Showing 102001 words to 105000 words out of 181864 words

Chapter 35 - Bororoji Compelet Book Document by Mai Dambu .txt

29 Jan 2025

6263

yayi mata, kasa zama tayi ta kasa tsayuwa.


***
Karfe shida na yamma ya shiga babban asibitin Niamey, wayar shi ya dauka ya kira Khausar.
"Kina cikin asibitin ne?"
"Eh Hammah ina ciki" da sauri ya fito tare da bude motar ya dauke ta, bayan ya rufe motar da kafar shi, ya shiga asibitin da mugun sauri, yana kallonta da yanzun bata da bambancin da gawa, yana shiga suna karo da Khausar.


"Ku kawo gado" ya faɗa da karfi, da sauri aka kawo ya daurata, aka Wuce da ita dakin gaggawa. Fitowa tayi da sauri tana niman wasu likitocin, aka nufi dakin da Moonah take, aka shiga ƙoƙarin ceto rayuwar ta, abin tausayi. Yana zaune yayi zugun. Har kusan awa daya kafin Khausar ta fito, ta zauna akan bencin da yake kai, ta daura kan shi a kafad'ar shi.
"Alhamdulillahi, Hammah mun yi nasarar ceto rayuwar ta, sai dai karta kuma aikata haka."
"Yarinyar tana cikin damuwa ne, kuma ni ne me laifin domin naga ta fita, amma kuma ban san me taje yi ba, ashe maganin mura tayi ta sha."
"Ba laifinka bane! Yanayin kaddara ce, mun yi mata alluran da zai lalata tasirin maganin."


"Nagode kanwata karki bari sauran su sani don Allah"
"Haba ai ciwon ya mace na ya mace ce, dan haka babu wani abinda zai faru, Insha Allah"ta faɗa tare da gyara zama. Suna zaune aka fito da ita bayan an canza mata kaya. Suka kaita wani daki na daban.
Zama yayi a jikinta tun karfe shida, Khausar ce ta kira kanin mijinta ya kawo mishi kome, bayan ta gama aiki ta nufi gida wajen karfe tara, ta kawo musu abincin. Lokacin yana addu'o'in. Bayan ya idar da sallah da ake bin shi. Jin ana turo kofar yasa shi juyawa.


Murmushi suka sakarwa juna, tare da kallon inda Moonah take.
"Hammah Sannun ya jikinta?"
Shafa kan shi yayi yana shafa addu'a, yace mata.
"Da sauki." Ajiye basket din tayi tare da kallon shi, kafin ta durkusa ta fara zuba mishi.
"Karki zuba dayawa, bana son cin abin dan dai naki ne"


Ajiye mishi tayi ya kalla kadan sannan ya dauka yana ci yana kallon Moonah.
"Hammah kana Sonta da yawa, tun ranar da ka gaya mana da Hammah take kiranka ya sani sauya maka daga Yaya zuwa Hammah, haka kawai nake ganin kun dace da juna"


Kallonta yayi sannan yayi murmushi, yana kallon Beauty ɗin shi. Idan ya tuna abinda ya faru kuma sai yaji ranshi ya b'aci sosai, dakyar ya cinye abincin yana ji kamar yayi ta fasa ihu. Domin jin kishinta yaƙe, musamman idan ya tuna yadda ya gansu a yau din nan kamar zasu shigewa juna, ajiye flet din yayi yana jin daci a ranshi.


Hiran da Khausar ke mishi ma kamar dole ce, karshe da taga baya son magana, tashi tayi ta mishi sai da safe, har gurin motar ta ya rakata, sannan ya koma cikin asibitin, tunda ya koma yayi alola, duba jakarta yayi ya hango karamin Alqur'ani, ya fara karatu kasa kasa, har kusan karfe biyu na dare, kafin ya ajiye ya kifa kanshi gefen inda hannunta yake.


Karfe uku saura ya farka sabida ya saba sallah a lokacin, dan haka ban daki ya nufa yayi alola, ya fito. Ya shiga kaiwa Allah kukan shi dan yayi Imani dashi babu me musu maganin taurarrun iyayen su, sai Allah Sarkin sakarakuna.


