Showing 129001 words to 132000 words out of 260204 words
Chapter 44 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt
d'aya zakayi mata kafahimci hutu na tattare da ita, da sauri yanufi wajenta had'e da gaishesa, rungumosa tayi ajiki kai kace bashine d'anta nafarin ba suka nufo wajen dadyn tana fad'in.
"Oyoyo mutanen kano ta dabo tumbin giwa yaro koda mekazo anfika, Amma inada tabbaci akan ba'afi yaron nawa ba saidai ayi gogayya dashi ko ba haka ba alhaji?" Taqarasa maganar had'e da jawo kujera ta zaunar da Dr nura.
Dariya sukasa shida dady kafin yace.
"Mezance hajia fareeda tunda kinriga kin fad'a, ai ko ba haka bane ta zauna, uwa da d'anta kome tace akansa ai babu wanda ya isa musa mata." Suka sake sa dariya.
"Son ya hanya da 'yata Ina fatar kuna lafiya?"
"Lafiya klw ammie, tace agaisheki sosai."
"Muna amsawa, injin tana amfani da maganin yanda yakamata? Nasan halinku na 'yan boko baku fiye ba maganin nan namu na gargajiya muhimmanci ba.?"
"Ahh ammie banda Fatima tana kulawa sosai da lokutan shansa yanda yakamata,"
"ALLAH sarki baiwar ALLAH, ALLAH yasa adace, yarinyar nabani tausayi sosai, tanada matauqar juriya da haquri wlh, badon haka ba idan irin 'yan matan nan namu na zamani ne da yanxu tabi ta tayar maka da hankali dama kanta ga abunda Babu mai iya baku sai ALLAH, kuci gaba da haquri, in Sha ALLAH lokaci nazuwa da ijaba zata sauka, muna nan muna yimaku addu'a,"
"Hakane nura! Kaci gaba da haquri kana kwantarwa da iyainka hankali, da SANNU ALLAH zai duba lamurranku ya share maku hawayenku, akoda yaushe addu'ar mu natare dake."
"Dady, ammie nagode da kulawar da kuke bamu tare da addu'o'inku, koda ALLAH bai bamu aihuwa ba ku kad'ai kun isa farinciki agareni domin babu abunda yakai samun nagartaccin iyaye aduniya muhimmanci, sune kad'ai farincikin da idan katuna zaya dad'a sanyaya maka zuciya."
Daidai lokacin umma tafito daga kitchen don tagama kammala komai zata koma part d'insu, "umma gafa d'anki da d'azu nake fad'a maki cewa yana kan hanya ya iso."
Dama tuni umma tadawo wajen hajia fareeda da aiki kamar yanda dady ya umurta kuma tanajin dad'in aiki da ita sosai don kusan komai atare sukeyi cikin girmamawa, sab'anin hajia nafeesa da saidai ta nad'e qafafuwa tana bada umurni, murmushi tayi had'e da qarasowa wajen tace.
"Sannu da zuwa.." Bata qarasa ba sakamakon juyowar da yayi suka had'a ido, cikin i'ina tace.
"Kaine?"
"A'a baba kece anan kuma.?"
Yafad'a yana nuna baba da hannu, binsu da kallo su ammie sukayi cike da mamakin ganin sunsan juna, nan Dr nura yabasu labarin ynda yasanta har yana qarawa da tambayarta cewa.
"Baba ina wanda naganku tare."
"Yana can shagon da alhaji yabashi yariqa kulawa dashi, ai shi d'in mijinane"
Tafad'a akunyace tare da komawa kitchen,
Dariya su dady sukayi kafin sushiga bashi labarin zuwansu ataqaice amma basu fad'a masa cewa sanadiyar b'atan 'yarsu sukazo garin ba.
Dawowa tayi d'auke da wani qaton try da suka shirya masa abincin da yafiso ita da ammie wato tuwon semolina da miyar kub'ewa d'anye, da sauri ammie taje tariqo mata tana fad'in.
"Kai umma ai dabari kikayi nazo na d'auko masa." Sannan ta ajiye abincin agabansa, yana bud'awa yaga best food d'insa ba shiri yature jikkar gabansa yana qoqarin fara zubawa yaci, d'an mangararsa ammie tayi aqeyar kai tana fad'in.
"Bazaka bari kafara watso ruwa ba.?"
"Awshh....ammie bara nagama cin abinci tukuna, ALLAH yawuna har sun tsinke."
Yafad'a yana shafa inda ta mangaresa, dariya umma dake tsaye tana kallonsu cike da burgewa tayi tana goge 'yan hawayen da suka zubo mata tunawa da tata 'yar sannan tabar wajen.
