Showing 234001 words to 237000 words out of 260204 words

Chapter 79 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt

kai irinta samarin yanzu da rashin girmamawa, ya fahimci hakanne ganin tunda ya shigo motar baiga wani abun ya had'asa da iyalinsa koda kuwa magana ce balle sayesayen kide kiden da zakaga anayi a mota ankai volume qarshe anayi ana canza batare da andamu da wud'anda ke cikin motar ba, haka yanayin yanda yake magana dashi cikin girmamawa da martabawa shiyasa yaron yaqara burgeshi sosai aransa.

Murmushi yayi sannan yasa kai yanufi cikin hotel d'in bayan yaga fitarsu don har saida motar tasu ta b'ace masa da gani sannan yabar wajen.

Akan hanyarsu tazuwa gida batool ta kalli little tace.

"Wai kasan wani abu Abu sumayya?."

"A'a gimbiyata sai kin fad'a."

Ya bata amsa had'e da juyowa yana sakar Mata murmushi,

"Wlh muryar bawan ALLAHn nan yanda kasan taka, ni da farko ma da yayi magana saida natsorata bakaga sanda najuya baya Ina son naga fuskar saba?"

Mangareta yayi ga kai had'e da cewa.

"Yawwa ai kin tuna mani, wato don kinibibi mijin wata kike qoqarin kalla, to da izinin wa kikayi hakan?, Ai tun lokacin naso mangareki albarkacinsa kikaci don kar yaga rashin kunyata shiyasa na qyaleki."

Dariya ta dingayi sosai har tana kwantar da kanta saman kujerar kafin tace.

"Oh ni batoolun Abbana!, Ashe kace abun yayi maka zafi haka, to i hak'uri ranka ya dad'e Abu sumayya abban hasssana da hussaina, gimbiyarka natuba ka yafeta bazata sake ba, Amma maganar gaskiya muryarku na yanayi sosai."

"Ko?"

Yafad'a tare da danna hancin motarsa cikin gidansu da tuni mai gadi yana ganin isowarsu taso ya wangale masu gate d'in."

Saida ya kashe motar bayan yayi parking sannan ya juyo ya kalleta had'e da cewa.

"Kinsan yanda ikon ALLAH yake, qilan qasar muce guda, hakan zata iya kasancewa amma dai ni banji hakan ba, kawai dai naji kamar na tab'a jin muryar awani wajen ne"

Ya qarasa maganar yana dariya had'e da mintsilar mata kumatu.

Dariyar itama tayi kafin tace.

"Ahaf! Ai tara na tare da goma , wani wajen yafi muryarka da kakeji kullum."

"Bawani gimbiya kindai zama mayyata kamar yanda nake mayenki shiyasa kikejin muryar kowa na shige da tawa."

Yafice yana dariya don yasan yasan ya tsokalota tunda yafad'i hakan.

Ita dai bata tankasa ba itama tasa qafa ta fito bayan ya zagayo ya bud'e mata gambun.

Kusan kwana sukayi suna shiri tare da imagining yanda tafiyar tasu zata kasance gobe zukatansu cike da farinciki.

••• ••• •••
A can qasar malesia kuwa tuni gidan labaransu na redio da talevision suka d'auki harmar labaran komawar shahararren likitannan da akafi sani da Dr N.I Aliyu qasarsa, wanda hakan baqaramin jawo hankulan manema labaran qasar yayi ba, gashi gaba d'aya bayada lambar wayar da za'a iya samunsa hannunsa balle su tuntub'esa da kanun labaran don suji dalilinsa nayin hakan bayan yafurta cewa bayada alaqa da qasar ashekarun da suka gabata, hakan kuwa ba qaramin cece kuce yajawo ba ga mutanen qasar da kuma su kansu 'yan jarida, Wanda daga qarshe har saida suka dangana da shugaban asibitin daya baro da kuma shugabar makarantar daya yayi wacce itace tazame masa tamkar uwa kuma uba aqasar, duk da dogon jawabai da bayanonan da suka samu hakan bai hanasu cigaba da yayata labaranba da kuma tofa albarkacin bakinsu ba akan hakan, aganinsu hakan da yayi tamkar butulcine yayi wa qasar tasu.

