Showing 117001 words to 120000 words out of 181864 words
da mik'ewa tsaye, yana huci.
"Karka mana hauka dan kasa mu Ubanka ya wanke ka akan laifin juyin mulki shine zaka zo kana mana ihu, dalla can lusari kawai"
Mohan bai iya musayan yawu ba, amma kuma ya iya kirb'awa mutum rashin mutunci, dan haka bai bari Ansar ya kwace mishi ba ya buga mishi wani naushi sai da ya fadi, zai kuma na shiga tsakanin su.
"Ya isa haka! Kai Hammah Mohan ka cika saurin fushi wallahi da fatar baki yayi maka magana da shi zaka rama ba da duka ba, kai kuma bari na tuna maka. Ni ne gaya maka koda maza sun kare ba zan tab'a sonka ba, bawai bana son ka bane a'a soyayya ce da kai bana ra'ayi, dan haka ka ji daga yau karka kuma gaya min kana Sona"
"Amma. Munnah zan iya zama dake a duk yadda kike! Zan zauna dake a duk yadda kika zo min. Munnah ina sonki babu kishin ki a raina, sonki nake so mai inganci." Inji Ansar,
"Ina son shi, amma haka zan rabu dashi, bana jin ko a mafarki xan kuma so wani bayan shi, dan haka ku fita mana a gida kar ka kuma ganin kafarku" na fada da karfi, haka suka fita a zuciye, bin bayan su nayi da harara. Domin sun bani haushi taya ina fama da Matsalata zasu kara min wani, daga Innah har Baba babu wanda iya min magana sai ma shiru da suka yi alamar dai abin yafi karfin su.
*** A waje kuwa dokuwa suka yi, sosai sai da aka raba su. Ansar ya daki gefen idanun Hammah Mohan, shi kuma Hammah Mohan ya dake shi sai da ya watsar mishi da hakoran gefen hagun shi. Tare da gaya mishi sai ya karya mishi muƙamiƙi.
"Ni kuma ba zan rama ba, amma sai na cusa maka bakin cikin da sai ka kusan mutuwa. Sai na maida mai mara amfani a cikin al'umma Zan sami nutsuwa, ka cigaba da abinda ka gadama, ni nasan kome kai ne baka san yadda kome yake tafiya ba, wallahi ranar da na tashi fitar da kome duniyar ka da duniyar Munnah sai ya jijjiga, sai na maida kai mara amfani ta yadda zaka wayi gari kana fatar da mutuwa kayi da...... Wash...
🙄🤔 Nagode sosai Joindah ba dan ke ba, tabbas da yau bani da wayar charger. Nagode sosai🤝
#Mai_Damby
[8/7, 10:06 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1111755716?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
BABI NA ARAB'IN DA BIYAR.
Kai Mishi duka Mohan yayi, Dan Ba'are ya rike shi. Ya kuwa fashe da dariya tare da kare kan shi kamar me tsoron duka, cikin fusata ya ce Mishi.
"Dake ni! Idan ka cika dan halal idan kai namiji ne ka tsaya muyi damben niman aurenta! Ka tsaya da kafarka bawai ka koma gefe kana ihu zaka dake ba, lusarin banza dan daudu kawai, mara lafiyar gaba."
"Ban ce Karku kuma min fada ba?" Na fito waje sakamakon hayaniyar su da nake ji, ganin yadda dukkan su, suka samu rauni. Kallon su nayi kafin nace musu.
"Ina cewa kashe ni kuke son yi? Ina ce rayuwata tace kuke bukata?"
"A'a Munnah babu haka, zan tafi zan tafi yanzun nan." Inji Ansar, ya shiga motar shi,.tare da d'aga min hannu. Kallon Mohan nayi yana kallona, juyawa nayi zan koma cikin gida yace min.
"Baki gaya min meye nayi miki ba, wallahi bani da nutsuwa ki gaya min meye na miki idan yaso idan rabuwar ce zan rabu dake wallahil billahi Azim,"
Takowa nayi gaban shi, ina kallon shi.
