Showing 249001 words to 252000 words out of 260204 words

Chapter 84 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt

wife.

Sannan ya miqa masa yana fad'in.

"Baba ga wayarka, nasaka maka lambobin da zaka iya buqata."

Karb'a yayi had'e dayin murmushi yace "agaisheka ALLAH yayi maka albarka."

Sannan yafara dudduba lambobin har yakai gata Rashida da yayi masa saving da my wife, editing ya shiga ya mayar habibty sannan ya jefa wayar a aljihu little na kallonsa ta gefen ido yayi murmushin shima, aransa yace.

"ALLAH dai yasa Kar habibty d'innan ta kwabsawa babansa don yalura ba kad'an yake jinta ba."

Yana wannan tunaninne yaji anfara kiraye kirayen sunaye har aka kai ga sunansu suka tashi suka shiga, bayan sun zauna cikin jirgin da yake waje d'aya suke kafin jirgin ya tashi Dr Nuraddeen ya ciro wayarsa had'e da kaikaita idanuwan little yashiga akwatin tura saqo yafara rubuta saqo kamar haka.
_I am sorry for all the pain, I am sorry for the tears I am sorry for the anguish, But please fulfill my only wish, Please forgive me this time, And I won't do this again, Nothing to pretend, Just forgive me! I am sorry!_

Ya karanta yafi aqirga kafin ya lalubo lambar habibty d'insa ya tura mata, Rashida da bata dad'e da kunna wayar ba tana zaune taji qarar shigowar message ta d'auko wayar ta karanta, ganin lambace yasa batare data damu da tabada amsa ba ta ajiye wayar, can bayan wasu mintuna tasake jin qarar shigowar wani message d'in ta d'auko wayar ta sake dubawa tana karantawa kamar hakan.
_Iknow it's very pain and It's hard to make you understand, But, believe me I don't pretend, Mistake has happened and I won't deny, Blame on the situation to defy, I just want that you forgive me through, So that I don't feel blue, Please forgive me now habibty!, b'coz it's all part of our destiny and I don't have any words or how! Forgive me! Habibtyyy_

Awannan karon wasu zafafan hawaye suka zubo mata domin tafahimci daga Ina saqon ke zuwa, juya wayar ta shigayi tare da rashin sanin mema zata cemasa kawai ta cillata saman gadon takife tana kukan da da'ace hawaye na qarewa to da tsakanin jiya da yau nata sun qare kaf.

Tun daga umma dasu Dr Babu wanda ya sanar da Rashida zancen zuwan Dr Nuraddeen saboda yanayin da suka ganeta aciki, gashi dama tun safe bata fito d'aki ba har zuwa wannan lokacin, abun karinta dana Rana duka saidai mai aiki takai mata a d'aki hakan yabasu Fatima damar yin shire shiren tarbarsu Dr yanda ya kamata kafin su iso,

Kasancewar akwai banbanci tsakanin tafiyar jirgi data mota yasa cikin mintunan da basu wuce arba'in zuwa arba'in da biyarba su little suka iso,

Gaban Dr Nuraddeen ne ya shiga fad'uwa saboda rashin ganin amsar saqonsa ko d'aya daga Rashida Wanda ya tabbatar tagani kuma tasan shine, hakan yasashi fargabar kada taqi amincewa ta amshesa bayan yayi nadamar abunda ya aikata kuma bayin kansa bane.

Little bai tsaya jiran azo d'aukarsuba ya tari taxi, saida suka shiga yakira dady ya sanar dashi sun iso gashi har suna cikin taxi ina zasu sauka yace su sauka gidan Dr suma gasunan kan hanya in Sha ALLAH.

Motarsu little Bata dad'e da ajesu ba tasu dady ta tsaya inda a babban falo Dr yayi masu masauki bayan yayi ma Dr Nuraddeen wato takwaransa babbar tarba.

Rashida kuwa har lokacin tana can a d'aki duk da kuwa qarar tsayawar motar da taji har sau biyu, tsananin bugawar da taji zuciyarta nayi yasata fitowa da sauri tana share qwallar idanuwanta taci Karo dasu umma, ummie, dady da hajiya nafeesa da suka shigo yanzu, da sauri ta qarasa jikin umma tare da fashewa da wani irin kuka dake tsima zuciyar duk wani mai sauraro.....





