Showing 15001 words to 18000 words out of 181864 words

Chapter 6 - Bororoji Compelet Book Document by Mai Dambu .txt

29 Jan 2025

6254

anyiwa yaran fada. Tare shi Salimah Dawood tayi tana kallon shi.
"Ka kyauta abinda kayi?"
"Meye ya faru!" Ya tambaye ta,
"Toh kenan baka san meye kayi ba?"
"Ina zan sani, tunda ba ofishin yan kai kara bane ni" ya faɗa zai wuce.
"Wai meye ka taka ne?"
Murmushi yayi tare da ce mata.
"Abinda kike bi, abinda kika gaza gani a kan sauran mazan makarantar." Ya taka gabanta tare da kallon cikin idanunta,
"Suna kike bi, abin da nake ji dashi kike bi, shi yasa baku gaba na karatu nazo yi"


"Dan matsiyata kawai dan an damu da kai"
Murmushi yayi sannan yace mata.
"Sabida kudin Ubanki kika gaza mai da hankali akan karatun ki, kina bin malamai Office suna kara miki maki, shi yasa aka cire ki a can aka kawo ki nan, toh ki duba nan baki daya sansani na ne, kika sake na kuma kamaki kina dambe da Daya daga cikin yan matan makarantar nan sai na zane ki a gaban jama'a mata, Ni matsiya ci ne, amma kuma me tsaye akan kafarshi me bin maganar iyayen shi, bake da baki jin batun iyayen ki ba."


Haka ya yab'a mata bakar magana sannan ya barta a tsaye a gurin, tana kuka.


"Ai dama bata san waye shi bane, shi Sarkin mu ne, gashi talaka da babban zuciya, shi ba irin sakarkarun makarantar nan bane." Suka tafi suna mata dariyar renin hankali, tuni ta fara kuka me ƙarfi.


Almamoon ba yawa ba dad'i, idan yayi yawa ma sai kayi kuka da kanka
[7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: *🐂🐂BOROROJI🫀🫀*

~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
BOOK ONE


Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Idris
I'm on Instagram as @s.square_fashion_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=gorfmwut2x22&utm_content=cgl6gfx


_Real integrity is doing the right thing, knowing that nobody’s going to know whether you did it or not._


Tafiyar ƙaddara..
BABI NA SHIDA
Rayuwar da aka gina shi domin Allah tafiya yake cike da Yardan Allah, duk wata nasara tana tafe da wanda Allah ya baka, wannan shine adadin farin cikin da Almamoon wanda yayi saukar Alqur'ani wanda yayi daidai da kammala makaranta shi na Sakandiri, kuma Allah cikin ikon shi ya samu tallafin karatun jami'ar Maryam Abatcha dake garin Maradi...


Duk wani ƙaddara ta fara ne daga wannan yankin, duk wani tafiya daga nan ta fara, sai gashi cikin Ikon Allah tafiyar ta kuma canzawa izuwa Maradin.


Bayan kwashe watanni suna jiran sakamakon, yana fitowa shi da iyayen shi suka kuma dawowa Maradi domin su abinda zasu iya mishi, Allah cikin ikon shi ya kuma basu tallafin wasu mutane, suka taimaka musu har aka kammala cuku-cukun makarantar, sannan suka dawo dashi gida, aka shiga fadi tashi yadda zasu sami damar nima mishi dakin makaranta domin nauyin karatun shi aka dauka su kuma zasu biya kudin daki da na littafai, abin tausayi wannan karon ma akwatin asusun ta kuma fasawa aka samu kudi me yawa, sannan ta bawa Malam suka dawo Maradi da Almamoon aka kuma biyan kudin makaranta. Sannan suka koma.


Cikin kewar shi suke kallon shi.
"Kasan waye kai? Ka kuma san dalilin ka na zama a gurin nan, akwai al'amarin da zamu gaya maka amma a yanzun shekarunka basu kai nauyin ɗaukar abinda zamu gaya maka ba.


