Showing 114001 words to 117000 words out of 181864 words

Chapter 39 - Bororoji Compelet Book Document by Mai Dambu .txt

29 Jan 2025

6275

nufi cikin gidan, da sallama ya shiga falon ya hango Benazir, a tsaye tana latsa waya. Dake masifa ya ciyo shi bai tsaya duba ba, kawai ya isa gabanta cikin fada yace mata.
"Gaya min meye nayi miki?" Ya fada da karfi, a razane ta kalle shi. Bakinta na rawa,
"Mohan Mamman Nasir Aghali, bani bace tana dakina bari na kirata, falon da mutane,
Sai lokacin wani mugun kunya ya kama shi, juyawa yayi tare da cewa.
"Kuyi hakuri don Allah"
Nuna mishi gurin zama Benazir tayi, ya je ya zauna sannan ta haura sama.
"Assalamu alaikum! Kamar Almamoon ko?" Murmushi nayi mata, sannan nace mata.
"Dama baki gane bane? Tun tuni na Fahimci kawar Almamoon ce ke ai abokiyar fada"
"Waw! Kizo Mohan Mamman Nasir Aghali ya zo?"
Murmushi nayi sannan nace mata.
"Kice ba zan zo ba, yayi tafiyar shi" na fada mata tare da gyara kwanciya na, kasa fita tayi tana kallona.
"Addah Munah!"
"Bana son jin maganarki don Allah fita"
Tana fita na mike da sauri zuwa ban dakin, ina shiga na dauke almashin da na gani a ban dakin na shiga yanke gashina mai mugun tsawo da kyau, na yanke shi kaf, sannan na dauki reza ina kuka sai da na kwashe gashin kaina, sannan na durkusa a gurin ina kuka, kamar raina zai fita. Zan koma gurin Innata, ina mai kama da maza sak. Buga kofar Dr Zainab take amma fir naki kula ta, ina jin ta bar dakin na fito, ashe yana tsaye. Har zan koma ya taso da sauri, abinda ya faru tsakanina da Malik ya dawo min wani irin ihu na saka tare da zuɓewa kasa. A rud'e ya karaso tare da daukata, ya dauko dani, Lokacin dan Ba'are ya shigo gidan kenan, dan ya gaji da zama.
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, d'azun muka dawo asibiti da ita fa, yanzun kuma wani abu ne ya same ta?" Inji Dr Zainab a rud'e.
"Mohan kawota Mommy likita ce."
"Bani kayan aiki Benazir" sake rikicewa Dan Ba'are yayi jin sunan Benazir, da gudu ta haura zama can sai gata da kayan, ta shiga dubata, kafin tace musu.
"Ta firgita ne, zuciyar ta yana bugawa sama da yadda muka dawo, ka firgitatta ne?"
"Akan me zan firgitatta, yarinyar da nake kauna? A'a kawai tana ganin na nufeta ta yanki jiki ta fadi bayan ta kwala kara."


"Hmm" tace a kasan ranta kuwa tace.
*Allah kasa ba sanadin fyaden bane wannan abin ya same ba?*
"Dr baki ce kome ba?" Ya kuma tambayar ta,
"Akwai abinda ya firgitatta ne, amma babu Matsalar kome" rubutu tayi sannan ta mika mishi.
"Kayi hakuri, gashi ka sayo mana maganin da ruwa," ta ciro kudi a jakarta ta bashi.
Mikewa yayi sannan ya ce mata.
"A'a barshi kawai"
Ya fita daga shi har dan Ba'are, kuma zuwan su tare bai zama dole ba, abinda yasa yayi haka dan ya katse mishi kallon BENAZIR ne, kuma yayi dacen haka domin tunda suka fita yake auna mishi maganar banza.
"Dan bakincikin da Hassada ina kallon annurin zuciyata zaka ja hannuna."
"Kai dan Ubanka yar mutane ba zata iya daukar nauyin ka ba, wallahi yaga musu ita zaka yi"
"Allah ya isa tsakanina da kai, wallahi zata iya dauka na, don Allah karka fara."


