Showing 246001 words to 249000 words out of 260204 words
Chapter 83 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt
nakira maka gimbiya.!"
Saida yafad'a sannan yayi saurin toshe baki yana dariya, ya manta agaban mahaifinsa yake bai kamata yafad'i hakan ba yace cikin ransa, waskewa yayi tare da cewa.
"Aww Ina nufin batool baba."
Murmushi Dr Nuraddeen yayi had'e da cewa.
"Babu damuwa."
Yana rufe baki saiga aunty marwiyya ta iso wajen tana tafa hannuwa.
"Ikon ALLAH, yanzu Kai little shine zaka jaye mahaifinka anan ana son ganinsa, to kazo maigidanka nason ganinka mu zamu wuce."
Hakan yasa ya fasa kiran ya kad'a wayar aljihu sannan yabi bayanta, bayan ansake tab'a wata firar little yayi masu rakkiya har inda zasu hau mota suka wuce shikuma ya dawo,
Ataqaice dai ranar har kusan goma na dare suna karb'ar baqi masu zuwa yiwa Dr sannu da zuwa da masu taya baffa murnar dawowar d'ansa harma da masu zuwa tsogumi, Wanda hakan yasa little ya kasa komawa wajen batool saidai sukayi waya inda anan ya sanar da ita komai akan dawowar mahaifinsa wanda ya kasance shine mutumen daya taimakesu ayau, duk da tajima tana zargin mijin nata nada alaqa da mutumen aranta hakan bai hanata mamaki ba sosai, musamman da taji koshi waye, tayi farinciki sosai tare da jin dad'i, cikin daren ta iske mahaifinta tabashi labarin mahaifin little yadawo shima nana take yanuna farincikinsa, da kansa ya d'auki waya ya amshi lambar da tayi waya dashi yakirasa yana tayasa murna, nan little ya had'asa da mahaifinsa yayi masa barka da isowa tare da tabbatar masa da cewa gobe zasu biyo hanya suma in Sha ALLAH.
Baba nusaiba kam yau gari nasu, abinci na musamman ta shiryawa babban d'a tare da babban jika, sannan ta kwashikke kayan yaranta mata tamayar a d'akinta tasa aka sharesa tass akasa qatuwar katifar nan mai tuli irinta family ta feshesa da room freshner da sababbin labulayye yayi gwanin sha'awa, koda suka shigo gidan su uku saisu baffa da suka rakkosu acan tayi masu masauki wanda hakan ba qaramin dad'i yayiwa baffa ba ta kawo masu lafiyayyen abincin data shirya masu sukaci suka sha suka qoshi sannan su baffa Usman sukayi masu sallama don lokacin dare ya miqa har qarfe d'aya tayi, Dr Nuraddeen yaso yabi su baffa ya kwana acan wajen mahaifiyarsa amma shauqin soyayyar d'ansa tasa ya shafa'a har dare ya raba suna zaune su uku suna fira cike da soyayya, duk little ya kalli mahaifinsa sai yaji wani dad'i aransa ya rufesa marar misaltuwa, yayinda shi kuma Dr ji yake ya tsani kansa sosai idan yakalli yanda mahaifinsa yakoma, Wanda ya tabbatar wahalace da kuma damuwar rashinsa akusa dashi ta jefasa aciki, nanma kasa jurewa yayi saida yayita kuka yana roqon mahaifin nasa da d'ansa yafiya don yasamu nauyin da yakeji aransa ya ragar masa.
Har aka kira sallar asuba suna zaune suna fira Dr nabasu labarin halin daya tsinci kansa aciki awaccan qasar da irin rayuwar da yayi, sun matuqar tausaya masa sosai don kam ba rayuwace mai dad'i ko ingantacciya yayi ba daga qarshe duk suka taru suka yafi juna tare da addu'ar ALLAH yabawa kowanensu tsawon rayuwar da zasuji dad'in juna, shidai baffa murmushi kawai yayi tare da amsawa da Amin don yasan shikam ai tafiya tayi tafiya saidai fatan cikawa da Imani, Saida baffa yatada baba nusaiba sannan suka wuce masallaci bayan sunyi arwala, da aka gamo sallah Dr Nuraddeen ya kalli mahaifinsa bayan ya gaishesa sannan yace yayi can babban gida wajen mahaifiyarsa.
Baffa ya amsa masa da "To ALLAH yatsare hanya ka gaisheta."
Ba kunya ba tsoron ALLAH little yaja qafafuwa yanda kukasan zariya yabi mahaifinsa yana yiwa baffa sai yadawo.