*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[11/14, 22:52] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___105πŸ’Ž

"A'a, a'a! Rashida meyene haka kikeyi sai kace wata qaramar yarinya?, Don ALLAH ni d'agani kada ki karyani, daga shigowa kongaisuwa babu sai kifad'omun ajiki kina kuka, fisabillahi ko gajiya bakyayi abu tun jiya!" Umma ta fad'a tare da cireta daga jikinta,

Riqo hannunta dady yayi suka nufi falo suka zauna itama ya zaunar da ita qasan qafafuwansa had'e da dafa kanta yace.

"Yi haquri Rashida, ita rayuwar mumini haka take, matuqar kayi Imani to dole sai anjarabceka, to Alhamdulillah yau Ina cike da alfaharin cewa 'yata tayi Imani kuma anjarabceta ta canye jarabawar da akayi mata, Abu d'aya yarage shine kimiqa godiyarki wajen ALLAH daya baki ikon canye jarabawar da yayi maki tahanyar rungumar sakamakon da yayi maki da hannu biyu kinji ko."

Cikin kuka ta d'aga masa kai yaci gaba da rarrashinta shi dasu ummi, umma kuwa batace komai ba sai kallon 'yar tata da takeyi har suka gama bata baki,

Dr ne ya shigo shida Fatima fuskokinsu d'auke da fara'a suka gaida iyayen nasu bayan suma sun nemi waje sun zauna,

"Ina shi little d'in dr."

Dady yafad'a yana kallonsa.

"Ai dady little ba'a magana, don yau shima yazame mana baqo yana can liqe da Dr suna cin abincin."

"Ah to Masha ALLAH, ai haka akeso, banga laifinsa ba iyaye ai rahamane, aqallah shima yanzu zaiji irin dad'in da kowane d'a kiji idan yana tare da mahifinsa, fatan dai sun iso lafiya ko?"

"Lafiya klw dady."

Dr yabashi amsa yana kallon fuskar Rashida data bayyanar da mamakinta qarara jin cewa wai little na garin kuma wai harda mahaifinsa, murmushi yayi kafin yace.

"Gwaggon yara kinfito?, Yau sai kika yimana yajin fitowa Saida kikaji takwarana ya iso ko.?"

Batace komaiba kanta na aqasa ta sake nocesa tana maijin zuciyarta na wani irin matsanancin bugawa da sauri da sauri,

'Dan harararsa ummi tayi had'e da cewa.

"Meye haka son? So kakeyi ka tsargamun 'ya agabana ne."

"Afuwan ummi, 'yar takice nakasa gane kanta daga jiya zuwa yau, ita da tayi haqurin shekaru da yawa sai naga tana qoqarin b'atasa tsakanin jiya da yau."

"To ya za'ayi, mubita ahankali, wlh al_amarinne da ciwo, Amma tunda ALLAH yakawo sauqinsa sai a haqura don asamu a cike mizanin lada ko kuwa 'yata."

Taqarashe maganar tare da d'ora hannunta saman kan Rashida, a daidai lokacin little ya shigo yana shafar ciki fuskarnan tamkar hasken farin wata saboda annurin dake kwance akanta na kasantuwarsa tare da mahaifinsa, ganinsu ya dashi sakin wani murmushi had'e da buga wata irin uwar gyatsa yana fad'in.

"Alhamdulillah."

Wajen dady yaje ya zauna tare da gaishesa idanuwansa nakan mahaifiyarsa yana son yaga awane yanayi take ciki amma taqi d'agowa,

"Barka da arziqi Nuraddeen, yau dai kewa ta qare, gaka ga mahaifinka, don haka sai kayi qoqarin kyautata masa tare da nuna masa nagartacciyar tarbiyar da mahaifiyarka ta jajirce wajen baka, kada ka kuskura kayi abunda zaisa ko kad'anne yaji aransa don baya tare dakai shiyasa kazama haka, Ina yimaka fatan gamawa lafiya tare dashe cikin amincin ALLAH da yardarsa."

"Nagode dady, in Sha ALLAH bazan tab'ayin wani abun daya sab'awa tarbiyar da kuka bani ba, zan zamo d'a nagari atare dashi har sai yaji cewa bababu wanda yayi sa'ar samun nagartaccin iyaye bayansu sama dani, sai na gamsar dashi cewa d'ansa ya tashi a hannun mutanen da sukafi kowa karamci da halacci aduniya, kuma na nuna masa irin irin nagartacciyar uwa da yayi sa'ar sama mani aduniya da zata iya kulawa dani had'e da bani nagartacciyar tatmrbiya ko baya nan!."