Jami'a ba kamar Sakandiri bane, a can gidan Yanci ne. Ba gidan da zaka zauna kayi laifi wani ya fito yayi maka fada bane, guri ne na kowa kanshi ya sani, dan Allah ka dubi girman Allah karka samu kuka, kamar yadda kace zaka sanya mu, farin ciki ka cika mana burin mu, mun san ba iyawar mu bane yasa kake kare kanka Allah ne yake kare ka, zaka shiga inda babu kunya ko tsoron Allah, don Allah karka watsa mana kasa a idanu, ka taimaka kayi abinda muka turaka Allah ya tsare maka imanin ka."


Kallon su yayi yaga yadda suke share kwalla, sai yaji a ranshi akwai abubuwan da ya dace ya tambaye su. Amma kuma,
"Babana me yasa kuke son na rayu a haka? Bayan akwai matsala idan wata rana."


Rufe baki Innar shi tayi tana kuka tace.
"Ban da karatun nan bamu muna biya ba, wallahi da ka fasa, tsoron goben ka muke ji, shi yasa muka lullube farin cikin ka, kayi hakuri kayi wannan tafiyar shima kamar tafiyar ƙaddara ce, babu wanda yasan me zaka taras a gaba, don Allah karka yarda wani ya yaudare ka, kaga kai ɗaya muka mallaka, don Allah ka rufa min asiri."


Kallonsu yayi yana son tambayar su, amma a yadda yake hango firgici da tsoro ya saka shi had'iye tambayar, ya haɗa kayan shi da wanda yake daya sakamakon dan kudin da iyayen shi suke bashi dukda ba wani samu suke ba, dan Tun lokacin da yace musu yana son fara aiki a kasuwa suka daina barin shi yana niman abubuwan bukata, wani lokacin har kuka yake me yasa ba zai tafi kasuwa ba. Haka suke kokarin faranta mishi amma sabida sun hana shi sake yasa shi hakura.


Yadda ake kaf-kaf dashi wallahi ko mace sai haka, akwai ranar da ya faɗa ai yana da yan mata, a makarantar boko, ranar sai da Innar shi tayi zazzaɓi, idan ta kalle shi sai ya fashe da kuka, tun yana daukar abin wasa har ya shiga tashin hankali, shi yasa ya daina subul da baka, domin yana tsoron abinda zai sami iyayen shi.


Ranar Lahadi suka saka shi a mota har da kayan abincin shi, bayan an mishi fada. Kamar kullum. Basu bar tashar ba sai da motar ta bar gaban su, suka bar tashan.


Haka suka koma gida cike da kewar dan su, me cike da al'ajabi. Karfe hudu tayi musu a garin Maradi.


Daga nan makaranta ya wuce inda ya nufi can dakin kwanan dalibai, ya nufi dakin su. Ya samu dakin akwai matasa biyu shine na uku, bai musu magana ba, ya dauki kayan shi ya shiga cikin dakin, ya shirya tsaf, sannan ya bude yar robar da yazo da shi na Abinci yaci sannan ya koshi. Sannan ya wanke shi, ya fita bayan ya gyara kayan shi ya rufe ruf ya nufi kasuwa, ya sayo abubuwan da zai bukata, sannan ya dawo dakin su.


Babu ruwan shi da kowa haka suma babu ruwan su dashi, washi gari ya riga su tashi dan haka har yayi wanka bayan yayi idar da sallah, ya zauna ya dama garin kunu yasha da yar kulin da Innar shi tasa wata makociyata tayi mishi. Yana ci yana kewar Innar tashi, bayan ya gama zuwa karfe bakwai. Ya fita abin shi har ya kai bakin kofar daya daga cikin yan dakin yace Mishi.
"Malam Almamoon! Yana da kyau idan ka shigo guri kayiwa mutanen da ka samu magana koda ba zasu kula ka ba, suna na Mubarak Habib, wannan kuma Rabilu Adam, ga dan mukulin dakin guda uku ne ni daya kai ɗaya shi daya, idan muka kasance bamu na daya nan idan kuma tsautsayi yasa ya fadi toh sai ka rike wannan, haka dai dukkan mu zamu kasance, dan haka ina maka fatan Alkhairi, Allah ya bada sa'a."


