Showing 27001 words to 30000 words out of 181864 words

Chapter 10 - Bororoji Compelet Book Document by Mai Dambu .txt

29 Jan 2025

6242

abokin arziki irin Dan Ba'are shi yasan Meye Mohan yake so, shi yasan Meye baya so, gashi Allah yayi mishi farin jinin Yan mata, shi kuma baya da lokacin su.


Sau dayawa Yan mata har kawo kansu suke gurin shi, amma haka bai tab'a burge shi ba, gashi da mugun miskilanci kamar wani Balarabe, ga wani baiwa da Allah yayi mishi na kwarjini, duk lokacin da zai tsaya a gaban ka baka iya koda motsi. Sannan duk da haka baya cin abincin kowa sai na Dadda kakar shi na gurin Uba. Itace kawai yake cin abincin ta. Sai na Chef Hurayyah, wata yar Kasar Libya da ya dauko ta domin cika mishi cikin shi da abincinta. Domin ta iya girki sosai, balle shi da mahaifiyar shi ta girma cikin Larabawa.
Babban matsalar Mohan yana da damuwa amma baya iya gayawa kowa sai Dan Ba'are, TOH shima basu cika zama guri daya na, dan haka yakan zauna yayi ta rubutun shi.


Kafin faruwan Al'amarin da ya same shi, akan ganshi yana yawan zama shi daya ko kuma yayi ta yawo a gonar shi da yake cikin gidan shi, baya cika magana dama kuma halin shine. Wani lokaci kuma zai fito afujajjan ko wanka yake zai fito yana zare idanun shi, mutum me yawan ibada da tsare hakkin Allah sai gashi an wayi gari baya Kaunar jin kiran Sallah, karshe sai dai ya koma daki ya kwanta, ko kuma a sayo mishi wani abun da zai saka shi barci.
Ranar da ya zama mafi muni a gare shi....
Biki ake tsakanin fadar shugaban kasa zuwa inda ake bikin, ko ina ka leka an cika makil, haka aka gama wannan bikin me cike da farin ciki. Kallon shi dan Ba'are yayi sannan yace mishi.
"Muje na kai ka gida" shiru yayi kamar me tunani. Can ya kalli Khalil Ibrahim Dan Ba'are.
"Kace me?"
Ya fada cikin rashin kuzari,
"Muje na kai ka gida" kurawa Dan Ba'are ido yayi, na wani lokaci kafin ya jinjina kanshi.
"Muje" ya kuma nuna mishi hanya, haka ya shiga cikin motar, a sanyayye. Koda ya shiga motar kallon waje yake,.kamar akwai abin da ya manta. Haka kawai ya fara jin kamar ana harbe harbe,. Duk da ya san karan bindiga haka bai hana shi firgita ba, har yana faɗin.
"Taka motar zasu harbe Ni"
Ya fada da karfi, abin mamaki shi dai Khalil bai ga kowa ba, haka ya tadda motar babu shiri suka bar gurin sai rike kanshi da kunnen shi yake, har suka isa gida.


Aikuwa a lokacin ne yayi karamin hauka, yayi ta fasa duk abinda ya kai hannun shi, haukacewa yayi sosai, koda aka kira likita, daukar shi aka yi zuwa asibiti, da farko yana gane kome yana magana, har yana faɗin zasu nan da bindiga ku bani bindiga na, na harbe su. Haka za ayi ta danneshi ana mishi allura.


Tun daga lokacin ya daina himm balle humm, baya magana kuma baya fahimtar me kake fada, duk abinda zaka yi sai kayi babu wanda zai ce maka ga abinda yake so. A hankali iyayen shi suka manta dashi, domin yana cika sati biyu zuwa uku, suka ajiye batun shi. Suka saka duniya a gaban su. Hatta yan uwan shi babu wanda ya iya tunawa da shi. Sai dan Ba'are, shima dole ya barshi sabida aikin da yake fama dashi.


