Showing 210001 words to 213000 words out of 260204 words

Chapter 71 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt

baqin cikin da dole suka qarfafa masa ya tafiyarsa, sannan tajawo matarsa tasamu damuwa da tab'in hankali saboda qazafin da akayi mata nacewa ita ta halakar da yarinyarku, har nake fad'a maka cewa aranar suka wuce asibitin sokoto da ita sunata ALLAH ya isar had'a jini daku, wlh balarabe duk wud'annan maganganun dana fad'a maka ba gaskiya bane, qagaggiyar qaryace na shirya don cimma wani burin nawa sai gashi sanadiyar hakan najawo matsaloli da dama arayuwar mutane, don ALLAH da girmansa kayi haquri kayafemun wataqil nasamu rangwame acikin hukuncin da ALLAH ya tanadar mun, na nayi kuskuren d'aukar mata a matsayin abokanan shawarata, nayi nadamar cutar da 'yan uwana da nayi dama ku kanku don ALLAH kuyafeni."

Shiru duk sukayi kowane yarasa abun cewa sai faman jinjina kawunansu sukeyi saboda giraman kalaman da sukaji nafitowa daga bakinsa, Banda kallonsa yana faman sheshshekar kuka tamkar wani qaramin yaro babu abunda sukeyi, tabbas ko ba'a fad'aba kasan rayukansu sun b'aci musamman baffa Usman, duk da kallo d'aya idan kayiwa baffa Ali zaka iya tabbatar da cewa daga kalamansa har zuwa yanayin fuskarsa yayi nadamar abunda ya aikata daga qasan zuciyarsa, jiki a sanyaye baba balarabe da tuni ya dad'e da gano qarya daya fad'a masa wanda har yasashi nadamar abunda yayiwa su baffa ya nemesu gafara, ajiyar zuciya yayi had'e da cewa.

"Wannan shi ake kira da ranar nadama da kuma dana sani, haqiqa baka kyautawa 'yan uwanka ba ka zaluncesu da yawa sannan kasa nima nacutar dasu tahanyar d'aukar hukuncin da bai kamata ba, nazamo silar raba zukatan daya kamata ace rouhinsu da gangar jikinsu nawaje d'aya awannna lokacin, saidai hakan yafaru duk bisa shiryowar ubangiji, ni tuni nayi nadamar abunda nayiwa 'yan uwanka don nagane ba gaskiya kafad'a mani ba kuma na nemi yafuwarsu duk da ban fad'a masu dalilina na aikata hakan ba saboda gudun lalacewar zumunci tsakaninku, sannan d'an uwa da d'an uwa dama sai ALLAH idan akayi qoqarin shiga tsakani kunya akeji, nasan komai daren dad'ewa matuqar muna raye sai wannan gaskiyar tafito kuma sai ALLAH ya bayyanata, don haka tunda yanzu kafad'i komai da bakinka inma kanada laifi awajena nayafe maka, saura naka kanemi yafiyar d'an uwanka domin shine mafi qololuwar cutarwa acikin wannan al-amarin, ubangiji ALLAH karabamu da biyewa zukatanmu da kuma aikin dana sani."

Yana gama fad'ar hakan yayi saurin juyawa yafice don gaba d'aya ji yake yau komai ya dawo masa sabo, da ace bai yarda da maganar daya fad'a masa ba aranar da yanzu Rashida da yaronta basu fuskanci baqin cikin da suka shiga cikiba akwanakin baya, wataqil da tuni Nuraddeen yadawo zuwa garesu, da yanzu d'an uwansa daya rasa ta dalilin hakan yana raye duk da dai mutuwa ita batada fashi.

Sallama mijin Yaya Maryam shima yayi masu sannan yabi bayansa cike da ta'ajabin hali irin na baffa Ali.

Kallonsa baffa Usman yayi cikin b'acin rai yace.

"Yanzu hakan da kayi daidai ne?, Kayi farinciki ka lalata sunnar annabi?, Kayi farinciki kasaka mu cikin damuwa? Kai kuma gakanan acikin farinciki madawwami ko?, tir wlh albasa batayo halin ruwa ba, iyayenmu kaf babu mai baqar zuciya irin taka, wace ribace zakaci don ka hana asanar damu dawowar Rashida alokacin daya kamata dahar tasa ka tafka mana irin wannan qaryar! Wlh Yaya duk abunda malan balarabe yayi sai yanzu nafahimci bayada laifi kuma wallahi da nine shi sai na aikata fiye da abunda yayi saboda banga yanda za'ayi wannan qaryar takasa samun gurbi azukatan da aka gama cutarwa ba tunda gabakin jininmu shaqiqinmu da muke tare waje d'aya dashi akajita, to mezaisa akasa yarda da ita tunda ba mutum yayi kanshi ba, bashi keda ikon zuciyarsa ba balle yahanata b'aci akan wannan baqar qarya wacce batada tushe balle mafari, Kai kam..."