Bayan ya kammala cin abincinsa yaje ya watso ruwa sannan yaje wajen hajia nafeesa matar babansa ya gaisheta daga can kuma yawuce wajen malamin da yake karb'o maganin Little Nuraddeen awajensa ya karb'o sannan yadawo gida lokacin kusan qarfe biyu na rana yawuce kai tsaye d'akin ammie tana zaune tana tilawar alqur'ani, Saida takai aya sannan tarufe taje ta d'auko wata leda cikin drower d'in madubi tadawo inda yake zaune gefen bedside d'inta ita kuma ta zauna agefen gado.
"Ungo wannan ka kaimata, don ALLAH kace takula da shansa tunda safe kafin taci komai, shi wannan ganyen koba don haihuwa ba yanada kyau adinga tafasashi ana sha da ruwan tea kafin aci komai da safe, yana wanke duk wata datti dake cikin jikin mutum har zuwa mara, hakama yana wanke dattin mahaifa sosai, hatta wannan tumbin da kake ganin kafara azawa idan kuna shansa tare zaya rage sosai, don haka kukula, shi magani da kuke gani dace ne bamusan ta ina ALLAH zaisa adace ba, ALLAH yabamu rayayyi masu albarka."
"Amin ammie, amma shi wannan ganyen mene ammie?"
"Ganyen guava ne."
"Guava fa kikace ammie!, Wannan guava dai dana sani."
"Eh mana, Ina tabbatar maki idan kuka gane shan tea da ita, bazaku tab'a bari ya tsinke maku va agida, da kanku zaku kirani kusanar dani amfanin da kukaji tayi maku ajiki."
"To ammie shikenan mungode."
"Yawwa ALLAH yayi albarka kuma yakiyaye hanya."
"Amin ngd."
Yafad'a had'e da miqewa ya kama hanyar komawa kano bayan yayi sallama da mahaifinsa.
••• ••• •••
Kimanin kwanaki uku Yusuf ya d'auka kwance yana fama da zazzab'i, baya fita ko ina daga d'aki sai d'aki har ALLAH yasa yasamu sauqi, baffansa nafita zuwa gona ya iske baba Usman a d'aki yana shiryawa zaije gidan baffa zasu koma wajen baba balarabe su sake bashi haquri akan abunda yafaru, dama Inna ruqayya tafita anguwa Inna Bilkisu kuwa tana waje tana share wajen dabbobinta da yayi datti, baffa Usman na gyara zaman hularsa akai yaji anriqo rigarsa, juyowa yayi had'e da cewa.
"A'a Yusuf ka taso? Yajikin naka da sauqi ko?"
"Eh baffa Usman naji sauqi sosai."
"Masha ALLAH, ALLAH yaqara sauqi , to ya akayi ne." Duba gefe da gefe yayi sannan ya leqa ta qofar shigowa d'aki yaga ba kowa ya matso dab da inda baffa yake zaune a gefen gado a kunnensa yace.
"Baffa aunty Rashida matar ya nura tadawo, naganta da idona Amma karka gayawa baffana."
A razane baffa Usman yamiqe had'e da cewa.
"Kai Yusuf bana son shashanci, a Ina kaganta ne?"
Hannu Yusuf yasa had'e da rufe baki yana qwalalo idanuwa ya juya yana kallon qofa,
Furzar da iska baffa Usman yayi had'e da kwantar da hankalinsa ya matso inda Yusuf ya dafa kafad'unsa.
"Yusuf ka kwantar da hankalinka, Babu wanda zaiji kaji ko?, Yimun bayani a Ina kaganeta."
"Bana son baffana yaji yace idan nafad'a nima zai b'addani kuma bazai sake bani abinci ba."
"Bazaiji ba nayi maka alqawari kaji ko?"
Nan Yusuf yayiwa bayanin baffa komai had'e da roqonsa don ALLAH kada yafad'awa baffansa shi yafad'a masa, jikinsa na rawa yabar d'akin shima baffa Usman jikinsa asanyaye yabar gidan yanufi wajen baffa yayi masa bayanin abunda Yusuf yafad'a masa, yayi matuqar shan mamakin cewa wai har yanzu baffa ali na adawa da Rashida, tsanar da yakeyi masu har takai girman da zai sake cillasu awata damuwar, tare suka fito suka nufi gidan lado mai kalanzir suka tambayesa abunda yafaru ranar tsakaninsa da Yusuf na zancen ganin matar da Yusuf ya tabbatar masu da cewa Rashida ce.