"Masha ALLAH, ubangiji ALLAH yabaka ikon yin haka, mukuwa da munci gaba da alfahari dakai har iya qarshen rayuwarmu."

Juyawa little yayi had'e da gaisheda su ummi sannan ya kalli umma ya d'aga mata gira yana fad'in.

"Na gaida uwar gidana, babuki ba canzawa komai tsufanki kina nan daram a muhallinki, kujerarki ba gudu ba ja da baya."

"Ja'iri, ja da baya kam ai saidai kar aqara, tunda kasamu batoolu ka watsar dani, balle yanzu da babanka ya dawo nasan nan gaba ganinka sai nacika fayil."

Umma tafad'a tana dariya su ummi na tayata, kallonta dady yayi had'e da cewa.

"Kwantar da hankalinki aini hakan yayimun dad'i, daga ni sai ke bawani da zai koma zuwa yana takuramu had'e da 'yar muryar neman ferfesun tsufa, sai kiyita zuba mani Ina cinye abuna ko ba haka ba." Dady yafad'a shima yana dariya.

Jin sallama da motsin shigowar Dr Nuraddeen da Dr nura yaje yayowa jagora zuwa falon shi ya katse masu firar tasu, da sauri Rashida da gabanta yayi wani irin fad'uwa tamiqe har tana tuntub'e da gefen kujera ta shige d'akinta acan sahenta data nufa.

Cikin girmamawa Dr Nuraddeen yashigo falon biye da Dr nura ya zauna qasa kansa na sunkuye qasa yana kallon qasa ya shiga gaishesu d'aya bayan d'aya cikin wata irin jin kunyar da yakeji tamkar qasa ta tsage ya shige.

Bayan sun amsa ya d'ago kai yanda zasu iya ganin fuskarsa ya shiga yimasu gaisuwar baba da ALLAH yayiwa cikawa tare da addu'ar ALLAH yajiqansa kuma yayi masa rahama duk suka amsa da Amin.

Shiru ya biyo bayan wasu mintuna kafin dady ya shiga yimasa tambayar ya hanya da ban gajiya ya amsa da duka Alhamdulillah sannan ya d'ora da fara bada haquri akan abunda yafaru don dama Dr nura ya gabatar masu dashi a matsayin mahaifin little kuma mijin Rashida wanda a daidai lokacin hajia nafeesa ta had'a ido da little ya sakar mata murmushi taji tamkar ta nitse cikin qasa saboda tsananin kunyar da taji.

Yanda Dr Nuraddeen ke magana cikin natsuwa tare da qasqantar da kai da nuna baqincikinsa da nadamar abunda yafaru har kuka na neman yaci qarfinsa yasa dady ya dakatar dashi ta hanyar cewa.

"Ya isa haka d'ana, mu musulmaine kuma munsan da qaddara maikyau da marar kyau kuma duka munyi Imani da hakan, wlh mudai baka yimana laifin komai ba, sannan shi musulmi aduk inda take d'an uwan musulmine, don haka ana buqatar tausayi, yarda, kyautatawa da kuma kyakkyawar fahimta a tsakani, abunda ya faru tsakaninka da iyalinka ne, mu bamuda wani zargi akanka ALLAH kuma shine sheda saboda haka ka kwantar da hankalinka, bayanan ma da muka gani a kafafen yad'a labarai wlh sun Isa suwankeka ga kowa, fatanmu ALLAH ya tsare gaba kuma yayi mana kariya da miyagun qaddarori,"

"Amin" Dr Nuraddeen yafad'a cikin jin dad'in yanda duka abubuwa kezo masa da sauqi, fatansa d'aya ALLAH yasa awajen habibty d'insa ma suzo masa da sauqi.

Nan dai yayita godiya tare da d'orawa akan wata godiyar ta kulawa da karamcin da suka nuna masa shi da iyalinsa da kuma ahalinsa daga qarshe yaroqi abashi damar ganawa da Rashida idan da yuyuwar hakan.