"Sabida kai, na rasa kome nawa. Sabida kaina ƙaddara ta fada, sabida kai yau nake kuka. Kasan me? Saboda nasan da kanka zaka juya min baya, zaka kore ni a rayuwarka, me yasa zan damu da kaina a kanka? Me yasa ba zan rabu da kai ba? Don Allah ka tafi ka barni ina son sauran farin cikin da ya rage min na hada na rufawa kaina asiri."
Sannan na juya zan tafi, riko hannuna yayi, ya saka a kirjin shi.
"Ji yadda yake bugawa! Ko kallon ki nake bugawar shi na daban ne, balle kuma idan ina jin saukar kalaman ki, ba zaki kashe ni ba. Ba zaki lalata min rayuwa ba, Moonah idan laifi naki ki gaya min wallahi zan baki hakuri kamar haka."
Ya zuba gwiwar shi dukka biyu a kasa.
"Haba Maimunari! Idan yayi laifi ki gaya mishi ke ba abin kunya bane mutum kamar Mohan yana zuba gwiwar shi a gaban ki, meye yayi miki da zafi haka? Idan baki kaunar shi."
"Khalil Ibrahim, kyale ta rokonta nake." Ya fada bayan ya mike, kukan da nake yaci karfina. Kwace hannuna nayi cikin tsiwa da masifar yadda zan rabu dashi na kama fada.
"Toh dole ne! An tab'a soyayya Dol..." Bakin shi na ji akan goshina. Bayan ya rungume ni.
"Ba'a tab'a soyayya Dole ba, kuma akanki ba za ayi ba, Nagode sosai idan na mutu karki min kuka don Allah, kiyi min addu'a."
Daga haka ya bude motar su ya shiga, tare da rufewa bai kuma kallon inda nake ba, bai kuma d'aga kai ya kalle ni ba, asalima kamar bana gurin haka sukayi tafiyar su. Durkusawa nayi a gurin ina kuka tare da shasheka, d'aga ni Innah tayi tana faɗin.
"Indai laifin shi bai girmama har haka ba baki yi hakuri mana ya a sonki yana kaunarki"
"So da kaunar ba zai min rana ba, zai iya gudu na." Kallona tayi tare da rike hannuna.
"Me aka miki Maimunari na?" Ta tambaye ni tana min wani irin kallon tsoro, bakina yana rawa na rufe tare da rike hannun ta daya.
"Innah!!" Jan hannuna tayi har cikin d'akinta, ta kuma zaunar dani, tare da durkusawa a gabana,ita kuka ni kuka. An rasa me magana a cikin mu. Sai gyada kai yake tana kara kallona hawaye na zuba a idanun ta.
"Meye ya faru dake?"
"Fy..de.." na fada a tsora ce. Domin nasanta da zafin rai, wani irin riko tayi min tana kuka ina kuka.
"Waye ne haka yayi miki wannan wulakancin? Waye ne ya tozartaki? Waye ne ya cutar dake haka? Me kika musu da zafi? Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun,Ya Allah ka tsayar mana haka. Ya Allah ka rufa mana asiri haka."
Da sauri ta ja kasan gadon ta, ta shiga niman wasu tarkace, fita tayi domin Baba yana ban daki bata zauna ba, can bayan minti arba'in sai gata, daura tunkuya tayi bayan ta wanke saiwowin da tazo dasu, ta saka a tukunyar ta haɗa mishi wuta. Ya cigaba da nuna. Ni kuma ta shigo d'akin. Tace min.
"Bude naga gurin domin nasan ai baki da lafiya."
A hankali na kwanta bayan na cire pant dina, dubawa tayi sannan tace min.
"Kinje asibiti ne?"
"Eh ban san wanda ya kai ni ba, ma dai farka ne na ganni kwance a gadon."
Murmushi tayi, sannan tace min.
"Da sauki sosai. Babu wani matsala zaki iya aure kuma zaki iya alfahari da kanki da darajar ki" kallonta nayi sannan na cigaba da lumshe idanuna hawaye na zuba, sannan ra gyaran min zanina. Tafita,
Tun daga ranar zance ban kuma zaman kasa ba, bana tafiya ba takalmi, gashi ta sani yin azumi uku. Sabida askin da nayi, da kanta tayi ta tattalina, tare da bani. Kulawa na musamman. Haka na share kwana sha biyar.
