Showing 174001 words to 177000 words out of 260204 words
Chapter 59 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt
zancen shiryawa ya wuce makarantar, wani saurayi dake nan gefe zaune da alama yaron baffane dake taimaka masa ya kalla tare da cemasa"
"Dan ALLAH idan kaka yadawo kace masa nawuce saboda nakusa makara."
Gyad'a masa kai saurayin yayi sannan shi kuma yawuce yana d'an d'aga qafa saboda yasamu yayi saurin isa da wuri.
Baiyi mintuna biyar da barin wajenba baffa yadawo yana tambayar saurayin ko ina yake? ya bashi amsa da cewa ai yawuce yace afad'a masa cewa sauri yakeyi yakusa makara shiyasa.
Ba haka baffa yaso ba don yaso ace yasan ainahin sunansa ko don mutuncinsa tare da kulawar daya bashi, amma duk da haka in sha ALLAH zai tambayi baba balarabe yafad'a masa tunda shi kullum suna tare a kasuwar.
Da lokacin tashinsu baffa yayi yasa masu yin dako suka d'aukar masa kwandunansa suka kaimasa bakin titi inda zai samu mota ya biyasu kamar yanda yayiwa little alqawari sannan ya d'auki kaji uku cikin sauran kajin da suka rage masa yanufi shagon baba balarabe dasu da niyar yabashi aba little amma ga mamakinsa sai ya isko shagon arufe da alama har ya rigashi tashi, Bai kawo komai aransa ba yawuce abunsa duk da aransa ba hakan yaso ba saboda dama wasu lokutan akwai lalurar da zata iya tasowa ya rigashi tashi ko shi yarigashi tashi, duk da dai su sunfi rigansu tashi saboda yanayin sana'ar tasu da kuma gari daba d'aya ba.
Baffa na isa gida bayan yawatsa ruwa yaci abinci yashiga labartawa matarsa nusaiba zancen saurayin daya gani d'an gidansu baba balarabe muryarsa da tafiyarsa sak ta Nuraddeen d'insa, kallo d'ayazakayi masa kaga banbancin farincikin daya samu yau fiye dana kullum, yaqare zancen yana fad'a mata cewa tabbas duk yanda akayi wannan yaron jininsa ne, amma zai tuntub'i balaraben yaji gaskiyar maganar don shidai jikinsa yabashi hakan.
Murmushi tayi itama fuskarta d'auke da farinciki saboda ganinsa cikin yanayin da tadad'e tana son ganinsa aciki tace.
"To kodai jita jitar da Yusuf yafad'a maku ashekarun baya gaskiyane cewa sunga yarinyarsu?"
"To banida tabbaci akan haka sai naje natuntub'esa tukuna, ada na musanta zancen na Yusuf saboda atunanina bazai yuyu ace anga yarinyarnan kuma akasa sanar damuba a matsayinmu na iyayen mijinta, koba komai muma munada haqqi musan halinda take ciki duk da mungaza wajen nemota, amma yanzu ganin yaron nan jikina yabani kamar akwai wani b'oyayyen al-amari da fushin zuciyar da nayi yasa nakasa saninsa."
"To koma dai meye ALLAH yasa hasashenmu yazamo gaskiya."
"Amin, maman Rashida, Ina suka shigane suda aminina."
"Sunje gidan baffansu gano Inna hawwa? Shikuwa amininka yana d'akinsa yana bacci." Tafad'a tare da qwallawa bashar da suke kira da Abba kira. Amsawa yaron yayi had'e da shigowa da gudu dama tund'azu ya matsu yaji kiran nata saboda yasan amininsa yadawo kuma tabbas yazo masa da wani abun.
"A'a Abba meye haka! Bazakayi tafiya ahankali ba sai kaje kajima kanka ciwo kabar mutane da wahala."
"Nadena Babar mu." Yaron yafad'a tare da nufar inda baffa yake yana dariya, hannu yabasa suka gaisa yana fad'in.
"Sannu da zuwa baffanmu kasiyo mana alewar?".
"Yawwa aminina, nasiyo maka kai kad'ai bada kowa ba." Rungumesa yaron yayi yana kallon nusaiba dake d'an harararsu cike da tsokana tana b'ata rai tace.
"Sufa 'yan matan nawa?, Adenafa yimasu 'yan ubanci akan aminin marar jin magana." taqare maganar tare da kaimasa ranqwashi akai, b'ata rai yayi zaiyi kuka baffa yace.