Yana gurin har karshe hudu, sannan ya nufi masalaci, yana can har aka yi sallah asuba, ya dawo cikin asibitin, yana jin barci amma babu yadda ya iya, dole ya jingina kan shi akan gadon ya fara barci. Karfe bakwai Khausar suka shigo ita da Radiyah, ganin yana barci, ya suka koma tare da rufe kofar.


Abin mamakin basu tashi ba sai karfe ɗaya na rana, sai dai Khausar ta shigo tayi abinda zata yi a hankali, tana gamawa zata fita. Kofar ma a hankali take jan shi.
Yana tashi ana kiran sallah azhar, dan haka ya nufi masalaci. Zama yayi a can sai karfe hudu ya dawo domin lokacin da zai fita sun hadu da Radiyah. Dan haka ya zauna a masalaci, yana dawowa suka gaisa, tare da zuba mishi abincin, yana ci yana mata yan tambayoyi, tana bashi amsa, haka suka zauna har dare sannan tayi mishi sallama.


Wasa wasa sai ga Moonah har ta shafe kwana uku cur, a cikin kwanakin nan kuwa. Idan ka ga Mohan zaka rantse da Allah shi yake jinya domin ya firgita tayi wani zuru-zuru. Sai ka zata shine ai da lafiyar ma. Sam ya manta da kowa sai Moonah, ranar da ta cika kwana uku, likitocin sun taru akanta. Suna tattauwana. A hankali nake bude idanuna. Da nake gani dishi dishi, lumshe su nayi tare da jin wasu irin yarerrika ake a kaina, tsikara min wani abu ya sani cewa.
"Wash" suna cewa "masha Allah" sake lumshe idanuna nayi sannan na kuma buɗe su, wani irin haske na gani ya wuce min. Daga nan ban kuma dawowa hayacina ba,


Sai washi gari na bude idanuna, yana barci cusa hannuna nayi cikin gashin kanshi, ina wasa dashi. Murmushi nayi tare da jin kome na raina da damuwa ta ya gushe, take kuma abinda na kaita ya dawo min kaina, dafe goshina nayi fa jikina babu kwari.
"Hammah" na kira sunan shi, a hankali ya d'ago kai yana kallona fuskar shi a daure.
"Kayi Hakuri" na mika mishi hannuna. Tashi yayi ya zauna a bakin gadon sannan ya rungume ni.
"Mahaukaciya waye ya gaya miki maganin mura yana rage damuwa, kinsan halin da kike jefa zuciyata kuwa? Kece kike kwance ni nake miki jinyar karki kuma min haka domin zan mare ni, ya faɗa bayan ya had'a goshin mu guri daya."


