Showing 165001 words to 168000 words out of 260204 words

Chapter 56 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt

taci kuma har tagirma haka take shiyasa duk girman mutum bata shakkar tsayawa agabansa tafad'i abunda keranta don yariga daya saba mata da hakan, inda kawai rayuwarta take da sauqi shine batayin fad'a ko wata rigima sai da dalili, bata son reni shiyasa batayar da tasa qarya acikin sha'aninta ba, takan girmama babbane idan ya got kansa amma daga lokacin daya bari yayi abunda zai jawo zubewar girmansa agareta to komai tsufansa zata iya tsayawa tayi masa tas akan gaskiyarta, wannan halayyar tata natab'awa hajia mama rai amma idan tayi magana sai mahaifin nata da take kira da Abba yace a qyaleta ai yarinyace, ita kuwa hajia mama babu abunda take tsoratarwa rayuwar 'yar tata kamar gidan wani zata ace tanada kafuwa da rashin d'agawa kowa qafa indai tana bisa gaskiyarta ita kuwa rayuwa ba haka take ba musamman ta gidan aure da kanaji kana gani da gaskiyarka za'a take maka ita kuma dole ka haqura, sai gashi yau tun ba'aje ko ina ba zata fara shan wahalarta a hannun wanda shine ya d'orata akan tarbiyar,

Da kuka hajia mama taje ta iskesa tafad'a masa halin da batool d'in ke ciki amma duk da yaji badad'i haka yaruntse idanuwa yace ta tafi tabashi waje, matuqar bazata haqura dayaron nan ba to saidai tamutu, hakan yasa takoma wajensu uncle h tasanar dasu halin da ake ciki,

Uncle hassan da kansa yaje qofar d'akin nata ya bubbuga had'e da kiran sunanta, lokacin tana kwance sai faman juye juye takeyi saboda yunwar data isheta, daqyar ta tashi taje tabud'e gambun tare da b'are baki tafad'a jikin uncle hassan tana kuka, da yake yanada sanyin hali ba kamar uncle Hussain ba ya d'agota yana sallallami yace da hajia mama.

Kingani ko hajia abunda muke fad'a masa akan yarinyar nan yakasa fahimta!, don ALLAH dubi yanda baqar sangarta da kafiya irinta yarinyar nan daya d'orata akai kenema ta illatata babu gaira balle dalili, meye amfanin wannan rayuwa haka?

Qara lafewa jikinsa tayi tana kuka saiga uncle Hussain shima yashigo, tsawa ya katsa mata had'e da cewa tanemi waje ta zauna, wani kukan tasake sawa da qarfi da yasa abban nata fitowa, yana ganin 'yan uwan nasa tare da ita yajuya zai koma uncle Hussain yace.

Ina kuma zakaje? Ai sai kaqaraso ka ida aikin naka tunda mun fiddo maka da ita, da sauri hajia mama taje ta d'auko abinci ta ajiye a tsakar falon uncle hassan yaja hannunta yaje da ita ya zaunar da ita gaban abincin.

Ganin yanda ta canza cikin kwana biyu ba yanda take son ganin taba yasa Abba d'an sassabtowa daga fushin da yayi ya matso kusa da ita, tana ganin haka tamiqe zatabar wajen yayi saurinsa hannu ya riqeta,

Batool yanzu saboda naqi amincewa ki jefa kanki cikin quncin rayuwa da yaron da baida asali kike nema ki illata kanki, yafad'a yana qare mata kallo yanda tad'an fad'a cikin kwanaki, juyawa tayi tana kallon uncle Hussain had'e da cewa, kaji ko uncle?, Fuskarta kamar zatayi kuka,tsabar takaici da bazai iya tsayawa yana kallon wannan kayan haushi ba yasa uncle hussain yayi tafiyarsa, haka hajia mama da uncle hassan suma bayansa sukabi suka ficewarsu suka barshi daga shi sai ita suyi yanda suke so...