Baffa ya amsa masa da "Adawo lafiya" yana murmushi.
Baffa nakomawa gida yanemi waje ya kwanta saboda akwai bacci sosai a idanuwansa, kan kuma kace me har yayi awon gaba dashi.
Su Dr kuwa Saida suka lelleqa d'akunan baffa Ali da baffa Usman suka gaishesu sannan suka wuce d'akin Yaya hawwa, tanaji anturo qofa tace.
"Bilki ce?, Wai Ina yaron nan nura yaje ko yamani wayau yasake tafiyarsa."
Dariya sukayi atare Dr. Nuraddeen yaje kusa da ita ya zauna tare da jawo hannunta yariqe yana d'an mammatsa mata sannan yace.
"Ina zanje kuma nabarki innarmu?, Barka da safiya, Ina kwana kin tashi lafiya?"
Saida ta zare hannunta tad'an shafa fuskarsa sannan tace.
"Lafiya klw, Ina katafi tunjiya baka dawo ba."
"Kiyi haquri innarmu, a gidan baffa na kwana kinga nan babu waje, amma yau anan zan kwana tare dake."
"A'a nura, kaje ka dawo da matarka, a wajenta yakamata ace ka kwana ba'a nan ba, Ina ance batayi wani auren ba ko?"
"Eh innarmu, Amma abune mai wahala tayarda nadawo da ita koda naje."
"Kaje zanyi maka addu'a, nasan zuciyarta mai kyauce zata biyoka kudawo tare, idan ba haka ba kuwa kada ka kuskura kadawo nan har saita amince kaji ko?."
Shiru yayi yana mamakin maganganun dake fitowa daga cikin bakin mahaifiyarsa, wai yau ita da kanta take bud'e baki tace yaje ya dawo da matarsa duk irin tarin tsanar da tayi mata ada, tabbas rayuwa na koyar da mutum darasi aduniya kuma duk abunda yasaka kuka to da SANNU SANNU wata rana zai saka dariya, yana wannan tunaninne yaji muryarta kamar zatayi kuka tace.
"Bakaji bane nura!, ko kana haufine da jin tsoron kada in aikata mata wani abunne makamancin waccan da nayi?"
"Ko kad'an innarmu, nasani bazaki yimata komai ba, wancan ma kuskurene kikayi da Babu wani mahaluqi aduniya d'aya wuce yinsa, zanyi yanda kikace, zan kuma yi iya qoqarina, saidai idan takasa amincewa to kiyi haquri zan dawo na Ida qarasa rayuwata hakan don ko kad'an bazan iya takurata ba."
"Karka damu, zata amince in sha ALLAH kaji ko?, Ina shi wannan yaron ko yatafiyarsa shima."
Kallon little Dr yayi alamun dashi take yace.
"Ganinan kakata mai kuka!, Ban tafi ko inaba nima ina nan tare da babana, wato so kike natafi na barki daga ke sai shi ko?, to Babu inda zani nazo kenan!"
"Shikenan, ai ni banida ja, kayi zaunenka kayita kallon mahaifinka kanajin sanyi, nima duk da bana gani ina matuqar jin dad'i azuciyata muryoyinku danakeji."
Haka yayita tsokanarta tana basarwa har ya gaji yabari ya shiga bawa mahaifinsa labari akan iyayensa na borno da kakanninsa wato Dr nura da fatima sai dady da umma da kuma ammie, sosai Dr Nuraddeen yashiga jinjina al'amarin ALLAH yanda ALLAH ya tsaro b'atan matarsa zuwa wancan garin sai kuma zuwan iyayenta acan don ya wanzar da qulluwr alaqar dady da umma mahaifiyar rashida da kuma alaqar d'ansa little da batool, tabbas al'amarin ALLAH da girma yake, tabbas zaiso yaga wud'annan irin mutane masu tsananin karamci da kuma halacci arayuwa dako atarihin mutanen da masu tsananin karamci bai tab'ajin irinsu ba.
Ana haka baffa Usman da baffa Ali suka shigo, gaida Yaya hawwa sukayi sannan suka bud'e sabon shafin fira, inda anan Dr Nuraddeen ke tambayar baffa Usman yanda akayi mahaifiyarsa tasamu lafiya wanda tun jiya yake son ya tambayi hakan.
