Showing 141001 words to 144000 words out of 181864 words
sannan ya bude inda nake, ya dauke ni.
Cikin gidan ya wuce dani, Abie yana zaune. Ya shigo dni.
"Ina zan kaita?"
Nuna mishi dakin yayi tare da shiga da sallama, dakin ta yara ce aka ware shi, domin akwai kayan wasa kala kala. Sannan ya kwantar dani bayan yayi min addu'o'in, Kafin ya ja min kofa ya fita.
**
Washi gari.
Da wuri na farka, na kuma shiryawa sannan na karya kafin Abie da kanshi ya kai ni. Airport,
"Uwata gashi kin kawo katin bikin ni kuma zan tafi Nijeriya taron bita na Alkalai, ban sani ba ko zan sami daurin auren amma duk yadda za ayi zan zo ayi dani."
Idanuna ne ya cika da kwalla.
"Toh shikenan!"
"Kiyi hakuri Insha Allah zan zo"
"Toh" nace ina share kwalla, haka kawai nake ji idan da Ubana ne babu abinda zai hana shi zama a daura aurena amma yau sai gashi ina niman ina ma zan ga Ubana su ko tausayina basu ji ne da suka tafi suka bar ni. Ba zan taba barin dana haka ba, har na shiga jirgin yana d'aga min hannu.
Bayan tashin shi yake kara jin babu dad'i, idan da yar shi ce babu inda za shi dole ya zauna ayi kome akan idanun shi, Allah sarki. Haka ya fada.
Yana komawa gida Mohan na zuwa sosa kai kai yayi sannan yace.
"Abie mun ina kwana?"
"Toh ta tafi lafiya lau!"
"Haba?"
" Zan maka wasa ne?"
"A'a ya faɗa tare da sunkuyar da kai yana kara jin girman Abie yau sosai.
"Toh, Allah ya sauke ta lafiya. Zan tafi"
"Ka gaida gida"
**
Karfe goma da rabi na isa gida na samu ana ta hidima.
... Biki ake sosai a gidan duk har. Ana gobe daurin aure aka sani a lalle, haka kawai zan zauna nayi ta kuka, sun zata kawai dan zan rabu da Innah ce a'a kawai kukan tausayin kaina nake ji.
Ranar sha biyu ga watan Maris aka daura aurena Ni da Hammah Mohan, da misalin karfe sha daya na rana, a babban Masallacin Damagaram, ana daura auren babu b'ata lokaci aka dauke ni a jikin Innata, ina kuka tana kuka. Haka muka nufi Niamey.
Ba zan manta da wannan al'amarin ba.
Niamey.
Tunda muka isa da yamma aka fara wani irin biki na fitan hankali..
**
"Boka kayi wani abu, bana son yarinyar ta shiga cikin gidan."
"Ai kin makara, shiga kuwa tuni ta shiga. Ni dai ku tafi bani da abinda xan muku idan kuka nace min kayana konewa zasu yi kutashi kafin masifar da kuka lakato ta same ni"
Koran kare yayi musu cikin kunar rai suka fito, kamar mahaukaciya Hanan take kuka tana ihu, garin haukarta ta taka wutsiyar maciji,a fusace ya zabga mata sara, tana ganin shi ta fasa ihu, tare da faduwa uwarta ma ihu ta fasa, haka Bokan ya fito ya same su. Ganin sarar maciji ne ya koma cikin Bukar shi ta dauko magani ya shafa mata, shine ta farka. Ya bata wani tasha. Tayi amai sannan yace musu.
"Maza ku tashi, gaba da gaban ta, yarinyar Allah yana tare da ita, idan kuka nace zaku mutu maza ku b'ace min da gani"
Jikin su yana rawa ta dauki Hanan suka bar gurin.
**
Ana ta shagalin na bikin babu wanda ya damu da kowa, sabida harkan arziki da ake.
"Hajiya kinyi bako!"
" A wannan lokacin! Kana ganin z a kai amarya d'akinta ne don Allah yayi hakuri Kuma kaga yanzun aka gama liyafa."
"Wai abin yana da muhimmanci ne don Allah ki zo"
Haka tafita ba dan taso ba, bayan ta haɗu da bakon, ta dawo jikinta yana rawa, tasan ba zasu bata goyan baya ba.dan haka ta ajiye abin a ranta.
