Showing 42001 words to 45000 words out of 260204 words

Chapter 15 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt

zuwa gobe sai asake dafa maka, ita madarar Kuma dama kamar nono take tahuce sai kasha."

"A'a d'auka tafi dasu nace maka" dole ba yanda zaiyi ya d'auka had'e da yimasa saida safe ya fice, baffa na kallonsa ya koma cikin gida batare da ya fitar daya tashi yiba, murmushi yayi yace, "ALLAH ya kyauta sannan ya komawarsa ya kwanta, sashensa yabud'e ya shiga tare da karanta addu'a ya rufe.

Koda ya shiga ya tarar har tayi bacci ya ajiye ledar hannunsa had'e da nufar inda take kwance da alama sallolin magrib da isha'i tagama bacci ya d'auketa, hannuwansa yasa ya tallabota tare da cire mata hijabinta ya dinga hura mata iskan bakinsa a fuska, ahankali tafara bud'e idanuwanta suka sauka saman fuskarsa ai kamar wacce aka mintsila tayi saurin zamewa daga hannunsa tana tattaro hijabinta tana rufe jikinta, murmushi yayi daga duqen da yake tare da cewa "tashi muje ki wanko bakinki a toilet." Yaqare maganar had'e da mik'ewa ya riqo hannunta suka nufi toilet d'in tana biye dashi tana kallonsa, bata tab'a kula da kyan da ALLAH yayi masa ba sai yau...








*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___19πŸ’Ž

Cike gidan yake maqil da 'yan uwa da abokanan arzik'i na nesa dana kusa da suka zo taya umma da baba murnar aurar da 'yar tasu tilo, duk wanda ka kalla awajen kasan cewa cike yake da tsantsar farinciki saboda yanda fuskokinsu ke d'auke da annuri anata gudanar da buki wan shagali.

Fuskar baba cike da fara'a ya shiga cikin gidan bakinsa d'auke da sallama yana rarrab'awa ta gefe gefe saboda yanda gidan yacika maiqil da 'yan buki sai faman shiga raha akeyi wasu na shiga wasu nafita, duk inda yabi sai faman gaishesa akeyi ana tayashi murna tare da ALLAH sanya alkhairi, da qyar ya samu ya shiga ciki had'e da nufar wani d'aki da suke ajiye kayayyaki aciki yasa wata tobashiyarsa ta kirawo masa umma dake can tsakar gida tasha adonta cikin wani had'ad'd'en leshi wanda saika duba da kyau zaka iya gane itace, yajima zaune cikin d'akin yana tunanin shikenan yau zai rabu da 'yarsa tilo da yakeji har cikin qoqon ransa kafin umma tasamu takuccikke daga baqin dake dad'a shigowa tanufo inda take, a jigace tashigo cikin d'akin tana fad'in, "ai sai kuyi babu wanda zan sake d'ebowa abinci in zaku tashi kuje kud'ebo da kanku ku tashi, ai Kuma 'yar takuce bani kad'ai nahaifeta ba balle kubarni da aiki, don haka ni nagaji bazan qara yimaku wani abunba, shikenan daga kara saiku barni da aiki."

Murmushi baba yayi yana kallon fuskarta sannan yace, "haba uwar amarya, wannan irin fad'a haka da kikeyi halan keda wa."

"Nida matan balarabe mana, su daya dace ace suke tarbar baqi suna kai masu abinci shine sunka koma gefe kowace ta hakince sai kace tukane suna kiran akawowa wance da wance abinci, sun barni ni kad'ai ke hidimata sai kuma fareeda 'yar wajen yaya maryama."

"A'a'a to wannan maganar tafi qarfina tsakaninki ne da qannenki ba Mai shiga tsakani, ni dama zancen kai amarya ne yakawoni kinga gari ba guda ba.." kafin yaqarasa tayi saurin cewa,

"To ai sai anyi sallar la'asar za'aje ko kuwa?"

"A'a, bayin ALLAHn nan sun roqi alfarmar abasu amaryarsu su wuce da ita don gaba d'aya suka zo d'aurin auren tare da motocin d'aukar amarya, don haka kishiryata in sha ALLAH yanzu zasu wuce da abussu"

"Amma malan bamuga 'yan biko ba haka zamu miqa masu ita kamar..."

"Haba maman Rashida kada kice komai da yanzun da anjima duka d'aya ne, kuma shi biko ai al'adace ba addini ba don haka kiyi hak'uri tunda har iyayensa maza sukayi magana tamkar sun turo bikon ne, aje ashiryota gamunan muna jiranta muyi mata hud'u ba sai suwuce."

