Showing 9001 words to 12000 words out of 260204 words
Chapter 4 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt
ya isko sajida takawo masa abinci da ruwa don gaba d'aya yau ko lunch besamu yayi ba saboda tashin hankali tana jiransa, qarasaw yayi tare da zaunawa k'asan kujera ya mik'e k'afafuwansa sannan yace,
"Sannu nabarki kina jirana ko, kinsan halin 'yar uwar taki..."
"Ba komai." tafad'a batare da tabari ya iyar ba ta tsiyaya masa ruwa masu sanyi a cup ta miqa masa, karb'a yayi ya kurb'a ruwan sannan ya ajiye agefe, k'ok'arin rik'e hannunta yayi lokacin da takai hannuwanta saman kular abincin yace,
"Kibarshi wifey, bazan iya ciba."
"Subhanallahi! Kayi hak'uri kaci kad'an kada yunwa ta kamaka"
"Bana cikin yanayin da abinci zai iya shiga cikina sajida..." Nan ya sanar da ita abunda kefaruwa da kuma rasuwar Abu sumayya.
Hannu biyu biyu tad'ora abaki tana qoqarin danne sautin kukan daya zo mata saboda ba b.kamal kad'ai ba hatta su da suke matansa sunsan da karamci da kuma kyautatawa irin ta abu sumayya, mutumne Mai mutunci da kuma tausayi da sanin haqqin musulmi d'an uwansa, rungumota yayi yana rarrashinta tare da cewa,
"Nayi rashin aminin qwarai daga cikin aminaina, yanzu babu abunda yarage awajena tsakanina dashi kamar inbisa da addu'a, haka kuma, domin shine zai tabbatar da soyayyarmu agaresa bisa kyautatawarsa agaremu." Addu'a tayi masa sosai tana kuka kafin yatayar da ita suwuce d'aki, har zasu shiga yaja hannunta suka shiga d'ayan d'akin da yaransu ke ciki ya kunna fitila yaga duk suna lafiya sannan ya sake gyara masu kwanciyarsu suka yimasu addu'a sannan suka wuce d'akinsu, kamar yanda yayiwa meenatu haka yayiwa sajida itama sannan yadawo falo ya zauna tare da rafka tagumi yana tunano hirarsu taqarshe kafin sutafi da kalar dariyar shaqiyancin da yatayi masa akan yanda yaga yana nan nan dasu meenatu saboda kada ran kowacensu ya b'aci, maganarsa zancensa na qarshe shine.
_ni dai Gimbiya ta isheni anan duniya babuni babu yimata kishiya balle inyi tunanin raba mata soyayyata da kuma kalaman bakina da zuciyata ita da wata, nayarda da ita da kuma nagartacciyar soyayyarta agareni, Ina fatar kuma ALLAH ya yarda da ita kuma ya sota, nine noora amma azahiri batool itace wannan sunan hasken da ake kirana dashi, wlh badon ALLAH yatsaro a aljannah dolene za'a bamu wasu matanba da ni Abu sumayya nace ALLAH yabarni da gimbiyata ta isheni, ALLAH kasa gaba d'aya matan hurul ayni da za'a bani kamanninsu da komai nasu irin na gimbiyata ne._
Girgiza kai yayi had'e da cewa, "ALLAHU akabar, duniya kennan, ya ALLAH ka amintar dashi ga dukkanin muradansa na alkhairi." Sannan yamik'e shima yayo arwala ya tayar da sallah, haka shima Abba kasa kwana yayi banda tunanin abubuwan da suka faru a shekarun baya da kuma tunanin halin da 'yarsa take ciki Babu abunda yakeyi, hakan yasa yayo arwala ya fuskanci gabas don samun sassauci, a b'angaren hajia mama ma dake asibiti itama d'in hakan tayi don samun sasauci acikin yanayin da suke ciki.
Daren ranar kam gaba d'aya wud'annan ahali guda biyu kasa bacci sukayi musamman Abba da gwaggo da hajia mama da kuma barrister kamal cikakken aboki managarci awajen Abu sumayya, kwana sukayi bisa abun sallolinsu suna addu'ah ALLAH yagafartawa Abu sumayya kuma yaba iyalinsa lafiya ya albarkaci abunda yabari, banda gwaggo da addu'arta ta tafi wajen ALLAH yaba yaronta lafiya ya tashi kafad'unsa shima yasamu cikar farincikinsa kuma yaraya masa abunda tahaifa yabata lafiya.
