Showing 129001 words to 132000 words out of 181864 words

Chapter 44 - Bororoji Compelet Book Document by Mai Dambu .txt

29 Jan 2025

6267

ya saka ni gaba muka nufi gidan shi, cire kayan shi yayi tare da saka wasu kayan, ya shiga min rubutu a jikin allon karfe, ya nutsu yana rubutun da tawwadar mai zafi,sabida tana tafasa ce ake rubutun dashi, yana gamawa ya wanke min da ruwan zamzam mai zafi dan har yana tiriri. Ya mika min fuskar shi babu alamar wasa yace min.
"Nasan kina addu'o'in neman tsari, amma sha wannan makiyan shi sun rub'anyan da! Ta ko ina aika zakina samu, dan haka nake kyautata zaton an fara bibiyar ki, maza sha ba mutum ba ko ifiritu yake, zai ganki ya barki sai dai a kare a makirci da munafunci ba boka ba ko malami ne, idan ya nace zai tab'a miki wallahi kwayar idanun shi tsiyayyewa zasu yi.


Idan kuma aka dage na miki sharri hauka mutum zai yi domin da bakin shi zai magana."


Sai da ya gama min bayani, sannan ya bani wani Magani nasha, kafin na kwanta a dogon kujeran falon shi, bai tashe ni ba. Sai da aka yi azahar na tashi nayi sallah sannan ya mika min abinci.


Awaran madara soyayya sai yaji da dafaffen nama wacce aka dafa ta da madara, har karasa yadda daɗin shi yake, sai shinkafar da aka dafa da ruwan kwakwa. Ina gama ci. Ya kalle ni.
"Duba wayarki mutumin ki ya shiga kotu sau uku yana niman ki"
A kunya ce na dauki wayar na kunna, sakonni shi kawai suke shigowa, kiran shi nayi.
"Kina ina?"
"Ina gidan Abie kazo ka ɗauke ni"


"Toh gani nan"
"Kina son Mohan kamar yadda yake sonki" sunkuyar da kai nayi, ina wasa da cokalin hannuna.


.. hira muka sama sama har ya iso, harara ta yayi sannan yace min.
"Kin kyauta min!"
"Zauna kaci abinci"
"Toh Abien Moonah" ya faɗa a zolaye, murmushi nayi na zuba mishi. A hankali yake ci yana kallona.
"Muna nake kika yi girkin nan ba? Domin nasan baki iya girki ba"


"Subhanallahi! Maimunari, dama baki iya girki ba?"
Taka Mohan nayi tare da hararan shi.
"Wash ta taka min kafa, Abien Moonah kaga zata cire min yatsu."
"Gulmar ka ya ja maka" ya faɗa mishi haka.
Wayar shi ya dauka bayan ya danna wata lamba yace.
"Akwai yarinyata zata fara zuwa daukar darasi Insha Allah Asabar da lahadi. Sauran ranakun idan ta taso aiki.zata zo"


"Abie har da Auta"
"Toh su biyu ne"
Hararan Mohan nake kamar idanuna zasu fadi kasa, mutum ya zama gulmammame,


Haka muka sha hira sannan muka mishi sallama, bayan mun kuma hanya yake ce min.
"Yau naji kamar nayi hauka da aka ce min kin suma, ina meeting na fito muje na ajiye ki a gida sai na koma domin ni suke jira."


"Toh Sarkin gulma"
"Eh na yarda"
Haka ya ajiye ni a gidan, na samu auta ta gama abincin, cikin tsokana nace mata.
"Kwashe kayan shirmen ki nan ba ci zanyi ba, naci me dad'i a gidan Abie na"
"Wallahi baki isa ba har dare shi zaki ci"


Haka dai yanayin yake tafiya, ban san wanda ya gayawa Ansar anyi baikona da Mohan ba, sai kirana yayi yana faɗin.
"Munnah amana bai ce haka ba, ashe kuma anyi baikon ku baki gaya min ba? Amma har yau ban cire rai da samun ki, domin nasan ke allura ce cikin ruwa mai rabo zai dauka, dan haka ina ban ina miki fatan Alkhairi, amma ban cire rai dake ba"


"Ansar ni fa bana son damuwa, dan haka ka bar ni da abinda nq zab'a don Allah ka nime wata mace mana, ina ruwana da kai ne, iya abokin shawara na dauke ka amma na Fahimci kai baka san haka ba, Mohan shi zab'in raina ne kai kuma iya abota kawai na dauke ka. Don Allah karka min abinda zan tsane ka har abada."