Kan kace me itama qasar tasa ta nageria sun fara qoqarin mauar masu da raddi tare da son ganin lallai sai sun gana dashi ta kowace hanya kafin isowarsa, haka wani jami'in labarai yaci gaba da bin diddigi har saida yasamu sanin ko wane jirgi ya shigo daga nan yatuntub'i jami'an jirgin suka yimasa bayanin cewa, sanadiyar hazo da gajimare da suka yima sama qawanya yasa Basu samu damar sauke pasinjojin nasu a jahar kano ba suka saukesu a jahar borno, kuma sun bashi tabbacin yana cikin jahar tunda isowar dare sukayi, idan har zai bar jahar to sai zuwa wayewar safiyar gobe idan ALLAH yakai mana rai,

Haka wannan d'an jaridar ya bawa abokanan aikinsa duk wani rahoton daya samu kafin safiyar gobe saboda shi d'an jahar adamawa ne.

Wannan daren ya zamo wani irin dare dake cike da ban al'ajabi domin kuwa a b'angaren su batool farinciki bai barsu suka runtsa idanuwa ba haka ma Rashida kwana tayi tana salloli akan ALLAH ya qaddara wannan tafiyar tasu little ta zamo alkhairi saboda yanda ta koma jin jikinta ba daidai ba, Dr Nuraddeen ma haka, d'oki da fargabar yanda zai riski iyayensa gobe basu bari ya runtsa ba, ga b'angaren' 'ya jaridu da 'yan gidan redio da talevision da sauran manema labarai suma kwana sukayi suna Shire shiren yanda zasu tarbi isowar wannan shahararren likita da labarinsa ya karad'e ko ina. Kowane b'an gare matse yake kuma qagare yake safiya tawaye don cimma cikar burin zukatansu.

••• ••• •••
A b'angaren Abba kuwa Yana gama waya da little yafad'a zaune saman katafaren gadon dake cikin d'akin tare dasa hannayensa ya dafe kai,

Kallonsa su uncle h d'aya tsayar tun d'azu sukayi had'e da tambayarsa ko lafiya.

Cikin raunin murya yace.

"Batool ce, ta dage lallai sai tazo, Kuma bana buqatar wani abun ya sameta, don haka dole nabar garin nan gobe."

"Ka natsu da kayi hakan a ranka?" Uncle Hassan yafad'a tare da zaunawa kusa dashi, jinjina masu kai kai yayi uncle Hussain dake qoqarin zama kusa dashi a d'ayan gefen yace.

"Shikenan ka kwantar da hankalinka, in Sha ALLAH gobe damu dakai duka zamu tafi, Amma Kuma kasa aranka cewa idan ALLAH yana nufin wanzuwar wani abunne akansu koda basu zoba to tabbas zai faru atawani sanadin daban saboda bawa bai isa ya kaucewa qaddararsa ba, Wanda muminin kwarai yazama dole yayi Imani da ita ya ALLAH mai kyau ko marar kyau."

Saida sukaga yad'an rage damuwa sosai sannan suka bar wajen suma suna masu addu'ar ALLAH ya kauda fitinar zamowar mafarki gaskiya.

Ita kuwa hajia mama kwana tayi tana kuka tana addu'a da Abba ya sanar da ita yanda sukayi da batool, don ta tabbata yanda take da kafiya da tsattsauran ra'ayin irin nashi ALLAH kad'aine ya isa yahana zuwan nata gobe kamar yanda tafad'a don haka ta dage wajen roqon ALLAH daya sauqa masu duk wata jarabawa da zai yimasu yanda zasu iya canyeta, haka kuma tayiwa Abba tambihi sosai akan kuskuren da yayi nafad'ar mafarki marar kyau baiyi yanda annabi yace ayiba, sosai yasake shiga damu don ta fahimtar dashi cewa alqawarin ALLAH ne duk wanda ya sab'awa umurnin manzon ALLAH yabi son zuciyarsa to tabbas zaiga ba daidaiba, wanda hakan yasa tanace da addu'a tare da qasqantar da kai ga ubangiji akan idan zai jarabcesu to yayi masu wacce imaninsu ke iya d'auka don haka sai shima Abba yayi nadamar hakan daya aikata yaci gaba da roqon yafiyar ALLAH akan sab'awa karantarwar annabi da yayi cikin rashin sani da kuma neman saussauci acikin wud'annan al-amurran.

••• ••• •••
Tun da asubar fari batool ta tashi ko nauyin cikin jikinta bataji tayi dukkanin abunda ya kamata, sannan ta tadashi suka hau shirin tafiya, koda qarfe takwas da rabi tayi suna qifar gidan Dr sun rakkosu bakin mota, a tsarin tafiyar bada su hassana zasuyi ba duk da taso hakan aranta saboda Abba yaga jikokinsa Amma saboda kawaici da kara da kuma alkunya ta kasa magana, suna shigewa cikin motar da zimmar tafiya suka ga 'yan biyun sun rugo a gyare tsaf Rashida na biye dasu da akwatinsu, karb'a Dr yayi yana dariya had'e da cewa.

