Showing 186001 words to 189000 words out of 260204 words
Chapter 63 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt
ince sunzo Kai tsaye ga kunnuwan mahaifin yarinyarnan cewa yaronku bayada asali wanda hakan yasa mahaifinta har yayi mata tsakani dashi bayan yasa anyi masa bincike acan garin antabbatar masa da cewa yaron nan bayada uba, kuyi haquri kada kuga nayi maku cin fuska, muna so musan sahihancin maganar ne don shi yayan namu yakafe akan bazata auresa ba sai gashi kuma yarinyar ta sanar damu zancen cewa zakuzo nema masa aurenta, hakan yasa mukayi tunanin zaunawa musaurareku don jin gaskiyar zancen."
Wani irin dimmmmm...baffa yajiya aransa duniyar ta shiga jujjuya masa saboda kalmar da yaji cewa wai jikan nasa shegene bayada uba, badon ALLAH yasa yana zaune bane to da Babu abunda zai hanasa fad'uwa adaidai wannan lokacin, wasu zafafan hawayene suka zubo masa a fuska da sauri yasa hannu yagoge yanajin wani qunci tare da takaicin d'ansa aransa.
Dady kuwa gabansa ne yafad'i jin kalmar da duk duniya mutum d'ayane yaji nayiwa little ita wato matarsa hajia nafeesa wacce baya tantama akan komeye yafaru itace ta assasashi.
Ganin duka yanayin da suka shiga yasa uncle Hussain jin badad'i aransa Amma ya za'ayi dolene suyi haka don susan yanda zasu kamo bakin zaren, cikin tausasa kalamansa yace.
"Ina nemawa d'an uwana dani kaina yafiyarku idan maganganunsa sun tab'a maku zuciya, har ga ALLAH ba muna nufin zamu yimaku walaqnci bane don kunzo neman alfarma wajenmu, a'a kuyiwa maganar kyakkyawar fahimta akan muna so kai tsaye mu binciki sanin kowaye yaronku tawajenku saboda munyarda daku, kuma Ina zaton ko a misulunce hakan ba laifi bane, idan bakwa buqatar hakan kuma to muna baku haquri tare da cewa kubamu d'an lokaci kafin muje muyi bince akai."
Da sauri baba balarabe yace.
"A'a babu buqatar hakan, asalima godiya yakamata muyi maku dakai tsaye kuka fuskancemu da wannan magana batare da kunje waje wurin neman sanin gaskiyarta ba, ni sunana malan balarabe qane ga mahaifin uwar yaron, Ina zaunene awani qauye da ake kira yarimawa, wannan kuma ya nuna baffa sunansa malan Idris Aliyu wato mahaifin baban yaron tare dashi kuma akwai qanensa malan Usman Aliyu, su kuma suna zaunene a qauyen bebeji, shi ya haifi uban wannan yaro da ake shegantawa ni kuma amatsayina na qanen mahaifin mahaifiyar yaron ni nabada aurenta a hannun wannan qanen mahaifin babansa bisa sadaki naira dubu hamsin, zaku iya zuwa atsakankanin wud'an nan qauyukka guda biyu kuyi bincike akan munda maganar alaqarmu don tabbatar da hakan."
A yanayin da yake yimasu bayani duk daqiqancin mutum dole yafahimci cewa yana fad'in gaskiyar zancene daga qarqashin zuciyarsa.
A hankali baffa ya d'ago kai tare da fara basu labarin dalilin da yasa aka jingina jikan nasa da cewa shegene, tun daga farko har zuwa qarshe batare daya b'oye masu gaskiya ko d'aya ba har yana zubar da qwallah, dady me ya d'ora masu cigaban labarin daga qarshe yakira Dr. yace yazo maza maza yana son ganinsa tare da bshi address d'in inda zai iskosu, ba'a jima ba saiga Dr ya iso dady yace ya sanar dasu kowaye little da mahaifiyarsa, kallonsu yayi d'aya bayan d'aya yace
"Meke faruwa dady?, Bazasu bashi auren tabane har sai an bayyana masu abunda yafaru akan mahaifiyarsa?, Ganinku bai isa ya gamsar dasu ko waye Nuraddeen d'inmu ba?, Idan ko hakane inaga babu buqatar hakan saboda babu yaddar da zata jawo auratayya a tsakani."
