Showing 96001 words to 99000 words out of 181864 words
nagode sosai Allah ya bar Zumunci musamman Team din Hajiya Innah da Hajiya Latifah 😁😛😜🤣_
Murmushi yayi sannan ya mike tare da cewa.
"Ba zan iya haihuwar Yara su tashi a wulakance ba, ba zan iya auren macen da bani da ita da ita ba, idan zaki duba alamarina ki duba amma tabbas ba zan iya daukar wannan kasadar ba, Moonah nake so. Kuma itace nake da yakinin zata zame min gata a gurin Yarana gaskiya kenan."
"Mohan ni na haife ka fa? Amma kake gaya min baka son zab'ina?"
"Ammyn ba haka bane baki daya gidan kin watsar damu, kin tab'a tuno sauran yaran ki? Haba Ammyn sauran duk matan da suke su suka aura me yasa ni ba zaki barni na zab'i abinda nake so ba? Dan tana ba yar kowa ba, ni Ita nake so wallahi"
"Mohan ba laifinka bane dama ai Bororoji kowa yasan su da mugun tsafi shi ta maka, dan haka sai na karya da Izinin Ubangiji." Kallonta yayi tare da juyawa ya bar falon domin idan ya cigaba da biyawa Ammyn zuciyar shi zata iya dirowa a kirjin shi. Dan haka ya dauke kai kamar bai ji ba.
Tana zaune a falon tana jiran Premie minister.
***
A babban falon bakin shi sun hadu baki ɗaya.
Chef of Army, Attorney general, Minister of defense, Inspector General of Police, duk sun hadu a falon.
"Yallabai ba zai yiwu Mohan ya dawo bakin aikin shi ba, sabida bamu da tabbacin me ya rike shi na tsawon shekara biyu baya nan ba, dan haka ba zamu dawo dai aikin ba gaskiya."
Kallon shi tayi cike da mamaki, shekara daya kenan yana bin su akan lallai a dawo da Mohan. Murmushi yayi sannan yace musu.
"Zai dawo bakin aikin shi! Matukar ina kan kujerata, tabbas Major Mohan zai dawo idan kun shirya toh idan baku shirya ba, Insha ALLAH nan da wata gudu dai dawo ranar bikin yancin kasa." Ya fada tare da mik'ewa ya barsu a falon. Murmushi suka yi a tare, sannan minister tsaro yace musu.
"Shi kenan tunda abinda ya zab'a kenan a barshi yayi yadda yake so"
Suka fada tare da mik'ewa suma, suna da yakinin lallai dole a dakatar da Mohan da Ubanshi domin babu adalci akan wannan maganar. Taya zasu yarda su bashi aikin da yana zuwa zai fara musu iyayi kamar wanda aka haifa a cikin soja. Kowannen su da abinda yake tsarawa a ranshi.
"Amma nake ga ba wani abu bane dan Mohan ya dawo bakin aikin shi tunda dama ai ba sallamar shi aka yi ba"
"Eh haka ne amma yaron ba zamu yarda ya dawo bakin aikin shi bane domin bai da kirki sam bai dan darajar mu ba, shi yasa."
"Toh lallai dole mu yi abu daya imma mu dakatar dashi imma mu kore shi."
"Bamu da ikon tafiyar da kome sai da Sannun Uban shi."
Da haka suka bar gidan, ran su babu dad'i.
**
Yana shiga cikin gidan ranshi a b'ace tashi mishi.
"Yallabai kaji abinda Mohan yake ciki kuwa?" Wani sabon tashin hankali ya kuma shiga, tare da kallonta zuciyar shi ta gama gajiya da damuwa yace mata.
"Me ya same shi?"
"Wai soyayya yake da yar matsiyata, nayi mishi magana wai ita yake so ita kuma ya zab'a." Wani irin takaici ne ya kuma kama shi ji yaƙe kamar ya dake ta, ko zai sami sassauci.