Dariya dady yayi kafin yace. "Ikon ALLAH, kaikuwa Mai zai hana mutum da iyalinsa?, Ai har yanzu Rashida na aqarqashin inuwar aurenka don tun bayan tafiyarka daidai da Rana d'aya Bata tab'a amincewa da abunda zai shafi auren naku ba, mu daine daga baya mukayi yunqurin samun iyayen naka akai maganar a kotu taraba auren kafin dawowarka saboda gudun kada acutar da ita Amma sai tanuna batada ra'ayin hakan don haka muma dole muka haqura, yanzu tsakaninka da iyalinka ne, idan ta amince ko yaune kanada damar d'aukar abukka kutafi.

Shiru Dr Nuraddeen yayi yana tunanin wannan irin Sadaukarwar kai da habibty d'insa tayi masa, koda me zai iya biyanta shi aduniya? Ya tambayi kansa yana goge hawayen da suka zubo masa saboda tsananin tausayinta.

Nan dai aka shiga d'an tab'a fira amma shi gaba d'aya hankalinsa na kan ta inda zai iya hangota, ganin hakan yasa dady yayi gyran murya had'e da miqewa yana fad'in.

"To malan Nuraddeen, bari mutafi marece nayi gashi anbaro yara agidan, son sai akira masa Rashida mu zamu wuce, duk abunda ake ciki saika tuntub'emu awaya."

Yaqarasa maganar yana kallon Dr nura, sallama sukayi dashi sannan suka fice umma nayi tana waiwayen yanda gaba d'aya ya canza ya zama cikakken mutum, koda yake jiya ai ba yauba tafad'a aranta tare da ficewa su Dr d Fatima nabiye dasu zaauyi masu rakiya, har sunkai qofar fita falon Dr yajuyo ya kalli lite dake zaune kusa da mahaifinsa yace.

"Abu sumayya jeka ka kirawo masa gwaggonku kace injini." Yafad'i hakan don yasan zata iyaqin fitowa sannan tajuya yafice daga falon.

Saman kujera Dr Nuraddeen yakoma ya zauna yana jiran fitowar Rashida tare da qurawa qofar da yaga little yashiga idanuwa.

Little ne yafara fitowa a maimakon yayo cikin falon sai yayi waje wajensu Dr da fatima da suka fita rakiyarsu dady.

An d'au tsawon mintuna uku kafin tafito lullub'e da mayafinta maigirma daya lullub'e mata ko Ina na jikinta kanta na sunkuye qasa.

Tunda tafito take kallonta har tasamu waje ta zauna acan d'ayar kujerar dake sakad'e a lungu, bata iya d'agowa ta kallesa ba amma saita samu kanta da iya bud'e baki tagaishesa, tunda ya amsa bata sake tankasa ba yaci magana har yagaji,

Duk wasu kalamai na ban haquri da nadama yayi mata, duk wani lallashin duniya da dad'ad'an maganganu da zasu sanyaya mata rai yayi Amma taqi tankasa.

Cikin karyewa muryar dake nuna gab take da yayi mata kuka yace.

"Me zan yimaki kiyafemun?, Mezan ce maki ki aminta dani, duka kalamaina babu qarya acikinsu, gaskiyace qwara d'aya nake fad'a maki habibty, bansan taya hakan tafaru dani ba, bansan meyasa qaddara tazab'amun hakan tsakanina dake ba, nayi rayuwata awaccan qasar ne tamkar wani bawan da bayada 'yanci, namanta wayeni, namanta komai nawa, abu d'ayane nakasa mantawa shine ni ruhi d'ayane mallakin gangar jiki d'aya, hakan yasa narayu tamkar maraya Kuma nakasa banbancewa tsakanin haske da duhu akan rayuwar aure balle nayi tunanin samun wani sauyi akanki, ke kad'aice tal mace d'aya da nayi alwashin rayuwa da kuma mutuwa atare da ita, ke kad'aice mace tilo dake da iko akan sarrafa zuciyar malaminta, bazan hanaki kuka ba domin ni mai girman laifine awajenki, bazan hanaki d'aukar mataki ba domin nacancanci kihukuntani iya son ranki, sai dai kuma Ina tabbatar maki da cewa ayanzu lumfashina kad'an ne, haka kuma rayuwata taqitacciyace matuqar kikace zaki ida rayuwa bada niba.."

Saida yagoge guntayen hawayen da suka zubo masa sannan yataso ya fad'i agabanta durqushe yanaci gaba da cewa.

