Showing 153001 words to 156000 words out of 181864 words
kulawar ta."
"Wannan shine matsalar ta?"
"Eh ina zaton haka!"
"Insha Allah zata zo, ta zauna da ita har ta haihu..
*HMM! BAN SANI BA KO A PAGES DA SUKA WUCE NA RUBUTA CEWA HAJIYAR MOHAN TAGA TSIRAICIN MAIMUNARI DA HAR YA ZAMA ABIN MAGANA AKAI KUNGA WANNAN BOOK DIN FREE BOOK NE! SABIDA KANANU MAGANA INSHA ALLAH VERY SOON ZAN KAMMALA SHI AMMA KAFIN NAN NI MUTUM CE DA NAKE TSAYAWA AKAN MAGANA TA DA KUDI NAKE NIMA DA BA ZAN YI BOROROJI FREE BOOK BA. AMMA DAKE WASUNKU BUTULCI BA WANI ABU BANE A RANSU WAI HAR SUNA MAGANA AKAN ABINDA BAN FADA BA INSHA ALLAH WANNAN ZAI IYA ZAMA NA KARSHE! WALLAHI DUK WANDA YAKE BIN BOOKS DINA KARYA YACE NA B'ATA MISHI LOKACI BAN YI POSTING KODA NA KUƊI NE, HMMM MAJI MA GANI AN BINNE TSOHUWA DA RAI. ALHAMDULILLAHI DA KUDIN KU ZAKU SAYI BOOKS SAI AN GADA MA AKE MUKU POSTING WANDA NA B'ATA LOKACI ANA GAYA MIN MAGANA AI BA WANI ABU BANE DABI'A CE TA DAN ADAM BUTULCI ALLAH YA BAKU HAKURI MASU BASIRA NI DA NAKE RUBUTAWA KU YAFE MIN KAR NA LALACE DAN NACE AN GA TSIRAICI YAR UWARKU MAIMUNARI!*
Dan haka ina ga babu amfanin na cigaba da Posting a WhatsApp.
#Mai_Dambu
[8/14, 8:18 AM] +234 815 778 5691: https://www.wattpad.com/1114877151?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=z9ZOtX44qohxpFic26GH%2Fsn4B4gALffG4rhIwdZgrEOLvK6sIq9knb%2FFjtTVFnjyKKX0u8D3JU062TWZvHMQK0nMVrMzF9JRvFiItDn%2BYZJxkFtAoVCSwYFXCySTxhIc
🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
BABI NA SITTTIN.
"Amma" rufe min baƙi tayi, bayan ta kashe karatun.
"Me yasa baki da Fahimta? Ki godewa Allah Kinji, abinda ya jarabce ki a kai kuma ki kara mishi godiya yana sane dake, karki yarda son zuciya ya saki, fadawa fushin Allah."
Gyada mata kai nayi ina wasa da rigar jikina,sabida ina jin motsin abin cikina,
"Kina fushi da Abie har yanzun ne?" D'ago kai tayi tana kallona,
"Amma ai kina sonshi, tunda gashi har kina zaune a karkashin inuwar shi, kawai kuma shirya kanku ko kuma wannan abin ya shirya ku"
Mikewa tayi sakamakon shigowar shi, tana faɗin.
"Allah ya shirya ki"
"Amin Ya Allah" ya faɗa bayan ya zauna yana kallona, cikin murmushin jin dadi yace min.
"Ga Budurwan da nayi sunan ta, Grace" kallon Mommy nayi wacce ta tsuke fuska,
"Don Allah? Na ganta Abie amma ai babba ce ko" na tambaye shi ina leka wayar hannun shi.
"Eh talatin da biyu fa"
"La ba wata babba bace, toh gaskiya zamu je mu ganta."
"Haba Kinga kuwa baturiya ce, sai a haifa miki kane farare"
Cikin zolaya nace mata.
"Mommy kece babbar kawar Ango, tunda nasan bai da abokai sai ke"
"Karki kuma saka ni cikin shirmenku" ta wuce fuuuu, aikuwa muka saka dariya, sannan nace mishi.
"Abie me yasa ba zaka gaya mata kana Sonta ba?"
"Ina jin tsoron ta ne"
Kallon shi nayi kafin nace mishi,
"Babu wani tsoro kawai ka gaya mata gaskiya, itama tana sonka fa"
"Da tsufana"
"Itama ta tsufa ai"
"Toh Allah ya sa mu dace"
***
Agadaz.
