Showing 18001 words to 21000 words out of 181864 words
our ladies please ku Basu damar koyar da Yaranku insha Allah zaki ji dadin haka, hausawa sunce a rashin tayi akan bar araha! Za a samu wannan damar ce idan kana garin kano a tuntube wannan Number 08147787720 mun gode only Kano sai an gwada akan san na kwarai,*
Sirrin Zuciya...
BABI NA BAKWAI.
Sai da Almamoon yayi musu bayani da irin taimakon da Malam Ansar yayi mishi, sannan ya daura da cewa.
"Bana tunanin kome akan malamina, sannan idan ma za ayi magana ne sai dai ace shi din Kamar Yaya yaƙe min, don Allah ku daina Yaɗa labarin karya akan mu.
Wallahi Billahi azim, malam bai tab'a min kome ba, asalima Alkhairi ne a tsakanin mu, idan nace zan fadi Alkhairin shi yawa ne dashi, dan haka kuyi hakuri. Shima Malam Ansar yayi hakuri. Da bai shiga lamarina ba, haka ba zai faru ba, su kuma masu jin ba dad'i a kaina suyi hakuri." Ya fada tare da sunkuyar da kanshi.
Hannun shi ya had'a a fuskar shi yana kallon yaron, idan ya nutsu yana magana a yangance wallahi sai ka dauka irin yan matan nan ne, Yayi imani da Allah da zai samu hutu fatarshi sai tafi haka kyau da haduwa. Balle kuma ya haɗa sabulai da mayukan shafawa.
Kawai hango Almamoon yake cikin riga doguwa, kamar wanda aka buge kanshi ya girgiza kai yana kallon yaron da kyau. Malamai da sauran mutanen cikin dakin taron suka bashi hakuri, da kuma tambayar shi idan bai yafe ba a dauki mataki.
"A'a ni kam na yafe"
Ya fada tare da niman izinin zai fita, babu wanda ya hana shi, anan malam Ansar yayi magana me kama hankali, tare da nuna musu muhimmancin Almamoon a cikin makarantar idan har suka sake wani abu ya same shi tabbas za ayi ta.
A kasar bishiyar lim ya same shi yayi nisa cikin tunani, dafa kafad'ar shi yayi da sauri ta cire hannun, yana karamin murmushi.
"Yallabai"
"Kaine Yallabai, me yasa ka yafe musu?"
Murmushi yayi sannan yace mishi.
"Suna jin babu dadi ne sabida ni ba kowa bane, kuma ina zuwa aka bani Matsayin da suka jima suna so, ko ni aka yiwa haka zan ji babu dad'i balle kuma su da suke tsofin dalibai na makaranta."
"Na zata kayi hakuri ne dan kawai an baka" dariya ce ya subuce mishi a dan karamin bakin shi. Yace,
"Wai ni din banza? Ni din wofi akwai mutane dai da su din wasu ne, na hakura ne dan bana son tashin hankali, kome ya wuce A bar zancen" ya faɗa bayan ya mike daga kujeran, yace.
"Na gode da taimako, zan koma dakin kwanan mu"
"A'a ban yi niyyar ka koma dakin ku ba, idan kuma kana zargina da abinda aka fada ne toh shi kenan ka bar gidan."
Duk sai yaji babu dad'i, tare kawai baya son takura kanshi kuma baya son takura wani, dan haka kai a kasa yace.
"Nagode"
"Toh ka jirani na kai ka gida tunda nima na gama" ya faɗa tare da tsare shi da idanu, diriricewa yayi ya rasa inda zai saka kanshi tunda yake babu namijin da ya tab'a mishi haka, sai ya saka Mishi jin nauyin Malam Ansar sosai.
"A'a yallabai zan biya ta dakin karatu na."
"Bana son gardama" kasa yayi da ido, baki daya ya rasa me ke Mishi dad'i.
"Toh shi kenan" ya faɗa tare da komawa gefe ya zauna, kanshi a sunkuye. Juyawa Malam Ansar yayi zuwa cikin ofishin su na malamai yaji gulmar shi da ake yi.
"Ni nafi zargin yana bin yaron nan kawai sabida ilmin shi ba wai yadda ake tsammani ba, bayan haka bana da wata manufa akan alakar su."