*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[11/14, 22:52] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___74πŸ’Ž

Murmushi yayi tare da juyawa yana kallon batool data kasa tashi sannan yace, gimbiya kidaure kitashi, lalle ayau nafara hango gwagwarmayar da zakisha wajen tattala mani soyayyarki, kidaure komai za'ayi maki akaina kijure matuqar zuciyarki tayarda da cewa nid'in zan cika maki alqawarin dawowa agareki da kuma zamowa Abu sumayyarki da kike mafarki akaina, ni kuwa ina tabbatar maki da cewa zanja daga kuma nayi d'amarar yaqi da duk wani da zai shiga tsakanina dake,

Bubbuga saiti zuciyarsa yayi sannan yaci gaba da cewa, wannan zuciyar ta Abu sumayya takice ke kad'ai gimbiyata, zagi da aibantawa basu isa suhanata qaunarki ba, kisa aranki ina sonki, Ina sonki, Ina sonki kuma ina qaunarki fiye da tsammani, cike da wani irin farinciki tamiqe tsaye tana murmushi tare da dawowa gabansa tana kalonsa tace, da gaske kakeyi kana sona?, kana qaunata? Kamar yanda kafad'a?.

Sosai kuwa gimbiya, fiyema da kalaman da bakina suka fad'a, kisa aranki nid'in nakine kuma kema tawace komai tsanani komai wuya, ba gudu baja da baya kinji ko?.

Nayarda, na amince kai d'in zaka zame mani tamkar wata fitila da zata haskake duk wani duhu dake tare dani kuma zaka zamo ruwa da zasuyi maganin duk wata datti da zata demeni aduniya, maida kallonsa yayi ga hajia nafeesa data koma tamkar wani mutum mutimi tsaye agabansu bud'e da baki tana kallon batool data daddage tana zarowa masoyinta kalaman da zasu dad'asa ya yadda da tsantsar soyayar da takeyi masa d'ari bisa d'ari sannan yacewa batool, kinyi alqawari?

Nayi alqawari Abu sumay..., Bata qarasa ba sakamakon buge mata bakin da hajia nafeesa tayi had'e da jan hannunta tabar wajen da ita, shidai baice da ita uffan ba saima kallon batool d'insa da take faman ja yakeyi itama tajuyo tana kallonsa had'e da sakar masa wani sassanyar murmushi mai cike da tarin ma'anoni kala kala shima yana mayar mata har sukabar wajen,

Wata irin ajiyar zuciya ya sauke had'e da cewa, coming home Abba, hakan d'ai zai bani damar mayar da duk wani martani ga waccan baiwar ALLAH,

Ai baka isa ba, domin duk wanda yasai rariya yasan zatayi zuba kuma ita halak ana barinta ko don kunya, kuma dama ai duk wanda yaqiji bayaqi gani ba, ummace kefad'ar haka da itama tun d'azu tafito da taji halshen hajia nafeesa tana koro kalamai marasa dad'in ji data tabbatar da cewa da jikan natane takeyi.

'Dan sosa qeyar kansa ya shigayi yana kallonta taqasan idanuwa ita saima yabata dariya, don gaba d'aya kamanninsa basu nuna yadamu da kalaman da hajia nafeesa tayi masa ba, mere baki tayi had'e da juyawa zatabar wajen tana fad'in, to ai shikenan duk tsuntsun da yajawo ruwa shi zasuci, yayi saurin cimmata had'e da d'ora kansa asaman kafad'arta yariqe hannunta yana cewa, kiyi haquri 'yar tsohuwa, ya zanyi da cutar data riga tashigeni kuma narasa magani,

Ai sai kayi indai Aishatu ce tana gefe iya karta dakai addu'a,

Yawwa kakata takaina, indai addu'arki natare dani nasan Babu abunda zai shiga gabana tunda tariqe gwaggona cikin amincewar ALLAH.

Sarkin salo, to ai saika cikani kuma ka d'agamun kafad'a kada angona ya shigo ya hangoka.

Eyyeee! lallai ummarnan karkisa kishina ya motsa yau aja daga tsakanina da shi, har kinada wani ango daya wuceni?.

Soqo tayi masa ga kai har zata sake kai mas na biyu yayi saurin d'auke kansa daga kafad'arta tare da sakin hannunta yabar wajen aguje yanufi sashen ammie yana dariya, tace ja'irin banza kawai sannan tawuce part d'inta.

Cike da sheshshekar shaqiyanci yashiga falon na ammie yafad'a kan kujera yana dafe qirjinsa, ammie dake zaune tana karatun qur'ani ta d'ago kai tana kallonsa bayan takai aya had'e da cewa.

Maigida lafiya?,

Ummace ke neman saka qwaqwalwata ababireshon saboda wani soqo data kaimun, shinefa zata qara nagudo wajenki don nasan ke tattalina kikeyi. Saida tayi murmushi had'e da rufe alqur'anin sannan tace, to halama kai mekayi mata ne?

