Showing 162001 words to 165000 words out of 260204 words

Chapter 55 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt

kallon Rashida da alamu tafara gajiya da shirmen nasa da tabiye masa sunayi yace, saboda kawai sunanki da take dashi, kinga sai adinga cemani d'an fa....bai qarasa fad'ar abunda zaice ba Rashida ta d'auki throw pillow d'in dake gefenta ta jefesa dashi tana fad'in, ungo nan marar kunyar yaro yatashi da gudu yana dariya yabar falon, maido kallonta tayi ga Fatima had'e da cewa, ALLAH yaron nan naki idan yayi wani abun har mamaki yake bani, duk wannan shiru shirun nasa da nike gani idan yaganki awaje haka yake sake baki yayita zaro suruttai cike da rashin ta ido sai kace bashi ba.

Ah to! barshi yayi, shida mamansa ne balle ayi masa gori, ni kaina mamakinsa nakeyi, zuwa nan da anjima kuma in kika gansa bazakice shine ba, musamman idan dadynsu na awaje, sai kiga gaba d'aya ya tattaro natsuwarsa waje d'aya, yana matuqar girmamasa fiye da lissafi,

Ai aunty shiyasa in za'a kwana ana kawoma uncle laifinsa bazaya tab'a yarda ba, Fatima tace.

Ai kuwa wlh, yo inama yai laifin balle har afad'a masa ya yarda,

Hmm! aunty kenan!, Rashida tafad'a tana murmushi,

Shikuwa bai jima da fita ba aka kira sallar magrib don haka saida yawuce masallaci yayi sallah sannan yanufi gidan dady, yana shiga batool nafitowa daga cikin part d'in ammie, dama yau tayi mayannu sunfi aqirga part d'in don tagansa tasa bayada wajen zama idan ba canba, cike da farinciki tanufi inda yake tana sakar masa wani qayataccen murmushi, ta qasan idanuwa yake kallonta yana susar gefen idonsa har taqaraso, zagayarsa tashigayi hanuuwanta duka nazube abayanta kafin tadawo gabansa ta tsaya tana qare masa kallo tundaga sama hara qasa, shima kallon nata yashigayi yana 'yar dariya sannan yafara zagayarta kaman yanda tayi masa had'e da cewa, ALLAH bazan yarda ba kishanyemun jini nima sai narama, hakan yasata sakin dariya had'e da d'aga hannu kamar zata dokesa, d'an kaucewa yayi had'e daja da baya, tace, kai ko?, Ina kashigane yau tun safe nake nemanka ban ganeka ba kasa gaba d'aya har bugun zuciyarta na neman tsayawa?, taqarasa maganar had'e dasa hannuwa a qugun tana kallonsa, Saida yasa hannuwansa guda biyu ga kunnuwa yariqe yana d'an yatsina fuska sannan yace da ita, tuba nake gimbiya, yau wajensu gwaggo naje shiyasa baki ganeni ba, amma zuciyata da kuma rouhina gaba d'aya suna nan wajenki, zo muje nafad'a maki wani sak'o kafin dare yayi inwuce.

Kana nufin yauma ba'a gidannan zaka kwana ba?, nida nake son musha firarmu har mugaji sai kuma kace haka!, taqarasa maganar tare da juya baya tana turo baki had'e da qoqarin barin wajen, bayan nata shima yabi yana cemata,

Ke gimbiya!, Ina kuma zakije daga magana,

Dena cemun gimbiya ni, kawai kace mun batool d'ina tunda munyi fad'a dakai, 'yar dariya yakama yimata tare da cigaba da binta yana fad'in.

Kai yaushe kuma akayi haka?, to tsaya mushirya mana,

Inaaa!, tafi kawai.

Shikenan! Bari kawai natafi, kicewa su ammie Ina gaishesu. yajuyawarsa kamar zai koma, da sauri tajuyo tabiyoshi baya da gudu shima yad'an ruga saida yaga yakusan kai bakin gate tana qoqarin cimmasa sannan ya baud'e mata tare da nufar gefen da wasu fararen kujeru suke kakkafe tsakankanin part d'in umma dana hajia nafeesa ya zauna yana dariya, tana qarasowa wajen tayi tsaye kamar zatayi kuka tana kallonsa da sauri yamiqe had'e da qamewa ya d'aga qafa yabuge qasa sannan ya Sara mata da hannu yana fad'in, sorry mah! Bushewa tayi da dariya ganin yanda yawani qame tare da zaunawa saman d'aya daga cikin kujerun har tana riqe ciki, Saida tayi dariyar mai isarta yana kallonta shima yana murmushi sannan yanemi waje ya zauna, cikin wani irin kallon qauna takallesa had'e da cewa. Abu sumayya a gaskiya zakayi kyau da soja sosai, ka ganka kuwa dake qame d'innan?

