Showing 75001 words to 78000 words out of 260204 words

Chapter 26 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt

tunanin haihuwarnan yasa kakejin haka, to kasanyawa ranka salama in sha ALLAH zan sauka lafiya kuma zan haifa maka chuluv d'inkacikin qoshin lafiya kaji ko" taqare maganar tana sakar masa kiss ta ko ina afuskarsa har da saman tsinin hancinsa, cikin dariya ya rungumeta shima yana sumbatar goshinta yace.

"Nagodewa ALLAH daya sanya cikakkiyar natsuwata a hannunki, ALLAH yayi maki albarka yasa kigama da duniya lafiya, nayarda da shawarwarinki da kuma duk tsarin da ALLAH yayi mani arayuwa, ALLAH kasanya farinciki ya zamo cikar gurbin yanayin da nake ji."

"Amin habibynah jarumin mazan duk duniya."

Karan hancinta yaja tare da lakatar kuncinta yace.

"Abaki kenan amma idan nace ingwada jarumtar tawa yanzu ai bazaki yarda ba, chuluv d'innan nawa naga nema yake tun kafin yazo duniya yafara takuramin."

"Karkai masa sheri domin Babu ruwansa, habibtynka ce kawai keyi maka rowa saboda nauyin da tayi amma yau bazata yimaka ba matuqar kanada buqata akanta." Tayi hakanne saboda ta tabbatar da tagusar masa da damuwarta amma ita tunda cikinta yashiga wata na tara takejin wahalar kwanciya da ita, hakan yasa shima yadena takura mata.

Cike da farinciki ya mirgino fuskarsa na kallon tata yace. "Da gaske habibtyn habiby zaki iya jurewa?."

Kad'a masa kai tayi alamar ta tabbatar da hakan, cikin dubaru da tausayi yafara sarrafata ta hanyar da yasan bazata wahala ba har ya biya buqatarsa, tun kafin yagama taji mararata na murd'a mata ga wani ciwon baya da taji yarufeta amma saboda qarfin hali da kwad'ayin samun natsuwarsa yasa tajure har saida yagama.

"Habibty tashi muyi wanka." Yafad'a yana qoqarin saukowa saman gadon, Sai data cije baki cikin tsananin zafin da takeji tace.

"Kaje kafarayi habiby daqyar idan zan iya yanzu saboda marata namun zafi."

"Yi haquri habibty duk nine najawo hakan, Bari nad'aukeki sai muyo ko?."

"A'a kafara zuwa kayi, idan kafito ko arwala ce nasamu nayi kafin asubar tunda annabi ya halarta yin hakan."

Miqewa yayi har ya aza qafarsa zai shiga sai kuma yadawo had'e da sumbatar goshinta yace.

"Ina matuqar sonki da qaunarki habibty and I dont want to loose you any more in my life, be couse you're my everything, if I say everything I mean everything including my entire life, I love you for ever and ever and ever."

Cikin wani yanayi da ita kad'ai tasan ya takeji tayi masa murmushi tare da cewa.

"me too all I have."






*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

😭😭 _THE MOST BREAKING HEART & HEART TOUCHING PART OF THE BOOK_πŸ’”πŸ’”