"Ya isa haka Usman, kada ka la'ancesa mana, kome zai faru yariga daya faru ALLAH ya shiryesa, yayi hakanne cike da tunanin zai d'auki fansar qarar dana kaisu ga hukuma ne aka kullesu, indai yarage wannan zafin da rad'ad'i azuciyarsa ai shikenan Bakomai, ni nayafe masa Ina roqon nima ALLAH ya yafemun daku baki d'ai, ka qyalesa kada kasaka mashi wata damuwar bayan wannan lalurar da yake ciki don ALLAH"

Wani irin takaici baffa Usman yaji aransa, Wai shi wane irin mutunne daya fiye sanyin hali haka, babu ta yanda za'ayi a qure haqurinsa har ya nuna b'acin ransa sai inta b'aci sosai, fiii yayi yabar wajen don baima san abunda zaice masa ba.

Baffa kuwa dake jin wani qunci aransa binsa yayi da kallo har ya fice yayi murmushi had'e da cewa.

"ALLAH yakyauta yasa mufi qarfin zukatanmu."

Hannuw baffa Ali yasake had'awa waje d'aya hawaye kwance a fuskarsa zai sake roqonsa gafara yayi saurin riqewa yana fad'in.

"Karka tashi hankalinka, nace nayafe maka duniya da lahira, bawai don banji zafin abunda kayi mani bane a'a, kawainayi hakanne saboda kwad'ayin nima ALLAH ya yafemun don mukam yanzu gangara kad'ai ya rage mana mu ida tare da fatan cikawa da Imani, saidai ina roqonka daka kasance mai iya sarrafa zuciyarka akoda yaushe bawai ita ta sarrafaka ba kaji ko Aliyu.?"

"Zan kiyaye haka Yaya in Sha ALLAH."

Murmushi baffa yayi tare da riqe hannunsa ya gyara masa kwanciyarsa sannan yace.

"Bari naje wajen d'an uwanka indawo kafin likita yazo muji ko zamu samu sallama cikin satin nan."

Yana gama fad'ar haka yafice aransa yana addu'ar ALLAH yasa shiriyar daya dad'e yana nemawa d'an uwan nasa ce tazo kuma yaqara had'e kawunansu waje d'aya.

••• ••• •••
A 'bangaren mahaifin batool kuwa gaba d'aya ya hana ko sunanta yaji an ambata a gidan, gashidai yanajin kewarta atattare dashi Amma baqar zuciya tahanasa fahimtar cewa itad'in wani b'angarece arayuwarsa dake da matuqar muhimmanci atattare dashi, tun yana keb'e kansa daga mutane izuwan duk fushine yakeyi har yagaji ya bari, su uncle h kuwa girman da suke basa ada sai sake lunkashi sukayi awajensa, ko kad'an sunqi nuna masa sun damu da fushin da yakeyi dasu da kuma shashsharesu har shima yagaij ya sauko don kansa ammafa har lokacin yaqi bada damar da za'a iya tunkararsa da zancen batool ko kad'an, sau da dama takan kira lambar wayarsa yaqi d'agawa ko kuma takira tasu uncle idan suna waje d'aya ya fahimci da ita ake wayar sai yatashi yabar wajen, hakama hajiya mama itama idan tana tare dashi yaji ankirata kuma takira sunan batool zaice ta tashi tafice masa daga d'aki ko tabar wajen daon baya buqatar jin koda sautin muryar tane, ganin yanda fushin nasa ya tsananta yasa gaba d'aya duk abunda ya shafi batool ba'ayinsa idan yana kusa saboda azauna lafiya, kuma hakan yasa yafara dawowa da yanayinsa nada duk da shi kad'ai yasan irin wahalar da yakesha aqoqarinsa na ganin cewa lallai lallai sai ya manta da ita arayuwarsa.

Batool kuwa kullum addu'arta ALLAH kajuyo mata da hankalin abbanta ya manta da abunda yafaru don wani zubin damuwar har hanata bacci takeyi tayita kuka sai little yata faman lallashi ko yakira hajia mama yafad'a mata tayi mata nasiha tare da kwantar mata da hankali tukuna sannan yasamu takwanta har tayi bacci.