Dan haka baya nan kawai sai jin labarin yayi a gurin Hajiya Safiya ta gaya mishi ai an maida Mohan Maradi, shima dalilin da ya sani sabida ya shiga cikin gidan nan ya nufi shashin Mohan, aka ce mai baya nan,. Koda ya nufi gurin Firaminista yace ya fita baya son jin sunan Mohan, itama haka Hajiya Latifah, dole ya nufi Hajiya Safiya ita ta gaya mishi ai Mohan an maida shi can, dan haka akan lokaci ya iso Maradi. Yaga kofar gidan babu masu kula da lafiyar shi, babu kowa sai yan sanda biyu da sojoji biyu, yana zuwa ya ga yadda gidan yake dama Mohan ya sha bashi labarin irin dukiyar da aka zuba a gidan bai tab'a zuwa ba, dan haka yana ganin yadda gidan yake kawai ya shigar da wani bayanai sai ga shi an rundunar sojojin sama da na kasa, da sauran jami'an tsaron,.masu kula da lafiyar shi.


Haka ba ƙaramin samawa Dan Ba'are nutsuwa yayi ba, dan haka Yasaka aka dauko Hurayyah, da wasu ma'aikata da zasu kula da lafiyar Mohan.


Wannan kenan....


A hankali yake tafiya ya jika jikinshi Jagwaf, a hankali yake rab'e rab'e, duk inda ya wuce sara mishi suke, haka ya shigo cikin falon tare da sake murmushin jin dadi, duk ma'aikatan gidan suka fito suna kallon shi, sunkuyar da kai yayi tare da haurawa sama da gudu kamar zai tashi sama, cikin tsannanin takaici da bakin ciki Hurayyah ta fashe da kuka, kasancewar tunda ta fara mishi aiki basu tab'a samun sab'ani ba, idan suka mishi laifi baya kula takan su, asalima sai ya daina shiga harkan su, kuma basu isa su daina girki ko kula da shsshin sa ba, abu daya yake musu idan suka mishi laifi, shine kara musu kwanaki a saman wanda suke misali idan yana biyan su duk bayan sati hudu ne, zai mai dashi sati biyar, kafin ya basu albashin su, daga baya ya bari sakamakon wani me mishi wanki da ya rasa Kanwar shi sabida bai biya shi akan lokaci ba, dan yayi mishi laifi.


Tun daga ranar idan suka mishi laifi sai ya zuba musu na mujiya. Zama tayi ya ci kuka sosai kafin ta kira Bilal, suka haura zama. Sai da suka dauki hodar da Hajiya Safiya ta bada ana saka mishi, sabida idan ya tirje, idan zasu saka mishi kaya dambe ake dashi kamar za a tashi sama, amma idan ya kama mutum sai ya sumar da kai yake kyale ka, haka ba karamin tashin hankali bane. Shi yasa suna shiga suke hura mishi iskar hodan.


Haka ce ta faru, suna shiga dakyar sha a hannun su, bayan ya musu dukar kawo wuka,sannan suka watsa mishi hodar ya fara barci, ita ta fita Bilal ya saka mishi kaya, sannan ya gyara mishi kwanciyar shi.


Suna fitowa dan Ba'are yana shigowa gidan.
"Barka da zuwa Yallabai"
"Yawwa ina Friend yake?" Ya tambaye su,
"Yana sama, barci yake."
Kallon agogon falon yayi sannan yace musu.
"Akan me zaku saka shi barci a irin wannan lokacin? Ko kunsan cewa bayi da lafiya kara mishi wani cutar zaku yi?"
"Kayi hakuri"
"Akan me zanyi hakuri? Jiya ma haka nazo ban ganshi ba, yau ma haka nazo har na tafi ban samu ganin shi ido biyu ba, me yasa kike saka shi barci?"
"Sir"
D'aga musu hannun yayi sannan ya wuce abinshi,ranshi yana barci dakin shi ya shiga tare da zama a kusa dashi, yana kallon kamilalliyar fuskar shi me dauke da kwarjini, rike hannun shi yayi.
"Friend!" Ya kira sunan a hankali.
"Kana cikin wani irin yanayi, ga Abbinka ce makiya sun sako mishi fitina a gaba" kamar wanda aka tashe shi ya bude idanun shi, kafin ya mai dashi ya rufe.
"Friend ka tashi haka, Mahaifinka yana bukatar ka, duk da bai san kome akanka ba amma yana bukatar ka a kusa dashi" ya faɗa kamar ya zubda kwalla,
Shafa kanshi yayi yaga yadda ya tara gashi yasan shi ba mutum ne da yake son zama babu gashi ba, dan haka ya shiga cikin ban dakin shi ya fara. Diban shaving cream, yazo ya shafa mishi sannan ya koma gefe ya duba jikin shi zuwa maran shi yasan da hankalin Mohan baka isa ganin dan kamfen shi ba, balle kuma jikin shi da yake riritawa.