Page___36πŸ’Ž

Sake miqewa yayi ya nufi toilet d'in bakisa d'auke da addu'a ita kuma ta lumshe idanuwanta tana jin wani irin azababben bacci na son d'aukarta, a wannan lokacinne madubin boka bargaji ya nuna masa cewa Rashida bata cikin tsarki, nan take yafara surqullensa yana turo mata miyagun aljanu masu matuqar qarfi, wani iskane yataso da qarfi cikin d'akin da sauri Rashida tafarko daga nannauyan baccin daya soma d'aukarta tana cije baki, kan kace me tuni tafara ganin duniyar na juya mata, qoqarin kama addu'o'i tafarayi abakinta amma duk wacce tajawo saita kucce mata, wasu
Halittu tafara gani cikin iskan daya mamaye gabanta suna nufato inda take kowane da kalar sigarsa suna qoqarin illatata amma qarfin addu'o'in da takeyi ya shamakance tsakaninta dasu, hakan yasa suka gagara yimata komai saboda aduk lokacin da suka tunkarota wani irin gilashi mai qarfi suke ganin ya shiga tsakaninsu da ita, basu dena tsorata taba ita ma batadena karanto addu'o'in da suke bakinta ba har saida azabar ciwon da take ji ya tsanantar mata, gaba d'aya tarud'e tashiga tashin hankali, wani irin yanayi take jin kanta aciki wanda tunda aka haifeta bata tab'a jin kanta acikiba, yanayine da kallo d'aya zakayi mata kasan cewa naqudace ta taso mata adaidai wannan lokacin, tun tana jurewa har tafara gazawa idanuwanta suka fara zubarda k'walla tana kiran "ALLAH, ALLAH." don alokacin iya shi kad'aine bakinta ke iya furtawa.
Ganin duk aljannun da bargaji keturawa sun kasa nasara yasa yakira wani mugun shed'anin aljani wanda aduk lokacin da aiki yayi masa tsanani ko yake nema ya gagareshi shi yake turawa kuma cikin ikon ALLAH zasuyi nasara saboda ALLAH ya riga daya sakar masu talala, cikin wani qamari da girgiza ya dumfaro Rashida da alokacin bata iya furta komai saboda azabar naquda data rufeta, wani surqulle boka bargaji ya sakeyi yanda idanuwan Rashida zasu bud'e, tun tana kwance saman gadon har tajid'o dafe da cikinta alokacin aljanin ya bayyana da wata irin mummunar siffa agabanta nan take ta some wajen ba tare data koma sanin inda take ba, duk iya abunda boka bargaji zai iyayi shida shed'anun dake taimaka masa wajen ganin ankawar mata da hankali ko mugun sammun da akayi mata yayi tasiri akanta sunyi amma cikin ikon ALLAH da nuna qarfin addu'a hakan ya cutara, nasara d'aya sukayi shine d'auketa da akayi akabar garin da ita, sanadiyar hakan aljanin ya dinga buga Rashida a jikin itatuwa yana wurgi da ita bisa duwatsuna, yamatuqar fusata ganin yanda yakasa aiwatar da aikin uban gidansa akanta Wanda wannan dalilinne yasa saida y azabtar da ita sannan ya Kai ya jefar inda suke sa ran bazata tab'a rayuwa ba kafin safe.

β€’β€’β€’ β€’β€’β€’ β€’β€’β€’
A 'ban garen Nuraddeen kuwa yana fitowa wanka riqe da d'an qaramin towel yana tsane ruwa akansa yace. "Habibty ki daure kitashi muje intayaki kiyo wankan nan, nasan yanda kika tsani kwana cikin irin wannan halin na janaba baccin bazai yimaki dad'i ba idan kikayi kwanciyarki a haka, gashi biyu har da rabi nadare ya somayi nasan lokacin tashinki shima yakusayi tunda ukku takusa. Pls daure ki tashi kinji?"

Yaqare maganar had'e da juyowa yakai kalonsa inda take kwance, gabansa ne yayi mugun fad'uwa da sauri ya nufi inda yabarta kwance yana jaye mayafin da suke lullub'ewa don gaskata abunda idanuwansa kefad'a masa, a firgice yaja baya ganin bata wajen kwance da sauri ya nufi falo cike da fargaba amma ga mamakinsa nan d'in ma bata nan, kasa gasgata kansa yayi ya dinga d'add'aga pilows d'in kujeru da gefe gefen kujera cikin tashin hankali gabansa na bugawa da sauri da sauri, curtains d'in tagogi falon ya shiga d'ad'd'agewa yana kiran sunanta, babban taahin hankalinsa ma qofar falon daya gani kulle Wanda yatabbatar masa daba fita tayi ba, da gudu yakoma uwar d'akan yana rerrega qarqashin gado da bayan wardrobe yana sake kiran sunanta da qarfi, bud'e qofar toilet d'insu yayi yaqara shiga yana dudubata har bayan gambu kafin ya fito jikinsa na rawa yabud'e d'akin gaba d'aya, gaba d'aya ya manta darene haka yadinga kiran sunanta yana bud'e qofar kitchen,

Jin qarara muryarsa da baffa Usman yayi yana kiran sunan matarsa yasa shi fitowa da sauri sanin halin haihuwar da a ciki ko yau ko gebe, "Nuraddeen lafiya.?" Baffa Usman yashiga bubbuga qofar shiyar tasa yana tambayarsa.

Sai a sannan Nuraddeen yanufo wajen da sauri yabud'e k'ofar daidai lokacin shima Baffa yafito, tare suka had'a baki shida baffa Usman lokacin daya bud'e qofar suna tambayarsa ko lafiya?.

"Baffa Rashida!."

"Me yasamu Rashidar?" baffa yatambayesa firgice ganin yanda yaga hankalinsa atashe,

"Baffa ban ganeta ba..." Kafin ya rufe baki a tsorace baffa yatura kansa cikin shiyar baffa Usman na biye dashi yana fad'in "kamar ya baka ganeta ba, ita tsinken allurace da zaka nemeta cikin d'akin kuna tare k'arasa?."