Baya ga wannan batada wata damuwa aduniya saboda tana samun kulawa sosai awajen mijinta da kuma ahalinsa, wata irin soyayya Rashida keyimata tamkar ta mayar da ita cikin ciki, duk abunda zai b'ata mata rai Rashida taja kunnen little daya nisancesa ko don halaccin data yimasa arayuwa, tana matuqar jin batool aranta da har wani lokaci take tunanin idan har ahaka akejin sarakanai ma'ana 'ya'yan d'anka arai meyasa ita tata uwar mijin bata so taba? Meyasa tanuna mata tsanar da ko kishiyarka bai kamata ka nuna mata ba don taga ummanta bata tab'a nuna cewa tatsani hajia nafeesa ba duk da irin cin kashin kare da aibatawar da take yimata ita da jininta.

Batool tazama 'yar gata, ba awajen mijinta kad'ai ba hatta su Dr da dady suna kulawa da ita sosai ba'a batun umma data d'auketa tamkar little jikanta, duk abunda ta yayo duniya ita dai akaiwa batool, ammie ma na iya qoqarinta don duk abunda zata yiwa matar faruq to saita had'a da batool da kuma imaan matar Shakur d'and'an hajiya nafeesa.

Ganin haka yasa umma tayi kwad'ayin yin haka koba komai ai dady ya kyautata masu baici ace ta wofantar da nashi ba tana nuna banbanci don itama takan sayi abubuwa wani lokacin tace akaiwa su Fatima da matar faruk wace yarinyarsu ma ta farin mai sunan ammie ana kiranta Islam tana hannun umma tun lokacin da za'a yayeta takarb'eta shikenan sai suka barta nan basu amsheta ba, gaba d'aya kulawarta tadawo tsakankanin ita da kuma ammien, hakan yasa ranar umma tasa ayo mata odar turarukkan wuta da khumra's masu qamshi acan kano wajen wata hamshaqiyar dilan kayan qamshi masu qamshin gaske dake saidasu bisa sassauqan farashi mai suna nana hafsat (miss xoxo) wacce anfi sanin sana'ar tata da sunan da takeyi mata laqani da *YERWA INCENSE* kayanta kam akwai kyau sosai don idan kagane amfani dasu to tabbas qamshi ya aureka duk inda kaje kaida 'ya'yanka, miji kuwa ba zancen zaman fira awaje saboda mararin yadawo gida ya shaqi wannan dadda'an qamshi dake kwantar da hankali da kuma natsuwar zuciya, ( _hajia wannan ba qanzon kurege bane, sai kin gwada zaki iya tabbatarwa, don haka idan kina son hana mijinki fira awaje saboda daddad'an qamshin da kikeyi keda 'ya'yanki da gidanki to kinemi YERWA INCENSE akan lambarsu ta talfo kamar haka👉 +234 809 521 5215 na tabbata zaki Sha mamaki kuma ki gode mani_ ) son da umma keyiwa kayan qamshinta yasa tasa aka kawo mata bokitayyen turarukkan da kwalaben khumra's d'in don ta rabawa sarakanan nasu, bayan ta kakkasa masu taba shahida ta d'auka taje ta kaimasu sai ta tuna da bata bada na imaan ba wato matar Shakur, da sauri tabi bayan shahida dahar takai bakin gate tana qwala mata kira riqe da bokitin turaren wutar d'aya da kuma kwalaben khumra's guda biyu a leda, muryarta da hajia nafeesa tajiyo yasata fitowa ta zauna akan d'aya daga cikin kujerun dake gefe wajen motocin Abba da alama baqi yayi suka tafi ta zauna tana lallatsar wayarta saboda tsabar gulma.

Batare da umma ta damu da ita ba tunda tariga tayi niya tamiqawa Shahida ledar tana fad'in.

"Ungo wannan mantawa nayi idan kin shiga kin bawa maman islam nata saiki biya ki kaiwa imaan wannan, kice muna gaishesu sosai..."

Ai bata rufe baki ba taji anbuge ledar da qarfi tafad'i qasa, da sauri ta d'ago kai sukayi ido biyu da hajia nafeesa sai wani faman huci takeyi sai kace wacce akayiwa laifi, bata tankata ba ta duqa zata d'auki ledar wacce ga alama kwalaben dake ciki sun mutu tasa qafa ta sake murza ledar bokin turaren ya fashe sannan tashurasu gefe tana fad'in.

