Showing 21001 words to 24000 words out of 260204 words

Chapter 8 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt

qarfin yakirasu da abokanai ko aminai saidai yace sud'in 'yan uwan sane shaqiqai, don haka yana roqonsu dasu riqesu hannu biyu bisa kyautatawa da kuma girmamawa, gaba d'ayansu ji sukayi jikinsu yayi sanyi saboda yanayin yanda yake magana tamkar wanda ke barin wasiya, murmushi yayi ganin yanda fuskokinsu suka canxa had'e da cewa "kada kusaka kawunanku cikin damuwa akan maganganun dake fitowa abakina domin natabbata daga cikinsu akwai wud'anda zasu sanyaya zuciyoyinku kuma su sakaku cikin farinciki marar misaltuwa" juyowa yayi inda d'an nasa me zaune yace, "Nuraddeen tashi katafi, ALLAH yayi maka albarka" ajiyar zuciya malan Idris ya sauke had'e da mik'ewa tsaye yad'an sunkuyar dakai agabansu alamar girmamawa sannan yafice daga d'akin,

Bayan yafita baffa ya kalli 'yan uwansa yace, "usman, Aliyu Ina son kunemawa d'anku Nuraddeen izinin neman auren Rashida 'yar gidan malan bashar a hannun iyayenta dake zaune agabanku idan har ba'a tsayar mata da miji ba kamar yanda d'annaku yabuqata cewa yana sonta"

Wani irin annurine da farinciki ya bayyana a fuskokinsu gaba d'aya jin kalaman dake fito daga bakin aminin nasu in banda baba da kuma aliyu qanen baffa, shidai baba tsantsar farincikine da kuma mamakin jin cewa wai malan idris nason 'yarsa Rashida, shikuma Aliyu tsananin bak'inciki da takaicin hakanne da yaji yasa yakasa b'oyewa saboda 'yarsa muneera yaso ya had'a aurensu da shi saboda yanda take tsananin sonshi. Sosai baffa yalura da sauyawar fuskar da d'an uwansa tayi Amma sai ya basar saboda jin Usman na fad'in "Masha Allah, alhamdulillah, agaskiya haka yayi kyau kuma shizai k'ara dank'on zumunci a tsakaninmu, don baka iyayen rashida kunji buqatar d'anku idan har yarinyar nan ba'a tsaida mata da miji ba, to muna nema masa izinin yafara zuwa wajenta donsu daidaita"

Gaba d'ayansu suka had'a baki wajen cewa, "to aimu da Nuraddeen da Kuma Rashida duk 'ya'yanmune, saboda haka indon ta tamu bamuqi jinin yau a d'aura masu aure ba, don haka mu tabakin malan bashar muke jira sai muyanke hukunci"

Murmushi baba yayi sannan yace "hak'ik'a nayi farinciki, farinciki kuma marar misaltuwa akan wannan al-amarin, narigaku azuciya ne sai kuma ALLAH yasa yaron ya rigani abaki, Amma ALLAH shine shedar azuciyata nayi niyar bawa Nuraddeen auren Rashida saboda yanda nayaba da halinsa da kuma nagartarsa, dad'in fad'awa da naji cewa shi d'an amininane kuma d'an wannan ahali masu d'inbin karamci da kyautatawa, saboda haka kamar yanda kukace ku iyayen duka biyunne to nima haka, gaba d'ayansu 'ya'yana ne don haka ga mahaifinta nan malan balarabe sai muji tabakinsa." Yaqarasa maganar yana nuna inda qanen nasa kezaune, murmushi malan balarabe yayi had'e da cewa, "to madallah tunda duk kunbar mani 'yar tawa nagode kuma ni balarabe Ina so ku sheda cewa ba izini kad'ai ba hatta auren 'yata Rashida nabawa d'ana Nuraddeen duniya da lahira, don haka duk sadda kuka so asa rana da kuma yanka maku sadaki sai ku nememu in sha ALLAH ko yaushene mu a shirye muke"

"Alhamdulillah" kowa yafad'a, baffa yace "Tunda hakane mezai hana ayanka sadakin kuma asa ranar yanzu sai ahuta ko me kukace?"

