Showing 60001 words to 63000 words out of 181864 words
kome, kuma ba shi da alaka da Ansar Yusuf. Wancan kuma akan case din su.."
D'aga mishi hannu yayi tare da kafe kofar shiga da idanu.
Sara mishi ya kuma sannan ya juya tare da barin d'akin, yadda kan shi ya dauko zafin nan idan ya cigaba daukar magana ji yaƙe kamar zata fashe shi yasa ya bar asibitin dan ranshi ya fara b'aci.
A hanyar fita suka haɗu da Dan Ba'are.
"Ina mara mutuncin yake."
"Yana dakin motsa jiki"
A fusace ya shiga tare da banke kofar, ya d'aga ruwa yana sha.
"Kai wani irin mutumin banza ne haka? Akan wannan maganar sai kayi zuciya da Yaron?"
" Kasan kanin Ubana ne da zan zauna muku" ya faɗa bayan ya ajiye goran ruwan,
"Banza kawai waye ya kawo batun Iyaye?"
Bai kula shi ba, zama yayi tare da sassauta murya yana faɗin.
"Mohan yaron yana bukatar kulawa"
"And so what?" Ya tambaye shi yana zare mishi ido,
"Jinin shi bai da karfi, kwayoyin sinadirin kulorin da kuma Cocin aka hada ya shaka, Kuma shi sinadarin yana lalata huhu da makogaro, don Allah kayi wani abu a fitar dashi kar ya rasa rayuwar shi, gashi ban san inda Iyayen shi suke ba Ansar Yusuf ne kawai ya san inda yaron ya fito"
A matukar tsoro yake amma kuma a yadda ya nuna rashin mutunci akan fuskar shi sai ka rantse zuciyar shi bata rawa akan abinda aka gaya mishi.
"Wani hali yake ynzn?" Ya tambaya fuska a daure,
Gyara zama ɗan Ba'are yayi Y
Tare da cewa.
"Yana nan dai sai a hankali, ina tsoron kar wani abu ya same shi ne wallahi"
Mik'ewa yayi ya fita tare da nufar dakin shi ya shiga ban daki, wanka yayi sannan ya fito ya bude wardrob din shi ya dauki kayan shi wani riga da wando, rigar ja ce sai wandon baki. Sakawa yayi tare da rufe closet din shi,bai cika amfani dashi ba, kasancewar akwai Abubuwan sirrin shi.
Lumshe idanun shi yayi lokacin da ya gama shiryawa ya fito, yana saukowa tare da nufar inda Dan Ba'are yaƙe. Ya dauke kai Kamar bai ganshi ba. Haka yasa dan Ba'are jan tsaki me ƙarfi. Bai kula shi ba dan yasan ya shaka ne yasa yayi tsaki.
Ko a motar babu wanda ya kula wani asalima dauke kai suka yi dan kowa da jin haushin dan uwan shi, suna isa asibitin Office din likitan suka shiga, suka samu yana duba wasu sojoji.fita suka yi tare da zama.
"Ko zamu je kaga yadda yake?"
Kamar ba dashi ake ba, shiru yayi yana latsa agogon hannun shi.
"Amma kai kan anyi dan iska idan ba zaka ba kayi min bayani mana ka tashi ka share ni kamar wani abu mara daraja" kallon shi Mohan yayi tare da tab'e baki yace mishi.
"Idan kai ne da kafana dauke ni ka kaini"
"Ok ince kai maganar bakin ka kashi yafi shi daraja"
Sanin bai son magana yasa shi dauke kai yana kallon yadda Asibitin yake. Mik'ewa yayi tare da nufar hanyar da zai kai shi cikin asibitin Dan Ba'are yana gaya mishi bi nan can zamu shiga har suka shiga inda Mamoon yake, Ya kai hannu zai bude kofar Dan Ba'are shima ya kai nashi hannun, a lokaci guda suna kalli juna. Tsuke fuska Mohan yayi dole Dan Ba'are ya cire hannun shi, koda ya shiga cikin dakin, rufe kofar yayi yana me jan tsaki.