Bayansu yabiyo tare dayin gaba yana fad'in "wlh baffa yanzu nabarta anan kwance nikuma nashiga in watso ruwa koda nafito ban ganeta banganta ba, dube dube suka shigayi suna leqe leqen cikin d'akin cike da mamaki,

Tare suka fito da fitillu a hannunsa suna dudduba cikin gidan amma babu alamun Rashida balle mafarinta,

"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, Inna lillahi wa'inna ilaihirrajiuun.." Nuraddeen yashiga fad'i yanajin kansa na jujjuya masa,

"Baffa nashiga uku, dama yau jikina nafad'amun wani abu zai faru dani, baffa ina Rashida zata shiga awannan cikin tsohon daren ba tare dana sani ba?, Wlh baffa akwai abunda ke faruwa ba daidai ba."

"Nuradden ka kwantar da hankalinka za'a ganeta, abun tambayar a ina tashiga?"

"Shine tambayar baffa, Kuma ko Ina akulle nagansa kamar yanda nabarsa, baffa kataimakeni inajin tsoro kada acutar mani da ita."
Nuraddeen yafad'a yana goge hawayen da suka fara yimasa kwaranya a idanuwa, ko Ina na cikin gidan su baffa suka shiga zazzagayawa harda Inna Bilkisu data farko lokacin hankalinta atashe jin abunda ke faruwa, d'akuna tashiga bi tana tambaya jikinta duk amace har zuwa wancan d'ayan b'angaren 'yan uwansu dake cikin gidan amma amsar d'aya ce, ba'a ganta ba!.

A cikin darenhankalin kowa yabi yatashi anata sallalami, baffa Ali kuwa kallon inna ruqayya da itama ta dan shiga tsinke yayi yana nuna mata Yaya hawwa dake tsaye ta rafka uban tagumi fuskata cike da damuwa kamar da gaske ammaqasan zuciyarta cike take da farinciki yace.

"Dubi Yaya hawwa, narantse da ALLAH tasan komai, d'akin kalleta Zaki tabbatar da kawai tashuka tsiyar don farincikine tattare da ita bayan waccan damuwar da kika hangota aciki."

Murmushi tayi had'e da cewa. "Ranar bayyanar asalin tata damuwar nakusa tunda tagama cimma nata burin."

Ganin kowa yayi cirko cirko ana jajanta maganar b'atan Rashida yasa Nuraddeen yanufi qofar gida a hargitse yana sabbatu da sauri baffa Usman yariqesa yana fad'in, "Ina zakaje Nuraddeen acikin wannan tsohon dare, qarfe uku fa ake magana yanzu, kayi hak'uri har muga abunda safiya zatayi."

Wani irin kukane yazo masa yana kallon baffa Usman cike da mamaki yace

"Baffa da bakinka kake fad'in inbar iyalina acikin wannan tsohon dare batare da sanin awane hali take cikiba?, Baffa amana ce fa agareni, bayan haka katuna halin da take ciki idan akace salame ce baffa kanaga zamu iya runtsawa awannan daren muna jiran wayewar safiya sannan muje nemanta?, Don ALLAH baffa kabarni inje koma meye yasameni nida ita, zuciyata nayimun rad'ad'in da zan iya mutuwa awannan lokacin idan natsaya dakon jiran dawowarta." Yana gama fad'ar haka yabud'e gambun yafita batare daya jira amsar da zata fitowa daga bakin saba, dagudu ya fice cikin gidan ko fitila babu a hannunsa Saida yakusa kai farkon gari sannan yafara yawo yana kiran sunanta, inyayi nan yayi can batare daya damu da yanayin dare ko duhun dake da garinba., Idan yayi wancan lungu ya shiga wancan yakoma wannan haka yayita yawo yana kiran sunanta, kallo d'aya zakayi masa kasan kwanciyar hankali tagama gushewa a jikinsa, wasa wasa har qarfe hud'u tayi ba batun Rashida, kaf ya zagaye k'auywn nasu da qafa ko takalma bashida yana kuka yana ambatar sunanta tamkar wani k'aramin yaro duqewa yayi yasaki wata irin qara had'e da jin kansa yana jujjuya masa, yafi minti biyar ahaka kafin ya miqe tunawa da 'yar qramar kasuwar garin da yayi ya nufi can da gudu, rumfuna rumfuna yadinga bi yana leqawa amma began taba, hanyar asibiti yanufa lokacin biyar da rabi na asuba yafara zagayenta tamkar wani tsohon mahaukaci sannan yashiga ciki yana lelleqa d'akunan majinyata, ganin nan ma Babu labarinta yasa yafara shiga dazukka dake cikin qauyen tamkar wani mashayi saboda yanda yake tangad'i saboda tsananin tashin hankali da gajiya, tun yana kuka har hawayen nasa suka qare, haka suma su baffa suka shiga nemanta cikin qauyen Amma babu labarinta, misalin qarfe shida na safe ko salla basuyi ba suka wuce qauyukkan dake maqwabtaka dasu amma har qarfe bakwai na safe balabarinta, a hanyarsu ce ta dawowa suka cikaro dashi saman hanya yashe mutanen gari sun zagayesa, da gudu baffa yaqarasa kusa dashi cike da damuwa ya tallabosa, ckallon yanda yayi bijib bijib da jiki ga qafafuwansa duk sun yayayyanke qaya ta sossokesa yasa baffa ya fashe da kuka yana fad'in.