Cikin rawar murya anensa Aliyu yace, "A'a yaya abari har sai sunje sun tambayi yarinyar idan ta amince ina ga hakan zaifi."

"Indai ta b'angaren yarinyar mune babu wata matsala koda had'asu mukayi munyarda da tarbiyarta zata amince ballema shi yaron yaganta yace yana so, don haka ayi abunda yakamata babu damuwa in Sha ALLAH" malan balarabe yafad'a cike da nuna yarda akan 'yar tasu,ko kad'an ran Aliyu bi yimasa dad'i ba Amma babu yanda zaiyi dole ya haqura tunda duk 'yan uwan nasa sun nuna amincewarsu, kafin kace me aka yanka sadaki dubu hamsin , nan take abokanan iyayen nasu su hud'u suka had'a kud'in suka ba qannen mahaifin Nuraddeen a matsayin tasu gudun mawar ga d'an nasu,

Hakan ba k'aramin sake farantawa baffa zuciya yayi ba tare da yiwa ALLAH godiya daya basa nagartaccin abokanai irinsu,

Abunda ALLAH yaso kuma yariga ya had'a ko ana so ko ba'a so to sai ya tabbata, a ranar su baba basu baro garinba har saida aka dindince ranar d'aurin auren nan da sati biyu masu zuwa tare da sadakin Rashida a hannunsu zuciyoyinsu cike da farinciki, nisawa mahaifin Rashida yayi yace "ALLAH mai iko kuma mai yin yanda yaso, mu da mukaje gano marar lafiya sai gashi mun dawo da sadakin 'yarmu a hannu, tabbas komai nada sanadi arayuwa, ubangiji ALLAH yasa hakan shi yafi zama alkhairi kuma ya had'e hankulansu waje d'aya" kowanensu ya amsa da "Amin" suna masu jinjina al-amarin ubangiji.

Aliyu kuwa suna tafiy bai zame ko Ina ba sai d'akin mahaifiyar Nuraddeen wato matar yayan nasa yay hawwa kmar yanda suke kiranta yana cika yana batsewa, nan ta taso tana tambayarsa ko lafiya ai kamar jira yakeyi ya zayyane mata qarya da gaskiya, ashar ta lailayo ta dire tna fad'in "ai wlh ba'a isa ba, yaushe har shi nuran yayi girman da ya isa yace ga wadda yake so da har za'aje ayo masa qulle qulle a aura masa wata can bare, to wlh bazan tab'a lamuntar wannan abun gori acikin dangi ba, haka kurum ajawo mani abun kunya da fad'a acikin gari, kowa yasan awannan garin namu auren zumunci akeyi, bamuda bare kuma ba'a tab'a kawo mana ita acikin gida ba, shikenan sai yanzu ace akan d'ana za'a fara?to wlh haka bazata sab'uba wai bindiga aruwa" wani farincikine ya rufe Aliyu yaci gaba da ingizata yana zugata haddasu cewa "Nima haka nagani yaya hawwa, Ina laifin ace ko muneera ce an had'asa da ita tunda tana sonsa amma wai antashi an had'asa da wacce batasan kimarmu da darajarmu ba, ga yaran cikin garin basuda mutunci da girmama na gabansu"

"Kai rufamun baki, muneera ko shashasha, tun yaushe nake cemata tadinga oqarin jawo hankalinsa amma takasa, shegiya mai gwalmad'ad'd'in qafafuwa ai koma meye laifin tane"

"Amma yaya hawwa kemafa kinsan yaronnan da baqin rai yake, har yaushe tag fuska balle taje tayi masa karairayar da zata jawo hankalinsa, yanzu dai ya kamata kisan abunyi kafin yarinyar nan tazo tarabamu da d'anmu ta tsigemu gaba d'aya"