Duk sai kunya ta kama shi, ya fita tare da cewa.
"Nagode"

...... Haka suka kasance, duk da babu wata mu'amalar arziki a tsakaninsu amma kuma dukda haka suna gaisawa da tambayar karatu.


Bayan wata hudu lokacin da aka yi jarabawar zangon farko na karatun su dan lauya ya zab'a, sai da ya kasance dalibi mafi yawan maki a tsangayyar su, domin sunan shi ne na farko da A1 da maki 4.8, sai gashi ana niman shi ido rufe, wanda bai san shi ba so yake ya ganshi.
(Abinda yasa na ke kokarin d'aga Darajar Almamoon ba kome bane dayawa yaran da suka kasance irin wannan a cikin al'umma zaka samu Allah yayi musu baiwar ilimin da daukaka na rayuwa, gasu nan dai basu da wata wata kyakyawan nasana, amma sai ka samu irin su Allah yana taimakawa rayuwar, idan kaga irin su sun lalace toh daga marikan sune, ko iyayen su. Ko uwa ko Uba, sun kashe musu sa ransu a gaban idanun su, irin wadannan Yaran idan ka tsaya musu da addu'a, ka basu ilimin addinin, ka nuna musu muhimmancin rayuwa da girman ƙaddara, sannan ka nuna musu ai suma mutane ne masu yanci wallahi sai su maka abinda dan Sunnah bai maka ba, su din kamar kowa ne, idan da zaka bincika su, zasu gaya maka suna jin kunyar amsa sunan suna na masu yanci, karka sarewa irin su gwiwa, show dem suma suna da Yancin irin na me Uba... Zasu rayu cikin farin ciki, amma idan society's suka fara kyamar su. Dayawa sai su fada halin banza da aikata abinda iyayen su suka aikata koda yake wannan hukuncin malam bahaushe ne, idan namiji ne za boye mishi asalin shi musamman idan yana da kudi idan kuma mace ce har karshen rayuwar ta, tana girban laifin da ba nata ba, don Allah al'ummar Hausawa mu sauya tsarin rayuwar mu, wallahi dayawa wasu nason fadan halin da suke ciki mune bamu basu kwarin gwiwa da fahimtar su. Abin tausayi...)


Haka aka yi ta niman shi, shi kuma yana can wajen makarantar yana zaune, yana kallon yadda dalibai ke shiga ke fita, musamman idan suka leka sakamakon su, bai yi kyau ba. Abinda ya hana shi zuwa gurin kenan duk da akwai cunkoso mutane.
"Kai ba kai bane Almamoon?"
D'ago kai yayi ya zubawa mutumin da yake tsaye ido, malamin sune, mik'ewa yayi sa sannan yace mishi.
"Eh nine"
"Toh ka shiga makarantar ina taya ka murnan ka cinye jarabawar ka baki daya."
Rufe bakin shi yayi yana murmushi, sannan tacewa malamin.
"Nagode sosai" kura mishi ido malamin yayi, tunda yake bai tab'a ganin abinda ya burge shi sama da wannan dalibi nashi ba, murmushi yayi tare da cewa.
"Toh a kara himma"
"Nagode Insha Allah" haka ta shiga makarantar, malamin ba bin shi da ido, wani irin bugu zuciyar shi yaƙe, har sai da ya dafe kirjin shi, yana bin Almamoon da idanun.


D'aga motar din shi yayi yabi bayan shi har inda ake kallon sakamakon, sannan ya juya. Bayan sunyi hutu.

Sai da yayi ta damuwa da yaron ya dawo. Domin kawai yana jin yayi ta kallon yaron burge shi yake.
Malam Ansar Yusuf Alhgabit, shine cikakken sunan shi, fari ne daidai ba me yawa ba, yana da matsanancin jiki me kyau, kyakyawa ne, kamar yadda ya kasance shi din Bazabarmen ne, daga garin Zinder. Dan kimanin shekaru talatin da shida, bai tab'a aure ba.


Yana da kane da Mahaifiyar su, tana can, duk karshen wata yana zuwa gida, ya yi kwana biyu. Wannan hutun ba karamin gajiya yayi ba da gida, dan Allah ya jarabce shi da son ganin Almamoon.