"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, allahummah ajirni fi musibati wa'ahlifni khairan minha." Cikin yanayin dake nuna Nuraddeen nacikin matsananciyar damuwa ya d'ago kansa yace,

"Baffa kunga matata Rashida?. Baffa kubarni anan kuje kudubo mun ita, raina fansane agareta koda zan mutu kuje kutaimaketa, qarfina yaqare gaba d'aya, lumfashinanema yakeyi ya rabu da gangar jikina saboda rashin sanin a ina take, Kuma awane hali take ciki, baffa kutaimaketa jikina yana bani cewa Rashidata nacikin wani hali.." bai qarasa maganar ba sanadiyar lumfashinsa daya d'auke, jijjigasa baffa yashigayi yana kuku had'e da kallon baffa Usman da shima kukan yakeyi yace.

"Usman kataimakeni kada inrasa d'ana da nafiso aduk fad'in duniya." Kan baffa Usman yaqarso wajen har baffa ya ciccib'o Nuraddeen da sauri baffa yaqarasa wajen ya kama masa shi suka nufi hanyar asibiti dashi asheme ko motsi ba yayi.

Kan kace me batu ya gama zagaye qauyen nasu cewa matar Nuraddeen ta b'ata da tsohon cikinta wata tara.

Baffa Ali kuwa fad'a yakamayi yana fad'in tun farko Saida suka guji wannan auren saboda Babu alkhairi acikinsa yanzu gashinan zasu jawo masu abunda yafi qarfinsu don yasan iyayen yarinyar nan dole suje su kaiwa 'yan sanda rahoto azo adamesu da 'yan tambayoyi,

Su baffa na isowa asibiti likita yaduba Nuraddeen tare da yimasa wasu allurai ya fad'a masu sumace yayi amma yanzu zai farfad'o, yana rufe baki Nuraddeen na tasowa da qarfi daga kwancen da yake akan gadon asibitin cikin matsananciyar qara yana fad'in.

"Rashidaaaa...."









*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ˜­*
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

_Amincin Allah ya tabbata agareku masoya littafin SANNU SANNU...haqiqa zan iya cewa tunda nafara littafinnan ban tab'a jin dad'in rubutunsa ba kamar jiya, saboda yanda naga ruwan comment d'inku har da wud'anda Raina bai tab'a kawomun cewa suna karatun saba, na matuqar jin dad'i har sai da zuciyata takoma tana rayamun cewa anya soyayyar da kuke yiwa Rashida batafi wacce kuke yiwa Billy ba?😰 What ever d case am feel a little jealous oo..πŸ˜‰lolz..nagode nagode sosai jazakumullahu bikhair, I LUV YOU ALL FILLAH_🀍❀️

Page___37πŸ’Ž

Juyowa su baffa sukayi tare da likitan suna rigegeniyar isa inda yake, tsaitsaye sukayi gabansa fuskokinsu cike da tausayinsa ganin yanda nan take duk yabi ya zabge kamar wanda ya buge watanni yana jinya, riqasa likitan yayi daga zaunen da yake ya maidashi kwance yana fad'in.
"Relax malan Nuraddeeni, in Sha ALLAH komai zai daidaita kaji ko?"

A hankali yarufe idanuwansa wasu zafafan hawaye suka zubo masa afuska, juyowa yayi yana yabud'e idanuwansa suka sauka saman na baffa Usman, kamo hannunsa yayi yariqe sosai har lokacin hawaye nazubowa daga cikin idanuwansa yace. "Baffa kun ganta kuwa?."

