Showing 111001 words to 114000 words out of 181864 words

Chapter 38 - Bororoji Compelet Book Document by Mai Dambu .txt

29 Jan 2025

6265

ta kai kanta ba taya zai sami damar lalata mata rayuwa yan matan mu na yanzun basu da kamun kai, gashi nan ya kai ta ya baro ta. Idan aka gaya musu su kame kansu maza basu da amana su ga kamar karya kake musu gashi nan bata wuce ashirin ba amma dubi yadda namiji yayi mata fata fata, wallahi na fi tausayin Yara kananu da ake musu haka sama da yan matan da ake musu wannan aika aikan, meye amfanin zubda mutunci ne? Shi ba aurenki zai yi ba kin je kin bashi jikinki"


"Akwai ƙaddara! Dr ki duba yarinyar mana, dubi fuskarta mana? Dubi yadda gefen fuskar ya kumbura sakamakon dukar da aka mata! Yarinya shekara ashirin, meye tayi mishi? Waye nata ya tab'a yar wani? Kisan yadda fyade yake da ciwo? Karki yi fatan haka ya faru da makiyinki ma balle masoyinki, karki yi fadan wannan mummunar yanayin ta faɗa kan wanda kika sani, wallahi akwai ciwo." Ta rushe da kuka, ta kasa aikata kome,."Dr Bawai muna zargin yarinyar bane, daga Yanayinta ya samu fahimtar halin da ta tsinci kanta amma kuma ai yan matan ne suka zama sai du'a'i,"
Gyada kai tayi zuciyarta yayi nauyi tace musu.
"Muna da y'aya mata, addu'a itace makamin mumuni, Allah ya kare mana su duk inda suke." Tana kallon su, suka gama aikin su tsaf, sannan suka mata sai da safe domin sun tashi aiki. Ita kuma ta Cigaba da lura da Yarinyar.
Sai da ta gama gyara gurin tare da rubuta magani sannan ta shafa mata wani cream kafin ta mike, faduwar da gabanta ya kuma ne yasa ta komawa ta zauna dabas, kuka ya tawo mata, sosai tayi kukan da rabonta da tayi tun ranar da ta rasa abinda ta haifa, mijinta abin alfahari ta, Uban Yaranta abin kaunarta. Kallon yarinyar da ta gama dubawa tayi, sannan ta mike, ta sanya mata ruwa da allurai. Ta gyara mata jikinta. Har lokacin kuka take.


Tausayin yarinyar da kaunar yarinya ya taru a ranta, har kusan uku na asuba, abun sallah ta shimfid'a a dakin da aka bawa Yarinyar, ta shiga gabatar da sallar nafilla. Tana gayawa Allah kukanta. Zata so ta ga iyayen yarinyar nan kuwa?


Waiwaye adon tafiya.


Wato masu iya magana suna cewa munafunci dodo ne, yakan ci ubangidan shi. Bari mu dawo tun daga lokacin da Almamoon ya fara aiki a gidan Mohan. Malik bai tab'a damuwa da shi ba, kuma bai tab'a kallon Almamoon da wata manufa ba zai da ANSAR , ko nace Hisham Waadi Ansar ya faɗa a gaban shi Almamoon mata maza ne, a da abin bai dame shi ba, sai dai yadda suka saba da Almamoon ya fara jin sha'awar shi, har ta kai yana kallon shi ina da zai same shi,duk da dama zaman da yake yana cikin mutanen da suke cutar da Mohan, ta hanyar saka mishi sihiri a cikin abincin shi da ruwan shan shi, zuwan Almamoon kuma sai ya kasa samun nasara akan Yaron, sai ya ma shiga taimaka mishi, a hankali kome ya canza, inda Ansar yayi ta cusa mishi kazaman kudi,. Suka fara abota har yana gaya mishi siririn Mohan.


Sai gashi duk lokacin da Mohan zai yi wani abu kamar a kunnen Ansar, shi yasa bai damu ba, koda Maimunari ta bayyana kanta sai ya zuba ido ya ga gudun ruwan su, yana kuma bincike akan Familyn Mohan, a haka kuma ya samu labarin Hanan, dan haka ya mai da hankalin shi lallai sai sun yi wannan Game din, da taimakawan Malik.