***
Daga Ni sai radiya da Auta tare muka zauna har angwaye suka zo, akayi abinda ya zame na al'ada, kafin suka mana nasiha,. Radiyah ta riko hannun Auta suna gudu daga bari muyi rakiya. Suna fita kuwa Hammah Mohan yana shigowa cikin ɗakin.
Zama yayi a bakin gadon, yana kallona.
"Alhamdulillahi gani ga Maimunari, Maimoon, Almamoon! Mamoon! Mata maza"
A hankali ya yaye mayafin fuskana, sanan ya matso tare da janyo ni jikin shi.
"Tashi muyi sallah"
"Toh"
Na shiga nayi alola sannan nazo muka gabatar da nafilla kamar yadda Manzon Allah ya umarta ya dage goshina yayi min addu'o'in da aka wajabta, kafin ya ya tashi ya kawo min kayan kwalamar da ake kawowa daren,
Alhamdulillahi munci mun sha, sannan muka kwanta, bayan na sauya kayana.
"Moonah dawo kusa dani"
"Hmm! Barci nake ji"
Na fada mishi.
"Toh"
Ya fada kamar Maraya,matsawa nayi jikinshi na kwanta, a hankali rayuwar da ya tsara mana tare da shirya mana wani irin rayuwa na musamman,. Wannan daren na yarda Mohan namiji ne na gaban kwantaccen, Mohan, Mohan ya kai ni duniyar da ban zata ba, ashe duk abinda nake fada duk cika baki ne, domin kuwa daga yan tab'e tab'e lashe lashe, tsutsa tsotse, sai da Mugun ya fara gangarawa madaidaiciyar hanyar na Fahimci Allah daya ne, yanzun na Fahimci abinda Innah ta gaya min da ban rasa kome na daraja ta ba.(zaku ji bayani nan gaba Insha Allah) domin baki daya abinda aka tura mishi aka gaya mishi a kaina ne a kasan ranshi, dan haka cikin salon kidima da yaji yadda gurin take da dumi bai san lokacin da ya buga iska.(😏🤣🚶🙆🏽♀️ Ya isa haka ku hango yadda Mohan ya gigice mana sai nayi fashin bakin har haka!)
Na sha bakar azaba a hannun shi nayi kuka na roke shi, na gantsara mishi cizo amma mugun dai da ya mai dani cikakkiyar mace, hankalin shi ya kwanta, ta tattara min gashin kaina ya rasa me zai min ma yaji dad'i.
Haka ya haska wutar gefen gadon, ya kalle ni yadda nayi laushi.
"Allah yayi miki albarka, kamar yadda kika faranta min Allah ya faranta miki." Tashi yayi ya shiga ban daki.
Kasa kasa nace mishi.
"Amin mugu!"
Dariya na bashi yace min.
"Bari na hada mana ruwa sai na kuma ko sau daya ne!"
Jan bargon nayi, kawai naji an fisgo shi, da sauri na rike tare da sake kuka zan mishi mita.
"Tashi Shegiya bakar munafuka, gurbatacciya! Kin shigo min tsabtataccen Zuri'ata, wanda bamu hada iri da shegu ba, tashi."
"Ammyn karki wulakanta ni a shimfid'ar d'anki, don Allah ki rufa min asiri na suturtta jikina!"
"Tashi dan Ubanki da ya dauke uwarki ranar aurenta yayi cikin ki aka haifi Shegiya irinki, yar zina. Kazamtar da tafi kowanne muni, ayi zina da matar aure. Aka haifi Shegiya irin ki! Tashi."
Kura mata ido nayi kome na kaina ya tsaya, a hankali na fisge Zanin gadon daidai fitowar shi daga shi dai towel, ganin uwar shi a tsaye ya sashi komawa cikin ban dakin da sauri ya dauko rigar wanka ya saka. Sannan ya fito.
"Ammyn lafiya?"
Kifa mishi mari tayi.
"Sake ta dan Ubanka. Shegiya ce mara asali kije ki tambayi Innarki da mijinta ke ba yar su bane maza sake ta kafin na tsine maka ka shiga duniya."
Yaki magana yana kallona ina kallon shi. Ni kam zunzurutun na shiga kidima bansan me suke fada ba.
"Sake ta nace ko na tsine maka!"