Na kashe wayar, tare da share batun shi kamar ma babu abinda ya faru.


***
Ina ajin daukar darasin girki aka kirani, ban dauka ba. Sai bayan da muka fito na dauka.
"Maimunari ce?" Aka tambaye ni,
"Eh nice" na bata amsa,
"Toh kizo gurin Saloon din Uwani"
"Ban gane ba dawa nake magana?"
"Idan kin matsu ki"
"Toh"


***
Hira suke da Khalil da sauran abokan shi, akan yadda za ayi tsarin bikin shi domin nan da kwana uku za a tafi Damagaram niman auren Maimunari. Sako aka turo mishi, yana kishingide ya duba wayar dan a tunanin shi Moonah ce.


A hankali ya bude an rubuta a kasar hotunan da videos din.
*Ka tambayi matar da zaka aura maza nawa ta sannan dadin su haka! Maza nawa suka kwanta da ita? Ka tambaye ta sau nawa tana zubda cikin? Wannan hujjojin idan basu isa ba, zan kara maka wasu hasken domin ina son na ceto ka daga gurbatacciyar zuri'ar da zaka kai cikin Ahalinka ne."*


Mikewa yayi tare da barin falon, ya bude videos da hotunan, zuɓewa yayi akan gwiwar shi, tare da fasa wata irin ihu,, sai da Khalil ya biyo shi. Saka wayar yayi a cikin aljuhun shi. Ya dauki Jacket din shi.


"Mohammed Mamman Nasir, lafiya?" Bai basu amsa ba.


Ya ja motar shi da gudu ya bar gidan. A sanyayye na sauka a motar, naci kuka har na godewa Allah.
A hankali nake takawa har na isa bakin apartment din naji wata irin birki, juyawa nayi naga Mohan ne, fuskar shi babu annuri. Yana zuwa ya fisgo hannu na, ya nufi motar shi dani.


Ya cusani sannan ya juya ya koma mazaunin shi ya tadda motar muka bar gurin, ban yi mamaki ba, sai da muka bar garin Niamey, ya faka birki tare da cilla min wayar shi. Yana huci.
Bude wayar nayi dake nasan key din, na shiga hango abinda nake b'oyewa.


Ban san ya akayi ba kodan zan rabu dashi ne, na sake mishi murmushin takaici, nace mishi.
"Meye a cikin dan kawai kaga videon ina holewa?"
A birkice ya kalle ni, ya ma rasa me zai min, kallona yake yaga babu wani abu a raina sai ma dauke kai da nayi, tare da fara kokarin barin cikin motar, ya saka lock, sannan ya kuma fisgar motar. Muka dawo Niamey.


Lokacin Mahaifiyar shi tana kiran shi, har bakin apartment ya dawo dani, ya bude min kofar da kanshi, na fita ina wasa da jakata.
"Ba zan iya miki kome ba, kuma har gobe ina kan baka nason aurenki amma ki sani na tsane ki kamar yadda na tsani abokin gabana, sai na azabtar dake ta hanyar da baki zata ba, munafuka mai fuska biyu."


Murmushi nayi mishi sannan sannan na shiga cikin gidan abina, ina shiga na wuce d'akina na zauna tare da rufe kofar, ashe kuka rahama ce, domin an wayi gari na kasa kuka ma. Haka ina ji ina gani barci ya kaurace min. Damuwa tayi min yawa.


Ban gaya kowa ba, haka na yi ta shiru ina gayawa Allah kuka na..
**
Yana shiga cikin gidan su, ya zube a falon Mahaifiyarshi, tare da dafe kirjin shi. Mika mishi Tap din tayi.
"Yarinyar da ka nuna kana son sama da kowa ita ce ta sayar da Soyayyar ka. Kaji irin hirar da suke da Hanan."