Sun samu amsa daidai da zancen Yusuf don haka ba b'ata lokaci suka nufi gidan baba balarabe.
Sai yanzu baffa yasake fahimtar dalilin fushin da baba balarabe yayi sosai, ya tabbata akwai maganganu da baffa Ali yafad'a masa marasa dad'i wud'anda sune suka tunzurasa, haqiqa ko shine malan balarabe zai d'au zafi fiyema da hakan domin d'a baifi d'a ba.
Duk qoqarin da yakamata su baffa suyi wajen yiwa baba balarabe bayani yanda zai fahimci komai sunyi amma gaba d'aya Sam yaqi saurararsu balle yafahimce su, da suka d'auko masa zancen ganin Rashi da akace anyi kuwa buga kai yayi ga qasa yace shi baima san da zancen ba, Dole suka haqura suka koma gida, kusan ko yaushe cikin kiransa suke awaya da isko shi gida suna son tabbar da zancen amma ko kad'an yaqi barin hanya ko kad'ance da zasu iya gane hakan, musamman suka turo abokanansu da mutanen da suke da kima abashi haquri ko zai sauko yafad'a masu cewa Rashi tadawo.
Amma baba balarabe yakafe akan bashida masaniyar hakan, ayanayin yanda yake sakin fuska da tarbar wud'anda suke turowa yasa bazasuqi amincewa da zancensa ba, gaba d'aya baffa yasake shiga damuwa har ya soma ramewa.
A kullum bayada lokacin kansa saina bin hanyar zuwa gidan baba balarabe, baya can baya gidan Yaya Maryam, hakama aunty marwiyya, duk inda yake sa ran zai samu tabbacin labarin zuwan Rashida yana biye dashi Amma k sunqi bud'e baki sufad'a masa gaskiya.
Duk zafin da aunty marwiyya ta d'auka akan maganar saida yasoma bata tausayi saboda irin yanda taga yana kaida komo gidanta shida d'an uwansa kawai saboda su sani ko Rashida ta dawo amma idan ta tuna cewa fada masu shine zai sake zamowa silar da Rashida zata koma acikin ahalinsu da Babu zuciyar tausayi ko Imani atattare da wasunsu sai taji zuciyarta ta karye, musamman idan ta tuna da rashin 'yar uwarta da tayi akusa da ita ta dalilin haka.
Ganin irin kai da komowar da baffa keyi a tsakankanin gidajen nasu su uku yasa suka yanke shawarar had'a Rashida dasu Dr nura su koma da ita acan borno domin hakan shi zai fimasu kwanciyar hankali tunda sunsan inda take, koba komai itama zata d'an rage damuwar da take ciki tunda har yau taqi sakin jiki kullum cikin qunci take.
Wata nakaiwa qarshe Dr nura sunzo yimasu bankwana yaya maryam takira baba balarabe da aunty marwiyya suka roqesa akan buqatarsu tasu koma da Rashi acan yafi masu kwanciyar hankali indai hakan bazai zamo takurawa agaresu ba har zuwa lokacin da ALLAH zai qaddari dawowar iyayenta,
Sun matuqar jin dad'i yanda suka basu yarda haka tare da amice masu akan 'yar tasu duk da babu wata alaqa inbata musulunci ba a tsakaninsu musamman Fatima da tunkafin Dr nura ya amsa cewa sun amince tace.
"Babu wata matsala sun amince ba komai." Har tana karb'ar little a hannun aunty marwiyya cike da farinciki.
Rashida kuwa babu yanda ta iya domin ta dad'e da tabbatarwa kanta da cewa batada wani sauran iko akanta tunda tarasa iyayenta akusa da ita, komai yanzu sai yanda akayi da ita, sunjima agidan kafin Yaya maryam taje ta har had'o mata kayanta dana little, aranar ma Rashida tasha kukan rashin iyayenta sosai tare da fawwala dukanin al'amurranta ga ALLAH tana mai addu'ar ALLAH yasa wannan qaddarar da zata d'auketa ta maidata garin da tabaro tazame mata alkhairi, ahalin yanzu ko kad'an bata ganin laifin tafiyar Nuraddeen, saidai takanji wani irin zafi da qunci azuciyarta Idan ta tuna dashi wanda batasan dalilin faruwar hakan ba.
Haka sukayita bata baki da rarrashinta sannan suka d'auki hanyar komawa borno ita dasu Dr.
Gidan iyayenta kuwa tuni Yaya Maryam da baba balarabe suka yanke shawarar saka 'yan haya aciki kafin randa ALLAH zai dawo dasu sai suna jujjuya masu kud'in...