Yaki ko guzau.
*Kar Allah ya nuna min ranar da ba zan iya amfanarki ki da kome ba sai ido* wani irin hawaye ne yake zuba daga idanun shi, Ni kam kukan ya tsaya min bana jin kome, a hankali ya dauki kayana yana mika min nasa hannuna amsa. Rufe shi da duka tayi, tana faɗin.
"Zaka sake ta ko sai na maka baki"
"Kiyi hakuri zai sake ki Ammyn! Insha Allah zai sake ni, ba zan kuma dawowa cikin duniyar ku ba! Mohammed kayi abinda tace kaji"
A hankali ya fita daga dakin na dauki kayana na shiga ban daki na saka, sannan na fito ina kallon shi. Mika min tai.
"Maza Allah ya raka taki gona abinda aka so a lalata mana siyasar mijina."
"Ammyn karfe ɗaya ne fa;"
"Ba zata kwana ba dan Ubanka, wallahi ka jima baka mutu ba" haka na fito ina jan kafa yana bin bayana, a daren na fita daga gidan shugaban kasar Nijer. Zuciyata tayi sanyi Abu daya zuwa biyu nake son ji.. wacece ni?....
Allura ta tono garma.....
*Intermission! Yanzun muka shiga tsakiyar labarin.... Da alamu na fara shinshimo karshe..... Amma haka ba zai samu ba sai na ga ruwan kaunarku da voting 🤣🙆🏽♀️🚶🏌️ rashin daraja*
#Mai_Dambu...
[8/14, 8:18 AM] +234 815 778 5691: https://www.wattpad.com/1113774799?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=wttFXwlCWTsu7Xd9brt9PkpuxFS1NA%2FyyAvcpakR2j0eLdqgraAaqKDIsHkdoAh9cMAZ0F3vUQbYnQqanCDd%2B8Ah01MAW4cg9qyzlshahFd%2FF%2Fce11kN%2Fe9K0RRl58%2BM
🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
BABI NA HAMSIN DA BIYAR.
"WALLAHI ka kuma taku daya sai na la'anance ka!" Ta fada da karfi, wani irin sanyi ne ya shiga jikin shi, ya kalle ta a hankali sannan yace mata.
"Anya ke kika haife Ni? Anya ke kika dauki nauyin cikina? Lallai Ammyn Kinyi abinda kike so ni kuma zan miki yadda kike so! Ba dai Maimunari kika cire a rayuwa ta ba? Alhamdulillahi na hakura da ita koda itace rayuwata Allah ya bata wanda ya fini."
"Wallahi naji wannan maganar a kunnen Yallabai sai na tsine maka wanda bai san ciwon kan shi ba, yarinyar da aka haife bata hanyar aure ba."
"Bani da lokacin da zan yi magana akan wannan Ammyn wallahi ba zan yi magana akan shi ba, amma Allah zai bi min hakina mata ta ina sonta kina rabani da ita, ina kaunar ta kika rabani da ita Allah yana nan"
A hankali ya juya zuwa cin gidan shi, ita kuma ya juya zata shiga cikin gida, ganin wani dogon abu tayi wanda bata hango karshen shi balle farkon shi yana tawowa da mugun gudu, aikuwa ta arta a guje, tana shiga falonta ta yanki jiki ta fadi saboda giftwar shi a falon. Ihu ta saka tare da firgita sosai.ihu take tana kiran mutane.
Kafin kace me haka gidan ya cika da jama'a,dole aka rufeta da Addu'a, kafin ta samu barci. me wahalarwa.
**
A hankali nake tafiya motar sojojin shi suna bin bayana, a hankali na tsaya a jikin wani mota, na jingina ina sauke ajiyar zuciya, saboda na gaji sosai. Wayata na cire a jakata da ya mika min kafin na fito. A hargitse nake dan haka koda ba kira Number Abie naji a kashe kiran Ansar nayi.
"Kana ina?"
"Toh ina masaukina ne! Lafiya a tsohon daren nan?"
"Kazo ka kai ni Damagaram."
"Ina Mohan"
"Zaka zo ko ba cigaba da tafiya?"
"A'a gani nan zuwa"
.ina tsaye a gurin, bayan wasu mintina sai gashi nan ya iso. Da sauri ya bude min kofar, na na ja kafana a hankali, domin zuwa yanzun dan tafiyar da nayi tare da motsa gurin da bai samu kulawa na tasa ina jin nauyin har kirjina.