Jingina yayi da kofar tare da kura mishi ido, tausayin yaron yake ji. Haka kawai ƙaddara ta kawo shi inda bai da muhalli, inda yana da gata babu me tozarta shi, amma yau gashi ana watangaririya da rayuwar shi.
A sanyayye ya mike daga jikin kofar, ya nufi inda yake a Mamoon yake kwance, ya dafa kujeran da yake gaban gadon, tare da juya shi a hankali sannan ya zauna yana fuskarta shi.
Riko hannun shi yayi tare shafa, shi a hankali yana me jin tausayin shi a ranshi, kara rike hannun yayi yana kallon shi zara zara, kafin ya kai hannun fuskar shi. Yana tuno abinda ya faru kafin wannan lamari d'azun da safe. Musamman yadda yake zaro mishi ido, murmushi yayi tare da cewa.,
"Allah ya baka lafiya" ya faɗa a can ƙasar makoshin sa......
*Har na bude data sai naga Yan Baroriji fans 😂 suna nimana ido a rufe kamar ka sace Mamoon na b'oye🙄😠😏 ku gode yau bana jin rashin daraja da ban muku typing ba🙄 Insha Allah na kusan fara muku rashin darajar nan.... Ban sani ba ko zan sami damar typing gobe, idan nayi zakù gani idan bai yi ba toh na tafi leka Gyatuma ce kusan abinka da mai kaka sai anayi ana leka su thank You so much 💓💞*
[7/23, 8:24 PM] Hafsatu Hafs: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
BABI NA ASHIRIN DA BIYU.
Karar bude kofar yasa shi maza ya mike tare da mai da hannun Almamoon, daidai shigowar Dan Ba'are. Wani irin b'ata rai yayi kamar wanda aka zo amsar wani abu a gurin shi.sai wani hura hanci yaƙe. Dariya yaso bawa dan Ba'are amma ya share shi dan bai da lokacin sa. Gashi ya wani tsare inda Almamoon yake sai wani b'ata b'ata rai yaƙe irin me kazo yi?
Ƙoƙarin leka Almamoon yake ya wani tare shi.
"Meye kake nufi?" Ya wani fada yana hararan dan Ba'are,
"Kai bana son Iskanci ka bari na ga halin da dan mutane yake ciki indai na so kake a fara sintiri munyi kisar kai"
Matsa mishi yayi tare da zama yana kallon su,.kai hannu Dan Ba'are yayi zai tab'a Almamoon yayi maza ya dauke kan shi saboda har cikin zuciyar shi yaji haka amma bai wani nuna a fuska ba. Kamar ance ya kalli inda Mohan yake yaga bai wani damu da abin da yake ba, dan haka ya sha jinin jikin shi bai kai hannun ba ya fasa tare da kallon Abokin nashi da yayi mishi mugun sani.
Idan ya fahimtar kamar dai kodayaushe baya son mu'amalar wani da abinda yake tare da shi yanzun sai ya iya cire abin a ranshi yayi mamaki da bai yi haka akan Mamoon dan yasan sun tab'a yin haka akan wata budurwan shi, yarinyar ta makalewa Mohan ba laifi ya fara kula ta, ba wai dan yana son ta ba, kwatsam sai Dan Ba'are ya fara kula yarinyar irin wasan abokin saurayin nan. Har su zauna su sha hira. Tunda aka yi haka a kan idanun shi ya b'ata rai bai ce kome ba. Aka kuma ba biyu bai yi magana ba. Yana tare da su.
Wata talata ya dawo daga tafiya yana shiga gidan su yaga yarinyar me suna Sayyidah tare da dan Ba'are suna jiran shi, yana sauka a motar Mohan ya tattara kashin su ya watsar suna mishi Barka da dawowa, amma fir yaki kallon inda suke asalima kamar bai gansu ba.
Allah Sarki kallon Dan Ba'are tayi sannan tace mishi.
"Ko na mishi laifi ne?" Ta tambaye shi a dame, tab'e baki yayi sannan yace mata.
"Babu abin da kika yiwa ɗan iska" ya faɗa tare da mik'ewa zai bar gurin,
"Ko zaka raka ni na tambaye shi?" Cikin takaici yace mata.