*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶♀️🚶🏻♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻♂️🚶♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎
_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*
_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋
_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞
*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖
*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️
Page___61💎
Ba qaramar rawar gani Dr nura da Fatima ke takawa ba wajen kula da farinciki da kuma walwalar Rashida ba ita da d'anta, duk wani abu da take buqata basa bari har saita kai ga furta cewa tana so suke yimata, mutanene su day sukasan haqqin zaman takewa da kuma sanin kimar d'an Adam, ko kad'an abunsu baya rufe masu idanuwa balle ya had'a ka dasu, sosai suka nuna mata cewa dasu da ita duk abu d'aya ne babu wani banbanci don haka tanada 'yancin tayi rayuwarta yanda takeso acikin gidan ita da yaronta matuqar hakan bai sab'awa musulunci ba.
Hakan yasa tafara sakewa kamar yanda suke buqata saboda taga tasasu farinciki yanda suke qoqarin sata itama.
Sunada sati d'aya da dawowa Dr nura yaje ya sanar da iyayensa batun zaman Rashida agidansa da irin taimakon da yayi mata wanda daga qarshe har danginta suka roqesa akan tazauna wajensu nawani d'an lokaci kafin ALLAH yadawo da mijinta lafiya.
Sun jinjina al-amarin sosai har ammie nayi masa fad'an meyasa tun farkon faruwar al'amarin bai sanar dasu ba sai yanzu, gashi sanadiyar banzar tunaninsa ya haifar mata da rasa iyayenta wanda da ansanar dasu dawuri da duk haka bata faru ba, haquri yabata tare da fad'a mata iya qoqarin yin hakan da yayi alokacin amma ALLAH beyarda ba sanadiyar wannan rubutacciyar qaddarar daya tsaro masu.
Dady kuwa tunda Dr yafara bada labarin yake ganin kamancece niyarsa da nasu umma duk da dai bakomai yafad'a masu ba, jin dayayi Dr nura ya ambaci cewa ita mijin nata na qasar waje yaje karatu yasa ya janye hankalinsa daga wannan tunanin, a tsammaninsa ma yarinyar 'yar masu kud'ice don haka sai dai kawai ya nuna masa yanda yaji dad'in taimakon da yayi da kuma qara qarfafa masa wajen sanin kima da kuma darajar d'an Adam, ya sake horonsa akan ya taimaki duk wani mabuqaci shima ALLAH zai taimakesa domin shi alkhairi aduk inda kayishi to tabbas zai biyoka aduk inda kake.
Haka ammie itama ta sake gargad'insa akan yariqa sanar dasu duk wani abu dayasan yinsa zai iya basa wata matsala ko akasin haka saboda suriqa bashi shawarwarin daya kamata harma da taimako idan akwai buqatar yin hakan, yadena yin gaban kansa akan wasu abubuwa matuqar suna raye dominsu har yanzu yaro yake agaresu, ya matuqar jin dad'in nasihohin da suka yimasa kafin yayi madu sallama yawuce gida suna masu sanya masa albarka da addu'ar ALLAH ya albarkacesa da zuri'a d'ayyaba.
Zama mai cike da girmamawa da kuma mutunta juna ke tsakaninsu da Rashida, basuda matsala da ita haka itama batada wata matsala dasu, rayuwarsu sukeyi mai tsabta inganci da kuma nagarta har little Nuraddeen ya cika wata goma aduniya lokacin har yafara takawa Babu inda bai zuwa, yayi wayau sosai gwanin ban sha'awa dashi ga surutu, koda yafara iya magana da gwaggo yake kiran Rashida saboda sunan da yaji ana kiran mai aikin gidan dashi kenan sai yazata itama sunanta kenan yake kiranta dashi, Amma yanayin shaquwa da sabon da yayi da Fatima ita mama yake kiranta shi kuma Dr da Abba yake kiransa saboda tunda suka dawo kusan duka renonsa a hannunsa yakoma, iyakar Rashida dashi bashi nono sai wasu lokutta da idan uzuri ya gittowa Fatima sai tayi masa wanka da gyarashi, hatta bacci wani lokacin awajensu yakeyi ataqaice duk wata kulawa daya dace uwaye suyiwa 'ya'yansu su suke yimasa, kallo d'aya zakayi masa kasan d'an d'an 'yan gayune saboda irin gyaran da yake samu daga wajensu, wata irin mahaukaciyar soyayya sukeyi marar misaltuwa daga shi har mahaifiyarsa, idanko zasu fita sau goma ayini yadinga ihu kenan yana zallo har sai sun tafi dashi, ita abun har mamaki yake bata don ba qaramin shaquwa yayi dasu ba, Babu abunda ma yafi bata mamaki irin kud'in da suke kashikke masa aduk lokacin da suka fita dashi sai take tunanin kamar tad'ora masu hidima sosai akansa, lokacin data roqesu surage yimasu hidima kada abun yayi yawa nan take suka b'ata rai had'e da nuna mata rashin jin dad'insu akan haka, dole tabasu haquri taci gaba da yimasu addu'a suma ALLAH yakawo masu nasu 'ya'yan masu albarka kusa kusa kamar yanda tasaba akoda yaushe.