Ina shiga motar kwanciya nayi, ya shiga mazaunin Driven, "ba zan kai ki asibiti ba kuwa naga kina bukatar taimakon?"
"Bana bukata Damagaram kawai zaka kai ni."
*
Abuja.
Karfe goma suka gama taron su na majalisar Alkalai ta yankin west africa. Dan haka yana gama abinda zayi ya ga lallai zai iya samun daurin auren tunda ba mamaki tunda yafi tsammanin da tsammanin ranar ne kuma zai iya kasancewa da azhar ne.
Dan haka akwai liyafar da aka shirya musu, amma baki daya ya kasa fahimtar kome, karshe gaya musu yayi zai kome gida akwai daurin auren da zai halarta.
Haka yayi musu sallama ya bar garin Abuja.
... Yana isowa bai tsaya ba, sai gidan shi ya sauya kayan shi. Sannan ya dauki katin auren da bai duba ba sai yau.
Maimunari Isma'il Wodaadabe. Abinda idanun shi ya hango mishi kenan, kan shi yayi wani irin dumm, maganar mutane ne ya shiga dawo mishi. Tare a tunawa da yadda suka yi ta cewa yar shi ce.
Wani irin jiri ne ya dauke shi, ya zauna dabas, tare da dafe goshinsa. A hankali yaji kwalla na zuba mishi,.Yar shi ce ya zauna da ita tsawon watanni bai sani ba,.ko dai ba shi Isma'il Wodaadabe bane, mik'ewa yayi ya haɗa kayan shi. Ya fita tare da nufar airport, sai kusan karfe biyar ya samu jirgin damagaram. Dake daurin auren a babban Masallacin Damagaram ne.
Shi yasa yana isa gidan bai zame mishi boyayyen gida ba, tun daga nesa ya hango Aminin shi Sanda. Kwalla ce ta cika mishi ido,ana isa kofar gidan mai taxi din ya tsaya, biyan kudin yayi sannan ya fito ya dauki kayan shi. Ya nufe shi, zama yayi a gefen shi suka gaisa. Kafin ya saka hannu a aljuhun shi ya dauko sarewa. Ya fara busawa. Hawaye na zuba mishi. Juyawa Baba yayi.
"Sama'ila!"
Bai mishi magana ba, ya cigaba da busawa hawaye na zuba sosai, daga cikin gidan Innah taji sautin sarewan ta fito da gudu, a hankali ta isa kusa dashi, ta zauna tare da daura kan ta a kafad'ar shi. Yana busa sarewar yana kuka.
"Ina ka shiga shekara Ashirin! Ina ka tafi ka barmu, Maimunari ta girma yau ake aurenta sun tafi da ita"
Cire sarewar yayi tare da kallon ta.
"Ki yafe min!"
"Baka min kome ba."
A hankali Abokin shi kuma wanda yake ji kamar dan uwan shi ya dauki kayan.
"Sanda na Barka da nauyi"
"Babu kome!" Cikin gidan suka shiga har falon Baba, anan aka shiga kuka kuma, kafin aka nutsu.
Ya fara magana a hankali.
"Bayan na bar ruga, ba zan iya fada muku abinda nake ji ba, amma wallahi ƙaddara jaririn shi ya sa na aikata haka, dan haka ina fita ban tsaya ba na kad'a shanun mu na tafi dashi. Tafiya sosai nayi har na isa Maradi, daga nan na fita daga yankin Nijar na nufi Nijeriya, tafiyar kwana da kwanaki ya kai ni Sokoto.
A hankali na nufi kasuwar dabobbin na sayar da su har da naki, nayi fatan Ubangiji ya albarkace shi, sannan na shiga niman sana'ar a zata rike ni, a hankali na sauka a wani gidan gwauraye, na fara fita ina zaga garin. A dan gaba da gidan da na sauka akwai wani attajiri, sai dai kuma daga shi har yaran shi an musu bakin asiri, kullum zaka samu ya zauna yana ta gyangyadi yaran ma basu da abinyi sai yawo da shashancin. Dan haka na same shi muka gaisa ranar mun fito masalaci.