Hutun sati Uku suka yi, amma Almamoon bai dawo a satin farko ba, sai a na biyu. Ya dawo ya bar Baban shi babu lafiya, kamar na zai dawo ba. Haka suka sashi a gaba ya dawo. Bai da walwala duk da malam Ansar Yusuf yayi ta tambayar shi bai gaya mishi abinda yake damun shi ba. Ranar juma'a aka tafiya masallatai Jumma'a, ya nufi tasha sai Damagaram, Alhamdulillahi ya dawo ya sami jikin baban da sauki sosai.


Rike kunnen shi suka yi tare da cewa.
"Shi mutum mara jin magana Allah ya shirya mana shi, sai mun fara zane ka da girmanka"
Cikin shagwaɓa yace musu.
"Wallahi satin nan ban san meye na karanta ba, tab mahaifina bai da lafiya ina Ni ina karatu, wallahi gudowa nayi naga halin da Ubana yake ciki laifine?"
Wannan kulawar da yake nuna musu yana masifar musu dad'i, dan haka suka ce mishi.
"Babu laifi tunda kana shan nono ai shikenan." Dariya yayi ta musu Kawai. Ranar Asabar suka saka shi a mota ya dawo Makarantar.


**
Ranar Lahadi ya fito zai tafi kasuwa ya hadu da Malam ANSAR.
"Ina zaka Almamoon?"
"Kasuwa zani!" Ya bashi amsa,
"Shigo na kai ka"
"Laa Nagode" ya faɗa tare da wuce motar, kura mishi ido Ansar Yusuf yayi ya kuma bin shi da mota.
"Shigo nace" yadda yayi maganar a dake yasa shi shiga motar cikin jin babu dad'i, ya zauna suka nufi kasauwa duk da babu wanda yayiwa wani magana amma kuma haka yayi matukar sanya Malam Ansar farin ciki, koda suka isa yayi sayayya karshe Malam Ansar ya biya kuɗin. Lokaci guda abin ya daurewa Almamoon kai.
"Malam wannan abun kamar bai dace ba, kuma idan ba zaka damu ba don Allah kayi hakuri karka kuma wallahi iyayena zasu min faɗa."


Ya fada kamar zai yi kuka.yadda yake maganar yayi matuƙar burge malam Ansar,
"Kai dube ka sai kace mace, amma yayunka mata ne ko?" Bai san ya tura baki ba, sai da yace mishi.
"Kaga abinda nake fada ba, amma kai ne auta a gidanku ko? Da alamu kai mata na biyo"


Sake fuska yayi tare da nuna mishi ya gode amma don Allah kar ya kuma wallahi karatu yazo yi ba kananun magana na,, haka suka dawo makarantar.


-- a hankali kome yake tafiya. Farin jinin shi da nutsuwar shi yasa an kuma zaɓen shi mataimakin shugaban dalibai na makaranta, duk da ko shekara bai yi ba a makarantar, a bangaren addinin sun zo bashi wani matsayi aka hada musamman masu jin haushinsa suka ce ai dan daudu ne, hatta maganar shi ta mata ce, sannan akwai wata alaƙa tsakaninsu da malam Ansar, abin da yayi mugun b'ata mishi rai kenan, ya fita hanyar malam Ansar.


A haka har suka gama aji daya suka shiga na biyu, a lokacin ma makin shi ya dara na kowa, lokacin da suka tafi hutu suka dawo, shakuwar shi da Malam Ansar tayi yawa, duk da akwai malaman da suma suke tare da Almamoon, musamman a ta bangaren addini, har tsoron shi ake idan yana karatun Alqur'an ko idan aka tambaye shi akan hukunce hukuncen addini, idan yana bayani sai ka zata babban shehin malami ne. Nan kuwa dan shekara goma sha takwas ne da ƙwaƙwalwar gigaby.


A hankali malam Ansar ya wani gari ya mutu a kaunar Almamoon, dan sau dari idan ya saka shi a gaba, da idanun shi yake sauya mishi fasali daga Namiji zuwa mace, har gani yake idan Mamoon yasha kwalliya a matsayin mace ya maza zasu yi. Dan yana girma bakin fatar shi tana kara wani irin yanayi har wani Golden Golden yake idan ya shiga rana.