Lokacin da Malik ya tura mishi sakon Mohan yace ya maida Maimunari Damagaram. Tura mishi sakon yayi tare da cewa.
*Nawa zan baka ka kawo min ita Maradi?*


Dariya yayi sannan yace mishi.
_Toh nawa zaka bani?_


*CF Miliyan goma*
Tsaki yayi tare da tura mishi cewa.
_Ni na matsiyaci bane rike kudinka_
*Nawa kake bukata? Zan baka*
_CF miliyan Talatin, sabida abinda kake so ce idan bai maka ba kaje gidan Iyayenta ta_
*Shi kenan ciniki ya faɗa ga miliyan ashirin da biyar sauran idan na iso na dauke ta zan baka shi*
Suna gama cinikin ta, ya tafi kiran Mohan, yana zuwa ya mika key motar shi lafiyarta lau, amma suna barin Niamey, ya fara Surutun motar ta lalace, a hankali dai yayi ta jan abin kamar da gaske, har ya yanke shawarar su tafi Maradi su kwana, ya kuma san yadda ya sakata layinta ya daina aiki, koda suka iso, ya kira Ansar ya gaya mishi, sun iso bai yi tsammanin zai biyo daren yazo ba domin shi ya riga su, isowa garin.


Shi kuma da iya iso kofar gidan, ya kira wayar shi bai dauka ba, ya kuma kira bai dauka ba, dan haka ya shiga cikin gidan, yana shiga ya hango abinda Malik yake shirin aikatawa, kawai yaja wayar da aka hada na receive ya fincika sai da ya watsar da kome na gurin kayan kallon sannan ya nufi dakin duka daya yayiwa Kofar, yana shiga bai tsaya wata wata ba, ya shiga zarga mishi wayar sai da ya nad'e wuyar shi tam tun yana motsi har ya daina motsi.


Jan zanin gadon yayi tare da lullube ta, sannan ya dauke ta. Ranshi na kara b'aci, yana daukar ya koma gaban gawar Malik.
"Hukuncin ka kenan, duk wanda ya tab'a Munnah."


Kaita mota yayi sannan ya dawo ya kwashi kayanta har da wayarta, a yanzun kan babu amfanin tafiya da ita wani gurin, dan haka. Yana kai ta Asibitin ya basu kayanta akan su bata, sannan ya biya kudin kome, ya bar asibitin. Tare da gudun mafaka, domin yasan tabbas za a nime wanda yayi wannan aikin, shi yasa ya cire Maimunari cikin gida har da kome nata, kar case din ya faɗa kanta.
**
Niamey.
Wani irin faduwar gaba ce ya same shi bayan ya gama shirya kome, dafe kirjin shi yayi, bayan ya gama daura hannun Fahad, kallon juna suka yi da Dan Ba'are.
"Ya dai?"
"Beauty tana cikin damuwa?"
"Ko?"
"A zuciyata nake ji!"
Shiru yayi sannan ya dauko ruwan sanyi wanda yayi kankara, ya jefa kafar Fahad a cikin ruwan. Kuka ya fara tare da girgiza kanshi yana mutsu mutsu.
"Yanke mishi wancan yar yatsar" Mohan ya gaya mishi, babu wani tausayi ko imani ya yanke yatsar kusa da ta babban, wani irin gurnani ya ke yana ihu, bayan sun toshe mishi bakin shi.


"Sake yanke ta karshen" inji Mohan, aikuwa Khalil ya yanke yatsar,
"Toh Yanzun gaya min su waye da waye"


"Dumm!!!" Garin Niamey ya dauki wani irin ƙarar me mugun karfi tare da daukewar wutar lantarki a garin baki daya, sakamakon faruwar fashewar.
"Duba ƙarar me?"


Da sauri ya fita, yaji garin yayi wani irin tsit, cire mishi tape din yayi tare da yanka mishi fuska da aska.
"Gaya min me kuka Shirya min?"
"Zan fada zan fada."
"Chief of Army Staff, Attorney general, Minister of defense, Inspector General of Police, tare da Minister of Information, sai Minister of affairs,sune suka shirya juyin mulki, yau Insha Allah. Sannan sun dakatar da babban kwamandan Sojojin sama, domin sun shirya kashe wasu ministocin Babanka, minister Lafiya, minister Ilimi."