Tab'a play yayi tare da kallon murmushin da take..
"Dama ba son shi kike ba?" Hanan ta tambaye ta,
"Bana son shi, idan zaki iya sayan soyayyar da nake mishi na karya bani kudi, na bar miki shi har abada"


Kallon ta Hanan tayi sannan tace mata.
"Yan mata dayawa burin su Mohan ke kuma kin same shi kin watsar."


"Mahaukacin zan so? Ina bani kudi domin soyayyar karya nake mishi" idanun shi yayi jajjur, ya mike a hankali, yana kallon aka mika mata chep ta mike tare da barin gurin.


Mikewa yayi tare da barin gurin Ammyn shi. Ya shiga dakin shi ya zauna ji yaƙe kamar zuciyar shi zata fashe, ranar ko masalaci bai shiga ba, a dakin shi yayi Sallah.


Bayan isha Hanan tazo ta kananeye shi, sai da ya buga mata tsawa ya wurgota waje daga dakin shi. Haka kawai ya tsani kowa.

**
A hankali soyayyar mu ta koma k'iyayyar mu, kulawar mu ta koma watsin mu, ban san me yasa Ubangiji ya saka min hakuri akan shi ba. Sai dai ko da wasa bana bin ta kanshi,, a hankali na sauya daga yadda nake na koma shiru shiru, Abie yaso fahimtar halin da nake ciki na ki.


A cikin tsakanin na nufi Damagaram, nayi kewar su. Kwana na uku, na dawo gurin aiki na.


--- Nazo shiga harabar gurin aikin na hango motar shi, dauke kai na nayi, tare da nufar hanyar da zata kai ni cikin Office din Abie.
Ji nayi an riko hannuna, ban yi mamaki ba, dan haka na juya na kalle shi, ja na yayi tare da kai ni cikin motar shi na zauna. Ya shiga, wani gurin shakatawa ya kai ni, inda babu cunkoson mutane, ya nuna min guri na zauna. Zama yayi yana kallon yadda na dauke kai na.


"Idan kudi kike bukata me yasa zaki sayar da soyayya ta? Duk fadi tashin da nake akan ki bai isa ba, kin ci Amanata ban miki wani abu ba, ace kuma ke da bakin ki. Kike fada cewa baki sona? Soyayyar karya kike min? Meye nayi miki da zafi?"


Ban ce mishi kome ba, sai murmushi nake ina kallon shi. Sannan ya cigaba da cewa.
"Na zata ke din kamilar mace ce,, mai daraja ashe ke din watsatsiyar mace ..." Bnsan lokacin da na kifa mishi mari ba, tare da kallon cikin idanun shi.
"Wannan ya zama kashedina da kai na karshe karka kuma tab'a kimata"


Na mike tare da barin shi a gurin cike da mamaki, ba marin bane ya bashi mamaki, yadda ta iya kare kimarta. Hannun shi ya kai tare da shafa gurin, sannan ya mike yabi bayanta, yana kallon yadda take share kwalla, haka ya tab'a mishi zuciya, yjaa kallon ta shiga motar haya, haka ya bi bayan su, aka ajiye ta a gida. Tunda ta shiga ta zauna take kuka.


Tana son Mohan, amma tana ganin kawai kamar yadda mahaifiyar shi ta bukata haka zaa yi.


Abinda ya faru kuwa bari mu waiwaya bayan.


**
Lokacin da na sauka a bakin shagon Aunty Uwani,.na shiga manyan motocin alfarma na gani ina ganin haka na fahimci daga fadar shugaban kasa ne, dan haka na shiga a sanyayye, na samu babu kowa a shagon sai Ammyn da Maman Hanan, sai Hanan da Jalilah, ina tsaye. A hankali naja kujera na zauna ina kallon su.


Tasowa Hanan tayi zata mare ni, ta kasa isowa inda nake komawa tayi ta zauna. Sannan tace min.


"Ki cire min zoben hannun ki" kallon zoben nayi tare da sake murmushin farin ciki.
"Ai ko mutuwa nayi zai yi wuya a cire shi a hannuna domin zobe ne da Masoyina ya saka min"


"Mara kunya! Ba zaki cire zoben ba, domin kasawa ce ta saka abinda kika saka.!"
"Allah ko?" Na tambayi Mamanta ina d'ge mata gira.