Kuka yayi sosai tare da rungume mahaifiyarsa yana maijin tausayinta akan qalubale da wahalhalun da tasha aduniya, haqiqa duk wanda ke tare dasu yakasa d'aukar darasin yanda duniya ke tafiyar da rayuwar d'an adam to tabbas yayi nisa koda kuwa zuciyar qarfene dashi, daga qarshe yayiwa ALLAH godiya tare da roqonsa yaci gaba da yafewa mahaifiyarsa har iya qarshen rayuwarta, haka itama Inna ruqayya yaji d'aci sosai aransa data jinkirta tuba har ALLAH ya amshi ranta, itama ya roqi ALLAH daya gafarta mata kuma ya haskaka kabarinta sannan yayiwa su baffa gaisuwar rashinta.
••• ••• •••
A can borno kuwa tuni labari ya Isa ga kunnuwansu dady da umma don kai tsaye Dr nura yaje yasanar dasu zancen dawowar mahaifin little, inda umma tanuna hakan ko ajikinta don ta d'auka almarane har sai bayan sallar azahar da dady yazo da sauri ya kunna tv saboda kiran da Dr Nuraddeen yayi masa yace su kunna sugani gaya nan ana fira dashi, ganin yanda abubuwan suka kasance da kiran dasu Yaya Maryam sukayi mata suka qara sanar da ita yasa ta gasgata hakan, yanda aka nuno baffa mahaifin Nuraddeen shine Abu na farko daya tab'a zuciyarta har yasata zubar da hawaye, tayi kuka sosai tare da nadamar irin tsattsauran hukuncin data d'auka akai, aranar babu wanda yafad'o mata arai, yanda ako yaushe yake tausarta idan ranta ya b'aci da irin nasihohin da take yimata akan tsaurara bincike kafin yanke hukunci da tsayuwa akan gaskiya komai d'acinta da rama alkhairi ga wanda yayi maka sharri, da haquri akan kowace irin zaman takewa amma tsananin soyayyar da takeyiwa 'yarta da ganin yanda kamar aka cutar mata da ita yasa tawatasar da duka wud'annan nasihohin tabi son zuciyarta suka d'auki alhakin bawan ALLAHn da akoda yaushe bayada burin daya wuce ya kyautata ga dukkanin wanda ya rab'esa, shidai dady banda kallonta babu abunda yakeyi har taci kukanta mai isarta tayi shiru sannan yace.
"To kinga irin ranar da awancan lokacin nake guje maki zuwan irinta, ba don kin d'auka da zafi sosai ba da bazaki rasa tunanin cewa taya mutum naji da ransa da hankalinsa zai guji qasarsa, iyayensa, iyalinsa da 'yan uwansa ya zab'i zama inda babu ko d'ayansu awajen bayan sune abun tutiyarsa aduniya, azzannu zanbun walau kana haqqun, wato zato zunubine koda yazamo gaskiya amma kai da ganin hakan kasan akwai wani b'oyayyen alamari da d'aurin goro acikin wannan batu, yanzu kam koma meye anriga an gama kuma tunaninki da damuwarki nasan duk bazasu wuce b'oyewa bawan ALLAHn nan gaskiya da jininsa da kukayi har tsawon wannan lokacin, to Alhamdulillah dama hankalinku da namu ba irid'aya ba, duk da ambi turbar yanda kukaso daga baya munyi tunani kuma mun had'a yaronnan da kakansa da sauran dangin mahaifin nasa, duk wani sha'anin aurensa da qaruwar daya samu dasu akeyi, anb'oye maku hakanne don azauna lafiya daku tunda ku mata baku fiye tunani akan abunda ke daidai ba."
Wani sanyi umma taji aranta cike da kunya tamiqe tabar wajen don bata masan me zata ceba, dariya dady yayi had'e da cewa.
"Ai nan kukafi gwanewa da auki, wato kunya bayan kun tafka shirme."
Ummie dake gefensu zaune tayita dariya har tana fad'in.
"To dama ai mu raunine damu, basai ka goranta mana ba, Wanda kuma duk ya tsaya biye mana shima irin wannan kunyar da mukeji zaiji kaga babu kafi balle na d'ara koda kuwa namijine."
"Ah to ai ku kuka sani, daku har wanda ya tsaya biye maku, Ina ai nima haka kika izani naje na biye maki da tsufana ka dinga tata mani rashin mutunci agida, kullum sai naji kunya idan aka tafka wata tsiyar, Amma yanzu alhamdulillah ALLAH yaqara bamu haqurin zama har zuwa lokacin da mai rabawa zata rabamu."
"Amin ya ALLAH, Amma saina nafad'awa hajia nafisa yanzu kagama yimata gugar zana, bayan abunda yawuce yariga daya wuce."
Ummi tafad'a tana dariyar dady.