"Tab! A yadda duniya ta lalace nan ne zaka yi tsammanin haka? Shima munafikin yaro yasan abinda suke kulluwa, ban da haka meye zai dauki yaron jiya ya maida shi gidan shi da babu kowa sai su? Idan mai magana wawa ne majiyin shi ba wawa bane" inji wani malami,
"Zato zunubi! Kuma tunda kuka fara wannan maganar ban saka muku baki ba, amma yana da kyau duk inda kuka ga musulmai ku kyautatta musu zato, domin babu wanda yasan daidai sai Allah, tayi mu da muke fada akan abinda bamu da tabbas mune akan b'ata basu ba, wallahi mu daina kashe wutar gaban mu muna hura na wasu sam Ansar bai da mugun nufi akan Yaron, da yana da shi da tuni ya gwada akan yaran makarantar, kuma duk idan hazikin dalibi yake kowa zai so mu'amala da shi, musamman wannan yaron da muke mishi kallon dan baiwa, don Allah mu wanke zuciyar mu kafin mu fadi Sharrin wasu mu."
"Allahu Akbar, yanzun dama ka iya wannan nasihar kake zaune anan? Baka tafi masalaci ko kasuwa ba? Toh bari na gaya maka ba zan daina yiwa Ansar kallon mutumin banza ba, akan me zai dauke hankalin yaro karami yana jan shi a jiki, yaron nan ko magana kake mishi bai tab'a baka hankalin shi sai idan Ansar yayi mishi magana zaka ga jikin shi na rawa, dan haka akwai abinda suke kullawa wanda babu wanda ya sani sai Allah."
Shigowar Malam Ansar yasa duk suka yi tsuru tsuru, murmushi yayi sannan ya nufi inda ya ajiye kayansa ya dauka, sannan ya juya abinci.
"Ansar Yusuf"
"La karka damu ban ji kome ba" ya faɗa yana lashe bakin shi, sannan ya saka kai ya fita daga ofishin, abin yayi masa zafi, kirjin sa sai zafi take kamar an cinna mata wuta,haka ya nufi gurin Almamoon. Tare da mishi alama ya taso su tafi, kura mishi ido yayi yaga yadda yake tafiya a hankali tare da dafe gefen cikin shi, lura yayi da yadda fuskar shi yake hade kamar baya jin dadi ne. A dame yace mishi..
"Meke damunka?"
Murmushi yayi sannan yace mishi.
"Kasan jiya sun dake ni a cikina, idan na zauna sosai yana mugun min ciwo, nafi son kwanciya"
Ya fada bayan ya bude bayan motar ya kwanta. Malam Ansar ya rufe motar.
"Toh mu wuce asibiti mana"
"Da wa?" Ya tambaye shi a birkice yana zare fararren idanun shi nan,
"Akwai wani bayan kai ne? Ko akwai wani a nan ne ban sani ba?"
Ya tambaye shi yana tsuke fuska, "a'a wallahi bani zuwa su min allura, kawai ka kaini gida idan na kwanta rub da ciki zai dai na min ciwo"
"Bana son shashancin,. asibiti zamu tafi"
"Toh wallahi" yadda ya zuba mishi ido ne yasa shi kasa da kai, kamar wani yaro karami ya fashe da kuka, yana mita.
"Ni nace ba zanje ba ka matsa min lallai naje uwar me zasu min? Ni wallahi ma barin gidanka zanyi na dawo makaranta."
"Toh Allah ya baka hakuri, sai kayi ta zama da ciwo tunda baka son kulawar da za a baka." Shiru yayi yana jin shi amma yaki magana, har suka isa gida. Babu wanda ya kuma magana da d'an uwan shi, yana shiga dakin shi ya saka key tare da kwanciya a saman katifar shi da ya dawo dashi gidan, yayi rub da ciki, kwance. Har dare babu wanda ya kuma jin duriyar dan uwanshi.
Sai washi gari. Ya fito tare da kallon Malam Ansar da yake zaune ya gama shiryawa yace mishi.
"Ina kwana? Ina da test dan haka zan fita yanzun sai an jima" ya faɗa da sauri yana barin gidan.