A'a gimbiya, amma tunda ke kingani ya wadatar, saidai ni bana sha'awar duk wani aiki na kaki saboda bana qaunar duk abunda zaisa nayi nesa da mahaifiyata, karatunnan ma da zanje garinku inyi saboda babu yanda na iyane kuma ita tagoyi bayan hakan da babu inda zanje.

ALLAH sarki, shiyasa nake qara sonka abu sumayya saboda kana matuqar girmama magabatanka musamman gwaggo, ya ALLAH kabani ikon qara qarfafa maka hakan idan munyi aure.

Amin gimbiya, wai nikam na tambayeki?, Cikin kashe murya tana kallonsa tace, Ina jinka Abu sumayya.

Meyasa kike kirana da Abu sumayya?, tunda muka had'u dake ban tab'a jin kin kirani da sunana ba, meyasa?

Shiru ta d'anyi kafin tace, sunanka nada matuqar nauyin da bazan iya kiranka dashi ba, kaga sunan abbanmu ne sannan kuma sunan babban Yaya agidannan so bazan iya kiran sunan gatsau ba, Abu sumayya kuwa da nake kiranka dashi mafarkina ne da kuma burina da nake fatan ya tabbata idan munyi aure muka haifi 'yah Ina son taci sunan sumayya, Ina matuqar son sunan tun lokacin da malamin islamiyarmu yayi mana tarihin irin gwaggarmayar da tasha acikin musulunci, to tun alokacin nak'uduri cewa idan nahaifi 'yata sumayya zan saka mata kuma duk mijin da zan aura komai dad'insa ni da Abu sumayya zan kirasa.

Iyyeee to idan shi kuma baya so fa?,

Saida ta d'an d'aure fuska sannan tace dashi, Dole ma yaso tunda nima naso sunan da yake yimani, murmushi yayi sannan yace da ita,

To shikenan, ubangiji ALLAH yacika mana burinmu na alkhairi, ni kaina inajin dad'in sunan sosai kuma Ina sonsa fiye da yanda kike sonshi, tace dashi ALLAH? Ya amsa mata da sosai kuwa.

Saida suka sha firarsu sosai sannan yabijiro mata da maganar da sukayi da mahaifiyarsa kuma ya tabbatar mata da cewa zaibi umurninta koda hakan na nufin zai mutune, duk inda hankali ke tashi hankalin batool yatashi, nan take tafara girgiza kai hawaye nayimata zarya a fuska,

Don ALLAH abu sumayya kada kayimun haka, Ina tsananin sonka kuma saida kai zan iya rayuwa, don ALLAH kataimakeni kada karabu dani har bayan cikar mafarkaina, idan ba haka ba zan iya lalacewa.

Haba gimbiya, meyasa zaki fad'i haka, taya za'ayi in saka idanuwa inaji Ina gani ki lalace adalilina, yakamata ki fahimceni gimbiya, bawai ina nufin murabu bane, ina so mujingine wannan maganar agefene har zuwa lokacin daya kamata, aduk fad'in duniya ban tab'ajin zuciyata zata iya son wata da sunan aure ba daidai da second d'aya, ke ce kad'ai azuciyata kuma ke kad'ai nakeda wannan buri akanki, amma hakan bazai yuyu ba har saina gama cika burin tawa mahaifiyar.

Amma mekake tunani zai haifar akaina lokacin da muka jingine wannan maganar agefe?, ita fa macce ba iyaye na renonta bane don d'ai su zauna suyita kallonta ko su ajiyeta ba har zuwa lokacin da cikar burin wani zaya gama cika, don ALLAH kafahimci wannan abun da kake shirinyi ba komai bane illa kuskure da kuma ganganci da zai jawo rabuwarmu d juna akowane lokaci, kasani ina sonka tun daga zuciya, jinin jiki, rouhina da kuma dukkanin sassan jikina, Abu sumayya zan iya rantse maka akan cewa kaine bugun kowane lumfashi nawa dake fita daga jikina.