Haka kawai abokan Wani dalibi da yaso a bashi mataimakin shugaban dalibai, suka nufi dakin su Almamoon suka mishi mugun duka, tare da watsa mishi kayan shi a waje, haka ya sa. Aka sami wani dalibi ya kira Malam Ansar yazo, ya dauke shi da kayan shi bayan sun rubuta Report da kome akan ɗaliban. Sannan suka nufi gidajen malamai.
"Sannun ga dakin nan ka zauna kayi wanka an jima na kai ka asibiti a duba maka jiki ko kayi rauni."


"A'a ba sai mun je ba, da sauki sosai." Tunda ya shiga dakin ya rufe kofar zama yayi yaci kuka sosai. Idan kaga yadda yake kuka sai ka tausaya mishi, bayan yayi wanka ya kwanta dan jikin shi ciwo yake. Dake ya gaji yana kwanciya barci yayi gaba dashi.


Bai farka ba sai da asuba, yayi Sallah sannan ya kwanta, karfe bakwai ya tashi domin yana jin ana shara a falon, yana fitowa ya samu wata dattijuwar bafulatana ce. Kallon juna suka yi sannan tace mishi.
"Akwai abinci a cikin dakin girki inji malam idan ka tashi kaci ga magani na baka," murmushi yayi mata sannan yace Mata.
"Nagode" kara kallon shi tayi a karo na biyu, yaron ya shiga ranta"
"Meye sunaka?" Murmushi yayi mata sannan yace mata.
"Mamoon" ya zauna yana cin abinci shi a nutse, kallon shi tayi sannan ta nufi kitchen ta dibo mishi ruwan zafin da maganin ta ajiye mishi, shigowar malam Ansar ya sashi mik'ewa yana faɗin..
"Ina kwana malam?"
"Lafiya ya jikin naka?"
"Da sauki sosai"
"Idan ka gama kazo ka wuce makarantar ana niman ka"
"Toh" ya faɗa bayan ya sha maganin ya nufi dakin ya saka kayan shi. Sannan ya fito. Suka nufi Makaranta,. Duk wanda yaga yadda Malam Ansar ya damu da Mamoon sai da suka yi magana domin kuwa wata mahaukaciyar soyayya yakewa dalibin shi, har ta kai sai da aka yi maganar a gurin ai kuwa nan Almamoon ya gaya musu cewa babu wannan tunanin a ranshi, yasan malamin shine, bai taɓa mishi wannan abu na rashin ɗa'a ba, dan haka sune suke tunanin haka.


Kuma batu na gaskiya Almamoon bai tab'a jin wani abu na burgewa....
[7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: *🐂🐂BOROROJI🫀🫀*

~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
BOOK ONE


Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Idris
I'm on Instagram as @s.square_fashion_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=gorfmwut2x22&utm_content=cgl6gfx


_Alhamdulillahi books dina baki daya wanda nayi su na kuɗi suna Okada akwai masu cewa suna bukata basu da Whatsp toh ga dama ta samu ku garzaya Okada na akwai su baki daya a can da sunan RamlatArManga_


_🙄🙆🏾‍♂️ Yanzun batun mata maza ya kare an koma Malam Ansar daga Taimako 😭 sai ya zama Shayyi 🙄😏_


*Assalamun Alaikum Jama'a, Ina iyayen da suke nimawa Yaransu malaman Lesson a cikin garin Kano! Dayawa basu da lokacin da zasu zauna sunyiwa yaran su extra lesson a gida toh shakurumin ku! Akwai dalibai mata shin ke Uwa ce? Indai har haka ne toh kin tab'a tunanin akan yaranki ko? Toh indai haka ne Mommy akwai Yan matan da suka kware a fanin computer, Islamic Studies! English da sauran darusa. Karki manta Yan matan nan dalibai ne, dan haka suke niman hanyar tsayawa da kafar su. Idan kika basu karki yi tunanin kome kisaka Allah a cikin lamarin zai tsaya mana Save

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login