Cikin tashin hankali ya kalle shi, bai san lokacin da ya caka mishi wuka ba.
"Wannan ƙarar fashewar jirgin ne?"
"Eh!" Ya fada a wahlarce,
"Shaidanun suna ina?"
"Suna ina?"
"Zasu kashe ka domin sun shirya maka" ya faɗa a wahale,
Bai kula shi ba, yayi waya kafin kace me. Har sun fita, kamar yadda suka zauna suka Shirya. Sharrin su haka suma, suka shiya musu, yayin da suka yi ta bin kowani dan banza suna kamewa, basu sami ministan harkokin waje ba ya gudu..


Ba iya shi ba hatta manyan sojojin da suke da hannu akan abin sun gudu, dan haka suka nufi cikin gari bayan sun saka akan kama, munafukan take aka fitar da wani sanarwan me mugun tashin hankali. Akan duk inda aka samu Mohan da Dan Ba'are, a kashe su. Domin suna da hannun akan hatsarin jirgin sama da aka yi, da kashe ministan tsaron ta akayi, tare da mutuwar jami'in tsaro da aka samu gawar shi a Maradi.


Domin sun yi kokarin yin juyin mulki ne sai sanarwan mutuwar Fasinjoji jirgin sama har da ministocin kasar biyu Dr Khalid Bashir da Dr Al-Amin Sahabi. Ba karamin tashin hankali dan Ba'are ya shiga ba.
"Kai kasan waye ya mutu?"
"Waye?"
"Malik"
"Ya aka yi kasani?"
"Idan bai tafi da Moonah Damagaram ba, Tabbas akwai hadin bakin da suke da ANSAR, kuma nasan zai iya kai mishi ita, abu daya nake tsoro kar ya aikata mata mugun abu, tsoron da nake ji kenan."


"Babu abinda zai faru, Insha Allah."


***
Karfe bakwai na safe ranar da Nijar ta samu yancin kanta Yau ya zamewa wasu iyalan ranar bakin ciki, musamman inda jirgin ya fado, ya kashe mutane da dama bayan fasinjojin cikin dari da ashirin, a nan akayi ta sanarwan mutuwar.


Fitowar Dr Zainab kenan, ta hango Benazir da Yumnah, tare da mai renon su. Da gudu suka tawo kanta.
"Mommy Daddy sun yi hatsarin jirgin sama." Kamar sauran aradu tashi maganar daga bakin su, kafatan ma'aikatan asibitin, suka sunkuyar da kansu, sabida sun ji labarin ita ce dai basu bari taji ba.


Kallon su take kamar wacce ta rasa tunanin ta, a hankali taji maranta yana murɗa mata, lumshe idanunta tayi sakamakon zafin da take ji har cikin ruhinta, mik'ewa take son yi amma ta kasa, haka Benazir ta d'ago ta. Amma ta kuma komawa sai ganin jini suka yi yana zuba daga tsakanin kafaffunta.
"Mommy!!!" Yumnah ta faɗa da karfi, baki daya suka rud'e, domin suma tayi. Haka likitocin asibitin da Nurses suka rufa akanta aka mai da ita dakin gaggawa. Inda aka shiga kokarin rike cikin jikinta.


Amma ina ya rigada ya fita, shima yabi mahaifin shi. Dakyar suka samu ta farfaɗo. Bayan ta koma barci, sannan suka fita.


Bayan kwana biyu.
Tun washi gari da abin ya faru dani na farka, sai dai bana magana da kowa, kasancewar babu wanda yake zuwa gurina. Na tsani kaina da kaina, duk da ina samun kulawa a gurin Nurses sosai, na bar haka da sunan taimako ne kawai.


Ranar da na cika kwana takwas, aka sallame ni, ina shirya kayana. Ta shigo, kallo daya nayi mata na dauke kai domin Nurses din suna gaya min cewa.
"Inji Dr Zainab tana gaishe ki, jikinta babu kwari ne." Ban santa ba, amma kuma ina jin ta a raina, shigowa tayi tare da cewa.
"Maimoon" juyawa nayi na kalle ta, sannan na cigaba da had'a kayana na dauka, ina haki.
"Ajiye drive zai zo ya dauka zo mu tafi"
Kallonta nayi, sai gashi na kasa mata musu a hankali na isa gabanta, ina jan kuka. Jingina kaina nayi a kafadar ta, danne kukanta take amma tabbas akwai al'amari me girma akan Yarinyar.
Haka suka fito sai suka ba da sani irin yanayi kamar yaya da kanwa, sabida dan tsayin su kusan daya ne, yanayin jikin su ma kusan iri daya ne banbancin Zainab fara ce kal, kallon su Benazir tayi da take gaban motar. Ta fito da sauri ta bude musu bayan suna shiga. Sai kallon Maimunari take, kamar tasan fuskarta ta. Haka suka zauna. Sai lokacin kukan Dr Zainab ya fito. Rike hannunta Maimunari tayi, sosai irin na rarrashin nan.
"Queen Bee, akwai kayan Addarki a dakin da ta kwanta ku kwaso keda Rabil"


Cikin asibitin suka shiga tare da kwaso kayan suka fito, a bayan mota suka saka, sannan suka shiga.