Banyi mata komai ba, wai kawai don nace batada angon daya fini kuma sai naja daga da tsohon mijinnan nata shinefa take nema tasaka qwaqwalwata awaqi'a..

Ai kafin yarufe baki itama ammie ta d'aga hannu zata sakar masa wani soqon tana fad'in, to bari natayata nima tunda qashinka yagi daya girma shiyasa kake neman jan daga da gudan alhajin namu, da sauri yaruga yana cewa, kai ashe gudun gara nayo..saiga dady yashigo had'e da cewa, ai kuwa ka fad'awa zago, fad'amun meka aikatawa matan nawa suke nema yau sukarya munkai, ga hajia nafeesa can nabaro tun daga bakin gate najita tana fad'a da yarinyar nan da tazo wajenta, sai gashi dana shiga kuma takawomun qararka, yaqare maganar tare da azo hannunsa saman kafad'arsa suka dawo cikin falon,

Cike dajin kunya yazube qasa bayan ya zauna shikuma dady nakan kujera ya sunkuuar da kai tare da gaishesa ya amsa yana kallonsa yana dariyar abunda hajia nafeesa tace masa azuciya, wai takamashi zai b'ata mata 'yar uwa, to gaba d'aya nawa yaron yake kuma cikin gidan inane da wurin da hakan zata iya faruwa batare da angansa ba, ahankali yafurta ALLAH yakyauta yana sauke wata irin ajiyar zuciya, sannu da zuwa tayi masa tare da kallon little Nuraddeen tace, to katashi kugwada mana, sum sum yamiqe yafita dady yace dawo ka zauna.

Tambayarsa ya shigayi meye tsakaninsa da batool, yayi masa bayani sosai batare daya b'oye masa komai ba, hatta yanda sukayi da umma da kuma mahaifiyarsa Rashida duk saida yafad'a masa, jinjina kai dady yayi sannan yace dashi, katabbata kana son yarinyar?, noce kai yayi had'e da cemasa eh dady.

Dady yayi murmushi tare da shafa kansa yace, shikenan! Kaje kayi karatunka da kyau kuma kafito da babban sakamako ni kuma nayi maka alqawarin matuqar Ina raye zan nemo maka auren batool in Sha ALLAH kaji ko.?

Little ya amsa masa cike da farinciki.

Kud'i yafiddo masu yawa yabashi yace yaje ya ida qarasa sayayyar abubuwan da suka rage masa kan yawuce jibi in ALLAH yakaimu, godiya yayi masa sosai sannan yamiqe zai fita dady yace.

Zauna abunka ni fita zanyi, kaidai kabi umurnin mahaifiyarka kuma ka kula da amanar da kad'aukarwa yarinyar mutane domin abun tambaya ce agareka, ni kuma nauyine akaina incika maka wannan alqawarin dana yimaka, maida kallonsa ga ammie yayi had'e da cewa, ranki shidad'e akwai wani abun? don dama part d'in umma yake kawai ya shigone yaga ya take da kuma intana buqatar wani abun kamar yanda yasaba ako yaushe in yana part d'in wannan to idan yadawo duk sai yashiga na saura tukuna zai shiga inda yake, girgiza kai ammie tayi alamun babu yace, to Masha ALLAH, ALLAH yamiki albarka, qoqarin ficewa yayi yana dariya had'e da cewa ashe ke hajia nafeesa abokin garawar nan tawa ganin yayi duk kun tsufa shiyasa yake neman d'auko maku wata shine like neman sakashi awaqi'a ko Nuraddeen? Sosa kai yashigayi cike da jin kunyar ashe duk yaji abunda take fad'a,

Bayan yafita ammie ta tadashi agaba tanata yimasa Sheri wai yaro dashi yana neman yatadasu tsaye da zancen biki yanata dariya had'e da cema yadaiji duk cikin kishine shiyasa tafad'i hakan, sun jima suna fira da ammie yaci abincinsa yaqoshi sannan yayi mata saida safe, part d'in umma yakoma da yake dady yasanar da ita duk abunda yafaru tanata fad'a har tana cewa wai duk laifinsa ne daya biye masa har yake d'aure masa gindin nemo masa aure shida baida komai nayin auren inbanda baqar rigima irin tasa, saida yace mata ai bayanzu take nufi ba sai nan da idan yagama karatu sannan yabar fad'an, harar Nuraddeen d'in daya shigo yimata Saida safe tayi sannan tafiddo wani saqo ta ce yakaiwa Fatima tana gaishesu da yaran gaba d'aya sannan yawuce