Tun da asubar fari ya kirawo abokanansu na kusa dana nesa ya sanar dasu rasuwar aminin nasu tare da tabbatar masu da cewa yanzu haka suna shirin tafiya can kano saboda acan yarasu kuma yanasa ran acan za'ayi jana'izarsa, rana nafitowa ya iske gwaggo bayan sun gaisa yace yakamata tashirya suje kano, hakan kuwa ya matuqar yimata dad'i saboda jiya zaune takwana ana nuno mata fuskar d'anta tare da hakaito mata yanayin da yake ciki, duk hankalinta yabi ya tashi taga nawar safiya tawaye, saboda yanayin da meenatu ke ciki yasa yace sajida tayi hak'uri tazauna gida Idan sun dawo shida gwaggo sai yakaita tayowa batool gaisuwa kafin itama meenatu ALLAH ya sauketa lafiya.
Haka kuwa akayi sajida ta gyara masa kayansa meenatu nata kuka don sai alokacin yasanar da ita abunda kefaruwa suka kama hanya shida gwaggo da wani mak'wabcinsu babban mutumne sosai tare da matar da kuma zainab da itama kukan takeyi jin d'an uwanta na kwance aadon asibiti shida autynta da take matuk'ar k'auna, abunda bata sani ba shi gaba d'ayama yabar duniya.
Koda k'arfe d'aya na rana tayi har sun isa garin kano dama yakira yasanar dasu Abba suna kan hanya, suna isa ambulance na ajiye gawar Abu sumayya a k'ofar gidansu Abba, tsayawa fad'ar halin da gwaggo tashiga ciki abun zubarwa hawayene sosai amma daga qarshe ta dangana tabarwa Allah,
Bayan kwana uku Abba yasa aka kirawota ya bata takardun da aka samu acikin aljihun Abu sumayya bayan ya sake bata hak'uri da kuma yimata gaisuwa akan rashin da sukayi, karb'a tayi taduba takardun ta farko takar dace data qunshi address d'in data bashi daren da zasu zo, dake d'auke da sunan malan NURADDEN IDRIS ALIYU, tare da address d'insa ak'auyen bebeji, tabiyu kuma takardun wata makaranta ce daya siya ahannun wani mutum acan borno d'auke dasa hannunshi da kuma na mutumen, ranar da zasuzo ya tsaya ya karb'i takardun wajensa wanda shine dalilin da yasa ya sanyosu aljihu suka wucikke.
Kallon Abba tayi had'e da cewa,
"Wannan takardar adreshin qauyen da nake tunanin zai iya gano mahaifinsa ne daka dad'e kana tambayar waye ubansa har kana jifarsa da cewa shi shegene, na qyalene alokacin saboda yanda naga qarfin soyayyar d'ana a idanuwan 'yarka shiyasa banyi yunqurin sanar dashi inda zai iya nemo saba idan har yana raye, shine awannan karon nayi tunanin fad'a masa inda zai iya nemosa don in tabbatar maka da cewa shid'in d'an halak ne gaba da baya, Amma cikin ikon ALLAH Sai gashi hakan bai faruba ya karb'i abunsa" ta qarasa maganar tana kuka.
Shiru Abba yayi kamar wanda aka zarewa lakka yana mai nadama da baqin cikin abunda yayi, saida tayi kukan mai isarta sannan taci gaba da cewa, "wannan kuma bansan kota meye ba, a ajiye har zuwa lokacin da ALLAH zaiba iyalinsa lafiya mai yuyuwa ne ita tasan kota meye."
Hak'uri su uncle Hassan dake gefenta suka shiga bata tare da ban magana tace,
"Aini ku bakuyi mani komai ba tunda kuka nunawa d'ana gata aduniya kuma banida bakin da zanyi maku godiya saidai ALLAH yasaka da alkhairi, shima d'in daya yimana bawai nariqesa araine ba, kawai ina tuna masane."
Da haka dai suka samu suka sake bata hak'uri tare da tausarta sannan ta ajiye masu takardun tawuce tabar d'akin tana sharar k'wallah.