Jiki a sanyaye umma tafita tamkar wacce k'wai ya macewa a ciki, duk tsawon kwanakinna bata tab'a d'aukar cewa tabbas zata rabu da 'yar tata ba sai yanzu, cikin k'arfin hali tanufi d'akin da Rashida ke ciki kwance tana kuka bayan andawo da ita wajen wanka ita da 'ya'yan malan balarabe qanen mahaifinta su uku, sunyi lallashi har sun gaji sun qyaleta suna ganin umma tashigo duk suka mik'e suka fita, dai dai wajen kanta umma taje ta zauna tare dasa hannuwa ta d'ago kanta, cikin kuka tafad'a ajikinta tana sheshheka, ko kad'an umma ba tayi yunqurin hanata ba domin itama kanta kukan ne yazo mata, saida sukayi mai isarsu sannan cikin muryar dattako umma tafara yimata magana har lokacin tana jikinta.

"Rashida kuka bai kamaceki ba, domin wannan ranar farinciki ce agareki da kuma mu iyayenki da Allah yabamu ikon ganin mun sauke d'aya daga cikin haqqoqanki daya d'ora mana kuma ranace da kika dad'e kina jiran zuwanta don haka kinatsu ki saurari abunda zan fad'a maki amatsayina na mahaifiyarki." Share hawayen da suka sake zubo mata tayi sannan tasa hannuwanta ta tallafo fuskarta tana share mata qwalla had'e da cewa.

"Rashida! Ina so kibud'e kunnuwanki kiji abunda zan fad'a, gidan aure da kike gani ba wajen zaunawa kace zaka huta bane ko kace kayisane don kasuwanci, wajene na gwaggar maya don meman lada da kuma aljannarki, shi gidan miji wajene da zaki jajirce wajen nunawa duniya nagartar gidanku da kuma ahalinki, duk wata kima da darajarki annan ne zaki tabbatar da ita ta hanyar nuna kamalarki ga ahalinda zaki riska ku zauna dasu, mijinki shine aljannarki kuma shine farincikin ki na duniya da lahira, haquri da kike gani shi ginshiqine na tabbatuwarki isashshiyar mace awajen mijinki, shi kuma ladabi da biyayya sune zasu zamo maki tubalin da zai mai dake kasaitacciyar mace awajen mijinki, girmama iyayensa abune da zai qara maki kwarjina da tarin soyayya azuciyar maigidanki, kauda kai kuma da iya dad'ad'an lafuzza ga 'yan uwansa shi zaisa su soki har su zauna dake lafiya, kwanciyar hankalin da zaki bawa mijinki ita kuma jigoce ta yalwatuwar arziqinsa, kyautatawa da yin alkhairi ga mutane shizai jawo maki girmamawa ga manya da yaran da kike tare dasu, kiriqe ALLAH, ki guji abun hannunki, kibi mijinki kiyiwa mahaifiyarsa biyayya tamkar yanda kike yimani ga duk abunda bai sab'awa ALLAH ba, rashin kunya, tsiwa da sakin baki acikin mutane sukan xubarwa da mutum kima da daraja don haka ki nisancesu, Ina mai roqonki da duk k'arfin tsanani da wahala kada kid'aga harshenki akan na mijinki, idan son samune kada ki zalinci kowa kibari ke azalinceki da SANNU SANNU ALLAH zai yi maki sakayya, shi khairan da sharran duka 'yan aikene duk inda ka aikesu za suje kuma su dawo maka, kiyi k'ok'ari kishuka alkhairi don ki girbesa, kizama mai haquri da juriya sannan kizauna da kowa lafiya, kiriqi tsafta nasan kinada ita amma ki qara haka girki shima duk da bani da wani haufi akai amma ki kula sosai wajen kiyaye lokacin yinsa da wajen dafasa, banda almubazzaranci ko rashin yiwa miji godiya ga duk abunda yakawo, kiriqi addu'a da azkar na safiya da marece da lokacin kwanciya insha ALLAH zasu zamo maki fitila arayuwarki, ki guji fushin mijinki, ki nesanta da duk abubuwan da kikasan baya so ta hakanne zaki samu cikakkiyar natsuwa a gidan aurenki, Ina roqon ubangiji da yayi maki albarka, yakare mani ke aduk inda kika shiga ga sharrin mutum dana aljani, ALLAH ya albarkaci dukkanin zuri'ar da zaki samu ya kareki daga fad'awa ko wace irin fitinar rayuwa ta duniya da kuma lahira."