"Allah Nagode maka! Alhamdulillahi Ubangiji Nagode maka, Allah ka gafartawa Khalid." Ta fada tana kuka. Kamar ranta zai fita, mijinta abin kaunar


ta, abin alfaharinta. Ya tafi ya barta da soyayyar shi.....
#Mai_Dambu
[8/7, 10:04 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1110873206?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=w9A2MuNtd%2B622l0%2BjIc2ASPfh3Zd6cFPBnC7ssNginYPPoEFUrAQ6F%2BPyB%2FEL3W27mCWwkzGM1DWmbWijxOkDE%2BgKcaqC15YNh%2Bfbe6kK1ewkr6qPiO5FQd5pOlySlZh


🐂🐂BOROROJI🫀🫀


~The Journey of Destiny💔~


Mai_Dambu


Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....


BABI NA ARAB'IN DA UKKU.


Ta bani tausayi. Amma a yadda nake hango tawa rayuwar taya zan fuskanci Mohan? Taya zan fahimtar dashi? Idan na gaya mishi zai yarda dani ko ba zai yarda dani ba? Yanzun na hango abinda Innah take nufi, yanzun na gane dalilin da yasa ta hanani zama a matsayin Mace, yanzun na Fahimci illar da take cikin rayuwar mata.


Ina kallon su kamar masu yanci. Ashe basu da yanci, ina kallon su kamar masu farin ciki ashe kowani dakika na rayuwar su hatsari ne. A haife ka a mace matsala, ka rayu a mace matsala, hawaye ne yake zuba min babu iyaka, dama tana tsoron kar wani mara imani ya min haka ne? Ashe dama can ƙaddara ta a tsare take, dama a shirya min kome nawa daki daki. Daga wannan ƙaddarar sai wata, sai wata.
"Hmm!" Naja wani iska mai zafi, sakamakon isowa wani Mahaukacin gida da zai iya cewa yana bayan gidan Mohan na can Jacader.
"Mommy ko fito" hannunta naji a samar nawa, juyawa nayi na kalle ta, kafin na bude kofar, ina takawa a hankali, sabida har zuwa lokacin gurin bai warke ba, muna shiga babban falon gidan, mutane ne. Yan gaisuwa, ana ganin Dr Zainab, suka rud'e da kuka musamman yan uwan mijinta. Dangin shi, haka ta zauna a cikin su. Zata yi kuka na matse hannunta a hankali ina murzawa. Jinjina min kai tayi alamar tayi shiru.


"Addah muje daki, ki huta" inji Benazir, gyada mata kai nayi. Na bi bayanta muka shiga cikin gidan, dagaske masu ruwa sune da kifi, domin dakin Benazir kamar irin dakin ya'yan Barber's doll ne. Kome na dakin pink da light blue ne, ban daki ta nuna min. Bayan ya shiga ta hada min ruwan wanka, shiga nayi. Na tube kayana. Bayan na zauna cikin ruwan, zafin yana ratsa jikina. Lumshe idanuna nayi ina kara sake ajiyar zuciya, domin dadin da nake ji. Musamman a gabana, domin ji nake kamar an daure ni baki daya.


Sai da na gasa kaina sannan nayi wanka da alola na fito, na samu ta ajiye min doguwar riga, dauka nayi na nufi ban daki, ina sakawa hawaye na zuba min, ina gamawa na fito nayi sallah, kusan kwana uku bana cika barci mai dadi, sai mafarkai. Haka ya tab'a min ciwo na, domin kuwa na fara jin ciwon kai da zazzaɓi, tare da nauyin kirji na. Haka na kwanta tare da kifa kirjina, akan matashin na samu barci mai daɗi.