"Ya isa, kayi abunda nace maka." Dady yafad'a in a serious tone, ganin babu wasa a fuskarsa yasa yafara labarta masu halin daya tsinci mahaifiyar little har zuwa lokacin data had'u da iyayenta agidan mahaifinsa, anan dady yafad'a masu yanda akayi har yasan mahaifin Rashida wato kakan little, lamba da address d'in abokinsa da marigayi ke karb'ar takalmi awajensa Wanda nanne yahad'u da baba yabasu yace suje wajensa suqara yin bincike akai.
Gaba d'aya duk inda ilahirin jikin uncle Hassan da Hussain yake saida yayi sanyi, sosai kunya da dana sanin tambayoyi da kalaman da sukayi masu tarufesa, sun matuqar tausayawa rayuwar baffa tare da jinjinawa qarfin imaninsa haka sun girmamawa karamci irin na surukin nasu wato dady da d'ansa, da za'a samu irin wud'annan mutanen aduniya to tabbas za'a zauna lafiya cikin wadatuwa da ni'imar ALLAH.
Muryar baffa Usman suka jiyo yana fad'in.
"Little dake son yarinyarku ba shege bane kamar yanda kuka jiyo daga bakin qananun mutane dake yiwa alamari hawan qahura, su zauna akai suyi sharhin abunda basuda masaniya akai, mune iyayen babansa kuma da izininmu yaje karatu waje, qaddarawar ALLAH da kuma jarabtawa da wanzuwar alqalamin qaddara akan yaronsa tahanasa dawowa qasarsa zaku iya zuwa can ma'aikatar ilimi a b'angaren qananan malamai dake da rauni data taimaka musu ku bincika don kutabbatar da hakan domin ita taturasu qasar, bamu fidda rai da dawowar mahaifinsa ba a kowane lokace kmar yanda bazamu dena cigaba da rayuwarmu ba har sai lokacin da ALLAH ya dakatar mana da ita, Kuma in Sha ALLAH kusa ko nesa zai dawo garemu don tabbatarwa da duniya cewa d'ansa ba shege bane da yardar ALLAH."
Cikin sanyinyin murya uncle Hussain yace.
"Kuyi haquri, kuyi haquri, shikad'ai zamuce, damu bawai mu muka sheganta yaronku bane, kawai munfad'i abunda mukajine daga bakin wasu, amma yanzu mun gamsu da bayaninku d'ari bisa d'ari, dama haka ubangiji yace,
" _yaa ayyuhallazina amanu injaa akum fasiqun binaba'in fatabayyanu antusibu qauman bijahalatin fatusbihu ala maa fa'altum nadimuun_" ma'ana
" _yaku wud'anda kukayi imani!, Idan fasik'i yazo maku da wani babban labari, to, kunemi bayani, domin kada kucuci wasu mutane acikin jahilci, saboda haka ku wayi gari akan abin da kuka aikata kuna masu nadama_,
Shiyasa dashi yayan namu yayi nasa binciken mukaga yadace mu tuntub'eku da maganar kamar yanda ALLAH ya umurta don kaucewa aikata abunda zamuzo muyi nadama akai kuma alhamdulillah bamu d'auki wani matakiba koyin abunda zaisa muyi nadamar abunda muka aikata, don haka a matsayinmu na iyayen batool mun ba Nuraddeen dama yaci gaba da nemanta har zuwa lokacin da zamu sake waiwayarku akan batun aurensu,"
Cike da farinciki baffa ya d'aga hannu sama yayiwa ALLAH godiya sannan suka had'a baki shida dady dake murmushi sukace.
"Bakomai mungode, mungode sosai ALLAH yatabbatar da alkhairi."
Nan suka shiga musabahar hannaye kowanensu fuskarsa na nuna jin dad'in yanda abun yakasance, suna qoqarin tafiya aka kira sallar magrib, don haka uncle Hassan yaroqesu akan subari sai sunyi sallah sunci abinci sannan sutafi, haka kuwa akayi anan saman dardumar baba balarabe ya jasu limanci sukayi sallah sannan sukaci abincin, cikin qanqanen lokaci suka saba da juna har sukayi musayar lambobi sannan suka wuce cikin yaba nagartar juna da fahimta.