"Kayi hak'uri Nuraddeen, in Sha ALLAH za'a ganta, kafara qarfafa zuciyarka tukuna tayanda zaka iya fad'an nemo masoyiyarka aduk inda tashiga, kada kabari raunin zuciya ya bayyanarwa da duniya gazawarka ga masoyiyarka dake neman taimakonka takowane fanni."

Baffa usman ne yafad'i hakan yana rumqe hannunsa sosai, cikin yanayin dake bayyana dukkanin raunin da Nuraddeen ya samu ta fannin zuciya, gangar jiki, kwakwalwa da kuma ruhinsa yace, "kaicona da riskar wannan lokaci da nayi, meyasa mutuwa batayi gaggawar d'aukata ba kafin wannan ranar tazo mani?, Meyasa rayuwa zata yanke mana wannan hukunci a daidai lokacin da muke tsananin buqatar juna?, Meyasa soyayya tayimun d'aurin goron dana kasa gano alfanun dake cikin komawar Rashida agaban iyayenta saboda kawai Ina buqatar kasancewa tare da ita akoda yaushe? Meyasa duniya zata juya mana baya a lokacin da ALLAH keshirin yimana kyautar da zata bamu jin dad'in zamanta?, Meyasa?, Meyasa baffa?" Yaqarasa maganar yana qara fashewa da wani irin matsanancin kuka maicin rai, da sauri baffa yajuya yabar d'akin saboda bazai iya jurar sauraren kukan d'an nasa ba, kowace hawainiya dake d'igowa daga cikin idanuwansa jinta yakeyi tamkar saukar qyanqyashe a saman zuciyarsa, baffa Usman kuwa sake rumqe hannun Nuraddeen yayi sosai cikin dakewa yace.

"Kayi haquri, kayi haquri, kajure kada zuciyarka tasa ubangijinka yayi fushi dakai, Babu dalilin dakesa ALLAH yayiwa bayinsa jarabawa kamar tsantsar imaninsu agaresa, wlh wlh Ina tabbatar maka da cewa duk inda matarka take bazata tab'a walaqanta ba domin ita yarinyace mai tawali'u ga ubangijinta, yarinyace mai tsananin riqo da addini da kiyaye dokokin ALLAH don haka dole ALLAH zai jarabceta harma damu dake tare da ita, saidai abu gudane nake da tabbaci akai da kuma kyakkyawan zato zuwa ga ubangijinmu cewa zai kula mana da ita aduk inda take fiye da kulawar da zamu yimata, mumunin k'warai shi ALLAH ke jarabtar kuma duk tsananin ibadarka da tsoron ALLAH bazai hana ajarabci imanin kaba saboda aqaramaka d'aukaka awurin ubangiji idan kaci jarabawarka, kayi haquri in sha ALLAH za'aganeta yau d'innan kaji ko?."
Duk da dai babu wani rad'ad'i da ya denaji azuciyarsa da kuma quncin dake damunsa ya yarda da duka kalman baffa Usman kuma zai gwada amfani dasu, kalaman data dinga fad'a masa daren jiya ne suka shiga yimasa yawo a kwakwalwa _Haba Nuraddeen, hasken idaniyata, zuciyata da kuma ilahirin gangar jikina, Kai kuwa meye zai tayar maka da hankali bayan kasan kanada ALLAHnka akoda yaushe kuma yana tare da kai, me zaka jiwa tsoro aduniya kai dake tare da sa albarka iyayenka, me kake shakku acikin rayuwarka bayan kana da yaqini akan zamu kasance atare, don ALLAH kadena fargaba akan komai koda kuwa wani abunne zai sameka ko kuma ya sameni, natabbata cewa tsantsar imaninmu da miqa wuya ga ALLAH shine kan iyasa ajarabcemu, muzama masu juriya cikin al-amurranmu alokacin da wani abu kenema ya gitto mana cikin rayuwa, sai musamu kanmu masu riskar ubangijinmu amadakata kyakkyawa, kacire komai aranka in Sha ALLAH babu abunda zai faru, nasan harda tunanin haihuwarnan yasa kakejin haka, to kasanyawa ranka salama in sha ALLAH zan sauka lafiya kuma zan haifa maka chuluv d'inkacikin qoshin lafiya kaji ko_

Tsananin jin yanda kansa keyi masa ciyo tamkar zai tsage yasa yai saurin dafe kansa da hannu bibbiyu yana sakin wata qara, da gudu baffa yadawo cikin d'akin ya tsaya yana fad'in. "Nuraddeen kayi haquri karka jawo nima in rasaka."

"Baffa kaina zai fashe." Nuraddeen yafad'a hawaye na dararo masa ta gefen idanuwa,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login