"Qyale babarku, 'yan matan nata ai sunyi girma da yawa baza'a basu ba, badon yayanku da baya nan ba da yanzu na aurar da Rashida itada zainaba, kaga narage maka abokan takara, ya rage daga asiya sai Bilkisu ko?"
"Yaya zai dawo baffa in Sha ALLAH ko?"
"Eh aminina kunadai yimasa addu'a ko?"
"Eh baffa." Yaron yafad'a baffa yaciro sweet da biskit d'in daya siyo masu yabashi nashi sannan yace yaje yajirasa a waje sutafi gidan baffa Usman.
'yan maganganu suka qarasa da baba nusaiba sannan yafito yariqa hannunsa suka nufi wajen baffa Usman da shima yanzu ya manyanta sosai,
Sun jima suna fira dashi akan zancen da yasanar da baba nusaiba na yaron daya gani tare da baba balarabe daga qarshe suka yanke shawarar zasuje masa a mutum su sake tuntub'arsa zancen Rashida don susan gaskiyar lamarin.
Baffa Ali kuwa ba'a maganarsa don tun shekaru biyar da suka wuce yaje gona maciji ya saresa a qafa har sau biyu, babu maganin daba'a nema masa ba amma ba'a dace ba, gaba d'aya qafar ta sundule masa baya zuwa ko nan da can, a d'akinda baffa yayi jinya ashekarun baya anan shima yake jinya, gaband'aya yayi baqi yarame amma babu wani sauyi da aka samu na halinsa, kullum cikin baqinciki yake na zaman da yakeyi waje d'aya baya zuwa ko Ina, duk iya taimako da kulawar dasu baffa keyi masa baya gani kullum cikin tsinarsu yakeyi, shi baya iya fita ya bid'o idan kuma sun kawo masa Inna ruqayya sai tace baza'a amsa ba tafiso tafita tayo bara da takarb'i abin hannunsu gori yayi masu yawa nan gaba, haka kuwa akeyi, bakunya ba tsoron ALLAH take Jan muneera sufita bara tana fad'in ataimaka mata mijinta ne ke cikin mugun yanayi gashi yabarta da d'iya, 'ya'yanta sunyi fad'a har sun gaji amma taqi bari, Yusuf da har ya girma shima yayi fad'an da rarrashi da ban magana Amma takasa fahimtarsa, idan yaje yayo 'yar buga bugarsa yanemo yakawo masu sai tace baya isarsu, haka ya haqura ya zuba masu ido duk da bai dena abunda yakeyi ba, in safiya tawaye haka zata kama hanya ita da muneera sufita bara tana yimata jagora basa dawowa sai bayan la'asar, abinci ma sai Inna Bilkisu ta samma baffa Ali dake jinya yayita qorafi an bashi kad'an ko yace badon ALLAH aka bashi ba, Kuma hakan bai hana yaci, Inna Bilkisu saidai ta kallesa tagirgiza kai domin tuni tagama d'aukar darussan rayuwa aduniya, acewarta ita yanzu batada lokaci inba nata qara neman kusanci ga ubangijinta ba saboda yanda shekaru sukaja, Amma su ko yaushe mugun nufi, qyashi da kuma hassada basubar zuciyarsu ba, halin da baffa Ali ke ciki idan shi mai hankaline ya isa yad'au darasi aciki domin qarara isgilin da yayiwa d'an uwansa ne ALLAH yamaido masa akansa amma yakasa fahimtar hakan, don ma ALLAH yataimakesa da samun d'a irin yusuf dake da matuqar jinqai da tausayi, akoda yaushe shike tare dashi yana bashi kulawa daidai gwargwado duk da baya yaba masa daga tsiga sai zagi da kuma ganin la'ari.
••• ••• •••
Baba balarabe kuwa tun ranar da yadawo kasuwa zazzab'i mai nauyi yarufesa, Saida yayi sati biyu bai koma leqawa kasuwa ba saidai su Hassan da hussaini suje, hakan yasa su baffa basu samu yin magana dashi ba, sunso iskosa gida da maganar amma da sukaji zancen bashida lafiya sai suka fasa, little kuwa gaba d'aya karatu ya d'auke hankalinsa, bayada wani lokacin zuwa kasuwa sai baka rasa ba kuma duk yaje sai yashiga wajen baffa, baffa na matuqar jin dad'in irin kulawar da yaron kebasa wanda hakan yaqara saka masa son sanin kowaye shi,
Wata irin shaquwace sosai tsakaninsa da shi da bazai iya kwatanta taba duk da dai bako yaushe suke had'uwaba, ana haka baba balarabe yasamu sauqi ranar da kansa ya shirya yaje har garinsu baffa bebeji don little nafad'a masa irin kyautatawar da yake yimasa, da yawan tambayar lafiyarsa da yakeyi wanda hakan ya tabbatar masa da akwai abunda take zuciyarsa yake son tambayarsa Kuma yad'auki alqawarin koma me zai faru zai sanar da baffa duk abunda yakamata yasani ko zai rage nauyin dake cikin zuciyarsa, saidai zaiyi hakanne tare da roqonsa alfarmar daya tabbata ba lallene yasameta ba amma yana fatar samunta ko don kaucewa lalacewar zumuncinsa da 'yar uwarsa...