Suna wucewa Abba na isowa wajen kamar zai tashi sama, kallo d'aya sukayi masa dariya ta soma kuccikke masu da sauri suka gintse,
"Nagode da maidani d'an iska da kukayi a matsayina na yayanku, wato ni Ina can zaune ina jiran isowarsu ashe ku har kunyi mani yanda kuke so sai dai cikin anguwa atareni ana tambayar halama yau baqi nayi?, Yau kun nuna mani cewa ba bakin komai nake ba agareku kuma ban isa gareku ba." Sannan yajuya yanufi cikin gida, ayanda yayi maganar yasasu jin cewa kamar basu kyauta masa ba don haka suka bi bayansa suna bashi haquri,
Kusan sati ya d'auka yana fushinda kowa agidan, hatta abincin gidan bayaci, haka kuma baya wuni agida bacci kad'ai ke dawo dashi gidan shima safiya nawayewa zai tafiyarsa, sun matuqar damuwa da hakan ganin yanda gaba d'aya gidan yakoma ba dad'i suka dinga binsa suna bashi haquri, saida suka had'a gaba d'aya gidan har matansu da yaransu sukayita bashi haquri sannan suka samu daqyar ya hanqura saidai yatabbatar masu cewa ya haqura kad'aine bisa laifin da suka yimasa amma akan zancen auren batool da wannan yaron har yanzu yana nan kan bakansa.
Qoqarin fahimtar dashi da yimasa bayani sukayi amma sai yaqara birkice masu akan wai shi be yadda iyayensa bane saboda anfad'a masa cewa had'in bakine akayi da mijin hajia nafeesa aka d'auko hayar mutanen da sukazo a matsayin iyayensa.
"Ya ALLAH! Yaya wa Kuma ya sanar dakai haka?, wlh qaryane yaya, mahaifinsa na qasar waje sun riqesa daya gama karatu, don ALLAH Yaya ka tausayawa yaran nan tunda suna son junansu"
Uncle Hassan daya tsani tashin hankali yafad'i hakan cike da damuwa, shi dai hussain tsoron ALLAH ma yahanasa cewa uffan sai kallon yanda yayan nasa ke kumfar baki yakeyi....
*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*ππ
[11/14, 22:52] Billy S Fari: πΆββοΈπΆπ»ββοΈ *SANNU SANNU*πΆπ»ββοΈπΆββοΈ
π _Bata hana zuwa..._π
_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπ*
_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*π
_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*π
*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*π
*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*β€οΈ
_Gaisuwa da fatan alkhairi agareki Auntynah *AUNTY RASHIDA GARBA π* sincerely i rilly dont know how to start thanking you for all what you did to me, you have encouraged me so much in my difficult time when i lost hope that i could ever do something like this, you were the one to push me on things, i am really grateful that i have such a wonderful sister like you in my life, and i just want to express my gratitude and my thanks to you. You are truly wonderful sister so thank you for the support, like, luv and everything to me..haqiqa karamcinki agareni mai girmane da bazan tab'a iya mantawa dake ba, i pray almighty ALLAH to give you a wanderful charming husband dt will luv you, care with you, support you and Charis you for ever in life,π *LSM AUNTY RASHIDA*_
Page___86π
Komawa yayi akan kujerar kusa da ita ya zauna ahankali yace.
"Gimbiya tah, meya jimaki a goshi?" Yana nuna wajen da yatsa inda yaga filista da hajia mama tasa mata jiya inda goshinta ya fashe.
'Dan shafa wajen tayi had'e dayin murmushi sannan tace.
"Abu sumayya ya kake?"
"A yanzu lafiya klw nake tunda gani gaki."
"Kaga yanda rayuwa ta sauya mana ko, meyasa hakan take faruwa damu, musamman ni da zuciyata gaba d'aya yakasa hango mun kowa sai kai, gashi sai wahala rayuwa ke bamu, mahaifina na matuqar sona, ya kula dani sosai, yabani farinciki fiye da tsammaninka, saidai yakasa karanto zuciyata yafahimci irin tsantsar qaunar da nake yimaka, d'ago kanta tayi tana kallonsa idanuwanta sun cika da hawaye tace.
" _Wish that i spend some time with you only the time where there would be two of us looking at the sky and gazing at the stars, wish that we would just run away from here and run away so far, i was thinking about this the whole day and i just want to say that my love for you is so true, no matter what the hardest time it's i will be thinking of you, when i think about you, my mind goes numb, i am not me, i become so dumb, because our love was so strong, It was to me you belong, then why all this happened, I miss you so much Abu sumayya_"
Kallon cikin kwayar idanuwanta ya dingayi yana karanto tabbacin gaskiyar duk wata kalma da take fad'a, yarasa wane irin so ne takeyi masa haka, yarasa dalilin da yasa ta qaunace haka, tabbas shima ya cancanci yabata dukkanin irin wannan soyayyar da take nuna masa koda hakan na nufin zai rasa farincikinsa da natsuwarsa nahar abada, wani sassanyan murmushi ya sakar mata lokacin data kai qarshen kalamanta had'e da cewa.