Hajia nafeesa kuwa cikin daren takira mahaifin batool ta sanar dashi cewa takamata tana soyayya da wani yaro agarin dake neman ya lalatata, Kuma yaron kowa yasani agarin shegene, gaba d'aya takwashe qarya da gaskiya ta sanar dashi har tana qarawa da cewa yu takamasu yaron yana neman lalatata, badon ALLAH yakawota ba da batasan iya abunda zai faru ba don haka yaturo a d'auketa gobe gobe, tsabar makirci irin na hajia nafeesa hadda fashewa tayi da kuka Wai tanajin tsoro tinda wajenta tazo kada wani abun ya sameta.

Shi kuwa mahaifin na batool wato alhaji umar fari Wanda ya kasance d'aya daga cikin jerin masu kud'in da za'a iya lissafowa dashi a garin daidai gwargwado ranshi ya b'aci sosai yanata fad'a, daga qarshe ma yace tabashi batool d'in,

Duk da tarin soyayyar da yakeyi mata haka yarufe idanuwa jin cewa tana tare da yaron da shegene bayada uba yaci mutuncinta sosai tare da cewa ta harhad'a inata inata gobe zai turo a d'auketa sannan ya kashe wayarsa yanaci gaba da masifa, 'yan uwansa dake zaune tare dashi suka zura masa ido suna kallon ikon ALLAH, Abu kad'an ke tunzura yayan nasu yayita fushi yana fad'a batare dayayi bincike ba, d'aya daga cikinsu wanda shike bimasa duk da dai qannen nasa 'yan biyune wato Hassan ya kalli d'an uwan sa hussaini sannan yamaida kallonsa ga yayan nasu alhaji umar fari yana fad'in, Haba Yaya ko meye dai kayi haquri tunda kayanke hukuncin da kake so, sai kajira idan tadawo kaci gaba da yimata fad'an, Amma yanzu ko Ina ana jinka kuma ba'asan koda waye kakeyi ba ai kaga babu dad'i, cike da zafin rai yajuyo yana fad'in, za'a San koda waye nakeyi idan nasa ankamo Mani wancan shegen yaron marar uba dake bibiyar 'yata,

Murmushin takaicin kalaman daka fitowa daga cikin bakin yayan nasu husainin yayi had'e da cewa, ashsha yaya, duk meyayi zafi haka da kake aibanta yaron mutane?, Kai kasan cewa duk duniya babu wanda ake haihuwa bada uba ba inba annabin ALLAH isa da adamu (a.s.w) ba, sannan idanma har aka haifi yaro tahanyar daba daidai ba to kuskurene akirasa da shege domin bashine shegen ba, iyayen da suka haifesa tahanyar daba daidai d'in ba sune shegun, kuma fa duk wannan fad'an da kakeyi ni banga amfanin saba tunda bakada tabbaci akan abunda aka fad'a, don ALLAH ka kwantar da hankalinka idan batool d'in tadawo sai ka binciketa kaji idan har gaskiyane,

Kubarni da ita, ganin Ina nuna mata soyayya shiyasa take nema ta kwasomun abun kunya agida kuma wlh hakan bazata tab'a yuyuwa ba, taya zata fad'a mani gaskiya tunda son yaron akace tanayi kamar jela, harfa kuka akace tanayi masa tan faman duqawa agabansa don tsabar sakarci, tir, tir halan Bata san cewa wutsiyar raqomi tayiwa qasa nisa ba?

Haka yaci gaba da suruttansa ko gajiya bayayi, ganin bashida ranar denawa yasa suka yimasa saida safe suka tafiyarsu batare da sun zauna sunci gaba da firar da suka sabayi dashi duk dare ba.

Batool kuwa ranar kwana tayi tana kuka tare dajin tatsani 'yar uwar tata dake nema tarusa mata dukkanin farincikinta, akaro nafarko kenan arayuwarta da mahaifinta ya taba yimata irin wannn fad'an harda zagi batare daya saurareta ba,

Ita kuwa hajia nafeesa wani irin farin cikine taji kwance azuciyarta, aganin tasamu hanyar da zatasa awalaqanta umma da ita har shegiyar zuriar tata kamar yanda take fad'a...