"Kai Aliyu tofar da mugun yawun bakinan naka, wannan baqar fata har Ina, Bari naje wajen malan dole a ajiye wannan maganar" fiiiii...tanufi shigifar da baffa ke kwance ta iskosa yana jan carbi, masifa tafara zuba masa yana kallonta har ta gama sannan ya ajiye carbin agefe yace "yanzu ke hawwa awannan yanayin da nake ciki har kinada k'warin guiwar zuwa kiyi tsaye agabana kina wud'annan maganganun, to bari infad'a maki ko kina so ko bakya so sai anyi wannan auren tunda yana son yarinyar"

"Ni kuma bana son yarinyar, don haka bazai aureta ba"

"Saboda meye?"

"Saboda ita d'in barece"

"A'ina aka fad'i hakan, qur'ani yafad'a ne ko a'a?"

"A al'adar garinmu dai ce ba'a tab'a yin hakan ba kuma baza'a fara akan d'ana ba"

"Kaji shirmen banza, al'adar tafi alqur'anin ne? To Bari kiji wannan aure kamar anyi angama ne da yardar ALLAH"

"Amma malan inkayi mani haka bakayi mani adalci ba sabo..." Bata qarasa rufe baki ba yace

"Eh jeki naji d'in ni yanzu barci nakeji bana son wannan hayaniyar!"


Duk inda ran hawwa yake inyayi dubu yab'aci, tafice buuuu.kamar zata tashi sama tana maseefa, karo tayi da Usman akan hanyar tsakar gidan da yake family ne duk anan suke zune tafara yimasa qorafi, murmushi yayi sannan yace, "ikon ALLAH, to aike yaya hawwa banda addu'a babu abunda yakamata kiyi tunda shi yaganta kuma yace yana sonta, don ALLAH don annabi ki kwantar da hankalinki, mai k'aya ya daure kuma sai ace mai cira na kuka!?"

Aifa nan shima tayi masa tatas har tana k'arawa da cewa ai duk munafuccin da akayi dashi akayisa, shidai murmushi kawai yayi yawuce abunsa batare daya sake tankata ba, Aliyu ne ya iso wajen yana kallon irin hararar data raka d'an uwansa da ita yace,

"Ahaf! Ai infad'a maki yaya hawwa duk munafuccin agindinsa yake, shine nan ya qulla komai." Tsaki taja had'e da barin wajen tana fad'in, "sakarci, to kai meya hanaka kwancewa daya qulla, ai wlh duk sai nayi maganinku ga baki d'aya."

😨 _TIRQASHI! RASHIDA KINA CIKIN MATSALA, GASHI KEBA ILIMIN ZAMANI BALLE KI KWACI KANKIπŸ€”πŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸƒπŸ»β€β™€οΈ_







*_ALLAH KAJIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ˜­_*
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___12πŸ’Ž

Kallo Aliyu yabi yaya hawwa dashi kafin yace "Kai wannan mata anyi fitinanniyar halitta anan, duk girmanka baza katab'a gwaninta awajenta ba, jarababbiya da ganinta kasan ba qaramin haquri yaya keyi da ita ba."

Kasa zaune da tsaye yaya hawwa tayi saboda tunanin hanyar da zatabi ta hana auren, in tayi nan tayi can kamar mai jiran sauraren wani sak'on, cije baki tayi aranta tana mai ayyana kalar uqubobin data tanadawa yarinyar matuqar bata samu nasarar ruguje auren ba,

Baba kuwa yana isa gida bakinsa ko rufuwa bayayi saboda tsananin farinciki yafara k'walawa Rashida kira alokacin ita kuma tana bayi tana wanka,

"A'a sannu da zuwa malan,lafiya naji kana k'wallawa 'yar taka kira tundaga zaure" tak'are zancen had'e da jawo tabarmar dake gefen d'aki ta shimfid'a masa sannan takoma d'aki ta d'auko ruwa masu sanyi takawo masa, fuskarsa cike da annuri ya nemi waje ya zauna sannan yace,

"Yawwa maman Rashida lafiya klw muka dawo, Ina ita Rashidar take, ko tayi islamiya ne?"