"Karki damu gimbiyata, a halin yanzu ina rayuwane wa sonki da qaunarki, nayi maki alqawarin zan iya bada rayuwata domin ceto soyayyarmu, ba ina nufin zanmutu bane akan soyayyarmu ba, Ina nufin na shirya tsaf akan zan fuskanci duk wata matsala ko qalubale don naga na killaceki a inda yakamata, zan rayu don in cika maki duk wasu burikanki da mafarkanki akaina, zan biya soyayyar da kika nuna mani da zallar halacci da kuma karamci don haka kidena damar da kanki, tun asali qaunace ALLAH yasaka tsakanin ni da kuma ke, so ya biyo baya ne kawai, kiyarda dani zan baki duk wata kulawa, zan maye maki farinciki da wannan quncin da kike ciki, zan share maki wud'annan zafafan hawayen na maye maki gurbinsu da sanyayyun hawayen farinciki, Ina so kisa aranki gimbiyata, Abu sumayyanki na sonki kuma yana qaunarki har zuwa fitar lumfashinsa naqarshe,"
Sun jima suna fad'awa junansu kalamai masu dad'i da kuma sanyaya zuciya da suka sake basu qwarin guiwar cewa komai rintsi komai wuya zasu rayune kad'ai idan suna tare a qarqashin inuwa d'aya, ganin lokaci na dad'a ja gashi Rashida tace dole yau yamaidata gida yasa yamiqe yaje kitchen ya d'ibo abinci ya zauna agabanta yana ci.
Cin abincin yakeyi yana kallonta tana yimasa dariya har ya canyesa tas batare daya ankara ba sannan yamaida plate d'in kitchen yadawo inda take yace.
"Gimbiya bari naje na watso ruwa mutafi kafin gwaggo tafito tasameni."
"Shikenan ka kula mani da kanka."
Bayan ya gyara cikin wata farar shaddarsa giznah da tamatuqar yimasa kyau yanufo falon bakinsa d'auke da sallama, tsabar kyawon da yayi batool batasan lokacin da ta sakar masa murmushi tare da cewa, "kamatuqar yin kyau Abu sumayya."
"Nagode oum sumayya." Yafad'a shima yana mayar mata da murmushi, kusan atare Rashida da Fatima suka fito daga cikin d'akunansu Fatima nariqe da makullin motar dasu little zasu tafi da ita tace.
"Har anfito little?."
"Eh mama."
"Ungo to ga makullin motar ubangiji ALLAH ya tsare hanya, don ALLAH akula da titi da kyau kaji?" tamiqa masa tana kallon batool da har lokacin kezaune kanta na aqasa, jitake kamar ta fusa ihu domin gaba d'aya bata buqatar komawa gida saboda abunda zata tarar.
Murmushi tayi had'e da cewa.
"Takwarata tashi kuje lokaci na tafiya kuma don ALLAH kihi haquri kibarwa ALLAH dukkanin lamurransa, kada kikoma yunqurin yin jayayya da mahaifanki domin hakan kuskurene kinji ko.?"
"In Sha ALLAH." Batool tafad'a muryarta na kakkarwa alamun tana so tayi kuka.
Dafata Rashida tayi had'e da cewa.
"Ashsha batool, kukan zaki komawa bayan nafad'a maki cewa kuyi hak'uri, bawa baya iya tab'a canza qaddararsa aduk inda yake don haka kuka bayada wani amfani ga abunda zartar maka dashi za'ayi bakai zaka zartar dashi ba, ungo wannan littafin hisnul Muslim ne, kintab'a amfani dashi.?"
"Eh dashi mamana tayi koyamun addu'o'in safiya da marece.,"
"Masha ALLAH, kiduba cikinsa akwai babin addu'o'in hammu wal hazan, kije ki laqancesu in Sha ALLAH zaki samu sassaucin quncin zuciya dana baqinciki da damuwa kinji ko."
Hannu biyu tasa takarb'a hawaye na zubo mata, Rashida tace.
"Au bazaki dena kukanba." Cikin sake d'aga sautin kukanta tace
"Ina matuqar jin tsorone gwaggo."
Shiru Rashida tayi kafin tace "shikenan, share hawayen naki kibani lambar shi mahaifin naki."
Fad'a mata tayi ta copy digit d'in awayarta sannan tace,
"Maza jiki yana jiranku, Allah yayi maki albarka kuma ya kaiku lafiya."