"Dalla can sai kace ba mace ba dan banza ya dawo dan bai kula ki ba sai ki damu karki sake ki fara nuna miki zakalewarki tun ynazun dan wallahi zaki wahala da Mohan."
"Toh uban munafukai zaku fitar min a gida ko sai na watsa ku a waje?" Ya fada yana daure fuskar shi alamar babu wasa da sassauci.
"Mohan yarinyar nan tun safe take jiranka kuma ka dawo ka watsar da ita, ai ko babu kome zaka girmama soyayyar da take maka"
Kallon mamaki yayi mishi kafin ya gyara tsayuwar shi bayan ya zuba hannun shi dukka biyu a cikin aljuhun wando shi domin wandon unifoam ne a jikin shi sai wata shimi ta soja. Kallon yarinyar yayi daga sama har kasa kafin ya mai da idanun shi kan Dan Ba'are.
"Kanin Ubana ka gama?" Ya tambaye shi tare da mishi kallon kurilla.
"Ayya Ayya Mohan wallahi ina kaunarka da dukka zuciyata karka wulakantani"
"Ka dauki wannan abin ku bar min gidana idan kuka sake na fito sai na saka bindiga na harbe yan iska mara sa mutunci irin ku masu cin amanar Abota."
Ya juya a fusace kamar zai wuce dakin, yarinyar kamar zata yi hauka, amma Mohan bai saka shi jin ya hakura ba, Dan Ba'are yayi mishi bayani amma fir yaki kula zancen kuma ba iya ita ba yan mata dayawa sun sha wulakancin shi.
Ajiyar zuciya Dan Ba'are ya sauke lokacin da ya koma bayan shi ya tsaya tare da cewa.
"Kayi duk abinda ya dace, Ni zan tafi dashi kai ka koma bakin aikin ka" ya faɗa tare da mik'ewa yana gyarawa Mamoon fuskar shi da take kara tsutsewa.
Cike da mamaki yake kallon Mohan,
"Amma kuma"
"Na baka umarni a matsayin shugaban ka." Ya fada tare da barin d'akin baki daya domin idan akwai abinda ya tsana ya zauna daki daya da wani, bayan wanda yake tare dashi, shi yasa ya bar dakin domin zuciyar shi ba zai dauka ba.
Kuma baya son ya kaftawa Dan Ba'are tijara, sannan shi wani irin mutum ne da baya son raba kome da wasu,idan zai yi abu akan shi yake tsayawa shi yasa yake jin haushin Dan Ba'are da ya zake akan Mamoon.
Yana fita aka bude mishi mota ya shiga, tare da zama yana kallon cikin asibitin ran shi yana kara b'aci sosai sama da farko. Ko minti biyar bai yi ba daga barin asibitin ya danna wayar shi tare da sakawa a kunne.
"Ku kai shi ya gan shi"
Sannan ya kashe wayar yana cizon lips din shi, tare da lumshe idanun shi, sam bai kaunar zalinci shi yasa har kwanan gobe yake yaki da azzaluman mutane. Bude ido yayi kar akan wayar shi da yake tsiwa.
"Hmm" ya saka a kunnen shi,
"Mohan kai ka turo Fahad da mutumin nan?"
"Hm"
Ya fada tare da kashe wayar ya cillar gefen shi. Yana kallon agogon shi, turawa dan Ba'are sako yayi.
*Kar mu wuce kasa da awa biyu*
_Mohan dan Ubanka Ni ba dan ka bane dan Bante Ubanka idan zaka zo kayi kome kazo idan ba zaka zo ba dan Ubanka ka zauna dan iska mara mutunci ai gwara ka zauna a haukarka dama abinda nake gudu kenan ka samu lafiya ka ishi mutane da mulkin Bala'i, dan kaniyar ka ba zan shirya kome akan lokaci ba sai dai yaron Ya mutu_
Dama yana cike da shi kuma Allah ya bashi sa'a ya gaya mishi maganar banza shi kuma ya tura mishi zungurerriyar wasika. Yana son wannan halin na Dan Ba'are, murmushi yayi sannan ya kuma tura mishi da cewa.