"Ho iyayen munafucci da asiri, wane mugun abunne za'a d'auka akaiwa matar d'ana don arabani da ita, meye alaqarki da ita ko ina ruwanki da ita da zaki d'auki abu kice akai mata ban da baqin sheri dake zuciyarki da kuma iyayi.!"

Duk wannan abu dake faruwa ashe agaban idanuwan Abba ne lokacin yafito daga part d'in ammie zai shiga na ita hajia nafeesar ya d'auko wasu takardu ya hango abunda hajia nafeesar tayi, ran umma ya 'baci sosai amma saita qyaleta saboda bata buqatar tanka mata har tazamo silar jawo wata fitina agidan tadalilinta, inda ta shura kayan umma taje tasa hannu zata d'auke sauran don wasu duk sun d'an watse musamman turaren wuta sai taga anrigata, d'ago kan da zatayi sai sukayi ido biyu da dady, lumshe idanuwansa yayi sannan yabud'e yana murmushi had'e da cewa.

"Amaryata wannan wane irin turaren wutane mai qamshi da kuma sanyaya zuciya haka?" Saida ya d'an lakuto damshin ruwan khumrar dake jikin ledar ya sake sunsunawa had'e da rufe idanuwa sannan yaci gaba da cewa "kai! Masha ALLAH, wannan qamshin khumra haka sai kace an tattara qamshin turaren duniya aciki, fad'amun a Ina aka sayeshi kuma nawa nima in siya don na burgeku." Yafad'ai hakan da gangan yana kallon gefen da hajia nafeesa ke tsaye kamar an dasa ta da gefen ijiya.

Yanda yayi maganar yasa umma sakin murmushin da seda haqoranta suka bayyana suka miqe tsaye tare yana riqe da ledar sai qara shin shina yakeyi, Shahida kuwa sai faman toshe dariyar dake son fito mata takeyi aranta tana fad'in wannan tsohon akwai gwamawa mutun takaici, can tajiyo muryarsa yana kiran sunanta da sauri ta qarasa had'e da cewa.

"Na gaisheka tsoho mai ran qarfe, kayi naka kayi ta raggo ka dad'e kayi shekaru adadin yawan gashin rago,"

Dariya yayi had'e dasa hannu aljihu ya qirgo dubo goma ya miqawa umma yana fad'in,

"Ungo wannan asake kawo wasu sai akai mata, ke kuma Shahida ungo wannan ledar kikaiwa imaan d'in kice tayi haquri sun fashe tayi amfani dasu za'a sake kawo mata wasu." Yaqare maganar had'e da miqawa Shahida ledar ta amsa tawuce tana kallon hajia nafeesa da tayi fam tana dariya.

"A'a alhaji kabarshi akwai wasu zan sake bayarwa akai mata, basai ka wahalda kanka da kashe kud'in kaba." taqare maganar tana qoqarin saka mashi kud'in a aljihu, riqe hannunta yayi had'e da cewa

"Maman Rashida kibarsu kije kiyi yanda nace kawai ai hakan shine adalci."

Kafin yarufe baki hajia nafeesa tayo kukan kura kan umma ya zura mata idanuwa yana kallo yaga mezata aikata shima ya aikata mata irinsa sai yaga taja burki ganin kallon da yake yimata tafara zuba ruwan masifa inda take shiga ba nan take fita ba harda fad'in.

"Indai zalunci abunyine yaje yaci gaba dayi, akan tsohuwar mace yabi duk ya susuce ko tsufansa baya gani don kunya Bata ishesa ba agaban jikoki, to wlh in su anbasu sun canye anayin yanda akeso dasu ita ba'a isa ba, munafuccine banxa da wofi ai wannan kinimbibine za'ayi mata."

Cin mutunci kam dashi har umma tayi masu sai wanda tamance saboda zafin kishin abunda yayi mata, gaba d'aya idanuwanta sun rufe ta manta cewa yayi mata jan kunne akan karta sake takoma d'auko masa wata fitina agida baya buqatar haka sai gashi abun yauma takansa ya qare, Saida tayi mai isarta tagama sannan yacema umma tawuce part d'inta ita kuma yace daga nan karta kuru taqara taku d'aya cikin gidansa ta tafi gidansu sai yanemeta.

Wata irin gud'a ta ski had'e da cewa.

"Tafi nono fari, don ko yanzu nafita gidanka bazan rasa mai so ba, don haka takarda ta yakamata kabani ba kace intafi gidanmu ba, kana tunanin wai zaiji baqin cikine don kace intafi gidanmu?, to wlh ko d'aya don ko yanzu kasuwa tawatse d'an koli mai rabonci yaci."