Amin batool tafad'a sannan tafice tana sharar qwalla, wani gauron nisha Fatima tayi had'e da cewa Rashida.
"Yarinyar nan tabani tausayi, wlh tana matuqar son little sosai, ALLAH yakawo mata d'auki don girman qur'ani,
"Amin." Rashida tafad'a sannan sukabi bayanta, Saida sukaga tashinsu sannan suka dawo cikin gida bayan Rashida ta tabbatarwa da little cewa yakula da batool sosai kuma yaje ahankali.
Kusan awanni biyar suka shafe akan hanya kafin su iso gida, tafiya ce sukayi mai cike da nishad'i da kuma jin dad'i wacce gaba d'aya ta mantar dasu halin da suke ciki saboda yanda suka d'ebawa juna kewa sosai, atarihin rayuwarsu wannan rana itace da bazasu tab'a mantawa da itaba soboda lokacin da suka samu wajen qara bayyanawa juna sirrin dake zuciyarsu.
Rashida kuwa saida ta kwatanta sun kusa isa sannan takira mahaifin batool, lokacin yana kwance gaba d'aya duniya tayi masa zafi saboda neman batool da aka shigayi tun safe ba'a ganta ba, Wanda hakan yasa 'yan uwansa suka fito masa da b'acin ransu qarara akan cewa duk abunda yasamu batool laifinsa ne kuma ALLAH zai kamashi dashi, a matsayinsa na mahaifi bashi kad'ai ALLAH yad'orawa haqqin 'ya'yansa ba, hatta qannensa, yannensa da mahaifiyarta da qannen mahaifiyarta da qannenta duk sunada haqqi akanta don haka sun gaji da zuba masa idanuwa yana neman cilla 'yarsu cikin halaka, ada sunyi tunanin barmasa 'yarsa kamar yanda yake iqirarin cewa 'yarsa ce, Amma ayanzu zasu had'a qarfi da qarfe suyi mata abunda take so, zasu bata zab'in ranta matuqar shine kwanciyar hankalinta koda hakan na nufin zai yakicesu daga jikinsa, sun shirya tsaf wajen nuna masa cewa suma 'yarsu ce kuma zasu bata gatar daya kasa bata ayanzu,
Maganganu masu zafi suka yab'a masa kafin su sake tabbatar masa da cewa zasu je su nemo 'yarsu da kansu amma ya tabbata yazare hannunsa acikin lamurranta don su suna buqatarta idan shi baya buqatarta, baban abunda yafi b'ata masa rai shine a gabansa suka kira wanda yayiwa alqawarin aurawa ita suka sheda masa cewa yayi haquri yazo yakarb'i kayansa, dayayi yunqurin magantawa gaba d'aya suka had'a masa baki wajen cewa matuqar yasake dakatar dasu akaro nabiyu acikin sha'anin 'yarsa to bazasu sake amsa sunan cewa su qannensa bane, Kuma zasu barmasa gidan suda iyalinsu in yaso yayi yanda yake so, sannan suka fice suka barsa cike da damuwar matakin da 'yan uwan nasa suka d'auka,
Jin da yayi wayarsa naqara yasashi tashi zaune had'e da miqa hannu ya d'auko wayar dake kan kujera, ganin sabuwar lambar da yayi yasa ya maida wayar ya ajiye tare da komawarsa ya kwanta fuskarsa na kallon sama,
Sake kira Rashida tayi akaro na biyu amma har ta tsinke bai d'aga ba sai akaro na uku taji ya d'aga.
Sallama tayi masa a mutunce cikin girmamawa ya amsa sannan tace.
"Sunana barrister Rashida bashar maitakalma, ni haifaffiyar cikin garin kano ce awani qauye da ake kira yarimawa amma yanzu ina zaunene agarin borno ni da mahaifiyata da kuma mahifina da ALLAH yayiwa rasuwa duk anan borno d'in.
Wata zabura Abba yayi daga kwancen da yake had'e da miqewa tsaye yana bin wayar da wani irin kallon tsana kai kace ita d'ince Rashida, jin da yayi taci gaba da magana had'e da cewa "ni..." Yasa yayi saurin dakatar da ita cikin b'acin rai tahanyar cewa.
"Kece uwar wannan yaron da bayada uba, yaron da bayada asali, yaron da duniya tasan rauninsa da rashin nagartarsa, yaron da ba'ada tabbaci akan koshi waye?, Yaron daya nacewa