Showing 138001 words to 141000 words out of 260204 words

Chapter 47 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt

sha kuma sun huta tukuna sai acigaba da jajantawa juna wannan al'amarin inaga hakan shiya kamata."

Takowa baba yayi zuwa wajen alhaji ubale fuskarsa d'auke da farinciki marar misaltuwa yamiqa masa hannu suka gaisa, murmushi alhaji ubale yayi tare da riqe hannun har suka nemi waje suka zauna yana fad'in.

"A gaisheka mai gayya mai aiki."

Juye juye baba yafarayi yana neman Dr nura wanda shine yaje yakirawosa ganin abunda kefaruwa, cike da mamaki ya hangosa ajikin qofa yanad'e hannayensa aqirji yana tunano ranar daya fara ganinsu baba, sai yau yatuna da muryar umma dako yaushe idan yai yake tunanin inda yasanta ashe ta maman boy ce, lalle ALLAH gagara misali ne kuma huwarrahmanu yau yaqara imani akan cewa tabbas duk yanda bawa yakai maqura wajen son had'a abu aikin banza yayi matuqar ba ALLAH da kansa yaso hakan ba, yamatuqar sha wahala wajen neman iyayen rashida don ya had'asu amma ALLAH bai yarda da hakan ba sai yau da yaga dama, sai gashi cikin sakanni ya had'asu da kansa, haqiqa al'amarinsa abun girmamawa ne kuma duk wanda baiyi imanin cewa shi kad'ai keda iko wajen had'awa da kuma rabawa ba, ansa da hanawa, qaddartawa da kuma jarabtawa, iko akan komai aduk lokacin da yake so, ayanda yake so,a kuma inda yake so haqiqa yayi asara duniya da lahira.

Da hannu baba yayi masa alama da yaqaraso daga ciki sannan yabaro wajen yana murmushi, duqawa yajeyi agabansa da sauri ya rungumesa yana fad'in.

"Nagode sosai dr."

Rashida kuwa gaba d'aya ta naniqe ajikin umma takasa bari tamatsa konan da can, so take ta tashi tariqowa ammie abinci ashigo dashi amma itama shauqin soyayyar 'yar tata yahanta motsawa wajen, gani take kamar inta saketa zata sake dawo ta tadda bata nan, gashi bazata iya barin ammie taci gaba da kaida kawo ita kad'ai ba, don haka sai tamiqe riqe da hannunta kamar wacce za'a kwacewa tanufi kitchen d'in da ita, gaba d'aya falon sukabita da kallo musamman Dr. da yau yamatuqar qara gaskata kamar dake tsakaninta da umma da kuma little dake hannun fatima yana zallo ta d'aukesa da sukazo wucewa taqi.

Suna kaiwa bakin qofar shiga kitchen sukaci karo da ammie ta d'auko kuloli da sauri umma tamiqa hannuwa zata karb'a tace.

"A'a umma, ai kuma yanzu shikenan wannan aikin yadawo hannun maishi dama taimaka mani ne kikeyi, gashi da alama yau maman boy bazata bari ko lumfashi kiyi ba."

Sai alokacin umma talura da yanda ta k'wak'wume hannun Rashida sosai da sauri tasaketa cike dajin kunya tana karb'ar kulolin hannun ammie sannan tabar kitchen d'in.

Ganin ammie naqoqarin d'auko wasu kayan yasa Rashida itama ta taimaka aka jejjere abincin kowa yaci ya qoshi,

Bayan sun kammala aka shiga maida maganganu inda Dr yashiga basu labarin adadin mayannun da yayi wajen nemansu da had'uwar da yayi dasu atasha da irin halin daya tsinci Rashida aciki tare da irin ciwon da little yayi tamkar bazai rayuba, duk dasu baffa da daddy sunsan da labarin tawani b'angaren yanzu su baba yake baiwa hakan bai hanasu jin tamkar yanzu suka fara jinsa ba, umma da baba sun zubar da hawayen cike da tausayawa 'yarsu sosai kafin baba yamiqa hannu yakarb'i little Nuraddeen dake hannun Dr.

"ALLAHU akabar, duk wannan abun daya faru anyisa ne saboda kada kazo duniya karayu, amma da yake kai alqawarin ALLAH ne saida ya tsaro fitowarka tahanyar jarabta mahaifinka da mahaifiyarka, haqiqa rashin sani yafi dare duhu sannan alqawarin ALLAH tabbatacce ne ko ana so ko ba'a so, badon haka ba dabanyi kwad'ayin aurar da mahaifiyarka abagiren da ba'a buqatar taba duk da dai nasan cewa matsalar ba daga mahaifin kabane."