"Ke da aka tashi miki aure ai ba a miki auren dole ba? Ko an baki ni a dole ne? Babu ruwan ki da rayuwar shi, duk abinda yaga ya dace yayi rayuwar shi ce ita wacce zaki hada ta dashi yaushe zata zauna ta kula da rayuwar shi, dan haka kamar yadda kika gurgunta min rayuwa ba zai yiwu ba ki gurgunta mishi rayuwa, kuma wallahi naji labarin kin yi wani shirme akan yarinyar da yake so zan baki mamaki"
Ya wuce tare da barinta a tsaye bakinta bude, dakyar ta ja kafarta ta bar falon ranta yana b'aci, ita zai ciwa mutuncin akan rayuwar dan su? Wallahi sai ta tayi maganin su dukkan su. Dan haka babu wani abinda ya dame ta, haka ya shirya gobe zata kira Karime.
**
Washi gari da safe.
Ya shigo zai gaishe ta yaji tana waya,abin ya kad'a shi dukda ya fahimci ba halinta bane, amma kuma ta bashi mamaki, dan haka ya gama sauraron ta, kafin ya juya yabar kofarta ya tafi ya shirya bai karya ba, a gidan ya nufi gidan su Dan Ba'are, yana zuwa ya nufi dakin Dan Ba'are yana barci ya dage ya maka mishi duka a cinyar shi, Allah sarki a firgice ya mike, yana sosa gurin.
"Dan iska mara mutunci akan soyayyar ka, na shiga gararin rayuwa meye nayi maka da zaka katse min mafarkin da da nake da Benazir"
"Yarinya ta na zo dauka dan Ubanka dan iska" a fusace dan Ba'are ya wurga da bargon ya mike, dariya Mohan ya saka mishi tare da nuna mishi wandon shi.
"Dan iska rago kawai, da ace kai ne lokacin da Almamoon yaƙe damkata da rungumo ni, tabbas da yanzun ka afka mata, mara mutuncin a mafarki kenan kake barin ruwa ranar da ka sami yar mutane dai an kawo mata dauki, wallhi ka zama me karfin zuciya. Ka daina daura sha'awa sama da soyayyar da kake mata, nasan kana Sonta, amma tsakanin ka da Allah meye ya ja hankalinka akan ta?"
Cikin sanyin da damuwa yace mishi.
"Wallahi kirjinta da k'ugun ta, shine abinda ya fisge ni."
"Kasan me yasa nake son Maimoon? Na farko Addininta! Na biyu haukatar,, na uku gaskiyar ta, kai idan zaka mata wani abu na tambaye ya wallahi zata gaya min, bata iya karya ba. Sannan bata da lokacin kananun magana, ban tab'a ganin suraanta ba, balle har ya d'aga min hankali, amma a baya idan ta rungumo ni, kwana nake ina juyi a gado, domin alamarin da ban mamaki. Dan haka karka so mace domin wani abu bata na jikinta kaso ta domin Allah. Taso min ita zamu tafi."
Wucewa ban daki yayi tare da gyara jikin shi, sannan ya fito tare da saka jallabiya, ya nufi cikin gidan, tare da Mohan yana gaya mishi abinda ya faru jiya, ran Mohan ya b'aci sosai. Da sallama suka shigo falon Umma, suka gaishe ta, sannan suka zauna.
"Bari na taso ta, ina ga kamar sallah take." Ta fada bayan ta nufi hanyar dakin da Moonah take. Ina karatun Alkur'ani ta shigo min, sai da na kai aya sannan na kalle ta tare da amsa sallamarta.
"Ina kwana Umma?"
"Lafiya lau, da fatan kin tashi lafiya?"
"Alhamdulillahi!"
"Masha Allah"
Shiru tayi sannan tace min,
"Karki kuma aikata irin wannan kuskuren, karki kuma barin gida domin saurayi, ki bar gidan ku akan namiji kuskure ne babba, dan haka ina me baki shawara karki kuma haka, idan baki hadu da me mutunci ba rabaki da martabar ki zai yi, dan haka karki sake irin haka ya kuma faru." Tayi min nasiha sosai, kafin ta fita bayan ta bani umarni na shirya na fito yana jirana a wajen,ta koma d'akinta ta haɗa min shatara na arziki,sannan muka nufi falon. Inda na same shi yana karyawa, zama nayi ina kallon shi, sosai nake tausayin shi.