Kallonsu tayi sannan tace mata,
"Kinsan girman baki uwa? Kinsan yadda Allah yake amsa bakin uwa? Da nace duk wanda ya shiga tsakanin Alhaji da Matar shi ban yafe ba shine kika kashe mishi aure yanzun kin dibo jiki akan Nuratu zata bar D'anta ya auri Kanwar Maimunari"
"Nahnah yarinyar da Shegiya ce? Sannan taya ma zan so ya had'a zuri'a da mayu, tunda ya sake ta yaron nan bai kuma samun sukuni ba, dan haka nake zargin kama mishi kurwa tayi"
Kallon tayi na wani lokaci, kafin yace mata.
"Idan har akan Shegiya ce toh ai kuwa Allah ne ya nufa zan haife ku a silar aure, har na auri buzu. Amma duk wanda yake cikin Zuri'ar mu yasan me ya faru a shekaru baya. Hmm Nuratu ki bashi yar ki Jalilah, Allah ya bada zaman lafiya"
"Nahnah wallahi Mohan ba zai zauna da wata mace ba, Maimunari yake so ki saka baki ta barshi ya dawo da matar shi."
"Wallahi ba zai sake ta ba, Insha ALLAH ba zai sake miki yar ki ba na rantse da Allah." Ta fada jikinta na rawa. Cikin takaici Nahnah ta kalle ta, kafin tace mata.
"Dalla rufe min baki, Ni nace kar ku raba yaran nan amma sake baki da imani shine kika saka ya wulakanta yar mutane. Wallahi ki saka ido kiga abinda Ubangiji zai yi dake tunda baki da imani" shiru tayi cikin yanayin na jin haushi domin duk inda taje niman auren Mohan,kin bashi aure ake.
"Ni dai ku taimaka min don Allah"
"Hmm! Allah ya gani ba zan yarda ya maida min Y'a bazawa ba, amma babu yadda na iya tunda Nahnah kin saka baki."
"Toh nagode"
"Nuratu kiyi hakuri"
Kamar mahaukaciya ta fado d'akin, tare da shake wuyar Hajiya Latifah, tana kai mata duka.
"Kun kashe min yarinya na, wallahi sai kun mutu kuma, ba zan yarda ba." Ta fada tare da rufe Hajiya Latifah da duka, sosai ta haukace musu, sai da maza suka shigo aka fitar da ita.
"Wallahi sai na kashe su, tubda suka kashe min Y'a, wallahi sai kashe su wallahi ba zan yarda ba, idan har suka shiga hannuna sai sun mutu."
Haka aka yi ta dambe da ita, cikin kuka Hajiya Latifah tace.
"Yau na shiga uku, meye nayiwa Karime da zata kashe ni?"
"Sharrin da kuka nemi kulawa yar mutane, shine Allah ya maida muku kaidin ku kanku, Alhamdulillahi da abin ya koma kanku. Wallahi Nahnah kin sani abinda ba zan ki ba. Amma da ba zan yarda Mohan ya auri Jalilah ba, yarinyar da tayi jinyar d'anki ma baki kaunace ta ba, sai yar da baki shiri da Uwarta sabida banbancin ra'ayi."
"Kiyi hakuri"
"Shi kenan Nahnah" ta faɗa idanunta yana cika da kwalla, domin Uwa ce ba zata iya mata musu ba, amma wallahi da Latifah ne ba zata tab'a yarda ta bawa Mohan yarta ba. A cikin kankanin lokaci aka shirya kome, haka Hajiya Nuratu ta kira Mohan ta gaya mishi, sunkuyar da kai yayi sannan yace mata.
"Umma ba zan sake ta ba, sai dai har ga Allah wallahi Maimuna nake so, don Allah ki ce karta shige min, karta dame ni. Karta shiga rayuwata. Wallahi zan aureta ne kawai sabida ke da Nahnah da kuma Abba sai kuma Khalil ba zan iya cin zarafin ta ba, domin abotar mu dashi gaskiya ce. Kuma ba zan iya juyawa akan abotar mu ba, ba zan iya cutar da ita ba, dan kamar su Radiyah take. Amma ki bata hakuri domin zuciyata yana gurin Maimuna"
Yana gama fadar haka ya juya tare da barin falon, ita kanta ta san gaskiya ya gaya mata, ita kanta ta tausaya mishi, ta kuma tausayawa yarta, dan haka ta ce mishi.