"A'a yanzunnan tashiga wanka, inaji yauma tayi latti ALLAH yakareta daga dukan malamai."

"Amin ya ALLAH" Yafad'a had'e da d'aukar ruwan data ajiye masa agabansa yasha,

"Malan shin ko abun sirrine tsakanin uba da 'yarsa naji kayi shiru, kai da naga kashigo da azamarka kamar Wanda akaba saqo yakawo mani." Murmushi yayi mata sannan yace

"To kusan dai kamar hakanne amma sak'on Kuma bake aka bawa ba 'yarmu aka ba."

"Tooo...! Kace dai harkar tason kaice, to bari nakama bakina, inbar uba da 'yarsa susha sha'aninsu"

"A'a ranki shidad'e ai abun bai kai can ba, ungo wannan riqe inyi maki bayani" ya ciro kud'i a aljihunsa ya mik'a mata, ansa tayi tana bin kud'in cike da mamaki kafin tace, "malan a ina kasamo wud'annan? Ina wajen ganin marar lafiya kuka tafi ko?"

"Eh a can mukaje?"

"To wud'annan kud'infa a ina aka samosu?"

"Kai maman Rashida wud'annan tambayoyin sunyi yawa, sai kace wanda yasato"

"To ai dole na tambaya saboda abun da mamaki!."

"kwantar da hankalinki to wannan sadakin Rashida ne kuma nan da sati biyu za'a d'aura auren in sha ALLAH..." bai qarasa zancen ba sukaji qarar fad'uwar bokiti daga toilet Rashida ta saki jin abunda kefitowa daga bakin mahaifin nata, atare umma da baba sukace,

"Ke lafiya?"

K'ok'arin maida hawayen da suka zubo mata tayi tare da ciro zanenta dake rataye ajikin k'usa ta d'aura sannan ta yafo towel d'in da tashiga dashi yarufe mata daga samn kai zuwa qirji tafito kanta na sunkuye qasa tawuce d'akinsu,

Kallo suka bita dashi kafin baba yace "ALLAH ya kyauta, ni bari inje muyi magana da balarabe yana waje yana jirana.!"

"Shine bakace ya shigoba zaka barshi zaune awaje sekace wani baqo"

"Bari dai natafi kije ki ajiye kud'innan idan nadawo ma k'arasa maganar."

"To ALLAH ya kiyaye kuma yasa adawo lafiya, ka gaidashi"

Yana fita itama Rashida tafito saye da hijabinta na islamiya tace "umma natafi" batare da tabari sun had'a idanuwa da ita ba don kada ta fahimci halin da take ciki,

"To adawo lafiya" itama tabata amsa atak'aice, sannan tamik'e tawuce cikin d'aki.

Rashida kam tana cikin yanayin da ita kanta batasan taya zata fassarashi ba, karatu akeyi amma tayi zaune tahad'a tagumi tana tunani, gashi dai auren da takeso za'a yimata amma damuwarta d'aya shine yanda alokaci guda soyayyar da malaminta ya dasa azuciyarta cikin kwana biyu tayi tasiri aranta har tana tunanin yanda zata iya auren wani idan bashi ba, ji tayi tafashe da kukan da batasan lokacin da yazo mata ba saidai taji malami na fad'in

"Ke Rashida me yake damunki ne?" Firgigit tadawo cikin hayyacinta tana zarar idanuwa had'e dasa hannuwa tana goge hawayen da suka zubo mata,

"Mik'e tsaye." Taji ya sake fad'a tare da nufo inda take riqe da bulala, mik'ewa tayi da sauri tana runtse idanuwanta don duk duniya babu abunda ta tsana kamar a tab'a mata jiki da sunan duka,

"Me kike tunani!"