"Wannan dai malamin daya kasa kauda idanuwansa akan rayuwarki abaya, wannan malamin da yayi alqawarin miqa rayuwarsa agareki nahar abada, wannan malamin daya d'au alwashin zai iya bada rayuwarsa fansa ga malamarsa yana miqo qoqon baransa bisa laifin daya aikata daki yafe masa, gangar jiki da kuma rouhi suna matuqar kewarki, idanuwa na mararin kallonki nahar abada, kunnuwa nason jin sautin muryarki, haka zuciya na neman tallafin chaji daga wajenki, kalmarki d'aya ta isa tagusar da baqin duhun data kasance acikinsa na tsawon shekaru, adadin zantukan kalaman bakinki kuma sun isa su gusar da duk wata tsatsa a kwakwalwata data toshe mani tunanina na tsawon lokaci, kiji tausayina don ALLAH kiyimun uzuri, na amshi laifina hannu bibbiyu kiyafemun."

Duk da tanajin dirar kowace kalma azuciyarta kuma tana son mayar masa da amsarta kasawa tayi saboda kukan da yaci qarfinta tun tanayi a hankali har tasoma yi cikin sauti, runtse idanuwa yayi da sauri saboda jin zafi da rad'ad'in sautin kukanta da yakeji a zuciyarsa.

Miqewa yayi cikin d'ari d'ari yana son ya rarrasheta amma yanajin wani irin kwarjininta da bazai iya hakan ba, sai ya miqa hannunsa ya tab'ata sai kuma ya kasa, ya sake miqawa sai yaji ya kasa, ita kuwa sai tsananta kukan takeyi yanda tasan zai iyaci gaba da hurting d'insa sosai.

Kasancewar little dadu Dr zaunensu sukayi waje saman kujerun dake gefen rumfar motocin dake a'aje bayansu dady sun tafi yasa bakajin tashin motsin kowa cikin falon inba sheshshekar kukan Rashida ba, a hankali ya sake runtse idanuwansa ya zauna kusa da ita tare da jawota ajikinsa yafara lallashi yana fad'a mata kalaman ban haquri a kunnuwa duk da bayada tabbacin zata iya fahimtars, cikin wani irin yanayi daya tsinci kansa aciki bayan tsawon wasu shekaru yake rad'a matasu a kunne kamar hakan.

" _I am really very sorry to start with habibty, Since the time you refuse to talk with me, I' m completely lost. I believe that things are not the same for me and for you. My intention was not bad, the timing was wrong. You know what I feel for you is really strong. I want to talk to you in a similar way as I did before. I want to play pranks with you as before. Please forgive me now and end this for all. Because this situation...!,"

Sai kuma yayi shiru ya kasa qarasawa sai 'yar sheshshekar kuka shima yaci gaba da sakar mata a kunne, wani iri yanayi taji tasoma shiga da zai iya skata manta abunda yafaru wanda bata buqatar hakan ayanzu, zumbur tamiqe adai dai lokacin da take fad'in.
" _I am really feeling so small for what I did, I ask for you forgiveness and hope you will do it now. Always Sorry from my side!_

Hannayenta tasa ta share fuskarta tana kallonsa cikin zafi da rad'ad'in qunar da zuciyarta keyi tunawa da kalaman da taji yayi ashekarun baya a cikin tv tace.
" _There is no place for forgiveness in this relationship, we've being separated for along time ago b'cos of so many embarrassed you couse to me and my son, always had issues but we held for too long, I do not have any more patience to be strong now, So i choose to breaking up with you peacefully, b'coz the love lost between us since!,_"

Tana gama fad'ar hakan tabar wajen batare data bari sun sake had'a idanuwa ba.

Kallo Dr yabita dashi bud'e da baki jin yanda take watso masa turanci tamkar ga bakinta aka halittosa, gaba d'aya ko kad'an kalamanta basu b'ata ransa ba, asalima farinciki yaji data bud'e baki tayi masa magana da harshen da baitab'a tsammani ba, wai matarsa Rashida, d'alibar nan tasa daya sani marar son karatu itace yau tsaye agabansa tana mayar masa da magana da kalaman dake nuna baqaramin gogewa tayi wajen karatuba kafin takai wannan matsayin da zata iya hakan, ji yayi kaso arba'in cikin damuwarsa ta ragu don ya tabbata da sannu zata haqura domin akwai banbanci tsakanin fushin mai cikakken

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login