Cikin yaranta ta qwalawa kira tace a d'auko mata mayafinta da takalmi dama wayarta na hannunta, ana kawo mata tasa had'e da cewa.

"To Ina jiran takarda ta mijin tsohuwar..."

Bata qarasa ba ya daka mata tsawa had'e da nuna mata gate yace tafita baya son ganinta...








*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___94💎

Batare data damuba tasa qafa taficewarta daga gidan, waje yanema ya zauna d'aya daga cikin kujerun dake wajen ya dafe kai, gaba d'aya yarasa wace irin rayuwace ga hajia nafeesa wacce batada lissafi da kuma sanin yakamata, ko kad'an bata gajiya da fitina arayuwarta duk kuwa yanda za'a jamata kunne, yana iya qoqarinsa wajen ganin yayi haquri da halayyarta har zuwa lokacin da zata canza amma hakan ya cutara har saida taqure haqurinsa tasa ya aikata abunda bai tab'a aikatawa tun qurciyarsa sai yanzu da manyanci ya kamasa.

Haka ya qarashi tunane tunanensa har yagaji yamiqe yakoma cikin gida yana mai Shan alwashi akan cewa koda zai amince tadawo masa gida saita gane gaba d'aya kurakuran data dad'e tana aikatawa tukuna,

Kimanin watanni takwas kenan da aurensu su little kuma adadin watannin cikin batool, zaune take tamimmiqe qafafuwanta tana faman yatsinar fuska saboda nauyin da cikin yayi mata, gaba d'aya duniyar tayi mata zafi ji take kamar ta fasa ihu, kallon little tayi dake mammatsa mata qafafuwanta alokaci d'aya kuma yana d'ibar wainar fulawa ga cokali yana bata abaki tace.

"Abu sumayya, agaskiya 'ya'yaye na d'auke da haqqin iyayensu sosai, sai yanzu nake jin tsananin rad'ad'in rashin kyautawar da nayi abbana azuciya akan kafiyar dana yimasa, da nabi komai ahankali da yanzu abbana bai haramta mani kusantar saba, wayyo...ni wannan karauniyar ce da akeyimun cikin ciki bana so wlh, Awwshhhh...ya ALLAH kabiya iyayenmu da alkhairi wlh da wahala renon cikin nan sosai,

Tafad'a had'e da d'an muskutawa tana qoqarin jinginawa a jikin kujera, cike da tausayinta ya d'anyi murmushi had'e da cewa.

"Ayya!, Yihaquri gimbiya, dama dole ai zakiji haka, kema ALLAH yabiyaki ya saukeki lafiya, idan summynmu tazo saina qwangare mata kai tunda ta wahalar mun da gimbiyata haka"

'Dan b'ata rai batool tayi tana turo baki gaba had'e da cewa.

"Karma kafara don bazan lamunta ba, yarinya 'yar gwal 'yar baiwa zaka dokanmun ita, ai kuwa da anjimu ko sumayya tah."

Taqare maganar tana shafar cikin nata tana murmushi, murmushin shima yayi mata tare da cewa.

"Kice akwai match agidannn don na lura sumy a partyn adawa zata zomun Kuma bazan yarda ba."

"Shikenan tunda kace haka, damankasan ita zatayi wining match d'in shiyasa kake adawa da ita, ni kama dena kiranta da sumy kana b'atawa yarinyata suna, sumayya take baiwar ALLAH."

"O'oh Anya gimbiya!, to shikenan nadena ranki shi dad'e ummu sumayya ALLAH ya saukeki lafiya."

Ta amsa da amin tana dariya.

Bayan sati d'aya da yin hakan takira mahaifiyarta hajia mama suka gaisa sannan tayi mata batun komawarta gida wajen wankan jego, ai kuwa nan hajia mama tayita yimata fad'a had'e da cewa tayi haquri ta zaunawarta gidan mijinta ta haihu babu abunda zai faru da ita in sha ALLAH tunda tana samun cikakkiyar kulawar da koda itace ke tare da ita iyakar ta zata bata, duk da bata so hakan ba haka ta haqura don kuwa ba k'arya gwargwado babu abunda tanema tarasa a fannin kulawa tun daga kan mijinta har zuwa mahaifiyarsa da sauran natare da ita, sun zame mata uwa da uba kuma sunyi mata gatar da bata tab'a tsammani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login