Showing 81001 words to 84000 words out of 260204 words

Chapter 28 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt

lokacin gata qaramar yarinya mai qanan shekaru, yanzu haka sharri da baqincikin d'a namiji yasata fitowa, kai walh wasu mazan basuda imani."

"A'a fatima karkice haka tunda bamusan dalilin daya fiddota be daga gida ba, wataqil wata matsalarce daban."

"Hmm! Bazaka gane ba swtht wlh yanzu hakan mijinne yakorota saboda wani banzan dalilinsa, ya ALLAH kadubi maraicinmu."

Tafad'a tana d'aga hannuwanta sama hawaye nazubo mata daga cikin idanuwa, qara matsowa tayi kusa da Rashida taduqo had'e dasa hannu tana shafa fuskarta,

"ALLAH sarki yarinya, ALLAH yatashi kafad'unki, wlh swthrt da ganin yarinyar nan akwai ban tausayi cikin al-amarinta, yanzu I babyn nata yake?"

"Yana can shima anbashi gado bayada cikakkiyar." Yafad'a tare da juyowa yafito wajen tana biye dashi ya zuba hannayensa acikin aljifan wandonsa, kallonta yayi yaga yanda gaba d'aya jikinta yayi sanyi, murmushi yai sannan yaci gaba da cewa "muje can kiga yaron nata, so nake idan kin amince nabar komai ahannunki kafin nadawo nan da zuwa jibi idan yafarfad'o muji daga Ina take, thank God ma nayi waya da Dr qasim can wajen aiki yace anyi shifting theater da zanyi sai nan da 24hrs saboda jinin patient d'in daya hau sosai."

"Babu damuwa swhrt ALLAH yabasu lafiya, idan da imani da tausayi a qirjin bawa ko bakasan mutumba ai katausaya masa, shikuma taimako bakasan ta inda zai yimaka rana ba wataran, na amince Babu wata damuwa akan haka."

"ALLAH fatina?" Dr nura yafad'a yana dariya.

"Sosai kuwa, yanzu kafasa bin jirgi kenan?"

"Eh da motar haya zanje sai inbar maki wannan koda wani abun zai taso, zan kira Salim ya kasance kusa idan kina buqata."

"Noo..kabarshi kasan bama inuwa d'aya da qanennan naka yafiye reni da yawa."

"To shikenan muje kigano yaron."

••• ••• •••
Baffa kuwa na fitowa daga asibiti kai tsaye gida yanufa ransa duk a dagule, gaba d'aya ya rasa mekeyi masa dad'i aduniya, yana shigowa cikin gidan ya tarar da yaya hawwa zaune a bakin rumfarsu Inna ruqayya takira mai tallar fankasu (na alkama) ta tasashi agaba sai ci takeyi tana dangwala yaji, tana ganin lokacin da baffa yawuce ta gabanta fuskarsa cike da damuwa amma ko kallon banza bi isheta ba, saida taci mai isarta taqoshi sannan tamiqe had'e da cewa yaron ya jirata tana zuwa ta karb'o masa kud'insa.

'Daki ta iskosa zaune abakin gefen gado ya rabka wani uban tagumi yana tunanin ta inda zai fara sanarwa da iyayen Rashida halin da ake ciki, cikin nuna halin ko inkula akansa tace. "Malan bani naira d'ari in biya yaron can kud'insa na fankasu dana ci." Tafad'a had'e da tura yatsa cikin baki tana qwalqwalo wanda ya laqemata a hauru, hannunsa yasa cikin aljihu yaciro d'ari biyu ya miqa mata ta amsa ba gode balle nagode taficewarta, ba'a jimaba tadawo tamiqo masa canjin naira d'ari ya sake miqa hannu ya karb'a yatura cikin aljihu,

"Yawwa nace ina nura take?, Nifa tunda yafitarnan hankalina ba kwance yake ba kar yaje garin neman gira ya rasa ido..."
Ai kafin tarufe baki baffa yamiqe tsaye yana nunata da d'an yatsa had'e da cewa. "Qarya kike, wlh qarya kikeyi kice kindamu da Nuraddeen, wai yanzu ke a tunanin ki ke uwace ahaka? tir da halin uwa ko in haka take, maqaryaciyar banza maqaryaciyar wofi, shashasha da batasan abunda takeyi ba, sakaryar uwa kawai to kitambayeni Nuraddeen damuwa kikayi dashine ko a'a?"

"Ya haka malan sai kace wanda ke jiraye dani daga tambayarka yarona saika rufeni da kwandon fitina?"