Kwanakin da suka biyo baya, bani da lafiya sosai, domin sai da aka danganani da asibiti, inda suka maza suka gano Matsalata. Ciwon zuciya ne ya tashi, gashi babu Number wani nawa da ta sani, domin bata bincika jaka na ba.
**
Niamey.
"Yallabai yaran nan kokari kare rayuwarka da ta iyalinka suka yi akan me zasu so kashe ka? WALLAHI daga Khalil har Mohan, babu wanda yake da nufin ya cutar da kai don Allah ka saka a janye batun kashe su da zaka yi don Allah"


Kallon Alkali yayi sannan yace mishi.
"Me nene shaidan ka?"
Laptop din shi ya bude bayan ya kunna mishi daukar da yayi na manyan mutanen da suke jikin shi, take ya gamsu tare da yarda da abinda ya faɗa, lokaci guda ya bada sanarwar ta hanyar mai yaɗa labarai na fadar shugaban jamhuriyar kasar Nijar, akan an wanke su Mohan, sannan kuma an saka duk inda aka samu manyan mutanen nan a kama bayan an sake videon su.


Sannan ya sauke baki daya manyan sojojin kasar, akan za a tura da sunayen wasu. Da za a basu matsayin kuma matasa masu burin kawo cigaba. Sannan ministoci biyu da suka rasu ta jirgin sama za a kaiwa Iyalin su, gaisuwa.


*
Kallon Mohan yayi yana murmushi.
"Tunda kome ya kammala toh ni ba zan kuma binka muyi irin wannan kasadar ba, aure zanyi idan zan mutu na mutu ina da matar da zata min addu'a dan kutumar Ubanka"


Kallon shi yayi ya watsar tare da lallubar wayar shi. Kira yayi cikin Sa'a ta shiga amma ba a dauka ba. Sake gwadawa yayi can aka dauka.


"Addah Mommy ta kaita asibiti tana ta aman jini, amma zasu dawo inji Addah Benazir!"
"Benazir!!?"
"Eh ai kamar su daya da Addana Munah kuma, kullum Addah Munah sai tayi ta kuka tana tari, shine rana na gayawa Addah Benazir, Mommy ta kaita asibiti, sun barni Ni daya na, gashi Daddy baya nan an ce ya mutu a jirgin sama waye kai?"


"Mohan Mamman Nasir Aghali!"
"Wow, joli nom Où es-tu maintenant? "
(Wow, Nice name Where are you now? Wow suna me dad'i, kana ina ne yanzun?"


*Tabdijam yau na hadu da tsinkankiyya* ya faɗa a ranshi,
""Alors où est Niamey, C'est ton nom?" (Ina Niamey, kema ya sunanki
Cikin shagwaɓe ta marairaice murya yace mishi.
"Tout le monde s'appelle Addah, je m'appelle aussi Adda Yumnah"
(Kaga kowa Addah ake ce mishi Ni ma ka kirani da Adda Yumnah) dariya ce ta kama shi tace mata.
"Toh amma ni katoto ne! Amma zan saya miki chocolat, ina Addah Munah?"
"Sunan tafi asibiti" ta faɗa mishi,
" Wani gari?"
"Maradi"
"Gidan waye?"
"Dr Khalid Bashir"
"Ok baban kune Minister na lafiya" a sanyayye tace.
"Eh"
"Bani wayar nan, dama bincike kike yi mata? Sai na gayawa Mommy"
"WALLAHI ba bincike nake ba, wayar ne take ta kara, Sannun Addah Munah, wani ne ya kira."


Amsar wayar tayi tare da cewa.
"Me yasa kika dauki wayar? Ince baki gaya mishi inda nake ba?"
"Kiyi hakuri na gaya mishi, kuma shima yana jin France"
Daka mata tsawa tayi, tare da cewa ta fita,, cillar da wayar tayi tare da jan tsaki.


Kashe wayar yayi yana kallon sunanta, mik'ewa yayi ba gobe ba, yau Insha Allah zai tafi Maradi. Bai tsaya na ya fita ai Dole Jelar shi ya bishi da gudu suka fita.


Karfe bakwai na dare suka shiga garin Maradi, da location na wayar ta, yayi ta bibiyarta har gidan, dakyar aka Barsu suka shiga dan sun ce ma sun zo ta'aziya ne.


Kiran wayar yayi taki dauka, fita yayi zai shiga gidan Dan Ba'are ya rike shi.
"Tana cikin gidan zan shiga naji meye nayi mata"
"Kayi" banza yayi dashi ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login