*Nagode sosai ka hada min akan lokaci*
_Toh Kanin Babana ba zan shirya ba ka tsine min na shiga duniya_
*Ko daya sai dai dole kayi yadda nace*
Gajiya yayi da mai da sakon ya kashe wayar baki daya ma, domin idan yabi na Dan Ba'are sai iya saka shi ciwon kai. Lumshe idanun shi yayi yana me daukar wayar ya duba wani sako sannan ya kashe ta Cigaba da lumshe idanun shi. Tausayin Mamoon yake sosai shi yasa ya kasa hakuri akan sawa a kama malam Ansar.
Bayan sun gama waya da Fahad, suka dauki malam Ansar suka fito dashi, basu yi wata wata ba suka watsa shi a cikin motar su. Tare da kawo shi asibitin. Kallon cikin Barrack din yayi jikin shi ya fara tsuma dan ya yi tunanin an kawo shi ne a ci kaniyar shi. Ganin sun wuce Asibiti ya sa shi sauke Ɓoyayyen ajiyar zuciya har suka isa cikin asibitin ward din da aka kwantar da Almamoon suka shiga VIP babu hayaniyar mutane babu cunkoson mutane sai dai Nurse da likitoci. Dakin aka bude mishi ya hango shi cikin kaya blue irinta ta majinyata, ga sumar kanshi da yake Baje a saman matashi,. fuskar shi ya wani irin motsewa sabida karfin gubar da aka shaka mishi. Kallon shi ɗan Ba'are yayi sannan ya turawa Mohan sako ya dawo mishi har suka shiga fada dashi.
"Shigo" ya faɗa tare da kallon Ansar, a hankali ya nemi guri ya tsaya a tsora ce ganin yadda yaron ya koma lokaci guda, tausayin shi da na iyayen shi ne ya kama shi. Bai san lokacin da kwalla ya shiga zuba mishi ba.
"Duk abinda zaka so matuƙar ba zaka ririta duniyar shi ba, toh ba kauna bace k'iyayya ce soyayya bata sakawa a lalata goben wani sai dai ya saka a gyara goben wani. Wannan Yaron karami ne kuma bai damu da kan shi ba matukar zai maka abinda zaka ji dadi me yasa kake cutar dashi? Me yasa baka tab'a tunanin yadda zai ji idan ka mishi wani abu? Ina ga kamar ba laifi bane dan kaso shi amma kuskuren shine tirsassa mishi, kayi ƙoƙarin raba kanka da cutar dashi domin shirun Mohan bai da Alkhairi idan ka sake yayi magana ko ya saba umarnin akan ka wallahi zaka kad'e har buzunka yanzun haka Saudiya zamu fitar dashi nan da awa daya meye amfanin abinda ka aikata? Sannan idan iyayen sun suka ji abinda kai mishi zasu ji dadi kuwa? Gaskiya ka sake lalle wannan ba adalci bane domin masoyin gaskiya baya cutar da abinda yake so"
Hawaye sosai yake zubdawa tare da tausayin halin da ya jefa Mamoon a ciki, kuma kamar wanda aka rufe bakin shi ya kasa magana, dan haka Fahad ya juya dashi kamar kayan wankin suka fita da shi, yana kallon halin da Almamoon yaƙe ciki yau yake nadamar abinda ya aikata domin da bai aikata haka ba tayu da Almamoon yana cikin nutsuwar shi.
Juyawa tare da barin d'akin kicibis suka yi da Mohan, kallon juna suka yi tare da jin wani irin abu a ransu, kowannen su yana jin kamar shi yafi cancanta zama da almamoon ba dayan su ba. Dauke kai Mohan yayi cikin wani isa da jin kai, irin na wuce yadda kake kallona, tare da mai da hankalin shi kan wayar hannun shi.
Wani gani gani yakewa Ansar tare da kallon shi daga sama har kasa.
"Kayi fatan Allah ya bashi lafiya" ya faɗa tare sake murmushin gefen baki, inji Mohan,
"Kai ka isa ka shiga tsakani na da shine? Ok bari kaga ikon Allah" inji Ansar,
Ya faɗa tare da wuccewa bai kuma magana ba, shima Mohan yayi gaba abinshi. Shiga dakin da Mamoon yayi.