Tun ranar da aka yiwa batool aiki har zuwa yau kimanin kwanahud'ubata farfad'o ba, tun anasa ran yau zata tashi gobene har iyayen sun fara sarewa akan al'amarin tare da fargabar abunda kan iya zuwa ya dawo, ana gobe gwaggo zata wuce gida sunje asibitin ita da barrister kamal da kuma zainab suna zazzaune cikin d'akin da aka kwantar da batool riqe da jariran da aka faraba madara yanzu sukaga ga hannunta yafara motsi, cikin farinciki duk sukayo kanta yayinda tafara bud'e idanuwa ahankali tana kallonsu d'aya bayan d'aya tamkar wud'anda bata tab'a gani ba, wani irin farinciki ne ya rufe gwaggo da hajia mama suka rungume juna suna hawaye tare da yima ALLAH godiya, barrister kamal ne yayi saurin fita sai gashi yadawo tare da likita, matsawa yayi kusa da ita yana duddubata sannan yace su tayar da ita zaune, ahankali yafara kiran sunanta kanta na duqe a k'asa, "batool, batool, batool" yakira sunan har sau uku, anan ukunne ta d'ago kai tare da kafesa da idanuwa, biron dake hannunsa yafara nuna mata saiti idanuwanta yana yawo dashi a fuskarta. Ahankali take bin biron da idanuwa aduk inda yayi dashi kafin likitan ya maidashi cikin aljihu yana murmushi had'e da juyowa yana kallon barrister kamal da shurahbil dake gefe a tsaye yace
"Alhamdulilah, ansamu tafarfad'o kuma in Sha ALLAH babu wata sauran matsala, yanzu abunda ya kamata ahad'a mata ruwan tea abata tasha." sannan ya rubuta wasu magunguna yabasu yace aje asiyo akawo idan tagama shan ruwan tea sai akirasa, juyowa yayi yasake kallonta har lokacin idanuwanta na saman aljihunsa da taga yasa biron aciki yayi murmushi sannan yafita.
"Sannu maman twins" barrister yafad'a sannan ta maido idanuwanta akansa daga kallon likita da takeyi shima tanata kallonsa harda karkace kai,
K'ok'arin had'a ruwan tea d'in hajia mama tafarayi yayin da gwaggo dake rik'e da maccen tamatso kusa da ita cike da tausayawa tace,
"Sannu uwar biyu, ubangiji ALLAH ya baki lafiya" kamar da gaske batool ta d'ago kai tace
"Amin." tare da mik'a mata hannuwa, hakan yasa gwaggo ta mik'a mata jaririyar had'e da cewa zainab ta kawo mata d'ayan jaririn aka aza matasu saman jikinta tabisu da kallo d'aya bayan d'aya, so takeyi ta tuna kosu waye atare da ita amma takasa, hakan yasa taji kanta yafara jujjuyawa kamar ana yawo da ita cikin wata duniyar, dariya dariya kuka kuka tafarayi kafin can tasaki wata irin qara had'e da ture yaran daga jikinta tana wani ihu wanda nan take hankalinsu ya tashi, badon zainab tayi sauri taro yarinyar ba da tuni tafad'a akan k'arfen dake gefenta na qarin ruwa yayinda shikuma d'ayan tuni yafad'o k'asa tare da tsanyara ihun kuka da sauri gwaggo ta d'aukesa tayi waje tana k'walawa nurses kira ita kuma banda buge buge da takeyi tana sakin wata irin qara da duk wanda yaji sai tsikar jikinsa ta tashi, hajia mama na kuka tafara qoqarin riqota saboda kada tajima kanta takaimata wani irin cizo da yaga amma hakan bai hanata takamata tariqeta sosai tana maimaita kalmar "innalillahi wainna ilaihirrajiun, allahumma ajirni fi musi bati wa ahlifni khairan minha, ya ALLAH muntuba kayafe mana kada kajarabcemu da abunda bazamu iyaba." Dukanta takeyi da dukkanin qarfinta amma taqi sakinta saima sake rungumeta da tayi sosai tana kuka, itama zainab d'in kuka takeyi tana riqe da jaririyar agefe, saiga shurahbil da barrister kamal da sukaje wajen sayo magani sun dawo, da gudu suka ida qarasowa wajen suka kamama hajia kaka ita suka rirriqeta tana kucce kucce saiga wasu likitoci harsu uku sun shigo gwaggo na biye dasu abaya tana sharar k'walla saboda nurses sun karb'i jaririn yana can suna dubashi.