"Nuna mata suwaye wadannan"
A hankali suka miko min hoton su Innah da Baba ne. Anan ne zuciyata yayi rauni.


"Zaki iya rabuwa da shi ko sai na saka a kashe min iyayenki! Idan har akwai abu me daraja toh wallahi bayan iyaye ne zaki rabu da Mohan ko sai na saka an yanke wuyar su."


Mikewa nayi tare da cewa.
"Zan rabu dashi, meye a cikin soyayyar shi bayan ina da iyayen da suka fishi. Alhamdulillahi da samun iyaye na gari da nayi, amma ki ajiye a ranki wallahi kin kashe d'anki da hannunki,.kin lalata farin cikin shi!"


"'Mika min chep tayi sannan tace min kar na kuma dawowa rayuwar shi " wannan sun ishe ki rayuwa domin iya arzikin da baki taba samun ko gani Bane!"


Murmushi nayi sannan nace mata.
"Zan dawo miki dashi lokacin da ya dace nagode"


Ina gama fadar haka na juya na bar gurin, ina tafiya ina kuka sai da nayi tafiya mai nisa, sannan na samu guri na zauna na sha kuka na ya ishe ni, sannan na mike na nufi gida, ina sauka yana zuwa ban san meye yasa kaddarata take da zafi haka ba......


Wasan yana tafiya fa.....


*_Wallahi kuyi Vote yau ina son na baku page 3 Insha Allah amma sai kunyi comments da Vote 🤷🏼‍♀️🤔🙄_*
#Mai_Dambu
[8/10, 11:13 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1112993401?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=lW5RihoQ3v8FZFWeHyymHjbPBLOXqm7aK4EKMuRrfSy%2BfSjbHsNuLRY8JQnuIpGqm8aZk9dQwvCQ4LSVWXgTHbqEvuaBGA%2Ba9UjO%2FHjd0TMtTTHl8QCE2uzXe1MDgaIR


🐂🐂BOROROJI🫀🫀


~The Journey of Destiny💔~


Mai_Dambu


Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....


BABI NA HAMSIN DA DAYA.


Ina dawowa ya tare ni da wani shirmen shi, taya zan saurarre shi. Bayan ya gama min duk abinda zai kuma yace zai tab'a mutuncina, akan Mohan na fada gararin rayuwa. Yau shi yake zagin mutuncina, saboda ƙaddara ta faɗa min.


A hankali na shiga ban daki nayi alola nazo na tadda sallah, ina idarwa na kwanta. Gashi auta bata nan ta tafi gida, bani zuwa ko ina.
Tsawon kwana uku ko kofar falon mun ban leka ba, ina kwance. Nasan ban da lafiya amma na rasa waye zan kira, ranar da jikin yayi min tsanani kamar zan mutu. Shine na tashi tare da ɗaukar wayata da ta mutu, dakyar na jonata, tana kawowa na kunnata.


Sakon shi sun kai dari dai na Abie da Auta, a hankali na shiga sakon Auta na kirata.
"Auta..... Kizo... Zan ... Mutu" na fada mata, kafin na kashe wayar, na kuma kiran Abie.
"Abie.. zan.. mutu... kirjina... Numfashina" a hankali na fada tare da komawa na kwanta.


** Ya fito kenan daga Shari'a, suna tattauwana da wani Alkali, kawai ya ga kiran Maimunari, dauka yayi tare da sakawa a kunnen shi, yana faɗin.
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, gani nan"
Da sauri ya shiga ofishin sa ya dauki abinda yake da muhimmanci, sannan ya fito. Driven shi ya mike.
"Maza kai ni, Apartment din yarinyar nan"


Da sauri ya shiga motar, suka bar kotun. Ita kam Auta tana katse kiran Mohan ta kira dan tana da number shi, yana ganin kamar ba zai dauka ba, ya saka a kunnen shi.
"Hammah Mohan, Maimunari fa bata da lafiya wallahi ta kira wai zata mutu."
Bai san lokacin da yayi watsi da abinda yake ba, ya nufi gidan. Yana isa ya samu ana ta kokarin bude kofar dakin su. Yana zuwa ya daki kofar da kafad'ar shi, amma bai bude ba, cikin zuciya ya ta fi da gudu ya tokari kofar dai da ta balle, ya hangota kwance daga ita dai kayan barci riga da wando, rigar me hannun shimi. Kuma rigar irin shara shara ne.