Ranar na sha shida Mohan ya kuma zuwa, ya samu tarba'n arziki a gurin su, Innah amma a gurina ko kallo bai ishe ni ba,. Haka duk inda na wuce idanun shi ne kaina kai karshe sai da na koma daki da zama.
Shigowa d'akina yayi ina zaune da Laptop, ina duba wasu takarduna. Jan Laptop din yayi yana kallona.
"Na kuma dawowa." Shiru nayi mishi.
"Nazo ki gaya min laifina ne? Ina miki son da babu wanda ya isa yace ga karshen shi! Ina kaunarki ainun, me yasa kike bani wahala"
Kallon shi nayi ya zabge ya lalace, gyada kai nayi sannan nace mishi.
"Yanzun nake karanta wani case wai wata ne suna cikin soyayyar su, ita yar manyan mutane ne shi iyayen saurayin talakawa ne, shine suka fara soyayya, karshe dai anyiwa Yarinyar Fyade kuma tana can kwance saurayin taki zuwa sabida yana kishinta. Na baka labarin ne?"
Kura min ido yayi sannan yace min.
"Da zafi sosai, amma kuma gaskiya ina da zafin kishi, zan kuma bincika sosai idan ba ita ta bada kanta ba, zan zauna da ita amma har abada ba zan daina kallonta da wannan abin ba, sabida babu namijin da zai so yana tare da mace a keta mata haddinta, duk lokacin da ka kalle ta xaka na tuno da abin da ya faru, shin zata iya zama da kai ko zata na bin saurayin da yayi mata fyaden a karshe ma zaman ba zai yi dadi ba, sabida zargi ya shiga."
Kafe shi nayi da ido, tabbas Mohan iya gaskiyar ya gaya min, dan haka bakina a laikum na rabu dashi.
"Ni kuwa idan ina son mutum gani nake ko a gidan karuwai yake zan zauna da shi, idan dan ta'adda ne ma zan zauna da shi sabida kaunar da nake mishi. Mohan Mamman Nasir Aghali,kayi hakuri baka tab'a min laifi ba, sai dai ba zan tab'a aurenka bane, kayi hakuri da ban gaya maka akan lokaci ba, akwai abokina na Yaranta shi nake son aura."
Juyawa yayi ina ganin kamar ma tangadi yake, oho mishi can ya kare kalau. Haka na cigaba da zaman d'akina, na bashi labarin abinda ya faru dani ya gaya min ba zai iya zama dani ba, toh me zan mishi. Dan haka ya tafi yayi rayuwar shi nayi nawa.
***
Allah ne ya maida shi gida lafiya, amma yana fita a motar ya fadi, domin kirjin shi tayi mishi nauyi, haka aka dauke shi zuwa Asibiti. Yana faɗin.
"Maimunari! Maimunari!! Maimunari!!!" Kira yake yana kara kira.
"Khalil wacece Haka?"
"Yarinyar da tayi jinyar shi ce, ban san karfin abinda ya haɗa su ba, sai dai ya bukaci rabuwa da shi."
"Tana ina yanzun?"
"Tana Damagaram"
"Muje" ya kalli Khausar yace mata.
"Mahaifiyar ku tana Dubai,.akan baikon shi, ki kula dashi. Insha Allah zan tawo da yarinyar."
Haka ya fita Dan Ba'are.
Su kuma likitocin suka rufa a kanshi, kallon juna suka yi.
"Dr MG zuciyar shi kumbura tayi fa"
"Toh meye abin yi? Idan akwai wani abu ku mishi mana," ta faɗa bayan tana kallon su. Haka suka dukufa akan shi, har sai da ya fara barci suka saka mishi ruwa da allurai, sannan suka fita dashi zuwa VIP 012.
**
Tunda ya tafi sai bani da nutsuwa kuma, kallon Innah nayi tare da ce mata.
"Zan koma gurin aikina."
"Toh ai nima bana son na miki dole ne yasa ni shiru, amma zaman gidan kara miki damuwa yake."
Innah ta koma Innah da na sani a baya, haka muka yi ta hira. Har bayan isha muna tsakar gida, muna cin tuwo miyar danyen kubaiwa,.Khalil yayi sallama, kallon juna muka yi sannan Baba ya mike tare da amsa sallamar shi. Sannan ya fita can kuwa sai gashi ya shigo da yace.