Haka ya aske a shi tass, sannan ya gyara mishi kwanciyar shi. Kana yayi shi sai da safe. Koda ya sauko damuwa ya shiga saura kwanaki ƙalilan ya koma gurin aikin shi, dan ma sanadin rashin lafiyar yasa an dakatar da Mohan har ranar da zai sami lafiya.


Shafa kanshi yayi yana nazarin abinda ya dace yayi akan Mohan yana son niman Mutum me gaskiya da Amana ya bashi kula da Harkokin lafiyar shi amma gani yake kamar babu wanda ya dace da kula da Mohan sai shi. Toh a ina ya dace a fara nima mishi wanda ya dace. Dan haka a cikin kwanakin da suka rage zai maida hankali sosai gurin niman wanda zai kula da lafiyar shi. Da wannan tunanin ya bar gidan.
***
Washi gari.
Da sassafe Almamoon ya bar gidan, ko karyawa bai yi ba. Abinda ya d'aga mishi hankali, mahaifan shi da yake mafarki dasu, haka ya mugun d'aga mishi hankali, shi yasa yaji gwara ya tafi yasan halin da suke ciki. Tun a hanya yake kuka haka kawai yana jin wani irin yanayi mara daɗi. Har suka isa garin Damagaram.
Daga tasha ya sami abin hawa zuwa gida. Haka kawai jikin shi ke kara sakewa, har ya shiga cikin gidan. Ya hango Innar shi tana sura hatsi.
"Assalamu alaikum"
Sake tabaryan tayi tana me dafe kirjinta.
"Almamoon?" Ya tambaye shi tare da kura mishi ido. A hankali ya taka jikin shi yana wani irin rawa.
"Innah!" Ya kira sunan a hankali,
"Na'am Almamoon"
Ya isa gaban ta tare da fashewa da kuka.
"Ya aka yi?" Cikin kuka ta fara magana,
"Ina Abba? Me yasa ya haife ni tunda yana son duniya tasan Ni? Na gaji sai zagi na ake ana aibanta ni?"


Daga bayan shi yaji gyaran muryan Baba daga daki.
"Baba na" ta juya tana me zare idanu, sakamakon kallon yadda wuta yayi mishi illar, amsa sallamar da yayi ya dakyar, zaman yan bori Almamoon yayi tare da sake wani irin kuka.
"Innalillahi wa'inna ilahirajoun,.dama abinda ya faru da kai kenan, wayyo Allah babana" ya rarrafa da sauri kamar zai kifa akan shi. Sai kuma ya zauna, tare da hade hannun shi,.mik'ewa yayi tare da bude jakar ya shiga zazzage kayan ciki..ya ciro kudin da yake samu a gurin malam Ansar ya juya zai fita.
"Zo nan" dawowa yayi da baya, ya zauna tare da kallon shi.
"Meye zaka yi?"
"Baba magani zan sayo maka"
"Barshi ka bawa Innarka kudin a kara mana a cikin abincin da zamu ci ko?"
Gyada kai yayi tare da sake wani irin kuka, d'aga labulen dakin yayi sannan yace mishi.
"Baba kana son wani abu ne?"
Ya tambaya hawaye na zuba mishi, sake kallon baban nashi yayi sannan yace mishi.
"Ko kana jin zafi ne?"
Murmushi yayi sannan yace mishi.
"Almamoon! Bana jin zafin kome sama da hawayen ka, ka daina kuka bana son ganin kukan ka"
Gyada kai yayi tare da rike rigar shi. Ya wani ja hancin shi, tare Sake shashekar kuka, muryan shi a raunane yace.
"Baba zan fita niman aikin yi ne"
Yadda yake maganar zai d'ago maka da sallar yarinta shi, yana yi yana wani murɗa yatsun hannun shi. Lips din shi sai wani irin rawa yaƙe. Yana kallon Abban shi.