"Lalle kinyi dubara kuma kin kyauta, yanzu nake zancen araina nace to ita wannan 'yar tawa wayau zatayi masu ta gudu wajen abbanta bada suba bayan suma tagudar masu da nasu abban? Sai gashi Naga kin tasosu agaba, inaga maman little wannan kora da haline kike yimasu don kema kihuta da rigimarsu kwana biyu."

Saida tad'an dara sannan tace.

"Aikuwa kamar kasani uncle, suje can wajen sabon angon nasu muma muhuta da qiriniyarsu kwana biyu."

Duk akasa dariya wajen tare da yimasu ALLAH ya kiyaye, suna qoqarin tashi Dr yaga tayarsu ta baya tayi faci yace.

"Ashsha! Kai takwara ai tayar motar tayi faci."

Fitowa yayi yad'an dudduba had'e da shafa kansa yana fad'in.

"Ahaf, sauri ya haifi nawa, to malama uwar zumud'i sai kifito, Bari naje nakirawo mai faci asa mana iska had'e da juyawa.

Har ya kusa kai bakin qofa Dr yakirasa had'e da lalaba gaban aljihun rigarsa yaciro makullin mota sabo dashi ya miqa masa yana fad'in.

"Karki tsaya b'ata wannan lokaci, jeka kaciro waccan sabiwar motar da shekaranjiya ka kai aka yimata service, Ina komai dai daidai ko ina andubata ko."

"Eh Abba, ammafa cewa kayi sai shahida zata dawo za'a lonceta."

"Manta da wannan, Kai da zakaje wajen surukinka babbar gaisuwa ta musamman da wajen dangin mahaifinka ai kai yakamata ka lunche mana ita muga yaya lafiyarta ko kuwa matana."

Dr yaqarasa maganar yana kallon 'yan biyu da sukayi cirko cirko da alama sun matsu atafi yana dariya.

Godiya litte yayi masa sosai cike da farinciki sannan ya amshi makullin motar yanufi inda take, bayansa Dr yabi yariqa masa suka cire ledar dake jikinta sannan yashiga cikinta bakinsa d'auke da addu'a ya fiddo tare da sake fita ya kwaso kayansu a waccan motar yazuba sannan suka sake yimasu sallama suka shiga suka tafi su Dr da ita rashidar da Fatima da sauran yaransu nayi masu addu'ar ALLAH ya saukesu lafiya bayan ya tabbatar masa dasu tafi ahankali har su isa lafiya don SANNU SANNU bazata hana tafiya ba...tunda har sun tashi dawuri.

Suna kan hanya hajia nafeesa takira awaya don tun jiya sukayi sallama dasu tace mata gasu sun kama hanya a sakasu a addu'a, cike da jin dad'i tayita zuba masu addu'a tanaji tamkar tabisu taga irin farincikin da Abba zaiyi idan yaga yanda batool d'insa takoma fiye da yanda take son ta kasance akoda yaushe, tasan baqaramin dad'i zaiji ba musamman idan yaga 'yan kyawawan jikokinsa.

Suna gama waya takira hajia mama da Abba tayi masu albishir cewa Batool d'insu nakan hanya batare da tasan zullumin da suke ciki akan faruwar hakan ba.

Suna gama wayar hawaye suka ratatowa hajiya mama a fuska, cikin tawakkali tare da miqa dukkanin lamurranta ga ALLAH tace.

"Ubangiji ALLAH ya kawosu lafiya, dama nasan kafiyar batool bazata bari ta haqura ba, musamman yanda kullum take fata da d'okin ganin wannan ranar da abbanta zai jaye tsattsaurar katangar daya shata a tsakaninsu."

Kallon Abba tayi da fitowarsa kenan wanka yana goge jiki yaji abunda hajia nafeesa tafad'a yayi mutuwar tsaye awajen.

"Kayi haquri ka amshi duk abunda ALLAH zai zo mana dashi duk da ni aqasan zuciyata banyi Imani da mafarkinka zai tabbata akansu ba, Abu d'aya nayi imani dashi shine, ALLAH yakan sassauta jarabawar bayin da suka roqesa kuma ya sauqaqa qaddarar daya tsaro zata faru akansu, don haka kawai ku haqura da wannan tafiya kuma muyi fatan ALLAH yakawosu lafiya."