"Ki karya"
"A'a na tashi da azumi ne" da sauri ya d'ago kai, ya had'e fuska tare da mik'ewa ya ja min kujeran ya nuna min da idanun shi.
Sunkuyar da kai nayi sannan na taso tare da nufar gurin shi, na zauna. A hankali na fara cin abincin shi da ya tura min flet din, ina ci ina kallon shi.
"Kin tashi lafiya?"
"Alhamdulillahi!" Na bashi amsa,
"Meke damunki yanzun?"
"Kirjina yake min ciwo" na fada ina diban abincin,
"Allah ya baki lafiya"
"Amin Ya Allah Nagode sosai"
"Dame fa?" Ya d'age min gira, murmushi nayi sannan nace mishi.
"Da kome"
"Toh sai kin biya"
"Toh nawa?"
"Duk yadda kika biya"
"Toh lallai kuwa zai yi araha kenan"
Na fada ina kallon shi, murmushi yayi sannan yace min.
"Maza kici babu lokaci ina son na dawo akan lokaci ne."
Haka nayi ta cusa abincin har na dan ji na koshi, sannan na mike na gyara gurin, muka yi musu sallama, dake a mota zamu tafi. Haka yayi ta jana da hira.
***
Maradi.
Haka yayi ta niman Number Mamoon bai same shi so yake yaji da gaske ne mace ce ba namiji ba, toh bai samu layin ba, haka ya tattara ya nufi Damagaram. Bai samu matsala da Inna ba, sai dai kuma. Taki sake jiki dashi kamar baya, dan haka yayi ta damunta ina Almamoon yake. Kasancewar Malam na gida, yasa ta jan bakinta tayi shiru, domin tana fara magana malam zai taso ta a gaba har sai tayi shiru. Haka Malam Ansar ya bar Damagaram. Rai babu dad'i.
Bayan tafiyar shi da awa biyar, muka shigo garin Damagaram, kallona Hammah Mohan yayi kafin yace min.
"Karki wani shirme don Allah,karki yarda ki yi abinda zai bata mata rai, don Allah ki nutsu ki zuba min ido Insha Allah zan baki mamaki zan shawo kanta cikin sauki."
Murmushi nayi domin bana jin zai samu kan Innah a saukakkakiyar harshe, dan haka koda muka isa gidan Baba yana kofar gida. Ina sauka gurin shi naje na zauna, tare da sunkuyar da kaina.
"Maimunari kin dawo lafiya?"
"Alhamdulillahi, Baba ka yafe min" na fada da raunanniyar murya. Alamar xan iya kuka ko wani lokaci.
"Munari baki min kome ba, sharrin shaidan ne da zuciya da bata da kashi, Yaron nan yana sonki sosai,don Allah ki kula da rayuwar shi, samun mutumin da zai damu da kai arziki ne, kin ga tashi ki tafi cikin gidan." Ba dan kome na sai dan kukan da nake sosai. Jan hancina nayi sannan na shiga cikin gidan, ina sallama. Sau daya ta d'ago kanta bata kuma d'ago kai ba, ta cigaba da abinda yake yi.
Zuwa nayi bayanta na zauna tare da kwanciya kamar yadda ta kwanta na rungume ta, ina kuka. Kuka nake sosai. Wanda tunda nake a rayuwata ban tab'a yin shi ba, lumshe idanun ta tayi tare da janye jikinta.
"Da kin san ke wacece ba zaki tab'a d'aga dokar da na saka miki ba, da kin san wacece ba zaki tab'a kallon da namiji ba. Amma kin makaro ba zan tab'a yarda ki auri wanda nayi imani zaki saka shi kuka, kema kiyi kuka ba. Nayi danasanin biye muku kika tafi Jami'a nayi dana sanin barin ki mu'amala da mutane, kinsan me yasa sabida idan kika dan tushenki zai yi wuya ki amincewa kowa, duniyar tsoro zata baki."