A fannin hajiya nafeesa kuwa yau ji take tamkar tabar doron duniya akan abubuwan data aikata abaya, gaba d'aya ta gagara fidda farincikin da take ciki itama saboda jimamin aibata little data dingayi tana kira masa shege duk da kuwa tasan ta dad'e da roqonsu gafara, safa da marwa ta dingayi a tsakar falonta tana tunanin yanda yaau zata had'u da umma ta d'aga kai ta kalleta, yanda zata kalli Rashida data jefa da mummunar kalma tazina alokacin halattaccen mijinta ya bayyana agareta, yanda zata kalli Nuraddeen data kira da shega ayayin da yake agaban mahaifinsa, so take tayi hawaye amma sunqi zuwa, natsuwarta da zaune da tsaye duka sun gagareta saima wani zazzab'i da takejin na Shirin taso mata, bata san lokacin data fara sabbatu tana fad'in.
"Kaicona kaico ni kaina, wannan itace ake kira da ranar nadama, ranar xubewar kima da matsayi, ranar da mutum ke tsanar harshensa, ranar da dana sani ke dabaibaye qwaqwalwa tare da raunata qarfin gangar jiki, ALLAH kasani na tubarwa laifukana, ya ALLAH kayafemun kabani qarfin halin fuskantar kunyar abunda na aikata."
Haka tayita suruttai ita kad'ai tana d'ora hannu akai tare da zagayar falon, zuciyarta sai bugawa takeyi tana fargaba tare da hasaso lokacin da zatayi arangama da wud'annan fuskoki data aibata agaban wanda yawankesu daga wannan zargin.
Rashida kam bacci qaurace mata yayi adaren, babu abunda idanuwanta ke hakaito mata sai fuskar habibinta, babu zantukan da kunnuwanta ke sauraro mata idan ba nasa ba, musamman alokacin da take cewa. _Babban qalubale shine rashin rouhi a gangar jikina da kuma kad'aicin abokanan da zasu tayani ingantacciyar rayuwa idan ba kayan aikina ba_ ta tabbata cewa awannna gaba'ar saqone take isar mata domin itace wannan rouhin nasa da yake fad'ar babu a gangar jikinsa don ya jima ako yaushe yana fad'a mata cewa itace rouhin gangar jikinsa, idan babu ita atare dashi to tabbas bazai samu ingantacciyar rayuwa ba, ayau ta yarda da hakan kuma ta aminta da kalamansa, saqonsa ya iso kai tsaye azuciyarta saidai bata tunanin karb'arsa hannu biyu bayan ya shafe shekaru batare da yayi tunanin tunata koda na rana sau d'aya ne, haka ta kwana tana faman juye juye akan gado had'e da bitar duk wasu kalamai nasa har aka kira sallar asuba ta tashi tayi sallah tana mai d'oki da kuma dakon zuwansa gareta akowane lokaci.
••• ••• •••
Tun daga can gida baffa yasa aka d'auko abun karyawa aka kawowa su Dr nan gidansu baffa yana biye abaya don shima bai karyawar ba, nan d'akin Yaya hawwa aka kai kayan ga itama Inna Bilkisu ta shirya masu lafiyayyen abun kalaci takai can d'in duk suka taru waje d'aya suka karya ana fira cikin jin dad'i da farincikin sake had'uwarsu waje d'aya, gani sukayi baffa Ali ya miqe ya koma gefe yana goge hawaye.
Tashi baffa yayi yakoma wajensa ya zauna tare da d'ora hannunsa saman nasa yayi saurin jayewa tare da matsawa gefe yanaci gaba da sharar qwalla.
"Meye haka Aliyu? Me yafaru kake guduna Kuma?"
"Ba gudunka nakeba Yaya, gani nakeyi kamar banyi maku adalci ba idan Ina cakud'a cikinku duk da kuwa wannan cutar da take tare dani, idan girman karamci da kawaicinku ya hana ku qyamaceni bai kamata ni kuma son zuciya yasa naciga da cakud'a daku ba, domin shine ya kaini yabaro tun abaya."
"Haba Aliyu, har sau nawa kakeso kaci gaba da muzanta kanka agaban idanuwan mutane?, Meyasa kake son tilasta kanka akan saika gamsar damu ka canza kuma kayi nadama baayan mu tuni zukatanmmu sun amince kuma sun gamsu da hakan, don ALLAH kadena qasqantar da kanka haka acikin mutane ya isa kaji ko.?"
"A'a kabarni naci gaba dayin hakan don nunawa zuciyata datayita azani bisa hanyar daba gaskiya ba da nunamun cewa ni wani ne in nuna mata cewa ni ba kowa bane, banida wani girma ko d'aukakar da zataci gaba da kamba mani aduniya balle har tasake cin galaba akaina."