Hakama dady da ammie suna matuqar son yaron sosai don duk lokacin da Dr zasuje tare suke zuwa dashi, shi kuma baba randa yafara ganin yaron saida gabansa yafad'i saboda yanda ya hango tsantsar kamarsa da 'yarsa da kuma ummanta atare dashi, yadad'e yana tunanin anya wannan yaron ba jininsa bane kuwa?, Amma sanin cewa jikane ga alhaji tunda baisan alaqar dake tsakanin yaron da kuma Dr ba yasa yakama bakinsa yayi shiru daga bayama sai yashiga tambayar kansa taya hakan zai faru tunda yasan kosu waye iyayen yaron?.duk lokacin daya ga yaron sai yaji gabansa na tsananta fad'uwa, ji yake tamkar Rashidarsa ce hakan yasa yafara qoqarin jan yaron ajiki,
Dady ma ranar daya ga little kai tsaye yacewa ammie yana kama da umma tayi dariya had'e da cewa.
"Ikon ALLAH dama haka abun yake, qila idan anyo taliyo yanada alaqa da ita tunda dama mutane 'yan uwan junane idan an bincika."
Basu wani d'auki maganar da muhimmanci ba shiyasa suka barta abakin nan batare da tayi tsayi ba.
Yau da misalin qarfe biyar na marece Fatima tafito riqe da hannun little suna takawa ahankali kamar yanda take tafiya yasha manyan kayansa irin na cikakkun hausawa hadda babbar riga da hannuwa masu clips kai karantse kace babban mutumne, kansa saye da 'yar madaidaiciyar hula irin mai qube d'innan da takalma have cover yayi matuqar kyau sosai har yagaji, murmushi Rashida tayi had'e da cewa Masha ALLAH aranta kafin tace "Haba aunty, uncle fa nawaje yana jira kin tsaya biyewa tafiyar wannan yaron da sai magrib tawuce baku qaraso ba,"
"Eh munji dai, ai SANNU SANNU bata hana zuwa ko my boy."
Taqarasa maganar had'e da d'aukeshi sannan taqaraso wajen tana d'agawa Rashida gira tana dariya had'e da kallon little tace.
"To ya kikaga yarona?."
"Ba kyau, kuma am jealous." Rashida tabata amsa had'e da wucewa gaba tana dariya.
"Lallai ma maman boy, kawai kice dai jealous d'inne yahana kiga zallar kyan dake zuba anan.?"
Saida suka iso suka shiga cikin motar sannan itama Rashida ta shiga sukabar qofar gidan, bayan sun hau titi sunfara tafiya Dr nura ya kalli Fatima yanda tayi kyau ita da little tamkar ace d'anta ne yace.
"Wow..Masha ALLAH, matar yau kincini tukuici, wannan wankan na takwara dole yahau Instagram, yaro sai kace donsa aka halitto kayan nan na hausawa, gaskiya badon kar ace nayi sonkai da yawa ba da nace maman boy kinfi kowace uwa azamanin nan dacewa da kyakkyawan yaro kamar takwarana."
"Kai uncle to ai wannan zancen naka ga mamansa nan azaune ita kad'ai zata iya fahimtarsa amma nikam yanzu haka nahango yaron daya fishi kyau da komai akan titin nan."
"Jealousy jealousy.."
Fatima tafad'a tana dariya.
"Yawwa maman boy yaufa wajen su ammie zan kaiki kugaisa, tun satin can take cewa na kaiki wajensu kugaisa amma ko yaushe sai namanta saboda abubuwa da sukayi mani yawa, Yauma matar ce tatuna mani ganin Ina shirin tafiya can nida takwara shine nace tafad'a maki kigyara sai muje gaba d'aya, Ina fatan bamu takuraki ba ko?"
"Laaa..uncle wace irin takurawa, ai nima matsayin iyaye suke agareni kuma kamata