_Bazance komai ba, Amma Ina mai roqonku don ALLAH da girmansa kuyi mani afuwa bisa jini da kukayi shiru, in Sha ALLAH bada jimawa ba zamu kammala littafin nan kusa kusa da yardar ALLAH ngd sosai👏🤝_
*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶♀️🚶🏻♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻♂️🚶♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎
_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*
_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋
_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞
*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖
*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️
Page___82💎
Ba gwaggo Rashida kad'ai ba hattasu Dr da dady sunyi farincikin sakamakon daya zomasu dashi tare da sanya masa albarka, nan take Rashida tashirya masa 'yar qwarya qwaryar walima don nunama ALLAH godiyarta daya gwada mata wannan lokacin,
Bayan ankammala walimar ne data samu halartarsu dady, ammie umma harma dasu Dr. da Fatima da suka kasance masu masaukin baqi, cikin zolaya Dady ya kalli Rashida had'e da cewa.
"To Rashida, tunda yanzu ALLAH yanufa ya kammala karatunsa lafiya sai kiqara dagewa wajen yimasa addu'a domin ba anan nake son karatunsa ya tsaya ba in Sha ALLAH har sai ya had'a master's d'insa, inda nake son turasa qasar Lebenon shida d'an uncle d'inki wato qaninsa Abbaty," d'ansu dr nafarin da akayiwa marigayi baba takwara.
Zaro idanuwa tayi tana kallon dady, da sauri su Dr da fatima harma da su ammie dake kallonta suka qumshe dariyar da tanemi kuccikke masu ganin kallon da takeyi masa suna kallonta, ganin yanda kowa ya tsuro mata idanuwa yasa ta had'iye maganar dake neman fitowa daga bakinta had'e da maida kanta qasa,
Dady da shima dariyar ke neman fito masa yayi saurin had'iyeta had'e da cewa.
"Rashida naji kinyi shiru bakice komai ba?"
Saida ta runtse idanuwanta saboda yanda maganar ta dirar mata a lokaci d'aya cikin zuciya tare da tuna mata da mijin nata da har yanzu takasa mantasa aranta sannan yace.
"Duk yanda kukayi dady ai kuma kuna da iko akan shi, banida ja ga duk hukuncin da kuka yanke akansa."
"To Masha ALLAH, in ALLAH ya yarda nan da wata uku zan..."
Bata bari yaqarasa ba tayi saurin d'ago kanta tana kallonsa had'e da cewa.
"A'a Dady! Agaskiya nidai bana sha'awar hakan ko kad'an, nafiso ya zauna anan gida tare damu yaci gaba da karatunsa ko kuma idan aure yake so sai yayi aurensa, hakan zai fimun kwanciyar hankali sosai fiye da yaje qasar wajen nan qaro karatu!"
Awannnan karon gaba d'aya kasa riqe dariyarsu sukayi duk suka kece da dariya don dama da biyu dady yayi hakan, yana so ne yaje kano nemawa Abu sumayya auren batool kamar yanda ya alqawarta amma baya son Rashida tadakatar dashi ta hanyar qin amincewarta saboda sanin matsayin da take dashi awajen 'yar uwar yarinyar da kuma qanqantar shekarunsa, don lokacin shekarunsa ashirin da biyar bai dad'e da shiga cikin ta ashirin da shida ba, wanda zata iya lab'ewa tanan tace abari sai nan gaba ko kuma tace tafiso yaci gaba da karatun, murmushi dady yayi sannan yace.
"Taya zayayi aure tunda bakyason ya had'a karatu da soyayya, kuma kinsan matuqar yana nan qasar dole sai ya had'asu tunda qara girma yakeyi, inaga zaifi sauqi yaje can yayi karatunsa kinga idan ya kammala sai yazo nan yayi aurensa hankali kwance kamar yanda kika buqata."
'Bata rai tayi kamar zatayi kuka tana kallon dr had'e da cewa.