"Amma bana kashe maganar nan ba? Ko bana ce kiyo hakuri ba? Ina cewa kika yi tafita tabar gidan yanzun ta dawo kina taso abinda ya wuce shiga Muhammad." Ya nunawa Hammah Mohan hanya, da sauri na shiga cikin dakin na, na dauko taburma yau ce karon farko da ya shigo inda talakawan Baban shi suke rayuwa, kallon yadda nake kaiwa da komowa yayi, har zuwa lokacin ban daina kuka ba.
Abun ya dame shi sosai, dan haka yake ta bina da ido, ina kawo mishi ruwa cikin kulawa yace min.
"Beauty zauna na gode, ya isa haka kukan nan idan ba so kike na fara kukan ba, ya isa haka."
Kallon shi nayi domin ya bani tausayi musamman yadda yake magana a dame kamar zai fasa kuka.
Gyada zama nayi ina kallon kasa, Baba yayi min nasiha ba iya Ni ba har Mohan din, sannan ya mike zai tafi ma raka shi, ina kallon shi ya shiga sauko min da kayana, tare da kawo min cikin gida da kanshi ni kuma ina jikin motar shi yace na tsaya.
Koda ya shigo zuwa yayi ta zube a gaban Innah, ya gurfanar kamar me niman gafara.
"Don Allah kiyi hakuri karki Zafaffa mata, kiyi hakuri karki juya mata baya, tunda ta bar gidan har yau kece a ranta, Innah idan wani yayi mata gori kece zaki fara jin ciwon abin amma ke da kika mata gorin har yau kuka take, Innah da xan iya rabuwa da Maimunari wallahi da na rabu da ita. WALLAHI ba kome nake nima a gurin ta ba, kaunarta da Allah ya daura min ya wadatar dani. Innah kiyi hakuri nasan baki son alaƙar mu amma ni, ina sonta sosai ina sonta kamar na cire zuciyata na bata, Innah wallahi da ki rabani da ita gwara ki zuba min yawan kuɗin da zan biya sadakinta ina son Maimunari ina kaunar Maimunari, ina bala'in kaunarta ina son ta."
Kasa magana tayi tana kallon shi yadda yake magana kamar mahaukaci, abin yayi mugun b'ata mata rai dan haka tace.
"Ba zan baka ita ba, kaje kayi rayuwarta itama tayi nata. Kuna da banbancin rayuwa dan haka kai dan masu kudi ne ita kuma kaga inda muke dan Allah ka fita a rayuwar ta, indai ba wani abu kake bukata ba."
"Kiyi hakuri zan cigaba da baki hakuri amma ba zan tab'a sarewa ba, domin ina son Maimoon ce" yana gama fadar haka ya mike tare da nufar hanyar waje. Ina kallon shi ya fito, yana zuwa bai tsaya wata wata ba ya rike kaina tare da sumbatar goshina..
"Kina raina koda yaushe" daga haka ya koma ya shiga motar shi sauke gilashin motar yayi sannan yace min.
"Kiyi hakuri idan sati biyu ya cika zan zo daukar ki."
Gyada kai nayi ina share kwalla da yake kwaranya a fuskana, daga haka na dauki sauran kayan na nufi cikin gidan, na samu ana rigima tsakanin Innah da Baba, banyi magana ba sai dai tunda na shiga dakin naki kula su,
***
Kallon mijinta tayi cikin kuka, wannan shine karo na sha takwas, zuwan shi rugar Alu. Babu iyayenta babu Sumail Wodaadabe da Kanwar shi.
"Mommy kiyi hakuri mana, sai kuka kike idan shi wancan baki ganshi ba, Baga mu ba. Kiyi hakuri mana kullum muka zo sai jininki ya hawa.
"Benazir baki da hankali ne? Kin san yadda take ji? Sai na sab'a miki mara jin magana" inji Dr Khalid wanda yanzun yake matsayin ministan lafiya.
"Dad gaskiya ba fada mata ai idan da tana son shi ba zata tafi ta barshi ba, dad ban san meye ba but wallhi ba zan tab'a barin Yarona a wani gurin ba ko ku da kuka haife ni ba zan bar muku Baby na ba, haka sai kace babu zuciya a kirjin ki."