Nan take sukayi mata allurar bacci sannan sukace su saketa sufito, taimakon gaggawa suka fara bata tare da yimata binciken daya kamata, sannan suma suka fito fuskokinsu cike da damuwa, da sauri hajima mama tanufi inda suke tace,
"Don ALLAH likita awane hali 'yata take ciki" gaba d'aya kasa tanka mata sukayi suka shige cikin wani office, turowa sukayi aka kira masu shurahbil alokacin Abba da uncle Hassan sun iso saboda wayar da shurahbil yayi masu ya sanar dasu halin da ake ciki hakan yasa uncle hassan ya dakatar da shurahbil d'in suka shiga shida Abba, wata takarda suka mik'o masu bayan cikin natsuwa Dr na'eem wanda yana d'aya daga cikin likitocin da sukayi mata operation yayi masu bayanin cewa,
"Alhaji kuyi hak'uri akan abunda zan sanar daku amma patient d'inku tana cikin wani mawuyacin hali sakamakon buguwar da tayi ga kai,
bincikenmu ya tabbar mana da cewa tasamu matsala a kwakwalwarta, dama tuni wannan muke tsoro ga farkawar tata tun lokacin da aka gama mata aiki but alhamdulilah tiyatar tata tawarke sai d'an abunda ba'a rasa, don haka yanzu wannan takardar zakuje kubiya kud'in wani scanning ne da za'ayi mata zuwa anjima.
Yanda abun ya matuqar girgza Abba yasa daga nan inda yake zaune sukaga ya b'ingire sanadiyar hawan jinin da yake dashi, dole shima nan take aka bashi gado kafin kaceme 'yan uwa sun taru a asibitin cike da jimamin wannan irin jarabawa da Allah ya aikowa familyn nasu acikin wannan lokacin.
Little Hassan kam babu abunda ya sameshi don anyi masa checkup sosai, haka Abba shima yasamu sauqi duk da dai har yanzu yana qarqashin kulawar liikitocin, gwaggo kam fasa tafiya tayi saidai tace barrister kamal yawuce ita zata jira har nan da kwana biyu, al'amarin batool kam ya tsananta, hauka tuburan takeyi wanda likitocin suka tabbar masu da basusan iya adadin lokacin da zata iya warkewa ba sai dai kawai suci gaba da addu'a da kuma nemar mata magani, yanzu haka dalilin daya hana suyi deparing nasu zuwa asibitin mahaukata saboda sauran raunukan dake jikinta ne da kuma tiyatar dake jikinta da suke treating badon haka ba ayqnayin da take bai kamata ace an ajiyeta nan ba, shiyasa kullum cikin yimata allurar bacci suke kuma tahakanne kad'ai yaran kesamu suna shan nono awajenta.
Rayuwar batool tazama abun tausayi musamman idan ka kalli jariran dake gabanta da kuma yanayin da take ciki, su hassana kam tuni sun samu sababbin iyaye saboda kulawar da zainab ita da d'an uwanta shurahbil ke basu, abunka da yaro rayuwarsu sukeyi cike da farinciki cikin sauran 'yan uwansu yara sai baka rasa bane zakaga sun aza rigama suna kuka sai ankaisu wajen dady da ummiensu, musamman cikin dare ko kuma lokutan da zasuci abinci sai kaji suna rigima waisu bazasu ciba sai I
idan dady da ummie ne zasu basu,
Abba kuma yasamu sauqi sosai har anbashi sallama amma yanda yayi rama saboda tsananin baqinciki da damuwar da yake ciki kallo d'aya zaka yimasa ka zubar masa da hawaye, yayi kuka, yayi nadama tare dayin tir da zuciya irin tasa, tabbas yayi dana sani abu adadi alokacin da SANNU SANNU yafara karb'a sakamakon abunda yayi, dama anfad'a masa cewa but khairan da sharran wanda duk ka aikata da SANNU SANNU zai riskeka, dama SANNU SANNU bata hana zuwa.....gashi yanzu anzo wajen da abunda ya aikata ya riskesa.