"Kayi hakuri, duk ranar da na rasaka a rayuwata tabbasa mutuwa ce ta dace dani, Hammah na, ina jin tsoro! Ina jin tsoron ranar da ba zaka iya taimaka min da kome ba sai ido, ina ji a jikina abubuwa dayawa suna tunkaro ni, Hammah Mohan kayi hakuri. Idan aka samu akasin ƙaddara karka juya min baya, idan aka samu sauyin ƙaddara karka guje ni, idan aka samu yanayin ƙaddara karka tafi ka barni, Hammah idan ka juya min baya daga zanen ƙaddara ta, wallahi billahi azim mutuwa ita ta dace da rayuwata ba, ba rayuwa ba." Kukan naja tare da kallon shi.
"Hammah! Kasan me wallahi wallahi wallahi mutuwa zan yi, domin kirjina kamar yana ci da wuta , Hammah ina da damuwa. Hammah ina ji kamar banbanci zama fa kai ba, me yasa na shiga rayuwar ka? Me yasa na takura maka. Hammah kayi min addu'a idan mutuwa xan yi na mutu a hannun ka, Hammah ina jin kamar nan gaba kowa zai guje ni! Amma kai! Zuciyata ta ki gaya min zaka guje ni. Hammah me yasa nake kuka? Kawai dan nace sai na zama mace ce ko kuma dan nace ina son kane ya kawo haka! Hammah!" Na kira sunan shi ina jin wani irin tari a daga zuciyata irin me kaikayin nan. Tarin na fara tare da jini,, gogewa nayi tare da kallon shi. Kamar wanda aka dasa shi, ya rasa gane meye yake mishi dad'i. Ji yaƙe kamar baya duniyar baki daya. Tarin ya tafi da karfina. Kwanciya nayi a jikin shi. Ya kuma rungume ni. Goge bakina nayi tare da bude baki zan yi magana, ya rufe min bakin da hannun shi.
"Ya isa haka, zaki yi dariya wata rana ki daina kashe ni da raina."
*HMMM! A KARAN KAINA BANI DA HAUFI AKAN YADDA ALMAMOON KO NACE MAIMUNARI BA ZAN SO TA TAGAYYARA BA! AMMA A YADDA LABARIN YAZO TAFIYAR KADDARA SHINE MADUBIN LABARIN BOROROJI INKIYAR LABARIN CE, AMMA SUNAN LABARIN SHINE TAFIYAR KADDARA! BANCE YA FARU DA GASKE BA. AMMA TOH DAYAWAN MU BAMU SON MUGA JARUMIN LABARI YANA SHAN WAHALA! TOH GASHI TAFIYAR MU NA DAN NISA KUMA KUN FARA SAREWA TAYA ZAKU ZAMU JI RAYUWAR JARUMAR AMMA TOH BANSAN ME ZANCE BA AMMA KUYI HAKURI KUYI HAKURI KUYI HAKURI SHINE ABINDA ZAN CE DA WANDA XAI ZO GABA da wanda zai wuce duk yana cikin tafiyar ƙaddara 💓❤️💞*
*Yau lalaci nake ji wallahi! Wai meye nufin Ku? 🙄 Anya ba zan yi rashin daraja ba toh Shikenan mu hadu nan da sati Uku masu zuwa tunda ba zaku yi voting ba🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️ sai na tafi hutun baba ta gani domin dama hanyar tafiyar nake nima kuma kun ki bani damar haka ba*
#Mai_Dambu.
[8/7, 10:03 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1109544279?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=jfVhi7eN9HoToyWK2IK1Om6sqMtZf1yyZ%2Bne%2FvH0bt9GhZlc9FG1phyPxEZrvJ9chyYJ%2FCfRfvUMri3Zq3pk4FzYixCktvZE2JvpFYpj4wiO1rqTM%2FpB2xa010KtsSOd


🐂🐂BOROROJI🫀🫀


~The Journey of Destiny💔~


Mai_Dambu


Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....


BABI NA TALATIN DA TAKWAS.


"Hammah" hannun shi ya kai kan bakina, tare da lumshe idanun shi. Yana jin cikar kwalla a kwayar idanun shi.
"Ki daina firgita ni, tsorata ni kike. Kina razana ni matukar tsoro nake ji, idan har akwai abinda zaki fada min ya bani tsoro kalmar mutuwa zaki yi! Kina son nayi kuka ne?" Girgiza mishi kai nayi sannan ya shafa gashin gaban goshina yana faɗin.
"Masha Allah good Girl, karki kuma fadar haka ina son ganin ki cikin farin ciki."


Hannuna na zagaye a jikin shi ina jin wani irin yanayi, tare da saukar kwalla daga idanuna.
"Hammah je t'aime" (wato i love You, ina sonka da France)
"Moi aussi Moonah!" (Me too Moonah, nima haka)


"Zan iya samun damar shiga kowani hali amma idan na tuna da ƙaddara ta sai naji kamar ban dace da kai ba, Hammah kai ne kawai kasan yadda nake ji, Hammah kirjina zafi. Hammah zan yi sallah nayi wanka. Ina son ka fitar dani yawo"


Mikewa yayi tare da duba wayar shi, ya nemi Number Khausar, suka yi magana can sai gata da wasu Nurse biyu, ina jingine da jikin shi, suka shigo.
"Matar Hammah Mohan, ko zaki tashi su rike ki." D'ago kai nayi ina kallonta, kafin na maida na rufe idanuna.
"Hammah na zai kai ni ban daki idan yaso sai su min wankan" kallon shi tayi tana kallon Moonah da take kara kifa kanta a kirjin shi. Alama yayi mata da hannun, suka fita da kanshi ya kai ni ban daki. Zai fita na rike hannun shi.
" Ka tayani warware gashin nan yana tsami."