"Don ALLAH uncle kace wani abun, gaba d'aya dady bai fahimceni ba."
Ware hannuwa Dr yayi alamun babu ruwansa ta kalli umma itama ta kauda kai gefe, wajen ammie tanufa tariqo hannunta tare da cewa.
"Ammie don ALLAH kicewa dady ko duka biyun zai had'a masa na amince amma kar ataurasa wajen nan, wlh tsoro nakeji kar yaje shima..."
Saurin rufe mata baki ammie tayi tana dariya sannan cikin muryarta dake nuna manyantar da tayi tace.
"Kenan kin amince yayi aurensa ko yaci gaba da karatunsa.?"
"Duka na amince ammie idan ma biyu yake so ya had'a amma anan qasarsa."
Dariya ammie ta kwashe da ita sauran mutanen dake wajen na tayata tace.
"Ja'ira, ai dama ansan halinki shiyasa aka b'ullo maki ta hakan, ni Ina ganin nakai ga maigida ya isa aure tunda yanada masoyiyarsa amma duk kikabi kika riqe masa mara kika hanasa fitsari, to yanzu tunda yagama karatunsa lafiya saiki sakar masa ita in Sha ALLAH wani sati alhaji zaije can kano su had'u aje gidansu yarinyar nan a nemo masa aurenta, Ina dai kin amince ko?"
Wata irin kunya ce tarufeta da sauri ta tashi tashige cikin gida sunata yimata dariya, gaba d'aya yau d'an kawicin nata da takeyi masu akn yaron soyayyarsa takasa bari tayi masu don bilhaqqi har qasan zuciyarta bata buqatar yaronta yafita kowace qasa da sunan karatu koda kuwa da gaske sukeyi bazata amince ba saidai aga rashin kunyarta.
Fatima data bita da kallo tana dubin yanayin jikinta, Inka ganta bazaka tab'a yarda cewa ita tahaifi Abu sumayya ba tace.
"Ina ruwan auntyn yara, ai banga laifinta ba nikam, tama d'an jure data iya saurararku, don da nice wlh bori zan azawa, dady ai ko abbaty bazan yarda yaje waje karatuba wlh balle ita da take ganin sanadiyar hakan mahaifin little yabarsu gaba d'aya."
"Da gaskiyarki kema my dota, ALLAH dai yaraya manasu kuma yanuna mana shima mahaifin nasa yadawo, wannan abun da yafaru yana d'aya daga cikin rashin amfanin fita wajen karatu, kawai bama ganewa ne, Amma babu abunda zakaje can qasarsu ka karanto da bazaka iya karantarsa anan qasarka ba, ko tsabar son kai irin nasu nasa suriqe mutum acan saboda basa son cigaban tamu qasar." dady yafad'a cike da takaicin abun.
Ita dai umma tunda taji an d'auko zancen mahaifin little batace komai ba saima komawarta gefe da tayi ta zauna tana kallon samarin dake har had'a kujerun da akayi walima dasu wasu kuma na warware rumfar da aka kakkafa, gaba d'aya bata son jin zancen Dr ko kad'an saboda duk daren ALLAH sai tayi kukan halin da 'yar tata keciki, wanda badon haka ba da yanzu itama ta tara nata zuri'a a gabanta kamar yanda su Fatima da Dr keda su, don yanzu 'ya'yansu bakwai aduniya, bayan haihuwar abbaty, shahid da shahida, walida, sultan da kuma jidda fatima ta sake haihuwar zainab wanda yanzu tanada shekaru goma aduniya saboda haihuwarsu da takeyi kusa kusa daga ita kuma bata sake haihuwa ba.
Ganin haka yasa little yaje inda take ya zauna tare dasa hannuwansa ya tallafe fuskarta yana kallonta, d'an harararsa tayi takai masa ranqwashi akai had'e da cewa.
"Lafiya?" Saida ya d'an sosa wajen yayiwa fuskarsa kamar zaiyi kuka sannan yace.
"Da zafi umma."
"Ai Kai kajawa kanka, meyakawo nan!"
"Haquri nazo nabaki, Naga kamar kinajin haushin mahaifina ne har yanzu?"
Jin tayi jikinta yayi sanyi saboda yanayin yanda yayi maganar sai taji yamatuqar bata tausayi, hannunta ta d'ora akan nasa tana d'an mummurzawa a hankali alamun ban haquri sannan tace.