Nasani gimbiya, amma nima Ina so kisani mahaifiyata da kuma cikar kowane muradi nata sune rayuwata, don haka kiyi haquri mu ajiye wannan soyayyar agefe har lokacin da zan kammala karatuna, nayi maki alqawarin cewa bazan kula kowace macce ba da sunan soyayya balle aure kuma zan reni soyayyarki cike da tausaya da kulawar da bazan tab'a bari wani abu ya tab'ata ba balle har tasamu wata tangard'a tamkar yanda mahaifiya kerenon 'ya'yanta har zuwa lokacin da zasu girma su koma ga ALLAH batare data bari wani abu yatab'a mata suba bisa son ranta, Ina fatar kema haka?.

Yana gama fad'a yajuya zaibar wajen qwalla nazubo masa, durqushewa tayi had'e da saurin kamo qasan rigarsa, ya rufe idanuwansa da sauri.

Cikin sheshshekar kuka taci, shikenan katafi izuwa cikar dukkani muraddan mahaifiyarka ni kuma zan jiraka komai daren dad'ewa, zan kula da soyayyarka har sai natabbata ta lullunku fiye da yanda zaka tafi kabarta, zan tanada maka kaina batare da gazawa ba har zuwa lokacin da zaka dawo gareni.

Sosai yaji tabashi tausayi, yatabbata soyayyarta agaresa mai girmace da darajar data lunka darajar lokaci, yatabbata tana yimasa son da ko rabinsa baya yimata kuma in sha ALLAH shima ya d'auki alqawarin da SANNU SANNU zai rama mata dukkanin qaunar data nuna masa.

Ahankali ya sauke wata irin ajiyar zuciya had'e da juyowa yana kallon yanda take sheshshekar kuka, kan ya ankara yayi qoqarin rarrashinta da bata magana kawai yaga ansa qafa anshureta, ransa ab'ace yajuya don yaga wane marar imanine ya aikata mata haka shima yaji an d'aukesa wani irin zazzafan mari.

Hajia nafeesa ce sai faman huci takeyi kamar zata fashe ashe tun d'azu tana tsaye abakin part d'inta tana kallon duk abunda ke faruwa sakamakon hasken qwayaqwayin daya mamaye harabar gidan, ganin batool da tayi durqushe agabansa shiya fusatata tanufo wajen cike da takaici har tayi masu haka?, Cikin wani irin matsiyacin kallo dake nuna tsantsar tsanar da take yimasa tace, meye alaqarka da 'yar uwata, koso kakeyi kajawomun irin abun kunyar da kayo gado tun asali don kana butulu marar halacci?, to bari nafad'a maka, wlh hanyar jirgi daban take data mota, kuma ruwa ba sa'an kwando bane sannan kaje katambayi magabatanka kaji, akwai tsantsar banbanci tsakanin d'an halak da kuma shege, koda yake ba lallai bane ace sunsan haka, balle har su iya fahimtar da kai, daga yau bakai ba 'yar uwata domin ita jininta halastacce ne ba gurb'atacce ba, inba haka ba duk abunda yafaru dakai kai kajawo...

















*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[11/14, 22:52] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___75πŸ’Ž

Tun cikin daren batool tahau shirin kayanta, hajia nafeesa dai nabiye da ido tana kallonta, saida takammala tsaf sannan tashige toilet ta watso ruwa, kallo d'aya zakayi mata tabaka tausayi saboda yanda idanuwanta suka kukkumbure akan kukan da taci amma sai qoqarin sakin fuskarta takeyi tana son nuna babu wani abun da yake damunta, kitchen tawuce ta had'oma kanta ruwan Lipton saboda yanda takejin bata sha'awar sama cikinta komai tadawo falo ta zauna tana kurb'a ahankali batare data tankawa qananan yaran hajia nafeesa dake faman mugun wasanni atsakiyar falon ba, shakur ne yashigo fuskarsa ba d'igon walwala ko kad'an yanemi waje kusa da ita ya zauna yana faman shinshinar qamshin body spray d'in dake tashi ajikinta,

Wata uwar harara ta zabga masa had'e da miqewa takoma d'ayar kujerar taci gaba da kurb'ar ruwan Lipton d'inta hankali kwance,

Miqewa yayi yasake binta zuwa inda take zaune shima ya zauna yana qare mata kallo tun daga sama har qasa yana lasar baki, sake miqewa tayi zatabar wajen yayi saurin sa hannu a fusace yariqo hannunta yana fad'in.