'Dago kansa yayi had'e da yima Dr godiya marar adadi kafin suma su dady yayi masu godiya sosai shida sauran 'yan uwansa san mazan suka tashi suka tafi wajen sallah su kuma matan suka tsaya nan part d'in ammie sukayi tasu,

Rashida kam bin umma tayi sashenta sukayi sallarsu atare, addu'o'i sosai da washi da yabo umma tayi ga ALLAH tana mai godiya daya maido masu da 'yarsu agaresu cikin qoshin lafiya, haka shima baba har kowa yafito masallaci aka barosa shikad'ai yanata yiwa ALLAH godiya.

Bayan sun dawo suna zazzaune falo ana sake maida firar yaushe gamo can sai ammie dake zaune tare dasu ummu taqara volume d'in makekeyir tv d'in dake laqe a bango tana fad'in. "Alhaji gafa maimaicin shirin da kake so nakiwon lafiya uwar jiki, da baka samu ka kalla jiya ba."

"Af sun fara?" Dady yafad'a had'e da maido hankalinsa ga tv sannan yace.

"Ai inaga saidai nahaqura wannan karon tunda banida lokaci, ki saurar inyaso anjima saiki maimai tamani tunda naga kema yanzu kina son shirin."

"Eh gaskiya Ina so saboda akwai abubuwa masu muhimmanci da ake qaruwa dasu ciki ko umma?"

Taqarasa maganar tana kallon umma dake zaune ita dasu Yaya Maryam suna fira, Rashida kuwa nacan d'aki ita da fatima da little.

Sosai ammie tanatsu tana sauraren bayanin da likita keyi akan wata cuta da matar da ake nunowa wadda ke d'auke da ita su kuma sunaci gaba firarsu.

"Yawwa 'yata zo kiga maimaicin labaran jiya da nakiraki na fad'a maki cewa yau ki kalla saboda it's very important to all the marry woman."

Ammie tafad'a tana kallonsu Fatima dake fitowa daga cikin d'aki,

Wata irin qara sukaji Rashida dake bayanta tasaki had'e da cewa.

"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, umma..uncle.baba."

Gaba d'aya duk tabi duk ta rud'e ta kasa yin magana sai nuna tv takeyi da ake nuno irin yanayin da Yaya hawwa keshiga idan ciwonta ya tashi.

Kafin kace me duk sun maido hankalinsu akanta Fatima na rirriqetatana tambayar ko lafiya, yanda sukaga hankalinta ya tashi yasa suka maido hankalinsu ga tv suma suna son fahimtar ko meye dalilin da yasata firgita hakan, iya kallon da zasuyiwa matar da ake nunowa a tv sunyi amma basu gano komai ba saboda da yawansu ma basu santa ba balle su iya ganeta cikin wannan lalurar da take ciki.

Saida aka d'au d'an lokaci ammie dake riqe da hannun Rashida jikinta har tsima yakeyi tace.

"Alhaji inaga bari akashe kallon nan, domin yarinyar nan jikinta har wani cira yakeyi."

Har tamiqa hannu zata kashe Yaya Maryam tace.

"A'a hajia dakata, kibarshi muga irin sakayyar da ALLAH keyiwa bayinsa wud'anda suka cutar da wasu bayin nasa, wannan matar da kuke gani ba kowa bace face surukar Rashida data nemi salwantar da rayuwarta data d'anta saboda son zuciya, ya ALLAH Ina godiya agareka da keke gaggauta yin wani hisabi tunduniya saboda sauran bayinka su wa'aztu."

Wata irin zabura baba yayi had'e da miqewa tsaye yana sallallami yana kallon Rashida don tabbatar da abunda yayar tasu kefad'a, jinjina kai Rashida ta shigayi tana kallonsa itama had'e da cewa.

"Baba innar mu ce, meye yasameta haka!?" Tana kuka.

"Anya Rashida itace?, Innarku fa kikace mahaifiyar mijinki Nuraddeen? don ALLAH ki kalla da kyau kada kitayar mana da hankali."

"Wlh baba itace, bazan tab'a mantawa d fuskarta ba, innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, nashiga uku umma Ina ya nura yatafi haka yabar Inna acikin wannan halin?, wayyo ni ALLAH baba, meye yasami Inna haka."

Duk wanda ke falon binta yayi da kallo cike da mamakin lafuzzan dake fitowa daga bakinta, musamman Yaya Maryam data soma hasala ganin kukan da takeyi, cikin b'acin rai ta katsa mata tsawa had'e d cewa.