"Insha Allah zan kokarta na nuna mata matsayinta." Ta fada mishi.
"Nagode sosai" ya mike tare da barin gidan, sannan ta kira Khalil ta gaya mishi, kin yarda yayi da nuna mata gaskiya haka cutarwa ce, domin da a bata mishi abotar shi da Mohan, mutuncin shi da Maimunari take gani ya zube.
Bayani tayi mishi tare da gaya mishi gaskiya ita kanta bata son haɗin, dan haka suna gama wayar ta kira Jalilah ta ci Ubanta da kyau sannan ta gaya mata a abinda yake faruwa. Yar banza dai gata tana ihu da murna, tana faɗin.
"Nice zan auri Ya Mohan! Wayyo Allah na, dad'i kashe ni" ta faɗa tana ihu, takaici da bakin ciki ya sa Hajiya Nuratu ta kai mata duka, cuno baki tayi tana faɗin.
"Ni wallahi ina son shi dama"
"Kaniyar ki da soyayyar yaci kaniyarta, toh shi ba sonki yake ba sakarya kawai."
"Koma meye ni ina son shi" ta fada tana tura baki, dan babu abinda ya dame ta, takaici kamar ya kashe Hajiya Nuratu, domin bata jin a ranta wannan shine hanya bullaliya, abu uku da yake hana mace zaman lafiya a gidan mijinta K'iyayyar Uwar miji, k'iyayyar dangin miji, k'iyayyar miji, wallahi bata fatan ta zauna da Mohan a wannan yanayin na zuciyar shi tana tare da wata. Amma ya ta iya sam Jalilah bata da hankali.
"Umma Idan na aure shi sai na sashi ya manta da Maimunari, wallahi sai na mantar." Make mata baki tayi,
"Kin ci gidanku, ana gaya miki gabar kina yamma, dan kaniyarki ba zaki tab'a iyawa ba, sadaukarwa da matar shi tayi shi kawai ya ishe shi mutuwa da rayuwar shi, ke kin san so? Kina son shi ne sabida yana burge ki ko? Toh ita ta sadaukar da kome nata ne domin shi, dan haka kar na kuma jin kince kina son shi zaki mantar dashi kome!"
Cikin jin haushi ta mike tare da barin gurin ita ta sha alwashin sai ta mantar dashi kowa ma, balle kuma Maimunari. Dan haka ta juyar da kanta lallai zata mantar dashi kome har da soyayyar Maimunari.
**
Diffa.
"Ina sonta Baba, wallahi ina kaunar Maimunari, don Allah Baba ka gaya min me yasa kace na rabu da Ita" sunkuyar da kai yayi sannan yace mishi.
"Ka hakura da ita Hisham mahaifinta ba zai baka ita ba, koda kuwa zaka mutu ka dawo! Ka kyale su ba zaka tab'a samunta ba."
"Baba don Allah ka gaya min meye yasa!" Shiru yayi sannan yace mishi.
"Kasancewar shi Baroro, mutum ne da yasan kan shi, kuma yasan abinda zai yi ya kare kanshi. Ni kuma Mahaifiyata bororo ce mahaifina Bazabarme, shima kuma yasan kanshi, sai dai shi yana rayuwa ne a daji mu kuma muna rayuwa a cikin gari, wani shakara ana bikin sallah, na hadu dashi. Wallahi da farko bani da burin zaluntar shi, sai dai lokacin mun nuna mishi muma bororo ne, yasa ya amince da mu.
Dan haka bayan sallah mun bishi har inda suke anan muna zauna na tsawon wata shida sai dai muzo cikin gari mu koma, ba dan kome ba sai dai Allah yayi mishi baiwar Ilimi na iya sarrafa Alqur'ani yayi abu dashi, dan haka zaman mu bamu tab'a nuna mishi mun zo cutar dashi bane domin ma bama da wannan alamar a ran mu. Abinda yasa muka shiga wannan al'amarin sai dan yadda muke son mu shiga harkan siyasa da wasu abubuwan. Dan haka muka mai da hankali gurin daukar wasu sirrin Alqur'an, bayan mun gama sai muka fara zuwa muka yi fashi, bayan mun yi fashin shine muka gudu tare da kai cunen shi.