Wai yane malama dana zauna saiki tashi, meye kika gani ajikina da bakya so, kallonsa tafarayi sannan takalli hannunsa daya riqe nata dashi alamun yacikata amma yaqi hakan ya fusatata ta yadda cup d'in a saman center carpet d'in dake tsakar d'akin don dama ta shanye abunda ke ciki ta d'aukesa wani irin azababben marin da yasa ya saketa ba shiri ya dafe kuncinsa, cikin halin ko inkula ta d'auke cup d'in had'e da juyawa tanufi kitchen zata mayar da sauri ta tsaya sanadiyar jin da tayi yabiyo bayanta,

Cikin takaici tajuyo tana kallonsa tace, lafiya malan kake biyata.

Kamar sakarai Shakur ya amsa mata da, batool ni kika mara don kinga ina sonki?".

Eh, yanzuma zan sake marin naka idan ka sake yunqurin tab'ani, anfad'a maka so haukane? Ko ko anfad'a maka ana so dolene?, To bari nafad'a maka ni ba sa'ar kabace don matsayin uwarka naka tunda qanwar mahaifiyarka nake, don haka kadena ganin ka girmeni sosai wannan girman dole kabani shi ka ajiye shashanci agefe, ni banida lokacin yaro irinka.

Tana rufe baki taji hajia nafeesa nafad'in, eh lallai batool d'an nawa kike neman yaqunawa haka?, Shi kike kira yaro bayan yabaki shekaru d'aid'ai har goma sha d'aya aduniya?, to shikenan naji shi yarone, shi kuma wancan shegen fa da kike tsaya kulawa, shi kuma menene?.

Oho! bazan iya ganewa ba don tarbiyarsa Bata barni na iya fahimtar ko shekarunsa nawa ba, ban damu ba koma jaririne shi amma kijawa yaronki kunne, karya kuskura ya sake tab'ani idanko ba haka ba...bata ida qarasawa ba hajia nafeesa ta d'aga hannu zata kaimata mari tayi saurin riqe hannun tana cewa.

Daga lokacin da kika kira mahaifina kika sanar dashi qarya da gaskiya akan masoyina, daga lokacin ne nima nadaina ganin duk wani mutunci naki da kuma kimarki, daga lokacin kika rasa dararjar da har zaki iyasa hannu ki dakeni in qyaleki, ko wancan marin da kika yiwa masoyina, rad'ad'insa dana dad'e inaji ajikina bai barni na iya haqura ba har saida narama masa ga d'anki, gashinan kuma ki tambayesa, yanzu idan yayi qoqarin sake maimaita abunda yayi mani, to tabbas shima wancan dayan marin da kikayi mani to tabbas kuwa zan sake ramashi akansa, kitsaya a iya huruminki nake 'yar uwatace ko ince 'yar uwar mahaifina, kada kisake kice zaki sake qoqarin shiga rayuwata domin bakida hurumi akanta, har yanzu lokaci bai qure maki ba domin akwai sauran burbishin kimarki da nake gani sanadiyar zamowarki silar dana had'u da farincikina, idan kuwa ba haka ba to ina baki tabbaci akan zan zubar da sauran kimar taki dake idanuwa na nayi maki abunda sai kinyi dana sanin shiga gonata, kuma kamar yanda kikace Abu sumayya yarabu dani to zaiyi hakan ammafa nawani d'an lokaci, shima d'in bisa umurnin mahaifiyarsa ne don kada ki d'auka cewa kinyi nasarar rabamune idan kinga hakan, Ina so ke kuma idan har kin isa ga d'anki kuma yatabbata shi d'in d'an halak ne to kice yarabu dani, yadena bibiyata domin bana sonsa kuma bana qaunarsa.

Shaqo wuyanta shakur da tuni yakai qololuwa wajen fusata yayi yana huci ya had'ata da jikin bangon kitchen d'in data nufa yana fad'in.