"Naji hawwa jiraye nake dake amma idan harda gaske kikeyi kina son ganin d'anki sai kifad'a mani ina 'yar mutane take tukuna, don bana haufi akan cewa duk inda yarinyarnan taje ko aka kaita kinada sa hannu aciki, don haka kifad'amun inda yarinyar mutane take naroqeki da ALLAH."

"Buhun ubannan, lallai malan kace wani abu, meya dameni da wannan yarinyar da har zakace akwai sa hannuna aciki, to wlh kul kar inji..." Bata rufe baki ba ya d'auketa kyakkyawan marin da saida ta birkita, kafin ta taso yaqara mata wani, zuciyarsa na tafarfasa yace.

"Anzo wajen hawwa, ahalin yanzu bana yimaki kallon daraja da kimar cewa ke matatace, baki isa kiyi mani jan kunne ba agabana, ayau kimanta da cewa ni Idris d'innan ne da kika sani mai sanyin hali da kuma haquri, wannan Idris d'in dake gabanki shirye yake daya sallamaki har abada, ahalin yanzu ba duka kad'ai da ALLAH ya haramta miji yayiwa matarsa ba hatta azabtarwar da zata iyasa kirasa rayuwarki na har abada zan iya yimaki saboda zaluncin da nake tuhumarki da aikatawa yarinyar mutane, don haka tun wuri ina fad'a maki kitanadi kalaman da Zaki fad'awa jami'an tsaro idan sunzo takanki don wlh bazan bar duk wanda keda hannu acikin b'atar yarinyar nan ba.

Tsaye Yaya hawwa tayi tabisa da kallo cike da mamaki don ko amafarki Bata tab'a tsammanin cewa baffa zai iya yimata hakan ba, tureta yayi daqarfi daga gabansa da take yawuce yabar d'akin, yanajin yanda tafad'a akan qarfen gado kanta yabuge qum..amma ko juyowa beyi ba balle ya kalleta ya wuce abunsa zuciyarsa cike da tsanarta ,
Shikuwa Baffa Usman yana fitowa daga asibiti kai tsaye tashar mota yanufa ya shiga motar da zata kaishi cikin birnin kano, gidajen redio da telebijin yaje yabada iya kud'ad'en dake hannunsa don asa masa sanarwar b'acewar rashida ta kafafen labarai saida ya tabbatar anyi komai tukuna sannan yashiga motar da zata kaishi qauyen yarimawa, cikin sa'a ya tarar da malan balarabe yazo wajen baba, cike da karramawa suka tarbesa duk da dai fuskarsa ta gama nuna baya cikin yanayi mai dad'i.
Bayan sun gaisane cikin natsuwa yayi masu bayanin halin da ake ciki ya qara masu da cewa yanzu haka shima Nuraddeen d'in yana asibiti rai a hannun ALLAH,

"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun" kad'ai baba ya iya furtawa daga nan bai koma cewa komai ba saidai sukaga ya b'ingire qasa daga zaunen da yake, ranar baffa Usman yaga tsantsar tashin hankali wanda ba'a samasa rana domin adaidai lokacinne itama umma data shigo d'akin kawo masa ruwa ashe duk abunda baffa Usman ke fad'a taji da kunnenta ne saidai sukaji fad'uwar kofin dake hannunta kan kace me itama tafad'i wajen a some...





*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___39💎

Cike da tashin hankali baba balarabe yaje ya d'ebo ruwa cikin gida aka yayyafa masu, kusan atare suka farfad'o amma babu wanda ke iya magana acikinsu, banda hawaye babu abunda kezuba daga cikin qwayar idanuwansu, ganin haka yasa malan balarabe yaje wajwn nemo mota don akaisu asibiti, yace wa baffa Usman dake gefe ya rabka uban tagumi cikin yanayi mai wuyar fassarawa yajirasa nan da mintota zai dawo.