"Muna tare da manyan baki ne shimfida mana babban taburma"
Mikewa muka yi tare da kai kayan abincin daki, aka shimfid'a babban taburma, sannan ya shigo dasu, Ni da Innah muka kawo musu abincin, dukkan su basu ci ba, sai da na gaishe shi sannna yace min..
"Almamoon ko?" Sunkuyar da kai nayi kasa, nace mishi.
"Abbu kaci abincin."
"Toh Almamoon ko Maimunarin Mohan ko?"
Murmushi nayi, tare da mik'ewa na kawo roban ruwa na ajiye mishi, sannan na koma dakin Innah na zauna. Sunci abincin kam ba laifi, kallon Khalil yayi sannan yace mishi.
"Rabona da naci abinci kamar haka ne manta, Allah yasa Maimunari ce tayi girkin"
Kallona Innah tayi tare da sake murmushin jin dadi..
"Kinga da ban ce kizo kiyi aikin tare dani ba, da babu yadda za ayi shugaban kasa ya yaba miki domin sai nace girkina ne"
Murmushi nayi bayan sun gama aka kira mu, zuwa muka yi na zauna.
"Maimunari bansan wani irin kaunarki Mohan yake ba, amma nayi imanin da Allah zai iya rasa rayuwar shi akanki don Allah ba dan ni ba, ba dan na isa ba. Kije ki ga halin da yake ciki. Nayi magana da mahaifin ki, yace min ya jima da bawa Mohan ke, amma ina son ku kara daidaita kanku Insha Allah zan dawo da kaina niman auren ki da Mohan. Don Allah Karki dauka dole ce, ko kuma karfin Iko ce wallahi a matsayin Uba nazo nan ba a matsayin shugaban kasa ba, don Allah ki rufa min asiri, duk yarana babu me sakani farin cikin da Mohan yake, don Allah ki so shi, yayi rayuwar kunci yayi rayuwar kaɗaici akanki ya fara soyayya."
"Insha Allah zata zo ma, dama yau take cewa zata koma bakin aikinta, idan ta shirya ta biku mana"
"A'a ta shirya a hankali, za a zo daukarta. Kin amince?" Kuka na saka mishi tare da gyada kaina.
Haka suka yi ya farin ciki, Ni kuma aka barni da kuka, bayan ya cika mu da Alkhairi, muka ki karb'a sai da ya nuna bafa a matsayin shugaban kasa ya bamu ba, a'a a wanda ya zo niman yardarmu Yar da tafi kowace ya Daraja yazo niman, yazo ne a matsayin mai nima kuma ya samu, dan haka nashi Alkhairi ne tsakanin mu, shi ba kowa bane. Haka suka tafi rarrashina Innah da Baba suka yi tayi.
Dakyar na hakuri tun asuba na gama hada kayana, ina karyawa aka ce ga mai kai ni Niamey yazo..tsoron abinda ya faru ya sani kin binshi.
"A'a airport zan kai ki,daga can kuma ai jirgi zaki bi." Shine na samu nutsuwa. Na bi shi muka tafi.
Karfe goma yayi min a asibitin,mik'ewa Radiyah tayi tana faɗin.
"Yau duk yan uwanmu zasu zo, sabida ke Hammah Mohan yake kwance don Allah karki juya mishi baya." Murmushi nayi mata sannan na wuce dakin da yake yana barci. Daga bakin kofar nake kallon shi. Sannan na juya tare da cewa.
"Zan tafi, amma zan zo an jima"
"Toh shi kenan."
Apartment din mu na nufa, Na samu Har Rukayyah Hussain Adam ta dawo..
"Yar gata sai yau kika gadaman dawowa."
Dariya nayi sannan na nafi daki na samu a gyare wanka nayi na ci abincin da ta kawo min, muka shiga hira kamar babu gobe.
Da la'asar liss muka nufi asibitin bayan mun yi sayayyan kayan dubayya, sannan muka nufi cikin asibitin, yan uwan shi da mahaifiyar shi sun cika dakin. Rukayyah ce ta samu shiga, ban iya shiga ba.