"Babu malan" tafad'a atsorace har lokacin idanuwanta na arufe, har zai dukanta sai kuma ya qyaleta had'e da cewa tafitar masa daga aji, maimakon tabashi hak'uri kawai sai taja jikkarta tafice daga dama tun d'azu hankalinta baya wajen balle ta fahimci karatun da yakeyi, acan bayan wasu azuzuwa taje ta zauna, ta d'ora daga inda ta tsaya ga tunanin da yakeyi, Bata bar wajen ba har sai da taga antashi sannan tabi sauran d'alibai suka wuce gida,

Tana isa gida ta isko umma na waya da 'yan uwanta dake borno akan zancen aurenta tana fad'a masu ai har ankawo mata sadaki an kuma sa ranar aurenta nan da sati biyu hakan yasake dagula mata lissafi tawuce d'akinta da sauri, kasancewar dama tana fashin sallah yasa batabi takan kiraye kirayen sallar magrib da akeyi ba tayi kwancenta, ita kuma umma kota kanta batabi ba tad'auki butarta tayo arwala sannan tawuce d'aki ta tayar da sallah.

Can misalin qarfe tara nadare bayan baba yadawo sun gama tattaunawa da umma sannan yayi mata bayanin cewa ai bayan sun gama dubiyar da sun kajene aminin nasa ya bijiro da maganar nemawa d'ansa auren Rashida ashe cikin ikon ALLAH ganin da yake yimata a makaranta yaji yana sonta tun kafin inyi masa magana sae gashi yafad'awa mahaifin nasa cewa ya nema masa aurenta." nan dai ya fayyace mata yanda komai yafaru, ajiyar zuciya tayi had'e da cewa "Alhamdulillah, aini sai yanzu nasamu natsuwa, amma tunda kabarni nake wasu wasin wannan al-amarin tare da taraddi jin kace nan da sati biyu za'ayi auren, amma yanzu Alhamdulillah, ALLAH yatabbatar mana da alkhairi, naji dad'i kuma nayi farinciki sosai ai malan idi mutumen kirkine da kowa zaiyi sha'awar had'a zuri'a dashi, ubangiji ALLAH ya bashi lafiya kuma yasa ayi munada rayuwa."

"Amin ya rabbi, ai don ma bakiga yaron ba, ALLAH dai ya tabbatar da alkhairi, tashi kije ki kirawomun ita" cike da farinciki umma tanufi d'akinta ta tsaya abakin k'ofa tana fad'in "Rashida, Rashida.." jin bata amsa ba yasa taqarasa cikin d'akin, kwance ta hangota saman katifarta, kallo d'aya tayi mata tasan da cewa ba bacci takeyi ba kawai idanuwan natane kad'ai a rufe, matsawa jikin katifar tayi had'e da cewa,

"Ke Rashida lafiya kikekuwa?" Firgigit tabud'e idanuwanta had'e da saukar dasu akan nata, "lafiya kike?" Tasake maimaita mata akaro na biyu, qoqarin miqewa zaune tayi had'e da sauko da k'afafuwanta k'asan katifar sannan tace,

"Umma kainane yake yimun ciwo."

"Ashsha shiyasa yau najiki shiru tunda kika dawo makaranta baki fito ba balle kid'auko abincinki kici, daure kitashi mahaifinki nakira inyaso daga can sai kici abinci kisha magani kinji ko" Kai tad'aga mata ita kuma tajuya tabar d'akin tana fad'in

"ALLAH yasawaqe ciwon kai kam ai babu dad'i"

Ko minti biyu umma batayi da zaunawa ba Rashida itama tashigo cikin d'akin tajawo hular hijab d'inta ta lullub'e mata rabin fuskarta tanemi gefen qofar d'akin daga ciki ta zauna, "Baba ina wuni andawo lafiya?" Tafad'a tana gyara hular hijabin zuwa kanta."