"Wannan yaron ko aljanu ne suke damun shi, baki daya ya kasa nutsuwa, kana mishi magana zai fita da sauri." Murmushi Baba Mari tayi sannan tace mishi.
"Yaron kuwa bai da matsala idan ka cire rashin maganar shi, amma babu wani abu na aibu a tare dashi,yanayin shi da maganar shi yana min ɗibi da na wata wacce na sani wallahi."
"Ayya! Yawwa Baba Mari kika ce min wata kika zo nima a cikin Maradi, shin kin gane inda take?". Shiru tayi sannan tace mishi.
"Har yau ban same ta ba, sai dai na kasa cire rai da ita, domin ina Ni a jikina zamu hadu, kawai abinda na sani naje inda nake tsammanin tana nan sunce min basu nan, kimanin shekaru goma sha kenan da rasuwar matar, yaron matar ma baya nan shi da matar shi. Ina cikin halin kewa da Kaɗaitaka, amma ganin wannan yaron ya sani jin kamar ina Da sauran dangi a duniya."
Cikin jimami da tausayawa yace mata.
"Kiyi hakuri, Insha Allah zasu bayyana. Na tausaya miki wallahi. Kuma Yar uwanki ce ko?"
Share kwalla tayi tare da kallon kasa.
"A'a Ƴata ce karamar Ƴata ce, kamar wannan Yaron, har da tsayin da yanayin su, kawai shi bakin fata ne ya rabasu kamar yadda kagannin haka take jajjur da ita..wancan tsinannen dabi'ar tasu yasa na rasa ta har abada, nayi kokarin komawa inda suke amma shima aka ce basu nan, na yarda da Allah kuma na yarda da ƙaddara shi yasa na amshi abin hannu bibbiyu, ina kuma mata fatan Alkhairi Allah ya bayyana min ita, dangina kan sunyi min nisa sai dai nasan akwai wasu a iyakar kasar nan."
Ta faɗa tare da zubda kwalla, kamar ba yanzun take murmushi ba.
"Insha Allah, Ubangiji zai kawo miki mafita, shin wacce irin dabi'a ce haka?" Kallon shi tayi kafin ta zauna tayi mishi bayani, jinjina kai yayi tare da hango tsagoron rashin imani domin ban da rashin imani akan me zaka aikata haka. Hakuri ya bata sannan yayi mata sallama. Tare da barin gidan.
Yana isa makaranta, ya hango mutumin nashi dalibai sun zagaye shi, yana musu bayani. Zama yayi a cikin motar, yana kallon yadda dan karamin bakin yake motsi hannun yana bayani da ita, fuskar me dauke da dan karamin gashin baki yayi mishi cass, wani irin farin ciki ne ya kama shi, ya kara zuba mishi ido, lokacin da daliban suka shiga mishi tafi, yana murmushi.
"Ya Allah! Kai ka sanya min kaunar Yaron nan Ubangiji ka sauya min da wata ban da wannan namijin dan haukacewa zanyi." Ya fada a zauce. Kai ina ba zai iya boye sirrin zuciyar shi ba , zai gaya mishi koma yayya ne.
Daga nesa yayi mishi horn. D'ago darara daran idanun shi yayi ya zuba a kan malam Ansar, a hankali ya mikawa wata abokiyar karatun shi littafan shi. Ya nufi motar, yana zuwa ya isa inda Malam Ansar yake zaune ya kalle shi.
"Baka da aji ne Malam?" Murmushi yayi sannan yace mishi.
"Ina da shi mana, kawai ina son nayi maka magana ne, sai kuma nake ganin kamar na haukace."
"Ka haukace? Kamar ya? Bayan gaka a zaune anan din? Toh meke damun ka?"
"Shigo sai na gaya maka"
Shiga yayi yana kallon malam Ansar.
"Ka tab'a ganin mahaukaci ido da ido?"
"Eh mana, na sha ganin su,"
"Toh amma baka tab'a ganin wanda ya kai ni hauka ba?" Kallon mamaki yayi mishi sannan yace.
"Subhanallahi, me yasa kake jifan kanka da miyagun kalamai?"
"Sabida na zare?"
"Kamar Ya?"