"Kayi haquri amma Ina matuqar jin haushin mahaifinka saboda yanda yasa mahaifiyarka ta b'ata duka qurciyarta akansa, dole naji ba dad'i ko kad'anne domin bana son ace yanda take 'yah tilo awajena itama yazamana taqare rayuwarta kai kad'ai awajenta, duk da wannan hurumine na ALLAH amma ina fatar ace ita tatara zuri'a fiye dani."
Sosai little yafahimci pain d'in da takeji a matsayinta na uwa, don haka sai yayita fad'a mata kalamai masu matuqar sanyi da kuma dad'i da zasu kwantar mata da zuciya har saida yaga tasaki takoma daidai yanda take d'azu sannan yabarta da yake su dady najiranta suka wuce gida.
Bayan anyi sallar la'asar little ya iske mahaifiyarsa cikin shirinsa na manyan kaya yayi matuqar kyau har yagaji, murmushi tayi data kallesa tare dayin hamdala tana Mai godewa ALLAH acikin zuciyarta da yayi mata ni'imar samunsa a matsayin d'ah, murmushi ya sakar mata ganin rin kallon da takeyi masa itama tana murmushi yace.
"Gwaggona barka da marece, anwuni lafiya?"
"Yawwa little, lafiya klw, wannan irin gayu kuma sai Ina?"
Saida ya sosa kansa sannan yayi qasa dashi had'e da cewa.
"Kano zanje in Sha ALLAH."
"Tohh!..injin dai lafiya?, Ina yau d'in nan da safe kadawo?, to kuma me zakaje yowa a can yanzu?"
Shiru yayi batare daya bata amsa ba yanaci gaba da sosa kansa har lokacin kan nasa na aqasa tayi murmushi don tafahimci inda zancen yanufa!.
"Au shiyasa tun dawuri kaje ka kai qarata gunsu dady akayi mani shigo shigo ba zurfi?"
Dariya yayi tare da d'ago kansa yace, "haba dai mamana!, ALLAH yatsareni da son duk wani abu da zaisa har inkai qararki ko awurin waye kuwa, shi dady kawai alqawari yayimun shiyasa yayi hakan, ni kuma bisa umurninki nayi mata alqawarin bazan sake waiwayarta ba har sai ranar dana cika maki burinki, shiyasa yau dana tabbatar da hakan nake qoqarin itama naje nacika mata alqawarinta."
"To kayi haquri ranka yadad'e har zuwa gobe tukuna kaga yanzu marece yayi, yaushe har ka isa kuma har kace kaje zakaje wajenta, ai kamata yayi ace yau kafin kazo kafara zuwa saboda kada jewad'in yayi yawa."
Zaunawa yayi ya tanqwashe qafafuwansa agabanta kamar mai shirin d'aukar karatu sannan yace.
"Duk duniya Babu wanda yakamata yafara sanin nasarar dana samu inba keba hakan yasa nafara zuwa agareki domin neman sa albarkarki da kuma addu'o'inki kafin naje wajenta, idan hankalinki yafi kwanciya dana bari sai gobe zanyi hakan don faranta maki koda kuwa zuciyata bata so."
"Eh bawai nafi son hakan bane, kakirata kaji idan tayarda kabari sai goben shikenan don kada ta d'aukeka cikin masu karya alqawari."
Murmushi yayi had'e da cewa.
"Dame zan kirata gwaggo bayan tunda muka rabu da ita bamu koma waya ba balle muhad'u da ita, asalima har nasoma mantawa da muryarta saboda nadad'e banji ba, wataqil itama ta canza lambar waya tunda jiya ba yau ba."
Riqe kunnensa tayi had'e da cewa.
"Da kuwa kazamo gajiyayye a fannin soyayya domin komai dad'ewar masoya basu had'uba idan da halacci bazasu manta muryar juna ba matuqar akwai amana a tsakani."
"Kiyi haquri mamana da abunda zance, kenan hakan na nufin har yanzu kema baki manta da muryar abbana ba?."
Jikinta a sanyaye tasaki kunnensa da take riqe dashi fuskarta na mai sauyawa daga yanayin farinciki da take izuwa damuwa, da sauri yayi nail down had'e da cewa.
"Kiyafemun idan fad'ar hakan ya b'ata maki rai, akoda yaushe Ina mai qoqarin nesanta kaina da duk wata kalma data shafi mahaifina saboda nafaranta maki kamar yanda kike buqata amma hakan ba yana nufin na manta dashi bane a matsayinsa na uba awurina, kiyi haquri bana gaji bane da bin umurninki kawai yau natsinci kaina da fad'ar hakanne sanadiyar abunda kika fad'a, don ALLAH kada kiyi fushi dani akan haka"
Ganin yanda yadamu yasa