"Hammah Mohan ya jikin ka?"
"Da sauki kawarmu" ya faɗa a sanyayye, yana kallon kofar, ido biyu muka yi dashi na juya tare da barin kofar, sunkuyar da kai yayi yana sauraronta.
Garin na bar gurin, na ban gaji wata mata ban sani ba, ina d'ago kai ta kwashe ni da mari, ban yi kasa a gwiwa ba, na rama. Sosai ta shige ta. Cikin ihu da masifa ta yo kaina, daidai fitowar shi, domin yana ganina baya fara kokarin cire karin ruwan, yana fitowa yan uwan shi suka biyo shi har da Mahaifiyar su.
Ganin Hanan ta cukume ni, ya sashi shi isowa, yana zuwa ya raba mu, sannan ya kalle ni sosai.
"Meye ya kawo ki? Kin zo ki karasa Ni ne? Ko kin zo ki bata min rai ne? Don Allah fita bana son ganinki." Ya nuna min hanya.
A hankali rukkaya ta tako inda nake tsaye, ina huci.
"Muje Kinji Kawata" ta fadi haka tana me rike hannuna.
"Sai dai kuma kayi kuskure." Ta fada mishi.
Komawa daki suka yi zasu mishi magana ya tsare gida.
"Nairah dauki kayan fruit din nan ki wanke min ki kawo min su zanci"
Kallon shi suka yi baki daya.
"Akan me zaka ci abincin ta, bayan bamu san me ta kulla a cikin kayan abin gaskiya ba zaka ci ba" inji Mahaifiyar shi,
"Idan kina son na rayu barni naci abin da ya fito hannunta, idan kuma mutuwata kike bukata shikenan."
"A'a me yayi zafi. Ci abinka" ta faɗa,
"Toh nagode"
"Hammah Mohan ga abinci na kawo maka" shi da yasan ba haka kawai za a kawo mishi abincin ba, ya zabga mata harara.
"Uban waye yace ki taba ta? Nace ina sonki ne?" Ya daka mata tsawa, yana dafe kirjin shi.
"Daga yau kar na kuma ganin kafarki anan kwashe kayan haukarki kiyi waje dashi"
Had'iye yawun tsoro tayi, tana jin kamar zai dake ta, da sauri ta fita, jikinta yana rawa.
"Amma Mohan ai."
"Ammyn zuciyar shi zata buga idan aka Cigaba da takura mishi." Mikewa tayi da sauri tabi. Hanan,
"Amma Hammah ban ji dadin yadda kayiwa Moonah ba" murmushi yayi sannan yace musu.
"Zata dawo, sai dai haka da na mata banyi dan na wulakanta ta ba, nayi ne domin kar Hanan da Ammyn su cutar da ita, Ba zan boye muku ba, Ammyn da Hajiya Karime suna kokarin mallake ni, da kunne na naji Ammyn tana bukatar a bata maganin da zai saka na bita na rabu da Moonah, idan ba haka nayi ba, zasu iya cutar da yarinyar, amma banyi dan na tozartatta ba, dan haka ku kyale ni dasu, Moonah zata cigaba da zuwa Ni kuma xan cigaba da koranta, sabida su gamsu bana son ta, idan ba haka na zasu illata mu.....
#Mai_Dambu...
[8/7, 8:55 PM] Sidrah❤️: https://chat.whatsapp.com/B50yxHYVIcVHx42qCXkmJ9
🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
BABI NA ARBA'IN DA SHIDA.
"Mun yarda gaskiya da abinda ka fada,.indai haka Ammyn ta koma dai Du'ai amma wallhi Hajiya Karime bata ji dadin ta ba. Karfi da yaji ta lalata mana Mahaifiya, Allah ya isa"
Shikam apple yake gutsira a hankali, yana murmushin jin dadi, yana kara tabbatarwa kan shi da Kudinta ta saya mishi, wani irin gutsira yayi yana kara taunawa kamar mai ciwon hakori, ganin ya shiga shauki dariya suka yi ta mishi.
"Hammah Mohan yarinyar nan ta maka mugun kamu, kan Uba. Dubi yadda yake murmushi sai kace tana gaban ka"
Sake wata lallausar