"Alhaji Ni kuwa naga wani abu a tare da kai da zaka bani dama da na gwada maka shi"
"Yaro xan tafi kasuwa ne, idan na dawo xan maka magana" yana fadar haka ya nufi kofar gidan shi ya zauna daga nan dai barci, ina gurin shi har aka kira sallah ya tashi zai tafi nace Mishi.
"Alhaji bana bukatar sisinka kawai ka amince min na taimaka maka, da abinda Allah ya wuwace min."
"Toh yaro muje"
Bayan mun yi sallah na saka ya sayi kayan aikin da kudin shi dan kar yace zan damfare shi, sannan na hada mishi kome nace ya tafi xan yi daukar Alqur'ani. Haka na kwana akan ruwan addu'o'in nan, washi gari da asuba kafin ya yi magana da kowa ya isa kofar gidan, yana bude kofa na mika mishi zai magana na rufe mishi bakin shi alamar yayi shiru, yana sha ya nufi masalaci, muka yi sallah.
Bayan mun fito zai magana nace.
"Kayi hakuri! Karka yi magana da kowa, ka dauki kayan ka ka nufi kasuwa Allah yayi mana tsari da muguyen mutane."
Haka kuwa ya faru, ya tafi kasuwar. Sai gashi babban abokin shi yana ganin shi yakira sunan shi waye? Meye ya dawo dakai kasuwa? Kai da aka maka iyaka da kasuwa. Sunan kasuwa ma barci zai saka. Yaran ka da suke kula da shagon ka suma haka. Dariya ya fara yana faɗin ai nasan za a rina. Hauka tuburan abokin yayi. Bayan kwanaki nayi mishi na yaran shi, suka sami lafiya suka koma kasuwa. Yayi yayi dani na auri yar shi. Hajara amma naki, sabida zuciyata tana gurin Zainab. A haka na zauna a gidan shi. Har na fara karantarwa.
Kafin na shiga yaki da jahilci, Allah cikin ikon shi na samu shekara hudu, kafin na dawo Nijar nayi diploma a harshen Faransa, sannan na shiga jami'a inda na karancin Shari'a, shekarau ashirin din nan ban yi shi karon iska ba, nayi karatu har kasar Saudiyya, kafin na hadu da Primer minister, ya bani babban alkalin Alkalai na kasar Baki daya, har zuwa wannan lokacin zuciyata tana gurinta."
Kuka suke suna bashi labarin yadda suka sha wuya kafin suka daura da rayuwar Maimunari. Murmushi yayi sannan yace musu.
"Na kasa amincewa ni na haifi wannan doguwar yarinyar, sai yanzun nake kara hango yanayin ta, yanayin mahaifiyarta. Ashe jini na ne, shi yasa da akayi ta jifarta sai da na koma baya, domin kare yarinya na, ko kuka bana son tayi sosa min rai yaƙe, gashi Allah ya bata yaron da zai iya bada rayuwar shi domin ita."
"Amma har yau bata san kome akanta ba Hammah Sama'ila ina tsoron kar ta sani ta birkice mana"
"Insha Allah Ubangiji zai yayyafa mata ruwa, me yasa kika boye mata al'amari haka? Ko yayya ne ai da kin gaya mata, gaskiya ban ji dadi ba. Koda nace idan ta kasance mace a boye min ita sabida tsoron kar a wulakanta min ita ne, sai ki gaya mata cikin lumana yadda zata gane wacece ita."
"Toh ya zanyi mata, bana son ta rasa farin cikin tane." Ajiyar zuciya ya sauke kafin suka shiga hiran da tafi wancan har magarib ta cimma su, suka tafi masalaci.
Kusan raba dare suka yi suna hira, da asuba suka nufi masalaci.
...
Wani irin azazzaben gudu Ansar yake, karfe shida na safe mun iso garin Damagaram.
A kofar gidan ya tsaya, a hankali na tashi tare da rintsa idanuna, kafin na mike na bude kofar a hankali, na sako kafana. Wani kwarin gwiwa nake ji, na dauki jakata, ban mishi magana ba, na shiga cikin gidan ina dingishi. Jini na sauka a kafaffuna.
Ina shiga na sami Innah tana abin karyawa sake wukar hannunta yayi tare da mik'ewa.
"Lafiya!" A sannun na isa gurin wukar na cire mayafin jikina na dauki wukar ina wasa da