Lokacin da ya samu labarin abinda muka yi, shine ya maza ya bar dajin. Aka yi ta niman shi. Bamu kuma haduwa ba, sai a hanyar Mali ya tafi da wata mace, itama kamar bafulatana ce. Dan haka matukar ka matsa kana son Yar shi zai iya tozarta ka, don Allah ka bar mishi yar shi."
Cikin bakin ciki ya kalli mahaifin shi, sannan yace mishi.
"Toh meye ya had'a ka da Abbun!" Kallon shi yayi sannan yace mishi.
"Shi wannan Sa'a yafi Ni, shi yasa nayi alƙawarin sai naga bayan shi"
"Lallai ka fini son kai, dan haka koda za a dawo maka da gawata, wallahi sai na auri Maimunari, shi kuma Ubanta dole yayi hakuri ya bar Ni da ita."
"Ka hakura ka bar mishi yar shi." Mikewa yayi tare da barin gurin.
"Na rigada na yanke hukunci sai dai a kawo maka gawata, amma tabbas sai na tafi ga abar kauna ta. Idan taurin kai da zuciya dabi'ar ka ce, toh ba makawa na gaje ka."
Daga haka ya fice daga dakin da Ubanshi yake, yana kara bibiyar layin Benazir, da ya karba a gurin yar ajin su. Tunda ya saka a kan google ya samo kasar, dan haka ya kwantar da hankalinshi ya gama hada kome zai nufi Zurich.
***
"Baba Mari Sannun kina ta hutawa!" Na fada ina zama, murmushi tai tare da kallona.
"Yo ni da kun mayar dani Nijar da na huta, na gaji da zaman garin nan" ta faɗa tare da kallona.
"Hmm! Babu inda zaki muna tare" shigowa Abie yayi Benazir tana kuka tare da fada mishi ita a'a, don Allah ya amince duk da bana jin English amma na Fahimci kamar an b'ata mata rai ne.
"Don Allah abie kasa baki wallahi na fasa auren shi" gutsiran apple nayi tare da kallon ta.
"Me yasa toh? Idan kinsan baki son shi me yasa zaki bar shi yayi ta wahala?" Na tambaye ta a fusace,
"Addah Munah, ban da bakin munafunci me yasa zasu hada kanwar shi da Hammah Mohan? Wallahi na tsane shi baki daya, ba zan kuma aure shi ba"
Wani abu naji ya tsaya min a wuya, kafin na had'iye tare da sake murmushin takaici, sannan nace mata.
"A'a karki b'ata soyayyarki akan wani banza da bai san hakkin so ba! Dan haka ki gyara tsakanin ku da Dan Ba'are, bai da matsala" na cigaba da cin apple din, shi kan shi Abie dariya yake mata domin tun d'azun take mishi bori ita kuma gashi nan tazo na gwatsale ta.
"Addah Munah! Haka zaki ce?"
"Toh don Allah me zance miki? Shi yasan me yasa ya gaya miki ai? Tunda Kinga ya iya gaya miki toh sako ya baki, dan haka ki ajiye batun zaki b'ata soyayyar ki dashi, domin babu amfanin haka, tunda yana sonki kuma babu amfanin kiyi fushi dan kawai Mohan zai auri kanwar shi. Sai kiyi fatan Alkhairi ba wai kizo kina cewa kin fasa ba."
"Addah Munah!"
"Kinga karki b'ata soyayyarki, domin kuwa wasu na niman damar da kika samu amma basu samu ba."
Ina gama fadar haka na tashi na bar musu gurin, na nufi can backyard, na zauna a kujeran da yake gurin, kwalla ce ta shiga zuba min ina sharewa amma kamar sake tulo shi ake wato har Mohan yana da kwarin gwiwar aure..
*Don Allah yau ku barni na huta na gaji baki daya👏🏼 wallahi*
#Mai_Dambu..
[8/14, 10:44 AM] Joindah: https://www.wattpad.com/1115269487?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=I5OLVif069AImr78w%2FlEumcHUFhhjB3GL%2BklLGDEG2mX72ge1I4j4pFlSrPzq7qgVMUX54J2flC9h4g6fi2m%2FvewJigtCSmbiskTJxpG%2BKNCCPD6AHygfMZwtAY2jz%2F0
🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
BABI NA SITTTIN DA ƊAYA.