"Kirufa mana baki ko inzo intakaki awurin, munji mungani itace, sai akayi me kuma da zaki azawa mutane kuka?"

"Haba gwaggo! Haba gwaggo, uwar mijina face!, Surukata kakar d'an dana haifa, taya bazanyi kuka ba tana cikin wannan yanayi, gwaggo kidubi fa yanda takoma, dubi irin wahalar da take sha, don me baza'a tausaya mata tunda rayuwace itama."

"Rashida fita d'akinnan kafin na sab'a maki, gwaggon taki ke fad'a kema kina fad'a?" Baffa yafad'a ransa a b'ace.

"A'a bashar, ba dakai takeyi ba don haka kabarni da ita."

Shiru baba yayi had'e da komawa yasamu waje ya zauna jikinsa a mace, haqiqa ubangiji Mai jujjuya al'amurransa ne aduk lokacin da yaso, yau gashi 'yarsu da akaso ajefa cikin wani hali a haukatar masu da ita ALLAH yakareta ita kuma wacce taso hakan agareta ALLAH yajuyar da al-amarin akanta dama haka rayuwa take _(aljaza'u min jinsil amala)_ sakayya nazuwa daidai da irin abunda ka aikata.

Muryar matar baba balarabe hajia Aisha yajiyo tana fad'ar.

"Banda abunki Rashida meye na kuka awannan al-amarin? abunda ta aikatane ya koma mata, to tawane dalilin za'a tausaya mata, kiduba adadin mutanen data jefa cikin wani hali fiye da shekara d'aya, su kwana cikin qunci da baqincikin rayuwa duk ta dalilinta, ke kanki da mahaifanki harma damu duka sai yau ALLAH ya yaye mana d'inbin damuwar dake dasqare acikin zukatanmu, taya za'ayi ALLAH yabarta da wud'annan haqqoqa data d'aukarwa kanta batare da anbima bima masu sub?, Ai addu'armu d'aya itace ALLAH yakaremu da son zuciya irin nata."

"Kar kice hajia mama," da yake haka suke kiranta.

"Dukkaninmu bayi muke ga ALLAH, kuma babu wanda yawuce ajarrabi rayuwarsa da khairan ko kuma akasin haka kuma bawai don namanta da abunda tayi manine ba nake tausayin wannan halin da take ciki, kawai ina tausaya matane saboda darajar haihuwa da tayiwa mijina koba komai ma ai baza'a tab'a canjawa tuwo suna ba, matsayinta na kakar jininku baza'a tab'a kankaresa ba, kuma idan kun duba itama rayuwace kamar mu, wlh hajia mama indai akan abunda ta aikata agareni ALLAH ke azabtar da ita haka nayafe mata duniya da lahira."

Bud'e baki Yaya Maryam tayi da niyar yin magana maigidanta alhaji ubale yayi saurin dakatar da ita.

"Haba Maryam, don me zakiyi qoqarin tirsasata bijirewa kyakkyawar zuciyarta, wlh bana tantama akan yarinyar nan bazata tab'a walaqantaba duniya da lahira saboda akowane irin yanayi dake samunta arayuwa takan kasance mai tsarkakakkiyar zuciya da kuma haquri, ni inaga ku k'yaleta, tanda ikon yafewa duk wanda taga dama, tazubar da hawayenta aduk lokacin da take so kuma ta tausayawa duk wanda taga yadace domin ita take da iko akan zuciyarta, kamata yayi kuyi alfaharin samunta a matsayin 'ya tagari ba kuyi qoqarin chanzata izuwa kangarariyar 'yaba."

Saida Yaya Maryam tawatsa mata wata iwar harara tukuna sannan tace.

"To ai shikenan saita shirya muwuce mukaita wajenta tazauna tayi jinyarta, inaga haka shiyafi kuma shi zatayi tanunawa duniya kyawon zuciyarta da kuma tausayinta."

Murmushi dady da tund'azu ya mayar da hankalinsa ga tv yana mamakin irin yanayin da yaya hawwa take ciki kuma har ahalinta suka tsaya b'ata lokacinsu wajen zuwa asibiti, duk wanda yakalleta da abubuwan da takeyi yasan ba komai ke damunta ba illa matsalar jinnu ce, duk abubuwan da suke fad'a yana jinsu kawai yayi shirune saboda atunaninsa ba huruminsa bane, amma yanzu kalaman Yaya Maryam dake nuni da yanda ranta yab'aci su suka sakashi murmusawa har yake tunanin yakamata yace wani abu awannan gab'ar, musamman idan yayi la'akari da cewa akwai rashin cikakkiyar wayewa atattare dasu wanda yasa har suka iya irin wannan musayar bakin a inda bai kamata ba, kamata yayi ace sun ajiye wannan matsalar a tsakaninsu idan sun koma gida domin sirrin suce amma yanayin qaramcin wayewa dake tattare dasu yasa sun kasa fahimtar hakan.