A hankali ya zauna ya warware min gashin sannan ya fara wanke min a hankali. Na tuna lokacin da Innata take wanke min gashin har ruwan kanwa take zuba min, domin ya karkarye yadda ba za a fahimci mace ce ni ba, yau gashi ana wanke min shi. Buga kofar aka yi yayi gyaran murya. Gashin ba wai ya fita bane, amma ganin yadda suka uzura ya fito ya sani koran shi, suka samu kan yake wanke min, taimaka min suka yi na yi wanka bayan gama suka bani towel na rufe kaina, muka fito waje na samu har sun fita. Doguwar riga na saka, sannan na kalli inda suka ajiye min abin sallah, sallah nayi musamman wanda na sani, Hammah na shigowa ina sallama.
"Kwana nawa nayi ina kwance?"
"Kwana uku da wunin yau hudu.". Dama nayi na jiya da yau. kawai na kawo kwanakin da ban yi su ba, tare da niman gafaran Ubangiji, sannan na shiga addu'a Allah ya bayyana min iyayena idan suna raye, idan sun mutu kuma ya jikan su, idan na mu tazo ta kyautatta tamu bayan su.


Ina cikin addu'o'in kuka ya kwace min domin sai lokacin nake jin kome yana zuwa min, haka na zauna na cusa kaina a cikin cinyoyina, zama yayi a taburman yana kallona, sai da na gama kukan ya mika min ruwan sanyi na karba hannuna yana rawa, sha nayi sannan na kalle shi.
"Ya isa haka! An jima zamu tafi yin hoton zuciyar ki, sabida kin fara tarin jini kuma ba son haka yana da illah." Ajiye kofin nayi sannan na ce mishi.
"Toh"
Abinci ya diba min da ruwan tea, na fara sha, ina amsar abincin yana kuma bani labarun ban dariya, sai dariya nake, muna gamawa na kwantar da kaina a kafad'ar shi, ina sauke ajiyar zuciya. Shafa hannun yayi yana jin kamar ya boye ni a kirjin shi.


Bubbuga bayana yaƙe yana bani labarin ban dariya, wani nayi shiru, wani nayi dariya haka dai har yanzu lokacin da aka ce mu shirya a min hoton, shi da kan shi ya kai ni, yana rike da hannuna, har inda za yi hoton. Duk da mun sami mutane. Ganin mu da Dr Khausar yasa aka ce mu shiga kasancewar an san yar Shugaban kasa ce kuma bata damu da matsayin Ubanta ba, tana aikin ta. Uwa uba an san waye mijinta, haka bai saka ta jin wata ce ita, bayan mun gama muka fito, ina jingine a jikin shi.


Kwana na bakwai aka sallame ni, gidan Khausar ya kai ni, na zauna na kara jin dadin jikina. Sannan ya kawo min kome da yayi min har da wani apartment na shi da yake cikin gari, koda muka je apartment din yayi min kyau, ya shirya kome a cikin gidan, juyawa nayi tare da kallon shi.
"Duk nawa ne?"


Lumshe idanun shi yayi sannan ya bude min, dariya nayi domin haka ya sani farin ciki.
"Hammah Nagode"
"Tu mérites mieux" (you deserve more, kin cancanci hakan) Kamar wacce aka samin battery, haka nayi ta mazari a gaban shi, kafin ya tako gaba, ya rungume ni. Murmushi nayi domin abinda nake son yi ne, na kasa shi kuma mutum ne da yake saurin d'ago ka.
"Bana tunanin banza a kanki, sabida ke Uwar Yarana ce, kullum burina taya zan mallake ki, taya zan samu nutsuwa idan na mallake ki, dan haka bani tab'a saka tunanin wani abinki a raina, ke nake so ba kayan jikinki ba. Ko kin manta ke mata maza ce" mintsinin shi nayi ina me ture shi.
"Auchewww, yarinyar nan kin zama kura wannan mintsin fa? Gaskiya sai na rama," fara zagaye falon muke ina dariya, yana bina ina zille mishi. Kafin na gaji na zube a saman sofa ina ajiyar zuciya.