*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[11/14, 22:52] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___78πŸ’Ž

Shikuwa ashe lokacin ko barci bai tashiba don gaba d'aya ya shafa'a da zancen fitar da zasuyi, kwance yake yana baccinsa hankali kwance uncle hussain d'in ya d'an bubbugi qafarsa ya tashi yace dashi.

"Kaje baba na kiranka tun d'azu ya shirya kai kad'ai yake jira."

Yana gama fad'ar hakan ya juya yafita da sauri yamiqe yafad'a toilet yayo wanka, bai tsaya wani abuba yana tsane jikinsa yaciro qananan kayansa yasa had'e da zura takalminsa yafito, a tsakar gida ya samesa yafito daga cikin d'aki matan nabiye dashi suna yimasa addu'ar ALLAH ya kiyaye ya gaggaishesu cikin girmamawa had'e da karb'ar ledar hannunsa yana gaishesa shima.

Kallonsa baba balarabe yayi tun daga sama har qasa bayan ya amsa masa gaisuwar had'e da cewa.

"Kar kace dani yanzu katashi bacci Naga kamar akwai sauransa acikin idanuwanka."

"Aikuwa dai, don gaba d'aya na sha'afa da zancen tafiyar nan, koda uncle Hussain yaje bacci nakeyi."

"To kawo ledar, maman 'yan biyu jeki kizubo masa abun karya warsa."

"A'a d'an tsohona mutafi, idan naje can sai na karyar."

"Anya zaka iya kuwa?"

"Eh mana, muje tunda ba noma ne zanyi ba."

Su maman 'yan biyu nata yimasa dariya had'e da tsokanarsa wai kar yaje yadawo masu kamar a hurasa yafad'i, murmushi kawai yayi masu had'e da juyawa yafita baba balarabe yabi bayansa suna biye dasu suma suna yimasu ALLAH ya kiyaye.

Suna isa kasuwar bayan ya taimakawa baba balarabe yabud'e shagonsa na kayan d'unki da yadukkan mata da yake saidawa suka gama jejjera komai sannan yasamu waje ya zauna yana kallon yanda d'aid'aikun mutane ke shigowa cikin kasuwar da sauran masu shagunan da suka fara bud'ewa, dariya baba balarabe yayi had'e da cewa

"Yaufa mazan boko ne akasu sai faman raba idanuwa sukeyi, ko yazata kaya dasu?"

"Sa ido kagani, zaka sha mamakin mazan bokon nan sosai, don yau zakayi cinakin da baka tab'a yiba."

"Ah..to madallah ai haka akeso, bara ni naje can nadawo." Yafad'a tare da ficewa yabar shagon, wajen wani mai saida tea da biredi yanufa yace ya bashi leda d'aya ta biredi da madarar ruwa gwangwo d'aya sai bonbita itama sachet d'aya sannan yasa ya soya masa qwai guda ukku tare da ruwan tea a cup ya karb'a yanufo shago dasu, a daidai bakin qofar shiga shagon nasa da yake akan hanya wucewa cikin kasuwar yake yaci karo da baffa d'auke da kondon kajinda yake sayarwa shida yaransa da suke biye dashi d'auke da sauran kwandunan kaji suna shigowa saboda tuni yakoma sana'arsu adalilin qarewar da dabbobin nasa da ada yake kasuwancin saye da sayarwa dasu, gashi badamar ya rabke hannuwa tunda iyali sun riga da sun taso masa don yanzu Masha ALLAH, ALLAH ya albarkacesa da 'ya'yaye har biyar aduniya, yanada 'yan mata hud'u da kuma namiji d'aya wanda shine qarami yanzu yanada shekaru biyar aduniya, hakan yasa yakoma sana'ar kiwon kaji acan gida irin buloros d'innan kuma yana zuwa dasu anan kasuwa yana saidawa kuma balaifi yana samun cinaki sosai da yake rufawa kai asiri dashi, da sauri ya qarasa wajensa fuskarsa asake yamiqa masa hannu yana fad'in.

"Barka da shigowa malan Idris anshigo?"

Baffa da kallo d'aya zakayi masa ka tabbatar da ankwana biyu aduniya shima yamiqa masa hannu fuskarsa ba yabo ba fallasa yana


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login