Gyaran murya baffa yayi yana kallonsu baba kafin yace,
"Malan bashar nasan kai kasan wannan" yana nuna d'an nasa sannan yaci gaba da cewa "don haka Babu buqatar in sake gabatar maka dashi saidai ko in wud'anna 'yan uwan nawa, amma ku su alhaji surajo, malan hashimu, sa'idu, malan shu'aibu da malan balarabe ga d'anku nan Nuraddeen wato d'an wajena koda ALLAH zaisa wata rana a had'u zaku iya ganesa shima yagane ku, wud'annan su biyun da kuke gani kuma qannena ne uwa d'aya uba d'aya wato Usman da aliyu, inafatar ko bana raye ace abota da kuma mutuncin dake tsakanina daku bai yanke ba, inaso ya zamana cewa idan anhad'u da juna za'a iya gaisa har kudinga tunowa dani kuna yimani addu'a"
"Ashsha malan idi! don ALLAH kadena fad'ar haka domin ita cuta ba mutuwa bace, mudai fatanmu d'aya shine ubangiji ALLAH yabaka lafiya kuma ALLAH yaraya manasu shi da sauran 'yan uwansa ya tashi kafad'unka acikin iyalinka." Haka suka dinga fad'a tare da yimasa addu'a,
Shiru baffa yayi yana kallonsu d'aya bayan d'aya nan take yaji wasu hawaye sun cika masa idanuwa, tari yafarayi wanda hakan yabawa hawayen dake maqale a idanuwansa damar zubowa, sannu duk suka dinga jero masa cikin jin k'warin guiwa ya kaikaita idanuwansu yana goge hawayen had'e da amsa masu,
Bayan tarin ya lafa masa ya maido kallonsa ga 'yan uwansa da kuma d'an nasa suma ya gabatar masu da aminan nasa inda har yak'ara masu da cewa shi awajensa abokan nasa sunfi