Murmushi yayi sannan yace mishi.
"Karka damu, Allah yana sane damu."


"A'a ko Allah yace a fita a nima don Allah ka barni na fita Insha Allah."
"Kana hauka ne? A kananun shekarunka zaka fita wahala, ai rayuwar mu dan kayi farin ciki muke, bawai dan kayi wahala ba, babu inda zaka"


Kallon su yayi tare da sake baki.
"Toh ni me yasa baku barina nayi rayuwa irin na kowa ne? Me yasa kuka tsani nace zan fita ne?" Ya fada yana ihu, sabida takaici.
Baki daya suka taru mishi, tare da rike hannun shi.
"A'a Almamoon! Karka mana haka, tsoro muke ji kai yaro ne, tsoro muke ji kar wani ya cutar da kai? Ka"


"A'a wannan ba hujja bane, kawai ku bari na koma aikin baba Insha Allah babu abinda zai faru" ya faɗa yana share kwalla,
"Don Allah" ya kuma fada a karo na biyu, haka ya cigaba da rokon su yana kuka,rike hannun shi suka yi tare da cewa.
"Zaka koma makaranta dan shine"
"Insha Allah zan kama kai na, amma don Allah ku barni na tafi aikin kun ji"
"Shi kenan" suka fada tare da kallon shi, basu so amma saboda kaunar da suke mishi yasa suka amince, rike hannun shi suka yi sannan suka ce mishi.
"Don Allah karka bari wani rudin duniya ya rufe maka ido, ka tuna da mu,.muna raye ne sabida kai. Don Allah ka yi abinda ya kai ka"


Gyada kai yayi sannan malam Ya gaya mishi inda zai tafi, a dace.
Cikin farin ciki ya tafi kasuwa da wata ƙatuwar rigar shi irinta Bugaje, sai uban rawanin da ya buga. Da takalmin roban shi, yayi mugun kyau, yana zuwa inda baban shi yake zama yayi musu bayanin waye shi.


Kai shi ruwan chairman aka yi, yayi mishi bayani. Murmushi chairman din yayi sannan ta saka aka mai da shi kan aikin baban shi,


Haka wunin ranar yaki zama a bakin kofar kasuwa, dako ya shiga fafa, duk da bai saba ba amma duk inda ka ganshi yana mugun gajiya, dakyar yake ɗaukar kayan, bai bar kasuwa ba sai dab Magarib ya dawo gida ya basu duk kudin da ya samo, yaci abinci yayi wanka ya sauya kayan jikin shi da tsumar jikin shi, sannan ya kuma komawa kasuwar bayan yayi musu sai da safe.


Kirga kudin suka yi CF dubu biyu, kamar su zuba ruwa a kasa.
"Dakon yayi mishi nauyi halittar shi ba irinta maza bane idan ya cigaba da irin wannan abun." Kura mishi ido tayi sannan tace mishi.
"Wani abu zai faru dashi ko? Ban taba jin haka a raina ba, kamar yadda yake rayuwa cikin maza" ta fada tana share kwalla,
"Addu'a zamu mishi Allah ya kare shi."


...
A kasuwa kuwa cikin dare aka kawo kaya, haka ta tashi yayiwa abokin aikin baban shi bayanin zai tafi aiki, bai hana shi ba. Haka ya nufi kasuwar ya........
Kuyi maneji, wallahi na saka shiririta ne a gabana wallahi 😜🤣 Yawwa masu tambaye account ɗina zasu sayi Aliyu Asadullah gashi nan, 0472282105 Ramlat Abdul Rahman Manga GTBNK...
#Comments!Share!Vote...
#Mai_Dambu,
[7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: *🐂🐂BOROROJI🫀🫀*

~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
BOOK ONE
https://www.instagram.com/batool_spices
Fatima Batool enterprise
Yaji
Ginger and garlic
Onion powder
Pepper soup
Curry
Biryani spices
Mixed spices
Indian spices
Arab spices
Chai masala
Baharat blend
Tandoori blend
Thai masala
Garam masala
Provence
Tea spice
Zobo powder
Gu garzaya Domin samun kayan kamshi na fatima Baool Enterprise. Domin samun yajin suyar na naman layya 😋


Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Idris


_Gaisuwa gare ku Masoyan MLM ANSAR! Da Masoyan Mata Maza, Koda yake naga mutum daya tana yin Wancan me tambotsan 😜🤸_


Zafin Nima...