"Beauty! Zaki fara aiki a babban Kotun koli na kasar nan, ni dai don Allah ki rufawa zuciyata asiri domin na ganki da wani wallahi." Hannuna na kai bakin shi ina kallon kwayar idanun shi.
"Insha Allah babu abinda zai faru, ina tare da kai ne saboda ina raye, idan babu kai tabbas ni matacciya ce, ba zan tsallake dokarka ba" hannun shi ya daura a kafadana yana kallon yadda nake, tab'e baki. Goshina ya sumbata. Tare da shafa bakina yana faɗin.
"Insha Allah ina nan zuwa kan ku"
Dukar kirjin shi nayi ina dariya.
"Hammah Allah ya yaye maka," na fada ina dariya, kitchen ya nuna min, ba laifi kome gidan yayi min, gyada kai nake ina dariya sannan nace mishi.
"Amma gaskiya gidan yayi kyau amma yayi min girma, ko zaka iya nima min roommate" jan hancina yayi yana faɗin..
"A yadda duniya ta lalace salon na dauko miki yar iska ta lalata min ke? Tab ba dani ba.". Rike hannun rigar shi nayi ina kallon shi.
"Don Allah fa" na fada kamar zan yi kuka.
"Wallahi Maimoon ki fita idona, babu wanda zan kawo miki ku zauna tare, gidan bai miki bane na sauya miki?"
"Hammah yayi min, amma idan da wani a kusa dani, zan ji dadi da nutsuwa ace babu kowa a cikin gidan, sannan ka duba da kyau bani da lafiya zuciya ta tana ciwo idan ciwon ya tashi waye zai taimaka min kafin wani ya sani? Amma tunda kace ga yadda kake so haka za ayi" na fada a hankali.
"Shikenan, zan duba miki koda dattijuwa ce"
Washe bakina nayi ina kallon shi.
"Nagode sosai" sumbatar goshina yayi yana faɗin.
"Tant pis" (wato Never mind, karki damu" haka ya shiga kitchen tare da daura afro, ina kallon shi, ya ciro kaza a frij. Yana kallona yana murmushi ya shiga aikin shi,
Bayan awa daya zuwa biyu, ya kammala girkin, sai had'iye yawun nake, ina lashe bakina.
"Hammah Abincin nan zai yi dad'i wallahi."
"Gashi ba zan iya bawa mai kwadayi ba"
"Ayya Hammah na, dan sammin dan kadan mana?" Na mika mishi flet, saka ludayi yayi a miyar ya dangwalo miyar ya saka min a saman flet ɗin. Yana murmushi.
"Hammah na, wannan ba halin mutanen kirki bane, samin don Allah wallahi yawuna ya gama tsinkewa."


"Toh daure shi tunda ya tsinke" ya faɗa yana murmushin jin dadi.
"Kayi hakuri kaji, ka ciyar dani kamar yadda tantabara yake ciyar da matar shi." Na fada ina wani tsuma,
Takowa yayi yana kallon cikin idanuna, kafin ya dauki flet din.
"Zan ciyar dake sama da yadda tantabara yake ciyar da iyalin shi, zan gina miki sheka kamar yadda tantabara yake gina shekar matar shi, zan kula da ke kamar yadda tantabara yake kula da matar shi, ki yarda dani a Duk lokacin da ƙaddara ta shigo mana kiyi min kyakyawan Fahimta, ki yarda dani, kiyi min adalci. Ki Fahimce ni, karki yarda shaidan da shaidanun mutane da aljanun su rabamu. Kin ji" gyada mishi kai nayi ina jin kwalla na zubo min. Share kwallar nai ina kallon shi. Amsar flet din yayi ya zuba min macaroni da miyar kazar, zuba min ya dauko ruwa ya ajiye min, sannan ya ciyar dani da hannun shi. Ina koshi na dauki cokalin zan fara bashi ya amsa, tare da cewa.
"Babu ruwanki dani," haka ya zubo na shi ina kallon shi yaci ya koshi sannan ya shiga min hira, kafin yaja hannuna zuwa ban daki yace min.
"Kiyi alola zan tafi masalaci, gidan nan akwai mutane masu haya, kasan shi shaguna ne, sai kuma ko kula da kanki akwai babban falo inda ake hira, ban da shiga harkan kowa. Babu ruwanki da su, kowa yayi harkan gaban shi. Ban hana gaisuwa ki Barka ba, kece kawai bana son ana shigo miki, kuma ban ce ki shigar musu ba, halin dan Adam da wuya karki shiga su sa miki damuwa."


"Insha Allah" na fada ina kallon shi, ban daki na shiga ya fita.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login