Kallo d'aya zakayi masu kasan akwai maganganu acikin bakinsu saboda yanda suka qurawa baffa Usman idanuwa Amma Babu bakin magana sai hawayen kawai da zasu iya fassara maka yanayin da suke ciki, ba'a jima ba malan balarabe yadawo da mota da Kuma matarsa d'aya don seda yakoma go ya d'auko kud'i, nan take suka d'aukesu suka nufi asibiti,

Waya baffa Usman ya d'aga yakira baffa yace ya iskosa yarimawa ga abunda ke faruwa yanzu haka suna asibiti, cikin azama baffa yakamo hanya batare daya sanarwa da kowa halin da ake ciki ba, tafe yake yana addu'o'i abakinsa har yasamu mota, tund'azu ALLAH ne kad'ai yasan awane yanayi baffa kejin kansa saboda tunanin yanda zai fuskanci iyayen Rashida ya sanar dasu zancen b'atar 'yarsu ashe har d'an uwansa yaje yasanar dasu, saidai ayanayin daya ce suke ciki yanzu kuma shine babban abunda yafi d'aga masa hankali, har aka iso qauyen yarimawa baffa baisan an iso ba saboda tsananin yanda damuwa tayi awan gaba da dukkanin ilahirin natsuwarsa.

Kai tsaye asibitin ya nufa yatarar dasu baba balarabe da baffa Usman tsaitsaye cikin halin jimami suna jiran fitowar likita, qarasowa wajensu yai jikinsa duk Babu qwari, cike da jin kunya had'i da damuwa yaba malan balarabe hannu suka gaisa, fuskarsa asake ya amsa masa yana mai tambayarsa halin da Nuraddeen ke ciki tare da jajantawa juna akan abunda yafaru, suna nan tsaitsaye likita yafito ya nufo inda suke, tambayarsa suka shigayi ya jikinsu baba da umma yace su biyoshi office tukuna,

Baffa da malan balarabe ne zaune saman kujerun dake kallon likitan shi Kuma baffa usman na tsaye, seda Dr yayi gyaran murya sannan yafara fad'a masu halin da suke ciki,

Sanadiyar tashin hankali da baba yashiga a lokaci d'aya ya haifar masa da ciwon hawan jini wanda ahalin yanzu yakamu da mutuwar sashen jiki ma'ana yasamu (stroke), ita kuma umma sun dubata amma sun kasa gano abunda kedamunta ba abunda take kira inba Rashida ba, wanda hakan yasa dole sai munyi mata gwajegwaje a qwaqwalwarta ko anan ne tasamu matsala.
Wannan shine cikakken bayanin da likita yayi masu akan binciken da sukayi, gaba d'ayansu sun shiga tashin hankali jin abunda likita yafad'a "innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, ALLAH Kai kasan dalilin jarabta wud'annan bayi naka, ya ALLAH ka samasu hak'uri da juriya kuma kabayyana masu 'yarsu aduk inda take." malan balarabe yafad'a had'e da sakin wata irin ajiyar zuciya.

Baffa da Baffa Usman kuwa jin duniyar sukayi gaba d'aya tayi masu k'uncin da suka rasa sanin ina zasusa kansu.

••• ••• •••
A 'bangaren Nuraddeen kuwa tun safe bai farko ba har sai bayan sallar la'asar, ko daya farfad'o yad'an samu sauqi sosai amma yana tuna zancen b'atan Rashida zazzab'i yataso masa, cikin qarfin hali yamiqe ya sauko daga kan gadon yana yatsina fuska, ganin bakowa wajen yasa yamiqi hanyar fita cikin asibitin don baffa Ali da aka bari ya kula dashi tuni yabar wajen, acan bakin wata bishiya ya hangosa shida wasu yasa andamamasa furarsa hankali kwance yana sha suna fira, bai tsaya bi takansa ba ya wuce gida, tafe take yana harhad'a hanya har ALLAH yasa ya isa gida lafiya, sashensu yanufa ya shiga cikin d'akin, tsaye yayi yana kallon ko ina cike da fatar zaiga Rashidarsa ta iso gare adaidai lokacin, yafi minti biyar ahaka kafin ya duqe wajen yasaki wani irin kuka mai tsima ran duk wanda ke saurare, jin yayi andafo kafad'arsa da sauri yaciro kai yana kallon sama cike da zimmar ganinta amma sai yaga ashe Inna Bilkisu ce, hannu tasa tagoge masa hawayen da suka jiqa masa fuska sannan ta riqosa ya tashi ta azasa saman kujera, cikin sanyin muryar dake nuna tattare take da damuwa tace. "Nuraddeen bazan hanaka kuka ba, domin b'atan Rashida ba kai kad'ai yashafa ba har mu, Amma Nuraddeen Ina so infad'a maka cewa yanzu ba lokacin kuka bane agareka, lokacine da zaka tattaro dukkanin natsuwarka kayi yaqin gano matarka aduk inda take, Ina so kayi amfani da kud'in da kake dasu ahannunka, iliminka da kuma qarfin jikinka kaje kagano matarka aduk inda take, wannan kukan da wani kwanciya duk ba mafita bane agareka, kazuba kud'inka a kafafan yad'a labarai asa maka cigiyarta, kayi amfani da iliminka wajen tsananta addu'a kuma kasa malamai ayi maka, kayi amfani da qarfin jikinka wajen shiga lungu da saqo kadubo matarka, idan ALLAH yayi za'a ganta Ina tabbatar maka da zaka had'u da ita tunda baka zauna ba kaji ko, don ALLAH kadaure duk yanayin da kake jin kanka aciki kanunawa duniya cewa kana son iyalinka ko tana tare da kai ko bata tare dakai, damuwa dolece amma kada kabari tayi tasirin da zata cutarwa da Rashida kai, don na tabbata aduk inda take matuqar tana a hayyacinta kaine mutum nafarko da zatayi fatan kasancewarsa cikin qoshin lafiya da kwanciyar hankali, don haka kayi haquri kuma karb'i qaddararka hannu biyu ta hanyar qarfafa zuciyarka kaji ko?."