"Sirrin Zuciya tace, zan ajiye shi har karshen rayuwata, Don Allah kar ka manta da kayi ta saka zararren malamin ka a cikin addu'ar ka, ba mamaki ko nasani saukin haukar da nake shirin farawa."
"Toh amma ai naga lafiyar ka lau, sannan kuma babu abinda yake damunka" inji Almamoon,
"Eh mana akan idanun ka nake lafiyayye, amma a zahirin gaskiya zararre nake, idan kana jin ana zararre ni ne lamba daya. Don Allah ka sanya ni cikin addu'a ba mamaki nayi katarin samun lafiya amma na haukace sosai."
Dariya Abin ya bawa Almamoon, yayi dariya yayi dariya, shima shagala yayi da kallon yadda yake kyalkyalewa da dariya bai san lokacin da da ya tsinci kanshi da dariya ba, suka tabbata mahaukatan a cikin motar, domin daga Almamoon har Malam Ansar an rasa wanda zai dakatar da wani.....
_#girmamawa.... Zaku yi min hakuri da Uzuri na kwanaki biyar Insha Allah, zan kammala Aliyu Asadullah ne Insha Allah don Allah ku gafarce ni, na san zan saka ku jiran amma Insha Allah idan na kammala, zan baku dogon page ina muku fatan Alkhairi 👏 And wallahi naga comments din Wattpad da vote yayi kasa, Insha Allah idan na dawo toh wallahi zan muku irin na zanen ƙaddara ta ne Yanxun haka yana Okada 700₦ zaka saya da shi da sauran books dina na kuɗi zaku iya samun shi a Okada, so ku motsa idan ba haka ba nima next zan bada a WhatsApp, kuma idan kika biyo ni daga Wattpad wallahi saya zaki yi shi yasa nake baku a free, idan ya koma WhatsApp toh wallahi ina gama book 1 Insha ALLAH zan kai Okada 2 ma haka. So ku karanta kafin na kai inda zan jin karan kuɗi 🤣🤸😛😜🤣😂_
[7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: *🐂🐂BOROROJI🫀🫀*
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
BOOK ONE
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Idris
I'm on Instagram as @s.square_fashion_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=gorfmwut2x22&utm_content=cgl6gfx
_Alhamdulillahi books dina baki daya wanda nayi su na kuɗi suna Okada akwai masu cewa suna bukata basu da Whatsp toh ga dama ta samu ku garzaya Okada na akwai su baki daya a can da sunan RamlatArManga_
Sauyin Yanayi...
BABI NA TAKWAS.
Tsagaita dariyar yayi yana kallon Mamoon.
"Me yasa ka dariya?"
Had'iye dariyar yayi sannan yace mishi.
"Cewa kayi ka zare, shi yasa nake dariya ban kuma ga ta yadda ka zare ba shi yasa"
B'ata rai malam Ansar yayi cikin damuwa yace mishi.
"Da gaske na zare da, wallahi ka bar batun wasa, ina cikin damuwa kuma naji a raina na gaya maka ko zaka taimaka min" ajiye shiririta yayi a gefe guda, sannan ya fuskance shi.
"Ina cikin soyayya mara iyaka, kuma na kasa fahimtar kuskuren da nake shirin aikatawa, shi zaka iya fahimtar dani?"
Murmushi Mamoon yayi sannan yace mishi.
"Ina ga kayi ƙoƙarin fitar da abinda yake ranka ga ita abar kaunar taka, zai fi ka rike abu a ranka kana yawo dashi."
"Kana ganin idan nayi haka babu laifi?" Shiru Almamoon yayi yana kallon shi, kafin yace mishi.
"Babu laifi matukar haka ba zai haifar da matsalolin a tsakanin ku ba"
Kallon shi yayi sannan yace mishi.
"Almamoon, ba irin soyayyar da kake tsammanin bane, SOYAYYA ce wacce duniya zata iya kirana da mahaukaci, Almamoon ina cikin jarabawar so, idan na fitar kyamata za ayi." Ya fada kamar zai yi kuka,
"Idan kace sai duniya ta baka lambar yabo ne akan abinda kake Muradin zaka mutu baka sami abinda kake so ba, rayuwar duniya cike yake da dimauta dan haka ka rufe idanunka, ka gayawa zuciyarka muradinka zaka bi ba muradun wasu ba"
"Almamoon! Ba yadda kake tsammani bane, ina jin tsoron fitarwa ne" ya faɗa a sanyayye,
Bude mota Almamoon yayi tare da cewa.