Saida yayi gyaran murya sannan yafara basu haquri akan su ajiye wannan matsalar daga baya saisu zauna su tattauna akanta domin hakan shine sirri agaresu sannan yayi masu nasiha sosai sannan ya sake tayasu farincikin had'uwa da junansu da sukayi.

Sai alokacin baba balarabe da duk jikinsa yagama sanyi yayi ajiyar zuciya tare da sake miqa godiyarsu agaresu shida d'ansa bisa taimakon da sukayiwa 'yarsu da d'an uwansu da kuma matarsa.

Saida akayi sallar la'asar sannan su baba balarabe suka kama hanyar komawa, sunso a haukarsu su koma dasu umma da baba amma sai Dr ya roqesu subari idan an kwana biyu sun shirya tsaf sai yawuce dasu tunda wurin aikin sane,

Haka suka tafi cike d'inbin alkhairin da dady da ammie sukayi masu suna masu yabawa nagarta irin tasu, haka Dr nura shima ba'a barshi abaya ba don yayi masu alkhairi sosai harda suturu ya siya masu da sauran kayayyakin da zasuyi tsaraba dasu, saida yarakasu har suka fita gari sannan yajuyo ya koma can gida suka shiga tattaunawa da dady akan qudurinsa na mayar da Rashida makaranta da yayi gashi kuma yanzu da alama iyayenta bazasu barta anan ba idan suka tashi komawa.

Murmushi dady yayi had'e da cewa.

"Haba nura, ai kayi wauta, taya daga baka amanar yarinya zaka d'auko zance maida ita makaranta bayan kasan akowane lokaci zata iya komawa hannun iyayenta, bayan haka karka manta yarinyar nan tanada aure bai kamata ace kai tsaye kana zartar da abubuwa akanta ba, don haka ka ajiye maganar komawarta makaranta, iya taimakon daya kamata kayi kayi basai kashiga hurumin da ba naka ba kaji ko."

"Eh dady." Yafad'a yana mai yaba hangen nesa irin na mahaifinsa, sai yanzu yafahimci gaba d'aya shirmene yaso tabkawa, nan suka cigaba da tattaunawa akan sauran alamurran dake gabansu kafin akira sallar magrib suwuce masallaci, bayan anyi sallar isha'i yashigo part d'in na ammie Fatima na kwance ta tattake da bargo ita kuma ammie na zaune tana karatun alqur'ani bayan tagama sallah, gaisheta yayi had'e da yimata seda safe sannan yace Fatima tafito suje gida.

Cikin qarfin hali tamiqe had'e da yima ammie saida safe itama sannan tabi bayansa, sashensu umma suka nufa tana biye dashi,

"Sweety don ALLAH kabarni anan zan kwana, gaba d'aya banajin qarfin jikina."

Juyowa yayi had'e da d'an dawowa baya yariqo hannunta.

"Kiyi haquri Fatima bazan iya bacci acikin gidan canba idan har bakya nan kuma kinga ammie bazata barni na kwanar mata ad'aki ba da sai inyi kwanciyata anan nima.

Cikin qarfin hali tayi murmushi had'e da cewa.

"Haba dr! Ai kaima kasan kayi girma da kwanar mata d'aki."

"Ok, to kinga sai kiyi haquri kawai muje gida gaba d'aya tunda nayi girma."

Da haka suka iso sashen dasu umma suke sukayi sallama abakin qofa kafin umma tabasu izinin shigowa, kwance suka isko Rashida bisa qafafuwan umma shi kuma little nagefe yana bacci sai faman firarsu sukeyi hankali kwance, suna shiga ta tashi zaune tare da matsawa jikin umma ta d'ora kanta saman kafad'arta, sau d'aya Dr yakalleta ya d'auke kai had'e da gaisheda umma yana tab'o little dake bacci.

"Takwara yau har anyi bacci dawuri ahaka!"

"Aikuwa kaganshi nan inba ALLAH yatsare muba sai tsakar dare yatashi ya hanamu bacci da shegen kukannan nasa." I'm tafad'a tana qoqarin zame kafad'arta daga kan da Rashida ta aza mata,

"Maman boy kitashi muje ko." Fatima tafad'a tana zolayar Rashi don tasan babu yanda za'ayi tabisu.