"Kayi hakan da dad'ewa baffa, Kuma insha ALLAH ALLAH ya yarda da tubanka, don haka kadena qasqanta kanka baya son haka domin shi da kansa yace ya karrama d'an Adam adoron duniya, kaga baici ace kuwa kana gardama hakan ba."
Baffa Usman yafad'a yana zaunawa kusa dashi yayinda shi kuma Dr Nuraddeen ya qura masa idanuwa yana karanto irin damuwar dake kwance a zuciyarsa tare da alwashin gusar masa dasu ko don yarama cutarwar da yayi masa da alkhairi.
Kamar dai jiya haka yauma gidan aka wuni mutane na shigowa ciki kuwa harda Abba dasu uncle h, inda little ya gabatar dasu ga mahaifinsa amatsayin iyayen matarsa kuma ya gabatar dashi a matsayin mahaifinsa, Abba kam yaji matuqar nauyi akansa sosai bisa abubuwan da suka faru amma haka ya daure ya bayyanawa Dr Nuraddeen komai abunda yafaru wanda daga baya yayi nadamar hakan batare da sanin cewa ashe yana gab da dawowa ba, Dr yaji Babu dad'i Kuma abun ya Sosa ransa yanda akankusa hanawa d'ansa aure saboda ana zargin cewa shi shegene bayada uba, Amma komai yariga daya wuce tunda gashi ya dawo antabbatar da cewa d'ansa d'an halak ne don haka bazai iya maido da hannun agogo baya ba, cikin mutuntawa yayi masu godiya tare da fatan alkhairi akan d'orewar zumuncinsu sannan suka tafi, ganin rana na somayi Dr Nuraddeen yaba little kudd'i yaje yayi masu bkin d'in jirgi don lallae lallae yau bazai sake kwana garin ba har sai yaje wajen habibty d'insa kamar yanda mahaifiyarsa ta umurcesa, yanzu kam gaba d'aya baya fahimtar komai kuma baya gane komai inba ganinsa yayi wajen habibty d'insa ba gashi tunda little yafita bai dawo ya barshi sai faman duba agogon hannunsa yakeyi, ashe shi saida yabiya wajen batool yaga tashinta da yaransa sannan yatafi wajen booking d'in ticket d'in jirgin, cikin sa'a ya samu akwai har sauran ticket uku na jirgin da zai tashi misalin qarfe biyu narana, nan take yayi duk abunda ya kamata sannan ya kama hanyarsa ta komawa bayan ya tsaya ya saiwa mahaifin nasa waya da layoya har guda biyu mabanbanta network.
Yana isa ya isko dandazon mutanen da suka kawowa mahaifin nasa ziyara ta b'angaren ma'aikatar lafiya, yana ganinsa ya taso batare daya damu da mutanen daya bari wajen ba. nan yayi masa bayanin jirgin da suka samu wanda zai tashi qarfe biyune na rana, cikin jin dad'i ya d'an bubbugi kafad'ar little yace ya maza yaje ya shirya yana zuwa shima da zaran ya sallami mutanen,
Bayan yayi sallama dasu yaje ya sanarwa da Yaya hawwa zai tafi tayita sanya masa albarka da addu'ar ALLAH yakaisa lafiya yasa ya dace su dawo tare da matarsa cikin qoshin lafiya, anan bayen dake shiyar Yaya hawwa yashiga ya watso ruwa agurguje ya shirya, dama ya sanar da su baffa don haka suka d'auki hanyar zuwa airport d'in auna masu yimasu addu'ar zuwa lafiya sudawo lafiya.
Kasancewar koda suka isa airport d'in akwai sauran lokaci yasa little ya zauna yakira battool ya sanar da ita don mantawa yayi da yaje d'azu bai fad'a mata ba, addu'a tayi masa tare da fad'a masa Abba yasa an d'auko motarsu da sukayi accident jiya har an gyara, Saida yace tayiwa Abba godiya kafin yakirasa sannan ya kashe wayar yakira dady da Dr nura ya sanar masu suna tafe shida mahaifinsa kuma jirgi zasu biyo.
Wayar mahaifiyarsa ya gwada kira bai samu ba don tun safe ya kirata lambar akashe, murmushi yayi tare da kad'a wayar a aljihu sannan yaciro ta abban nasa ya dinga saka masa lambobin da yasan zai iya buqatarsu ciki kuwa harda ta mahaifiyarsa da yayi saving da my