"Toh ka kashe soyayyar bata da anfani matukar ba zata amfani wanda ake dominta ba, Malam bari na gaya maka tunda nake ban tab'a son wani abu a raina ba, idan kaga ina son abu toh tabbas abin me daraja ne, malam ko da ake surutu akan mu wallahi wai muna mummunan alaƙa, malam da ace mace ce Ni ba zan tab'a baka matsayin masoyi ba, matsayin Yaya ne kake min. Ban tab'a jin ko fadawa yanayin ina sonka ba, kayi hakuri gaskiya na gaya maka, amma ina mutumtaka sama da yadda kake tuna, kai Ubane min, shi yasa tunda naga kana kokarin tsayawa rayuwata ya sani maka kallon Babban Yayana."
Kamar wanda aka watsa mishi ruwan sanyi kalau, abin tausayi jikin shi yaji mugun mugun sanyi. Duk haukar da yake ashe da gaske da sikago yake raye, murmushin karfin hali yayi sannan yace mishi.
"Balle kuma waye zai yi soyayyar jinsin ai haramun ce" yana dariya me mugun ciwo, haka ya fita daga motar suna kallon yadda dalibai suka watse, kowa ya kama gaban shi.
"Almamoon" aka kira sunan shi. Wasu yan mata da samari ne na departmen din su.
"Wai shin kai mace ce ko namiji? Ko dai mata maza ne bamu sani ba? Ai toh ko dai dan daudu ne musu mu duba dan kamfen ka"
Suka fada tare da kwashewa da dariya. Murmushi yayi sannan yace musu. Kallon su yayi na wani lokaci, kafin ya tab'e bakin shi, yace musu.
"Yo ku nan mata ne? Na zata kartin maza ne da sufar mata" ya fadi haka tare da barin gurin, yana. Zunzurutun maganar tayi musu zafi kallon kansu suke kawai cikin tashin hankali.
"Ta ina muka yi kama da maza?" Suka juya suna niman wanda zai ganar musu da cewa basu kama da maza. Dariya samarin suka yi tare da cewa.
"Amma Mamoon dan iska ne, duk duniya ban tab'a ganin mutumin da maganar shi take daidai da amsar mutane kamar Almamoon ba."
Cikin fushi wata yarinya me suna Bara'atu ta kwasa da gudu, ta nufi inda Almamoon yake tsaye zai shiga aji ta janyo rigar shi dai da ya kusan faduwar.
"Kai wai namiji ne?"
"A'a kece a tsaye" ya bata amsa zai shiga cikin aji,
"Dan daudu kawai" ta gaya mishi haka, wata shegiyar dariya yayi sannan yace mata.
"Don Allah waye mai madubi a cikin ajin nan?" Ai kuwa aka samu wata ta mika mishi ya karba a yangance yace mata.
"Ina ga kamar baki tab'a kallon kanki a madubi bane, amma babu wacce ta kai ki sufar maza duk cikin makarantar nan. Mai fuskar maza kawai"
"Banza jaki dan luwadi kawai?" Cak ya tsaya yana kallon ta, kafin ya sake murmushi me ciwo, sannan yace mata.
"Toh nagode, jakar aji" ya fadi haka yana me barin gurin ta, da gaske kalmar ta dake shi, ihu ta saka tana me sake kokarin shigowa ajin dalibai yan ajin suka hanata.
"Kin zage shi ya rama, kin gaya mishi magana ya rama, yanzun ma kin gaya mishi ya kuma Ramawa me kike so ki mishi? Ba zaki hakura ba kenan?"
Wani takaici ne ya kamata, ta shiga ihu tana faɗin.
"Dan luwadi kawai mata maza, mara amfani kai har ka mutu haka zaka kare, kai ba mace ba kai ba namiji ba, dan iska karuwan namiji kawali kawai."
Kifa kai yayi a kan kujerar shi, yana shashekar kuka, sabida kalmomin