"Keep quiet! Dauke ni yayi ranar aurena yayi" tayi shiru wani irin kuka ne ya kuma kwace mata, tana kallon yaranta guda biyu da kafin Allah ya bata su sai da tasha mugun wahala. Benazir da Yumnah.
"He rape me! Sannan ya kashe min mijina, taya zan dauki wannan gagarumin lamari da wasa? Ya rabani da dangina sannan ya ya tafi dani wata duniya inda yayi ta azabtar da ni idan zai kwanta dani, taya kike tunanin zan yafe mishi.
Flashing back.
_mu tafi baya ne ko mu hakura a yafe rayuwar baya Cigaba abin mu domin tafiyar zata kuma tsawaita amma amsar yana gare ku, maybe mu karkare a page guda idan muka leka bayan🤣🤫😜_
#Mai_Dambu...
[8/7, 10:03 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1109232023?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=voxV4XBY%2FnUwatlpE90PRZr0Cb7P5MxReaPUgkD%2Blwo2EZiniMNkAjlJvmFplzmwPYyD1fajKTXN8iPH845IBz%2FlfSldshawiZ5sqrdtJ6HwqYEtA6fZUVlL3erim6GO
🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
BABI NA TALATIN DA SHIDA.
Shekaru ashirin baya.
Cikin sauri da karfin hali suka isa Paris, tun a cikin jirgi zazzaɓi mai zafi ya rufe Aabuh. Musamman nonuwarta da suka cika har suna zuba ta rigar ta, tun a jirgin yake bata kulawa har suka isa, babban birnin Faransa. Tunda suka bar airport din, masauki suka nufa tare da taimaka mata tayi wanka. Tun a ban dakin yake bibiyarta da bukatar shi bata kula shi ba, har suka dawo dakin,anan dai zancen ya sauya salo, a ruwan sanyi Khalid ya rike matar shi. Tun tana yawaita damuwa rashin abinda ta bari har ta daina sai dai idan baya nan zata yi ta kuka.
A hankali kwanakin suka wuce satika suka kawo kai, kafin ce me har wata ta shigo, sai da suka share wata biyar kafin ta samu sauƙin rashin Yaronta. Wani tausayi tana samun cikin daga ranar da ta bude baki tace tana da ciki zai lalace, sai da ta suka shekara uku cif, kafin ta samu cikin Benazir, boye maganar cikin tayi har sai da ya shiga wata biyar kafin ta iya gayawa mutane cewa ciki ne da ita, dama shi kam Khalid ya san da haka.
Bayanta haifi Benazir, ta kuma ɗaukar shekara goma kafin ta haifi Yumnah, daga kanta ne aka ce haihuwa ya tsaya sabida mahaifar tana da matsala. Dai dai gwargwado, Khalid yana da rufin asiri, kuma ga aikin da yake ga kuma wanda aka dauke shi. Wasu asibitotin aikin. alhamdulillah za ace domin rayuwar takai musu, sai dai duk da haka ya tsayawa matar shi tayi karatu me zurfi, a wannan shekarun da suka yi sai da ta had'a degree uku kuma a fannin lafiya, dan shi ya zab'e mata.
Wani aikin Cigaba da kasan Faransa tayi wa ƙasashen da suke karkashin tsarin harshen ta yasa Dr Khalid haduwa da Prince Minister, wanda ya ji dadin ganin Dr Khalid, har yake ganin idan da zai kawo shi kasar su za a cigaba ta kiwon lafiya, shine bayan Dr Khalid ya gama abu da yake shi kuma ya saka aka bincika Mishi waye Khalid a can da irin aikin shi, domin ba zai dauki matsayi ya bashi ba, ba tare da ya san status din shi can ba.
Wannan abin da yayi ya kuma kara Mishi darajar Khalid a idanun shi domin Dakyar aka bashi Khalid, saboda suma turawan Faransa basu so rabuwa da Khalid ba, Khalid ya fara zuwa ya duba kome, sannan ya gyara gidan shi da yake maradi, kafin ya koma can. Yana dawowa ya fara aikin shi Nijar, watan shi huɗu da dawowa Zauna itama ta dawo bayan