Kinyi qarya kice zaki walaqantani akan wani shege da ba'asan aslinsa ba, halama waye ubansa da zaki zab'esa akaina?, to bari kiji nafad'a maki duk duniyar nan idan ta taru babu wanda ya isa yarabani dake, shi d'in wa da zaki fifitasa akaina?, Yaron daya tashi agabana cikin inuwar d'an uwana data mahaifina da suka yimasa sutura shi zaki nemi had'awa dani? to bari kiji in fad'a maki, idan ma mafarki kikeyi toki farka don narantse bakida miji aduniya saini, don haka kizuba mugani...., yana kaiwa nan ya jefar da ita gefen kujera yawuce fuu...kamar zai tashi sama yabar wajen, har ya kusa kai bakin qofar fita cikin qarfin hali ta tashi tare da cewa, kai sakarai,

Cikin b'acin rai yajuyo tayi murmushi had'e da cewa, Ashe kasan sunanka?, to bari nima in buga maka kashedi akaina kamar yanda kayimun, nunasa tayi da hannu had'e da murza 'yan yatsunta har Saida sukayi qara sannan tace, karubuta ka ajiye, ni d'innan mallakin Abu sumayyace wato 'yar da zan haifa mana nida shi don haka kadena wannan mafarkin nacewa zaka zamo mijina, waye kai kuma wa kake dashi da kake tunanin zai tsaya maka? Aunty nafeesa ce dake qoqarin amfani da zafin ran mahaifina? Ko kuwa zuciyarka da batada qwarin guiwar da zata iya fighting da tawa har taci galaba akanta?, to bazasu iya ba domin ni inada tsayayyu a hannun damata da kuma haguna, sannan zuciyata jarumace da zata iya fuskantar duk wata matsala kuma ashirye nake nabada rayuwata akan wannan d'an yaron daya tashi aqarqashin inuwar gidannan aka yimasa sutura, don haka ni dakai shege kafasa.

Kanta yayo a fusace da sauri hajia nafeesa da tayi tsaye tana kallon tsantsar rashin kunyar da batool ke zuba masu tariqesa tana fad'in.

Qyaleta shakur, jeka d'akinka kawatsa ruwa ka huta, duk rashin kunyarta kaine zakayi maganinta, tayi iyayinta don SANNU SANNU Bata Hana zuwa, in Sha ALLAH sai tazo hannunka a matsayin matarka kayi duk yanda kake so da ita kaji ko?,

Mere baki batool tayi had'e dayin tsaki tabar wajen tana fad'in, lallai kuwa iska na Shirin wahalda mai kayan kara.

Wani irin naushi yakaiwa bango yana huci yace, mom nifa bazan iya jurewa irin wud'annan walaqancin ba, kinajin yanda yarinyar nan ke fad'in maganganu amma kice duka na haqure, bazan iya ba.

Yaqare maganar a fusace had'e da barin wajen zuciyarsa na tafarfasa.

Bayan sati d'aya lokacin har little yawuce makaranta ita kuma batool takoma gida, tun ranar da takoma mahaifin nata kefushi da ita saboda abunda hajia nafeesa tafad'a masa kuma daya tambayeta kai tsaye ta amsa masa da cewa maganganun da hajia nafeesa tafad'a gaskiyane tana soyayya dashi saidai ba shege bane kamar yanda tafad'a kawai hassada ce da tsabar baqinciki dake cinta yasa tafad'i hakan don tab'ata masa suna.

A maimakon yafahimceta saima d'auketa mari da yayi yana fad'in bata isa ba tagurb'ata masu jini da yaron da ba'asan asalinsa ba, tunda har aka fara jita jitar cewa shid'in bad'an halak bane to tabbas akwai qamshin gaskiya aciki, don haka dole ta yakicesa azuciyarta don bazaya tab'a barin ta auresa ba koda shikad'aine namijin daya rage aduniya dole tahaqura tarabu dashi, kasancewar yariga daya b'ata batool tun farko saboda soyayyar daya nuna mata fiye data sauran 'ya'yan da yake dasu yasa takasa saurararsa ballema har tafahimci abunda yake cewa tabar wajen aguje tana kuka, ta tabbata irin soyayyar da yake yimata ita zatasa ya sauko idan tayi hakan don baya qaunar b'acin ranta balle kukan ta gashi takafe kai da fata batacin komai sai kuka duk don yasauko daga dokin naqin daya hau. Amma sai taga abun yasha banban awannan karon don ko kad'an baibi takanta ba balle tayi tunanin zaibarta tayi abunda takeso kamar yanda yasaba mata akoda yaushe, mahaifiyarta kuwa hajia salmah da suke kira da hajia mama tayi lallashi har tagaji amma batool taqi saukowa kullum sai kuka, qaramar yarinyace da anriga ansabo mata rayuwarta cikin gata da sangartawa don tun tanada shekara biyar aduniya duk abunda tace tanaso ayi agidan shi akeyi, idan kuma tayi fushi taqi cin abinci shikad'aine ke zuwa ya lallasheta yabata abaki sannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login