Kasa cewa komai yayi yayi qarfin hali yagyara yaje ya sanar da 'yan uwansa da tuni suma sun shiryo da zimmar tafiyar, nan take duk sai sukaji jikinsu yayi sanyi Amma sai sukayi qoqarin b'oye hakan don kar damuwarsa ta lunku.

Arwala hajia mama tayi taje taci gaba da ganawa da ubngijinta akan ALLAH ya kawo masu su lafiya.

••• ••• •••
Dr Nuraddeen kuwa yana tashi da asuba bayan ya gama sallah tare da azkar yasamu manajan hotal din yace yana buqtar a bincika masa idan akwai jirgin da zai tashi zuwa kano yau ayi masa booking..

Nan take da yake sun gashi da maiqonsa ba'afi mintuna goma ba suka binciko masa amma jirgin sai zuwa Sha biyu da rabi na rana zai tashi, baiso hakan ba, gashi bazai iya doguwar tafiya ba saboda yanayin gajiyar dake tare dashi da wani iri da yake jin kansa saboda fargabar data addabesa kuma bazai iya bin motar kasuwa ba yasa dole ya haqura yace ayi masa booking dinsa hakanan.

Tuni ma'aikatan airport d'in suka sanar da 'yan jarida da 'yan redio cewa shahararren likitan da ska buqaci subasu bayani akansa jirginsa zai tashi nan da awanni hud'u da rabi kamar yanda yayi booking da safennan.

Kan kace me tuni manema labaran suka Isa filin jirgin bayan sun sanar da abokanan aikinsu dake kano cewa su zamo cikin shiri don wanda suke neman labaransa zai iso nan da awanni biyar da rabi masu zuwa.

Lokaci na cika ya shirya cikin suit d'insa farare sai jar riga ta ciki da farin necktie yasa takalma irin cover shoe's din nan suma farare sannan ya d'auki jikkarsa yaje ya biya charges din masu hotel d'in tare da yimasu alkhairi Mai tsoka suna ta jin dad'i had'e da yimasa godiya.

Tsabar farinciki manajan da kansa ya d'aukesa cikin motarsa ya kaisa airport,

Yanda yaga taron manema labarai ya tabbatar masa da cewa sun samu labarin dawowarsa kenan, cikin halin ko inkula yafito ya fara takawa zuwa bakin jirgin don tuni an soma kiran pasinjas don har sun soma makara, kasancewar tuni fuskarsa ta bayyana ga labaran qasar malesia yasa suna ganin fitowarsa sukayo ruuu kansa, sai dai yaga hasken kyamarori na bugar masa buska da wasu dogayen abun magana da aka karo masa,

Fuskarsa ba yabo ba fallasa ya tsaya yana fuskantarsu daidai yana jiran tambayoyin da suka shirya yimasa, Wanda kai tsaye labaran suke tafiya ga kafafen yad'a labarai.

Tunda suka fara tambayoyinsu bai amsa masu ko d'aya ba har sai da yaji sun saurara.

Daidai lokacin Rashida ta shigo cikin falon su Dr da fatima na zaune suna kallon labaran da tun safe suke jin ana yayatawar dawowar wani shahararren likita, amma ko kad'an basu kawo hakan aransu ba cewa wai Dr Nuraddeen ne mijin Rashida, Saida sukaji cikin harshensa na turanci yafara amsa masu tambaya d'aya wacce ita kad'ai yaji zai amsa, lokacin Rashida na bayansu tayi mutuwar tsaye ganin fuskar da bazata tab'a iya mancewa da ita ba.

_"Nadawo qasatane awannan lokacin saboda duhun da ALLAH ya yayemun dake kaina har nakasa banbance koni waye, Wanda shi kad'aine yasan dalilinsa na jarabtata da hakan, batun shekarun dana kwashe awaccan qasar batare dana waiwayo qasata ba shikuma rubutacciyar qaddarar rayuwata ce dako ina so ko bana so saita tabbata akaina, zancen iyayena, ahalina da iyalina Kuma..."_ kafin ya qarasa kawai sai akaga ya fashe da kuka tare da haye matattakalar da sauri.

Ita kuwa Rashida sai jin kukanta kawai sukayi ta duqe wajen, cikin wata irin murya mai cike da ban tausayi tana fad'ar.