"Eh Inna Bilkisu nagode." Yafad'a yana goge hawayen da suka jiqa masa fuska, miqewa tayi tafita tana fad'in, "Ina zuwa.?"

Binta da kallo yayi aransa yana burin inama ace itace mahaifiyarsa, daya rungumeta yayi kukan sosai yanda zata fahimci yanayin da yakeji koya samu sassauci, yana wannan tinaninne Inna Bilkisu tadawo riqe da kwanon abinci da wani kwanon ruwa da damammiyar fura aciki, saida tad'an riqe fuska tukuna ta ajiye masa kwanon abincin agabansa tace

"Maza sauko kaci abinci kaji."

"Bazan iyaba Inna Bilkisu, wlh bana tunanin abinci zai iya shiga bakina bacin bansan halinda Rashida ita da abun cikinta ke cikiba."

"Ungo wannan to kasha, ai haquri zakayi, idan bakaci ba taya zaka samu qarfi ajikinka har ka iya zuwa nemota. kadaure ko rabine kasha kaji ko."
Inna Bilkisu tafad'a had'e da bud'e kwanon ruwan takai abakinsa, awannan karon Babu yanda zaiyi dole yafara tsutsar furar ahankali yana sha tamkar wani jariri, cike da tausayi ta raja'a akallonsa kawai sukaji anbuge kwanon furar yafad'i qasa gaba d'aya tazube, d'ago kai dashi har ita sukayi da sauri don ganin wanda yayi wannan aika aikar, dik da dama gaba d'aya zukatansu sun gama hakaito masu dako wacece, cike da masifa Inna hawwa tafara magana.

"Kam buhun uban nan, Bilki me nake shirin gani anan?, So kikeyi shi kuma yaron nawa bayan halin da yake ciki ki hallaka mani shi ta hanyar asirce manishi sai yanda kikayi dashi don mugunta?, To wallahi jinina yafi qarfinki munafukar banza munafukar wofi, hadda wani d'auko abu kina bashi abaki, kai Kuma sakaran banza da bakasan inda duniya tayi ba kasaki baki kana sha."
Yaya hawwa taqarasa fad'a tare da jawo hannunsa zatabar falon dashi tana cika tana batsewa, cike da tausayin mugun halin da ALLAH yayi mata yajarab tawar rayuwa dashi Inna Bilkisu ke kallonta kafin tace. "Dakata Yaya hawwa, kiji tsoron ALLAH, kiji tsoron ALLAH kitausayawa yaron nan halin da yake ciki, a matsayinmu na iyaye bamu kad'aine ALLAH ke hukunta 'ya'yanmu akan haqqoqan muba idan suka danne, hatta mu kanmu ubangiji na kamamu da haqqoqansu kuma yayi mana hukunci mai tsauri idan muka taushe masusu, su amana ne agaremu kuma ALLAH zai tambayemu, Nuraddeen d'anane duniya da lahira tunda nake auren qanen mahaifinsa, don haka banga ribar da zan samu ba idan nacutar dashi, dama haka rayuwa take idan kana abu sai kayi tsammanin kowa ma yanayi, kitaka sannu haqqin d'anki kad'ai ya isheki aduniya balle na sauran rayukan da basuji basu gani ba, agidannan Banda darajar mijina da yayansa da kike ci saita haihuwa da kikayi badon haka ba da saina koya maki darasin rayuwa, amma ko yanzu muje zuwa da sannu duniya zata koya maki."