Da wani karfi ya maida Abie waje.
"Don Allah ka tsaya, Iyalina ce karka je kanta haka wallahi mutuwa zanyi idan wani ya kuma ganin matar da zan ajiye a Ƴaƴana" ya faɗa idanun shi na kawo ruwa. Murmushi Abie yayi tare da jin tausayin yarinyar, cire ƙatuwar jacket din shi yayi yana faɗin.
"Kaji a ranka ni Ubanta ne, ba zan tab'a ganin wani abin da zai d'aga min hankali ba, saka mata bamu da lokaci."


Haka ya saka mata sannan ya dauko ta cak, ya fita da ita, motar shi ya saka ta. Suka nufi asibiti da ita, kuma dukkan su. Cikin rawan jiki aka amshe ta, tare da nufar dakin gaggawa da ita, tun da ya dauke ta, yaga yadda take zubda kwalla. Haka ba karamin d'aga mishi hankali yayi ba, zama suka yi kowannen su da abinda yake damun shi. Lokacin da Khausar ta fito.


"Me ya faru ne hakan jinin ta ya hau sosai ga zuciyarta yayi mugun kumburi, wallahi aka Cigaba da haka. Zata iya rasa rayuwar ta, don Allah a kula sosai domin rayuwarta yana cikin hatsari" ta faɗa tare da mikawa dan uwanta, takardan fita yayi da mugun sauri. Kifa hannun shi yayi a fuskar shi, tausayin halin da yarinyar take ciki ya kara raunana mishi zuciyar shi, kaunar yarinyar a jinin shi yake jin shi.


Haka ya dawo da kayan da aka bukata, kiran Khausar yayi ya mika mata, ta shiga dashi. Yana zaune a gurin har zuwa azhar, sannan suka fita zuwa masallacin sabida lokacin sallah da ta shigo, bayan sun idar, suka dawo lokacin an sauya mata daki,haka suka zauna a jikinta, aka rasa waye zai tafi ya bar dan uwan shi.
Dole Mohan ya kira Radiyah, ita tazo ta zauna. Sai da ta kwana ta wuni sannan ta farka daga dogon barcin da ta samu, tayi.


A hankali nake jin zafin da yake kirjina yana raguwa, ina jin sauƙin duk wani damuwa da yake raina ya ragu, a hankali na fara bude idanuna, haske ne ya cika min idanuna kafin na lumshe idanuna, na kuma buɗe idanuna. Lumshe su na kuma.


*Indai da haka zaki rayu sai kin mutu sau dubu! Tashi domin ki tsaya da kafarki bude idanun ki! Rayuwa anyi shine domin bautar Allah da kuma faffutikar rayuwa tashi domin faffutikar rayuwar tashi domin rayuwar iyayenki suna tare dake maza tashi*


"Aaaah!" Na ja numfashi tare da bude idanuna tar, ina kallon su. Murmushi Abie ya sakar min yana dauke kwallar da yake gefen idanun shi, ya karaso inda nake ya rike min hannun.
"Muna sonki! Muna kaunar ki, me yasa ba zaki rayu dan mu ba? Don Allah ki tashi muna nan domin ke!"


Ya fada tare da damke hannuna, kwalla ne ya zubo min ina kallon shi. Tare da gyada mishi kai.
"Toh tashi, tashi ki nuna min jarumta ki" kokarin tashi nake ya dage goshina.
"Da saura amma ki kula da lafiyar ki"


Daga haka ya mike tare da barin d'akin, haka Radiyah da Khausar suka taimaka min na tashi, brush ta kawo min da ruwa na wanke bakina, sannan suka bani ruwan zafi nasha, tare da taimaka min na shiga wanka.


Ina fitowa naji karfin jikina sosai, sannan na gabatar da sallah da ake bina, tare da wanda ya wuce ni, ina idarwa na fara azkar. Shigowa yayi tare da Dan Ba'are. Ko kallon shi ban yi ba, haka na idar na mike muka gaisa da Khalil, sannan na juya musu baya, ina tari

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login