"Amma baka isa gida ba ko?" Shiru yayi yana kallon Almamoon, tare da jan kujerar yayi tare da zauna, tare da harde kafa daya akan daya. Yana kallon Dan Ba'are.
"Dama zaman ka nake?"
"Matsalata da kai bakar magana"
"Hmm" ya faɗa tare da wani b'ata rai, yana kallon Dan Ba'are.
"Dan iskan can ya taba shi ne?"
"Kai haba ko kusa dashi bai zo ba"
Mikewa yayi tare da zuba hannun shi a cikin aljuhun wandon shi.
"Zaka iya tafiya"
Ya fada tare da mai da hankalin shi window dake d'akin.
"Amma Mohan me yasa kake katange Ni da Yaron?"
"Sabida na san lafiyar kai na, bai zama dole kowa ya iya sarrafa kanshi ba, so ka bar ganin laifina akan Yaron" cike da mamaki Dan Ba'are yake kallon Mohan idan ya fahimta Mohan yana gaya mishi shi zai iya zama da Almamoon ba tare da ya ji kome a ranshi ba, sannan shi yana da lafiyar da ba.
"Mamman kana nufin ba zan iya rike kai na bane sai na hakewa dan mutane?" Ya tambaye shi tare da kankance fuskar shi.
Murmushin cusa haushi yayi mishi kafin ya zauna yana me daura kafa daya akan ɗaya, ya kalli Dan Ba'are, bayan ya nad'e hannun shi a kirjin shi. Ya d'aga mishi gira.
"Kasan idan ina tare da abu bana son zakewa? So ba wani abu bane dan dai kasan mata basa gabana balle kuma da namiji so kawai manta zan maka bayani"
Ya fada yana kallon Dan Ba'are da idanun shi suka yi jajjur,
"Da wani ne ya zarge ni zan iya mishi kome amma kai Mohan? Kasan Yaron nan namiji ne kuma akan me zan?"
"Ba akan kome bane, naga abinda kake adanawa a ƙwayar idanun ka, Naga chemistry a cikin idanun ka don Allah karka zama kamar wancan Mahaukacin." Ya fada cikin tattausar murya da lafazin, yadda shi kan shi dan Ba'are ba zai ji zafi akan Mohan ba.
"Amma me yasa?" Ya tambaya a sanyayye kamar zai sake kuka,
"Saboda shi Yaron na musamman ne shi din ba kamar sauran Yarana bane, please karka kawo kanka cikin lamarin Yaron" inji Mohan, jikin dan Ba'are ne yayi masifar sanyi yana kallon Mohan, karon farko da yaga ya damu da abu a ranshi.....
#Mai_Dambu
[7/24, 10:23 AM] RamlatArManga: https://www.wattpad.com/1104788648?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=q5d7yQUTBcJ8BdXrs84PaortqtGlVo0sxj15rZPXOdrLAxFvWQgJa%2BsauKrirmCAI6CTRR9OwqxP0GgCqsNrnu%2B64lqmFiENdCsHVuJcnC%2Bq1rbT7zaXMbV7vn44ciXw
🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
_Ban san Meye Ansar ya tsare muku ba kowa sai haushinsa yake ji...😌😠_
Fatan Alkhairi ga Baroriji fans 😂 kuna abinda ya dace!💞💓😍😘Much love....
BABI NA ASHIRIN DA UKKU.
"Mohammed Mamman Nasir Aghali akwai abinda kake boye min" ya faɗa tare da kallon Almamoon da yake barci, dauke kai yayi yana kallon yadda Mohan yake kokarin barin gurin da Dan Ba'are yake. Rike hannun rigar shi yayi cikin damuwa yace mishi.
"Ko akan matsalar shi ne na jinsin mata maz..." Fauce hannun rigar shi yayi tare da nuna Shi da yatsar shi. Kamar wanda aka gaya mishi wani magana mara dadi.
"Karka kuma, kayi abinda na saka bana son kowa ya rab'e shi ne, ni nace ka nisance shi idan kuma ba zaka iya min wannan Alfarmar ba thanks you can go away."