"Lafiya klw Rashida, lafiya kike kuwa?" Kafin tace wani abun umma tace

"Au kagafa na manta infad'a maka ba tajin dad'i, na iskota kwance shine dana tambayeta take fad'amun kanta ke ciwo don tunda suka dawo islamiya banga tafito waje ba balle ko abinci tasamu ta d'auka taci."

"Subhanallahi, injin to da sauqi" yafad'a yana kallon Rashida

"Eh da sauqi baba," tafad'a tana goge zufa a goshinta, wani d'an guntun tsaki yaja had'e da cewa

"Matsalar ku kenan mata baku fiye kula ba wani lokacin, shiyasa ake ganin sakacinku yayi yawa ace mutum nada d'a yaga yayi awa kusan biyu a d'aki bai fitoba kuma bazai je yaduba halin da yake ciki ba sai mai faruwa tafaru kaji ana fad'in ai kuwa tun d'azu najishi ko najita shiru ad'aki ashe kaza da kaza yafaru bamu sani ba, to meye amfanin hakan? Kin jita shiru amma kin kasa dubota kiga ko lafiya take sai yanzu da nace ki kirawota, ALLAH ya kyauta"

"Ayi hak'uri malan in sha ALLAH za'a dinga kula"

Hannunsa yamik'a gefensa a qarqashin pillow dake kan gadon ya d'auko kud'in da yakarb'a a hannun umma ya mik'awa Rashida had'e da cewa,

"Ungo wannan ki k'irgamun su nawa ne?"

Mik'o hannunta tayi yana makarkata ta karb'a sannan tafara k'irgawa d'aya bayan d'an shi kuma yana kallonta, saida tagama sannan ahankali ta d'ago kanta tace,

"Dubu ce guda hamsin" murmushi yayi had'e da cewa, "ban fahimta ba"

"Ina nufin naira dubu ce sau hamsin " girgiza kai yayi cike da takaicin dubu hamsin ma 'yarsa bazata iya fad'a daidai ba, wannan wane irin rayuwace, kallonta yayi yanaji kamar ya maketa kafin yace,

"Rashida kenan, ai bahaka ake fad'aba, naira dubu hamsin zakice a hausance kinji ko?."

'Daga masa kai tayi tare da sake mik'a masa kud'in,

"A'a kiriqesu a hannunki, nakine mallakinki duniya da lahira" d'ago kai tayi tana kallonsa cike da alamar tambaya atattare da ita,

"Eh, kud'in kine na sadaki da aka bayar kuma a musulunce bai halatta kowa yayi amfani dasu ba idan ba keba koda kuwa mune saboda hak'k'in k'ine shiyasa na hannunta makisu a hannunki duk abunda kike so kiyi dasu, mudai munfita hak'k'inki koba haka ba?" Yaqare maganar yana kallon umma, jinjina masa kai ita Kuma tayi alamar tabbatar da zancensa.

Muryarta na rawa tace "Babu abunda zanyi dasu baba don ALLAH ku karb'a umma"

"A'a kirik'e hannunki abunda babanki yafad'a shine daidai kinji ko?"

"Umma nifa babu abunda zanyi dasu, baba.." dakatar da ita yayi had'e da cewa, zaki iya ba ummanki ta ajiye maki, tashi kitafi ALLAH yayi maki albarka"

Mik'awa umma kud'in tayi sannan tamik'e zata fita, har ta aza k'afarta abakin k'ofar mahaifin nata yace,

"Rashida bazaki tambayi ko wanene na zab'a maki ba?"

"A'a baba, babu buqatar hakan domin nasan bazaka tab'a yimun zab'in daba daidai ba." Tana gama fad'ar haka tafice idanuwanta na hawaye, tabbas tasan takamu da soyayyar malaminta amma bazata iya yiwa mahaifinta musu ko kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login