Rab'awa tagefensu tayi tawuce bayan ta d'auko kwanon abincin data kawo masa tare da furar da Yaya hawwa ta b'arara,

"Kagani ko shashashan banza da wofi, bakasan mai sonka ba, dubi yanda tayi tsaye ta cimun mutunci agabanka amma ka kasa cewa uffan saboda tariga data gama da kai, dallah wuce mutafi samna sakaran banza, biye yake da ita kamar hoto har suka fito sashen tana rafka uwar masifa da zagezage, daidai bakin qofa taci karo da fadeela Inna taturota tagyara inda furar tazube, hannu tasa ta bangajeta gefe da kad'an tafad'e da sauri Nuraddeen yariqe mata hannu.

"Gidan ubanwa zakijene" Yaya hawwa tafad'a tana watsa mata wani mugun kallo,

"Inna ce tace nazo nagoge inda fura ta zube.."

"To ahalin kicifaffi anyo gadon ashibilanci da iyayi maza kiwuce kibar nan kafin in makeki, shegu d'iyan bani na iya.."

Da sauri fadeela tabar wajen tun kafin tarufe baki ita kuma tajawo gambun qofar tarufe har lokacin tana riqe da hannunsa kamar wani qaramin yaro,

'Daki tashiga dashi ta zaunar saman gefen gado ta jawo wani kwano da dambu aciki sannan ta d'ebo ruwa ga kofi ta ajiye agabansa,

"Maza kaci kada yunwa ta illataka, yanzu haka duk inda ta tafi tana can hankalinta kwance tabarmu da tashin hankali anan." 'Doga kansa yayi yana kallon mahaifiyar tasa had'e da cewa.

"Kamarya duk inda tatafi innar mu, taya Rashida zata bar gidannan da tsohon cikinta haihuwa ko yau ko gobe?."

"Eh mana, ai haka na iya yuyuwa idan taji tagaji da zama dakai, to don ta tayar maka da hankali tunda taga kana sonta, ya kamata kiyi tunani anya ba guduwarta tayi ba tunda auren naku na had'ine?." Murmushin da yafi kuka ciwo yayi kafin yace.

"Innar mu kenan! Ai aurena da Rashida ba had'in iyaye bane balle tagudu tabarni, ni naganta da kaina nace Ina sonta kuma itama ba tilastata akayi sai ta aureni ba, ita da kanta taji tana sona kuma ta amsa mani, kinga batun guduwa anan ga masoyan da sukaji sun amince da juna ai bata taso ba, Rashida inada tabbaci akan d'auketa akayi amma su waye? Meyasa? Duka ban sani ba, tsorona d'aya aduniya kada ace mahaifiyata nada sa hannu aciki, Ina addu'a kar ALLAH yasa tsanar da kike yimata bata Kai mizanin da Zaki iya salwantar da rayuwarta ba."

Hannuwanta yariqo had'e da durqushewa agabanta sannan yaci gaba da cewa, "innar mu duk duniya banida maccen da takai matsayinki araina domin ke kika haifeni, kikayi d'awainiya dani tun Ina cikin cikinki har zuwa girmana amma duk da haka farincikina da kwanciyar hankali na suna tattarene a hannun matata Rashida, don ALLAH idan kinada masaniya akan inda take don ALLAH innar mu kisanar dani kafin nakoma marar amfani adoron duniya."

Wani banzan kallo tayi masa kafin a hasale tace. "Tashi fita kabani waje tunda naga kai bakasan abunda kakeyi ba." Tsom ya tashi ya miqe jikinsa ba k'wari ko kad'an ya koma sashensa, bai jima da shiga ba yafito sanye da wasu kaya yamiqi hanyar fita gidan.

"Ina zaka?" Yaji muryar Yaya hawwa tana fad'a cike da gadara, batare daya juyo ba yace.

"Zantafi nemo farincikina." Bai tsaya sauraron abunda zatace ba yaci gaba da tafiya, daidai bakin qofar fita gidan yaci karo muneera tashigo aguje da alama wani tajawo sauran k'iris ta bangajesa tawuce, jikinta na rawa tatsaya tana fad'in. "Don ALLAH ya nura kayi haquri" kota kanta baibi ba yawuce abunsa batare dama yasan da ita awajen ba, biyo bayansa tayi tana fad'in, "ya nura, ya nura."

Ko juyowa beyi ba balle ma yakalleta har tasa ran zai tanka mata, hakan yasa tafashewa da kuka had'e da rugawa cikin gida, da sauri

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login