Duk da Rashida nacikin damuwar rabuwa da iyayenta hakan bai hanata jin dad'in lafuzzan mahaifiyarta ba agareta, gaba d'aya zuciyarta da kuma qwaqwalwarta sun gamsu da nasihohin data yimata kuma tayi alqawarin zatayi aiki dasu komai rintsi komai wuya, cikin sheshhekar kuka tace,

"Amin ummata, zan kula da duk abubuwan da kika fad'a mun kuma nayi maki alqawarin zamowa mai tsananin haquri da yiwa mijinta biyayya tamkar yanda naga kinayi." Rungumeta umma tayi tana murmushi had'e d cewa,

"A'a Rashida, bana so kiyi yanda kikaga inayi nafiso kiyisu fiye da yanda nakeyi kinji ko?." Cikin kuka tace,

"In sha ALLAH, ummata zanyi, don ALLAH kiyafemun duk wani abu Dana yimaki, ummata Ina matuqar jin kewar rubuwa dake." Taqarashe maganar tare da naniqeta ajiki tamkar zata tsagata ta shige tana mai k'ara tsananta kukanta,

"Rashida kenan! wake maganar yafiya anan bayan ummanki cike take da soyayyarki da kuma alfaharin samunki taya har za'ayi kiyi wani laifi kome qanqantarsa agareta kuma har yasamu muhalli acikin zuciyata?, Babu komai tsakanina dake face tarin d'inbin albarka da nake yimaki fata awajen ALLAH" cireta tayi daga jikinta sannan tamik'e taci gaba da cewa, "kije kishirya Rashida mahaifanki na jiranki a d'akin kaya kinji ko?." Tana gama fad'ar haka tajuya tafice daga d'akin, wajen qanwarta aunty marwiyya tanufa tayi mata magana akunne sannan tawuce wajen bak'in da suka shigo yanzu, da sauri ita kuma aunty marwiyya tashiga d'akin da Rashida take tasa ta tashi tashiga toilet tayo wanka da ruwan turarukka masu qamshi sannan tasa ta tsuguna saman turaren wutan da tana fitowa ta isko tahad'a mata, bayan yagama shiga jikinta tabata wani had'in madara daya sha kayan gyaran ni'imar jiki tace tashanye sannan tahau kimtsata yanda ya kamata, ba'afi mintuna ishirin ba sai gashi tafito da ita cikin had'ad'd'iyar shiga mai kyau da kuma d'aukar hankali, duk inda Rashida ta gotta sai zuba qamshi takeyi fuskarta a lullub'e, daidai lokacin malan balarabe yashigo cikin gidan yana fad'an afito da amarya anbar mutane zaune suna jira, ganinta yasa yayi shiru tare da nufar d'akin da d'an uwan nasa ke ciki suna jira, acan aunty marwiyya tanufa da ita suka shiga kan Rashida naqasa har lokacin tana zubar da k'walla, Saida ta duqar da ita agabansu sannan ita kuma tajuya tabar d'akin, naseeha sosai suma suka yimata sannan suka aika aka kirawo umma itama ta sake yimata wata sama sama, rungume baba tayi tana kuka mai tsima rai tare da roqonsa gafara nan take shima yaji kukan na nema ya kucce masa, da sauri yamiqe yana fad'in "nayafe maki Rashida ALLAH yayi maki albarka" ya fice daga gidan yana goge hawayen da suka zomasa, wajen umma tanufo ta sake rungumeta tana kuka umma ta dafa kanta had'e da cewa,

"Kitafi gidanki cikin amincin ALLAH da kuma yardarsa Rashida, ALLAH ya albarkaci rayuwarki yakareki ga dukkanin sharrin shaid'an da kuma ahalinsa" tana gama fad'a itama tajuya tayi cikin gida tana hawaye.