"Ko kad'an bayada gaskiya, bazai iya wanke kansa ba, wannan kukan duka na kunya ne da nadamar abunda ya aikatawa qasarsa, iyayensa, matarsa da kuma d'ansa har taya zai iya bada wannan amsar bayan yasan tuni yabada ita ga idanuwan duniya."

_afuwan idan bakuji dad'in rashin had'uwar little da mahaifinsa ba, ko kad'an yau idan suka had'u a titi abun bazai bada ma'ana ba balle ya qayatar, SANNU SANNU dai bazata hana mu Isa wajen ba gobe in sha ALLAH, pls kuyi haquri kuma kusani cikin addu'o'in ku saboda zazzab'i na nema yayi Mani qawanya👏thanks all_




*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

_Gaisuwa tare da fatan alkhairi agareki ROUHINAH, *FATIMA TAMBARY (BATOOL)* Aminci ya tabbata agareki tare da dukkanin alkhairan Allah bisa soyayya da qaunar da kike nunamun, fatana ubangiji ALLAH ya baki miji nagari da zai kula dake har qarshen rayuwarki kuma yakare mana ke aduk in da kike, soyayyarki ga wannan littafi na matuqar faranta mani, ubangiji ALLAH yabar tare har a aljannah fiddausi👏_

Page___103💎

Tsaye sukayi had'e da qurawa motar idanuwa suna kallo, yayinda d'an jaridar naganin motar ya juya da gudu yanufi wajen riqe da makirfon d'insa hannu.

Kafin kace me tuni manema labaran sun dandazo a bakin motar sai hasken kemarori kawai kake gani nafita tako ina tun kafin yafito, so yake yafito amma duk sun tare wajen babu ta yanda za'ayi ya bud'e gambun motar balle yasamu fitowa, hakan yasa yayi zaunensa aci yana kallon ikon ALLAH, wata motar jami'an tsaro ce naga ta shigo aguje wanda mataimakin gwamnan jahane ya sake turosu saboda sanin taron da 'yan jaridu sukayiwa garin don kar wata matsala tafaru, tun kafin motar ta tsaya wasunsu suka dingi dirqowa daga samanta suna kukkutsawa cikin mutane da tutturesu gefe har suka iso bakin motar suna faman mazurai da idanuwa.

Saida suka tabbatar an saki hanyar da zai iya wucewa sannan wani yasa hannu ya bud'e masa gambun motar, a hankali ya azo qafarsa waje kafin ya ida fitowa da gangar jikinsa gaba d'aya yana qarewa qofar gidansu kallo, tana nan ayanda yasanta babu wani sauyi atattare da ita balle jikin gidan, wata irin damuwa yaji tarufesa yana mai tuhumar kansa akan cewa duk laifinsa ne daya jawo wannan rashin samuwar sauyin da aka samu ako Ina cikin wannan shekarun atattare da iyayensa, ji yayi wasu zafafan hawaye sun zubo masa xubo masa a fuska ga 'yan jarida kuwa sai famana aikinsu sukeyi na yimasa hotuna, cikin sanyin jiki ya fara takawa zuwa wajen yayin da su kuma su baffa dake kallon ikon ALLAH daya ishesu tun d'azu ganin yanda hankalin kowa yakoma akan wannan motar ana jiran fitowar ko suwaye aciki amma shiru yaqi fitowa suka fara qoqarin juyawarsu da nufin shigewa gida, suna juyawa suka sake juyowa da sauri saboda tozalin da idanuwansu suka yimasu da fuskar mai fitowa daga cikin motar da bazasu tab'a manta tab'a, cikin wani irin matsanancin mamaki baffa ya shiga nunasa da hannu, murza idanuwasa ya sakeyi yana son gasgata abunda suka gane masa, tabbas ba shakka wannan Nuraddeen d'insa ne, cikin karkarwar murya bakinsa na rawa yafara matsawa zuwa garesa yana cigaba da nunasa yana fad'in,

"Sh..shi..shinefa Usman, d'a..d'ana ne nu..ra!,"

"Tabbas shine ne yadawo Yaya, nuran mune bako shakkah." baffa Usman yafad'a yana hawaye, baffa Ali kuwa cikin d'ingishin katakon da yake takawa dashi yanufi wajen Dr Nuraddeen dake nufowa wajensu idanuwansa na tsiyayar da hawaye saboda yanda idanuwansa sukayi masa tozali da iyayensa awani yanayin da ba hakan yaso ba, yanda 'yan jaridun suka yimasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login