"Wato nice zai tozarta nice zai mai da ba kome ba, bayan faffutikar da nayi dan na same shi amma sake subuce min yayi, meye nayi mishi? Dama duk abinda yake fada min karya ce, dama ba zai tab'a tayani kuka ba, lallai yanzun na gane kuskure na."
Sosai nayi kuka nayi bakin ciki tare da zama gurin, naki shiga cikin gidan domin kar a ce min ma nayi kuka dan na damu da Mohan, na san ina son shi amma ban zaci haka daga gare shi ba, wacece irin k'iyayya Ammyn take min haka da ta gwammace ta rabani da abinda nake so! Babu damuwa na bar mata Mohan ba zan kuma damuwa dashi ba.
Dafa kafadana Mommy tayi bayan ta zauna.
"Bayan na tafi na barki zama cikin kad'aici yana daga cikin abinda Dr Khalid yayi yaki akan shi domin na tsani zama cikin jama'a, bana son magana da kowa. Kinsan yadda nake ji a lokacin. Ismail ya lalata min kome na, ya rabani da iyayena da kome nawa, uwa Uba na rabu da abinda na haifa, sau uku ina samun ciki da zaran nayi mafarkin abinda na bari zai lalace.
Ina da yakinin hakkin abinda na bari yake bibiyata, ban wartsae da haka ba, kawai na fara fuskarta matsala daga Mahaifiyar shi, nasan yadda kike ji, amma ba zan iya cewa ga yadda naji ba, Maimunari nayi kuka na roki Allah ya dauki rayuwata da halin da nake ciki da Surukata, ta tsane ni dan ban haifa mata jiki ba,.gashi Yaron nata iya shi daya Allah ya bata, Maimunari ina gaya miki ne dan na yarda dake, amma a lokacin idan da zan ga mutuwa zan so shi sama da kuncin da nake ciki.
Khalid sai da ya juya min baya sabida mahaifiyar shi, ba dan kome ba sai dan ya dakata farin ciki, nasha tambayar shi dalilin da yasa yake kin kulani. Murmushi yake kawai, domin karfi da yaji hajiyarshi ta dawo Paris, kuma haka yake kokarin ganin ya kyautatta mata amma baiwar Allah nan, bata fasa gasa ni ba. Haka na hakura da ita har Allah ya amshi rayuwar ta, ban tab'a fushi da shi ba, domin da ya fahimtar dani yana hana ne domin kar ta tsananin ta, k'iyayyar da yake min ya sani kara kaunar shi. Hajiya tayi fatan taga abinda xan haifa sai gashi ina da cikin Benazir Allah ya amshi rayuwarta, kin san me? Tana da kirki amma saboda son da takewa D'anta yasata juya min baya, Maimunari duk tsanani yana tare da sauki, duk wanda kika ga ya zama wani toh kafin ya isa gurin waye shi.
Na sha zama na duba wata irin ƙaddara ce take bibiyar rayuwata? Na zata kawai dan abinda ya same ni ba zan kuma fuskarta wani matsala ba, sai gashi bayan rasuwar Hajiya Khalid yan uwan shi sun kuma juya mishi tunani, su dai lallai yayi aure, a lokacin bani da wanda zai tsaya min sai Allah, nafi yarda da cewa hakkin abinda na bari yake bibiyata.
A lokacin na kuma bazara rayuwar mutane, ba dan kome ba sai dan yadda nake kokarin na kyautattawa dangin Khalid haka bai saka sun kaunace Ni ba, idan har zamu je hutu Nijar haka xan hada musu shatara na arziki, amma ashe duk abinda nake musu ba, bai musu ba su dai kawai Khalid ya auri yar dangi kin san yadda hankalina ya tashi, haka kawai suka kirkiro bala'i da tashin hankali a tsakanin mu, ina ji ina gani abu kadan zanyi ya fusata Khalid, gashi har lokacin Benazir nake goyo, gashi babu wani nawa, bani da kowa sai shi. Shima ya juya min baya.
Munah ina ji ina gani na zama mahaukaciya, karatun da yake biya min ya daina, dan inda nake jin dadi ya katse min, sabida kawai yana son auren wata Yar uwars shi, ban kuma tsinkawa dashi ba, sai da aka gama kome ana jibi daurin auren ya gaya min, haka na saka shi a gaba nayi ta kuka, amma bai saurare ni ba, haka suka yi al'amarin auren su. Ranar da ya tafi Nijar dakyar ya ajiye min abinda