Aunty marwiyya ce tazo tarik'ata sai kuma yaya Maryam (yayarsu baba) dama tuni ansanar da 'yan bukin duk mai halin zuwa kai amarya ya gyara yanzu za'a kaita ba sai anjima ba kamar yanda aka tanada, Kai tsaye aka fiti da Rashida tana reren kuka yayinda suna isa bakin gida suka tarar da motar da aka tanada don amarya har anbud'e ana jiran isowarta, aunty marwiyya ta duqar da ita tana mai rad'a mata akunne cewa ta tashiga da _"Bismillah tawakkaltu alallah wala haula wala quwwata illah billah"_

Cikin zuciya tadinga karantota duk da kuwa kukan da takeyi na nema ya rinjayi zuciyar tata sannan sukuma sauran mutane suka shiga sauran motocin aka tayar, dama mota biyarce aka kawo takai amarya sai motarsu baffa sukuma tuni ana fitowa da ita sukayi musabaha da malan balarabe da kuma baba had'e da yin godiya suka wuce gaba, saida mota biyu tashiga gaba bayan tasu baffa sannan wadda rashida keciki tabi bayansu sannan biyun suka bi bayanta suma, wani irin kuka mai tsimarai Rashida keyi tana nazarin kalmar da akoda yaushe take d'auka mai sauqi wajen furtawa (aure nake so) wacce gaba d'aya bata natsu wajen fahimtar kome take nufi ba sai yanzu da aka rabata da iyayenta, tabbas tana farincikin samun muradinta da kuma auren amma rabuwa da iyayenta gaba d'aya ya shamakance ta da bayyana wannan farinciki, tafiya mai d'an nisa sukayi kafin su isa garin bebeji lokacin har anfara kiraye kirayen sallar magrib amma koda suka isa dandazon yaran shiyar dake qofar gidan suna ihun ga amarya bazai bari kaji sautin kiran da akeyi ba, motar da take ciki na tsayawa gabanta ya fad'i da sauri tafad'a jikin aunty marwiyya tana kuka,

"A'a Rashida wai kukannan naki bazai qare bane? Yakamata kiyi hak'uri haka domin duk wata d'iya mace dake gidan mijinta saida ta fuskanci hakan."

A hankali ta tsagaita kukan sannan yaya maryam tarik'ota tafito daga cikin motar tana fad'in kiyi addu'ah _"hazbunallahu wani'imal wakeel"_ Rashida tafad'a acikin zuciyarta kafin ta azo qafarta tafito daga cikin motar fuskarta a lullub'e, ihu yara suka hau suna fad'in, "yeeee.. amarya, amarya, ke kicce kinaso da bakice kina so ba da ba'a baki shiba." ahankali suke tafiya da ita tamkar k'wai har sukazo bikin k'ofar shiga gidan, qafarta ta dama ta aza tana karanto addu'ar "

_"Allahummah inna naj'aluka fi nuhirihim, wana uzu bika min shururihim"_ ma'ana (ya ALLAH! mu muna sanya ka a gabansu, kuma mina neman tsarinka daga sharace sharracensu.) sosai taji tasamu 'yar natsuwa daga ynayin da takeji suka shiga da ita, cike da farin ciki Yaya balkisu ta tarbesu hannu biyu ita da sauran 'yan uwa dasu kareema 'ya'yanta suna "sassannuku da zuwa, ku wucikke, masha ALLAH, kuwucikke da ita nan." Ana nuna masu shiyarta wacce koba tambaya kasan b'angaren amarya ne, suna tsaye kafin su shiga suka jiyo muryar matar baffa Ali tna fad'in,

"To mudai gidannan bamu da bare sai yanzu, ALLAH kasa ba'a d'ebo mana miyagun dangi ba.." kafin wasunsu su ankara da abunda tace inna bilkisu tace dasu "kuwucikke mana kun bar mana amarya tsaye kada qafafuwanta suyi ciwo." Murmushi aunty marwiyya tayi had'e da cewa "A'a muna jiran agwada mana sashen uwar mijin tatace mukaita wajenta tukuna."

"Ahaf illar bare kenan komai nasa daban yake, To mudai ba haka mukeyi ba anamu al-adar, kufara shiga da ita d'akinta tukuna sai tafito da kanta tagano d'akin uwar mijin nata donmu auna hankalinta, mu haka mukeyi inyaso ku kwa jirata anan har tafito" suka sake jin matar baffa Ali dake can bakin k'ofar d'akinta zaune saman wata kujera tafad'a tana tamnar cingwam, cikin sakin fuska Yaya Maryam tajuyo had'e da cewa.

"To kuyi hak'uri tunda har bare nada wata illa Kuma ahaka kuka gani kukace kuna so, kuma mu al'adarmu zamubi ba taku ba tunda bare muke." Wani irin dad'i inna bilkisu taji da amsar da Yaya maryam taba matar baffa Ali kafin tace dasu "kuwucikke ga shiyarta can" tana murmushi ta wuce gaba suka bi bayanta, sallama sukayi Yaya hawwa nakwance saman gadonta d'an bono tana jinsu fiye da minti biyu Amma bata msa ba balle ta taso hakan yasa inna bilkisu leqawa taciki tana fad'in.