BABI NA GOMA


Fita yayi ya nufi gurin su, tare da gaya niman shugaban yan dakon.
"Don Allah kasan mahaifina ya kone, ko zaka taimaka min na shiga cikin mutanen ka, don Allah don Allah" ya shiga rokon shi tare da jin kamar kwalla zai zuba Mishi.
"Yanzun kai saurayi! Toh shi kenan, Haliru ga dan gidan Malam Sanda nan a yi aikin dashi"
" Toh shugaba, kai saurayi zo nan"
Da sauri ya nufi gurin su, ya tsaya aka ciro buhun alkama suna tambayar shi.
"Zaka iya kuwa?"
"Insha Allah"
Daukar bugun suka yi tare da daura mishi a kafad'ar shi, sai da yaji kamar zai fadi, amma da ya tuna dusa yaga Innar shi take sakawa da sauri ya cira, cikin mugun yanayi da rashin sabo, ya nufi hanyar inda zai ajiye, abinka da kuruciya, sam baya tuna kowa sai Iyayen shi, haka suka yi ta kwasar kayan, har asuba tayi, dake bai da tsarki, tattarawa yayi ya nufi gida, bayan an bashi kudin shi da suka ga yadda yayi aikin ma kara mishi kudi suka yi tare da mishi fatan sauki na Babansa.


Yana isa gida ya zube a gaban Baban shi yana sauke ajiyar zuciya.
"Almamoon! Meye ya faru?" Suka tambaye shi a tsora ce. Cikin sansanyar murya yace.
"Dako" sannan ya ciro kudin ya mika musu.
"Inna Kafadana da wuyana ciwo" ya fada a sanyayye.
"Maza daura ruwan zafi akan wuta, a gasa mishi jiki" inji Baban shi.
"A'a Inna zauna kawai" ya kuma mikawa dakyar ya nufi wajen, ya haɗa wuta, sannan ya daura ruwan zafi, yana zaune sai gyangyadi yaƙe. Har Innar shi ta juye mishi ruwan ta dawo tace mishi.
"Tashi dan arziki irin albarka dan da aka haifa tsiya tana barci ba ta farka ba balle ta rab'e shi"


"Inna muje ki gasa min jiki don Allah" ya faɗa tare da marairece fuska.
"Toh muje"


Mikewa yayi ya shiga dakin shi ta cire kayan shi, ya dauki jallabiyar shi ya saka, sannan ya nufi ban dakin, ya cire rigar shi tare da zama ya juya bayan shi.
"Innah ki shigo" ya faɗa a gajiye, tana shiga ta kalle shi, cikin tausayawa. Hannunta ta kai kanshi ta shafa gamon da ya tufke gashin kanshi a keyar shi, ita kanta gashin sai da Innar ta warware shi.
Tsarki ya tabbata ga Ubangijin halittar farko da karshe, Allahu Akbar. Shi kansa gashin baki ne wuluk, har kasa domin idan ka ce zaka kimanta zai yi wuya.
"Innah don Allah ki saka almakashi ki yanke gashin nan damuna yake,"


"Kul na kuma jin haka daga bakin ka" shiru yayi yana kallon yadda take wanke gashin kafin ga dauki tsuma ta shiga gasa mishi kafad'ar shi, sai lumshe idanu yake.
" Innah"
"Idan ana ban daki ba a magana" shiru yayi, har ta gama gasa mishi jiki, shima yayi wankan tsarki, sannan ya dauki zanin sa ta kawo mishi ya nad'e gashin. Kafin ya wanke tsumar jinin shi. Ya fito tare da kaiwa dakin shi ya shanya.


Sannan ya gabatar da sallah asuba da ya tsare mishi, kafin ya kwanta a gurin, sai barci. Wunin ranar a gajiye yayi shi, shi yasa bai farka na sai uku saura ya tashi yayi alola a gurguje yayi Sallah azhar, yana addu'o'in ya fita gurin iyayen shi ya zauna.


"Sannun ku." Ya fada me jan kwanon abincin, ya fara ci a hankali. Yana gamawa ya tattara kayan kaf ya fita ya wanke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login