Shiru tayi batare data amsa ba Dr. Yamiqe yana yima umma Saida safe,

"Rashida tashi kuke ko?"

Yanda Dr. Nura yaga ta shagwab'e fuska kamar zatayi kuka yasa yayi 'yar dariya had'e da cewa, "Kai maman boy saki fuskarki da wasa Fatima keyi, dama nazo muyi saida safe kuma muga yaronmu don nasan yau babu mai cewa ya rabaki da umman nan taki yasan ko waye ya aikesa."

Dariya duk suka sannan suka wuce bayan itama tayi masu seda safe.

Kusan ranar rashida da ummanta zaune suka kwana shikuwa baba masallacin dake cikin gidan yayi tafiyarsa ya kwanta bayan sun gama firar dashi kusan qarfe d'aya na dare.

_kuyi haqnayi manage ne nayi maku typing, sai ahankali wlh yikawai nayi, don ALLAH Ina baran addu'arku kada kumanta daniπŸ˜°πŸ™πŸ»_





*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[11/14, 22:52] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___64πŸ’Ž

Cikin daren Yaya Maryam takira aunty marwiyya tasanar da ita zancen tafiyar zuwa borno tace.

"Bazata samu dama ba saboda itama mai gidanta bayajin dad'i, Amma don ALLAH idan sunje su gaishesu sosai."

Kasancewar son sukeyi suje ranar sudawo yasa tunda sassafe suka shirya, aron mota baba balarabe ya samo masu su hud'u, dashi da alhaji ubale mijin Yaya Maryam, sai ita da kuma matar baba balarabe guda wato uwar gidansa sukasa mai sannan suka d'auki hanyar zuwa borno...

β€’β€’β€’ β€’β€’β€’ β€’β€’β€’
*FEDERAL NEUROPSYCHIATRIC HOSPITAL (KWARE) SOKOTO.* canne asibitin da Yaya hawwa ke jinya, duk wani qoqari da yakamata ayi wajen bata kulawa anyi amma abun sai sake hab'b'aka yakeyi, allurori, magunguna da gwaje-gwaje don gano matsalarta da kuma yimata maganinta kullum cikin yimata ita ake, baffa yakashi kud'i da baisan iya adadinsu ba amma babu wani sauyi ko cigaba da aka samu, kullum al'amarinta jiya iyau, kimanin shekara d'aya da watanni kenan yanzu.

Duk wanda yasan Yaya hawwa duniya ya kalleta ba lallene ya iya ganeta ba saboda yanda tabi talalace haukan dake saman kanta yafi hauka muni don hatta mahaukatan dake tare da ita sunfara tsoronta saboda tana cutar dasu, hakan yasa aka killace ta ita kad'ai batare da kowa ba, idan abun ya motsamata saidai jami'an lafiya suga tana lallaqe ailin da bango tamkar wata halintar daba mutum ba, sunaji suna gani zata dinga buga kanta ga jikin bango har sai yayi jini kuma duk wanda yaje cetonta in sunkai su goma suna fitowa da wata kamar tadaban daba tasu ba, kasancewar ma aikatan lafiya mutanene masu matuqar qoqari da kuma jajircewa wajen ganin sunyi yaqi da duk wata cuta dake damun marasa lafiyarsu batare da sun nuna gazawarsu ba yasa gaba d'aya likitocin suka zauna suka yanke shawarar had'a taron gaggawa na qarawa juna sani daga b'angaren mabanbanta likitoci kamarsu daga wasu asibitoci da sauran garuruwa akan wannan sabuwar cutar da Yaya hawwa ked'auke da ita wacce suke tunanin tana nema tafi qarfinsu don samun mafita mai d'auke da topic _HOW TO TREAT PATIENT WITH UNKNOWN NEUROSIS.._

Cikin qanqnen lokaci taron ya wakana, manyan likitoci daban daban sun tashi sunyi bayani kala kala akan wannan matsala tare da samun solution d'aya da suke tsammanin shine qarshen matsalar,

Haka kuma tundaga sokoto wani babban likitansu yaje kano don samun cikakken bayanai akan asalin yanda lalurar tasami yaya hawwa, da baffa Usman suka fara cinkaro kasancewar sun sanshi tunda sune suka kaita asibitin, duk wasu tambayoyi da suka yimasa qin amsa masu ko d'aya yayi har saida ya aika aka kira baffa, gefe suka keb'e dashi yayi masa bayanin abunda ya kawo likitan, d'ari bisa d'ari baffa yayi masu bayanin cewa cutace kawai da suka wayi gari suka ganta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login