"Assalamu alaikum Yaya hawwa ga bak'i nan sun iso." Tana qoqarin shiga ciki, wata irin tsawa Yaya hawwa ta dakawa inna bilkisu da tasa saida Rashida tazabura had'e da rik'e Yaya Maryam tana fad'in,

"Kul! kada wanda ya sake ya shigomun d'aki, bak'i ai nakine don haka kiyi qoqari ki karramasu ki zame mata uwar miji hakan zaisa nasan cewa ked'in 'yar kanzagice lamba d'aya." Shiru bilkisu tayi tanaji kamar ta zubar da kwallah saboda walaqancin da yaya hawwa tayi mata agaban mutane gashi tayi alqawarin bazata sake kula ta kanta ba balle tamayar mata da magana daidai yanda tayi mata, murmushin dake cike da takaici tayi tare da juyowa tana kallon 'yan kawo amarya da sukayi cirko cirko suna sauraren ikon ALLAH, cikin qarfin hali tace,

"Kuyi hak'uri kuzo muje akaita d'akinta ga motocican suna jiranku naji sunata faman yimaku oda" taqarasa maganar tare da juyawa tana qoqarin b'oye damuwarta.

Adai dai bakin k'ofar shiga sashen Rashida inna bilkisu ta tsaya, sunaji matar kawo Ali ta tintsire da dariya tana fad'in "Yaya hawwa tayi tsiyar kenan ko bilki." Had'e da tuntsirewa da wata dariyar, gab d'ayansu babu wanda ya tankata suka wuce ciki bakin Rashida d'auke da addu'a jikinta har wani rawa yakeyi sannan tashiga haka lokacin da zata shiga d'akinta har ta aza qafa aunty marwiyya tadawo da ita baya had'e da aza qafarta ta dama tace, "kiyi bisimillah da ayatul kursiyu, sannan ki karanta _allahummak finihim bima shi'ita_ (ya ALLAH ka isar mani su da abinda kaso) don wannan gida da kike gani sai kinyi hak'uri, baiwar ALLAH nan kad'aice nagani da alamaun mutunci."

"Marwiyya menene haka!" Yaya Maryam tafad'a tana kallonta,

"Hmm Yaya Maryam kenan! Wlh tunanin abunda zan barwa yrinyarnan yasa nakasa tankawa da wllh tundaga waccan angulun har uwar mijin tata saina yimasu wankin babban bargo."

"Ya isa haka marwiyya ALLAH yakyauta." Lokacin Rashida tagama addu'arta sannan suka shiga, nan kallo yakoma cikin d'akin don ba qaramin k'ok'ari baba yayi ba, hatta tv da vedio da fridge duk saida yasa aka sakawa Rashida, komai yayi kyau gwanin burgewa, nasiha suka sake yimata da tayi taka tsantsan da sha'anin mijinta da kuma duk wani abu da zai had'ata da mutanen gidan don kaucewa rashin mutunci sannan sukace tarik'e inna bilkisu hannu biyu ta d'auka 'yar uwarta ce da zata dinga magance matsalolinta kafinsu don sun yaba da halinta, daidai lokacin inna bilkisu tashigo sashen ita da 'ya'yanta salame da kareema d'auke da ledojin ruwa dana muhallip da kuma wani kwali babba dake cike da tarkacen biskit da mintuna da cingwam wanda bafffane ya aiko dasu yace abawa 'yan kawo amarya, sake gaggaisawa akayi ta sake basu hak'uri bisa abunda yafaru sannan ta basu kayan, cikin jin dad'i sukayi godiya sannan yaya maryam tace.

"To bilkisu ga amanar Rashida nan mun baki, duniya da lahira mun amince kiyi mata hukunci daidai yanda kike yiaw 'ya'yanki idan tayi ba daidai ba, mun baki amanarta ki kula da ita batada kowa saike don ke muka sani yanzu, Rashida qaramar yarinya ce da hankalinta bai isa banbance daidai da rashinsa ba don haka kiyi mana taimakon d'orata akan hanya aduk lokacin data kauce, mungode mungode sosai, ALLAH yasaka maki da alkhairi kuma yabaku haqurin zama."

"Amin nagode nima, karku damu da abunda yafaru sharrin shed'annne kunsan halinsa la'ananne ne, dukkaninmu abu d'aya muke kuma in sha ALLAH zamu kula maku da amanar Rashida domin itama 'yar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login