A 'bangaren mutumen dake iqirarin soyayyarsu hassana da hussaina kuwa tun ranar da yaji kalaman da suka fito abakin shurahbil yadena bayyana agaresu amma hakan bai hanashi bibiyar rayuwarsu ba akoda yaushe hatta rasuwar Abu sumayya dashi akayi jana'iza saidai ko kad'an bai bari sukayi arba da shurahbil ba saboda tsoron kada wancan tunanin ya zauna aransa, haka kuma yakanzo asibiti duba jikin batool saidai baya zuwa sai lokutan daya tabbatar su shurahbil basa wajen ko sun shiga sallah tukuna, hajia mama na lura dashi Idan yashigo amma bata tab'a kawo komai aranta ba,saboda aduk sadda yashigo sai yafara zuwa ya dudduba marasa lafiyar dake ward d'in tare da yimasu alkhairi sannan yake zuwa wajensu hakan yasa tunaninta yatafi akan qila irin mutanen nanne dake zuwa dudduba marasa lafiya suna yimasu alkhairi don suma duk sadda yashigo dubo goma yake ajiye masu, har ta tab'a nunawa Abba dasu Uncle h shi, Amma ALLAH bai tab'asa suka gane saba ko kuma suka had'u da shurahbil ba sai yau, shurahbil na shigowa da motarsa asibitin ya d'auko su gwaggo da matar uncle hussain yaga shikuma yafito, hakan ya matuqar d'aure masa kai har yafara tunanin ko waye wannan mutumen, tunowa da compliment card d'in daya basa ranar yayi da sauri ya ajiyesu gwaggo yajuya motarsa yakoma gida, yana zuwa yanufi wajen daya sargafe kayan dayasa ranar ga hanger yafara laluben aljihun rigar, cikin sa'a yanasa hannunsa cikin aljihun rigar na gefe yaci karo da compliment card d'in,
Wata irin ajiyar zuciya yayi don dama tuntuni ALLAH ALLAH yakeyi inbai yadda shiba, rubutun da akayi jikinsa yafara karantawa kamar haka,
*_ALLAH KAJIK'AN IYAYEN MUππ»π_*
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πΆββοΈπΆπ»ββοΈ *SANNU SANNU*πΆπ»ββοΈπΆββοΈ
π _Bata hana zuwa..._π
_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπ*
_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*π
_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*π
*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*π
*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*β€οΈ
Page___6π
Rubutun dake jikin compliment card d'in shurahbil yaqurawa idanuwa kafin yafara k'ok'arin karantosa cike da mamaki,
" _DR. N.I.ALIYU (PSYCHATRIC DR.)_" ya sake maimaitawa aransa, sannan yabi sauran address d'in dake rubuce da kuma numbobin waya har guda biyu da kallo, jujjuya card d'in yafarayi yana son tunano inda ya tab'a jin wannan sunan, Nan take yatuna cewa ai babban likitan da yasha ji ana zance agarine akan k'warewarsa wajen iya kula da mararsa lafiya musamman masu fama da matsalar k'wak'walwa ya matuqar sanin aikinsa tare da tausayawa mararsa lafiya sosai wanda wannan dalilinne yasa nan take yasamu d'aukaka cikin qanqanen lokaci, shekararsa hud'u kenan da yasa akayo masa transfer daga minna zuwa kano, kuma cikin ikon ALLAH yanzu babu inda labarinsa bai kaiba acikin garin saboda tausayi, kamanta gaskiya da kuma taimako acikin aikinsa, ajiyar zuciya yayi tare da cewa "tabbas babu ko shakka wannan mutumen shine likitan da naji ana zance agari, idan kuwa hakane yazama dole na samesa har gida saboda matsalar auntynah tunda ance shi mutumne mai sauqin kai wataqil zai iya bamu wani taimako kodon saboda soyayyar da yake yiwa yaranta" haka yaqarashi zancensa shikad'ai yana safa da marwa acikin d'akinsa kafin ya kad'a katin a aljihu yabar d'akin, yana fitowa yaci karo da zainab tafito ita da twinse zasuji wajen bukin wata qawarta, da gudu suka nufi wajensa kowacensu na Kiran "oyoyo uncle" tare da bud'e hannuwa, shima bud'e nasa yayi suka shige Yana dariya yace,
"Iyyeee 'yan matan aunty Ina zuwa akaci wannan gayu haka?."
"Party zamuje" hussaina tafad'a tana kallon zainab data qaraso wajen, duka hassana ta kaimata had'e da cewa "ke kuma bikine zamuje ba party ba ko aunty zee" tafad'a itama tana kallonta.
Dariya zainab tayi sannan tace "Gaskiya kam hassana fad'amata mu biki zamuje ba party ba, haba hussaina wane party ana zaune lafiya, ai sai kija uncle hussain ya kakkarya mu idan yaji haka!." Kallon shurahbil da shima dariyar yakeyi tayi sannan tace "don ALLAH ya shurahbil Ina zakajene?."
"Ya akayi ne?" Ya amsa mata atak'aice tare da mik'ewa tsaye daga duqen da yake zai wuce don yasan halinta, yanzunnan me zatace ya ajiyeta, bai qarasa fitaba ta biyoshi da sauri tana fad'in. "Emm.emm dama cewa nayi ko zaka rage mana hanya pls"
"Ok, dama nasan shine zancen" yafad'a tare da ficewarsa, da sauri ta dawo baya tariqa hannuwansu sukabi bayansa suna yimata 'yan tsalle tsalle.
Bayan sun shiga mota shurahbil ya tayar suka bar gidan ya juyo Yana kallon zee da tasha kwalliya qamshin turare na tashi ajikinta tako ina yace,
"Zainab kinji fitinannen qamshin