Dariya abin ya bashi bai kuma kula shi ba, har suka sayi maganin a wani Babban kanti. Wayar shi ce tayi kara, ya saka a kunnen.
"Yallabai Nagode domin na san aikinka ne"
"Karka damu, Mahaifinka yana don magana da kai ka nime shi."
"Nagode sosai, Insha Allah zan Nime shi."
"Toh babu kome, kayi ƙoƙarin dai."
Daga haka suka yi sallama, lokacin da suka isa gidan ruwan aka saka mata a dakin Dr Zainab da yake kasa.


Sai da safe suka mata, sannan suka wuce gidan Mohan da yake Jacader. Sun samu babu kowa. Dan haka suka shiga abin su, daga nan suka wuce cikin gidan.


***
Karfe biyar na asuba, ina jin motsin Dr Zainab tana ban daki, na mike tare da cire ruwan da yake hannuna, sannan na dauki biro da takarda, na tsaya ina kallon shi. Kuka ne ya tawo min haka na hadiye, ina jin zata fito na koma na kwanta.
Fitowa tayi, tare da fara gabatar da sallah nafillah, Ni kuma ba shiga ban daki, nayi alola da wanka. Sannan na fito na bar dakin na haura zama, sai da na gama shiri tsaf na duba jakata babu kome a cikin shi. Ina saukowa kasa na hango jakarta ban tab'a sata ba, amma a karon farko dan nisanci Mohan, na bude jakar na dauki kudin mota da na shan ruwa, sannan na ajiye mata wasikar godiya da fatan Alkhairi tare da laifin da nayi mata na satar Kudinta ta yafe min zan tafi gida ne.


Ina isa bakin get na mikawa Baba shima nace mishi.
"Bba akwai wasu maza biyu zasu zo zaka ga dayan su kato ne ka bashi wannan wasikar" sannan na fita daga gidan.


Ina fita da sauri, babu ababen hawa, dakyar na sami abin hawa. Ya kai ni tasha, ina zuwa na samu mota amma saura mutane biyu, haka na sha zama har karfe bakwai saura, kafin Allah ya taimaka muka tashi. Ajiyar zuciya na sauke lokacin da na Fahimci mun hau kan hanya.


Na tsani kome na rayuwa, tun banyi nisa ba, kome ya lalace min. Tun ban yi dogon tafiya ba. Na rasa mutuncina, ina kuma da na matsa kaina, rayuwata zan rasa ba mutuncina ba, tir da wannan soyayyar da bata da riba, daga lokacin da na hadu da Mohan fara fuskar yadda rayuwa take, nagodewa Allah, Innah tana raye. Amma ba zan iya gaya mata wannan mugun labarin ba, domin Mohan zata daurawa......
UZURI💓
*Bai zama dole gobe ku ga Posting da safe ba. Domin wallahi ina jin barci kuma yara sun sami hutu dan haka idan kun gani toh Madalla idan baku gani ba! Sai dare Insha Allah idan ban zama Busy ba kuma sai jibi Insha Allah domin ina da uzuri gobe Insha Allah*
#Mai_Dambu
[8/7, 10:04 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1110763041?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=PYEroEpzcfPkMnsivXwBeeuxpzKGK0fkWNcFQtCIRTayJ6sMVuy4zCFcXax%2BjsXVmcWqYu7JpcasekmM2WVikzyWFlN%2FH2zr4nlW%2F5vRpIWR%2BVC4yv60%2F1T6BeQc23Yo
🐂🐂BOROROJI🫀🫀


~The Journey of Destiny💔~


Mai_Dambu


Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....


BABI NA ARAB'IN DA HUƊU.


Ajiyar zuciya na sauke lokacin da na fahimci na bar Maradi naji burkina ya cika, hankali na ya kwanta. Taya zan fuskanci Innah da wannan abun. Share kwalla nayi tare da alkawarin ko wuta tace na fada sai na shiga saboda na kyautatta mata.


***
Karfe tara na safe.
Fitowa tayi tare da kallon falon a gyare, zama tayi tana kallon hanyar sama, tana nazarin yaushe zasu fito. Karar sautin takalmin Benazir ne ya sa ta, d'ago kai tana kallonta.
"Beenah ina Addah Munah?" Wannan shine tarbiyyar da tayiwa yaranta da ita kanta, indai Babba ne zata kira shi da sunan manyan tare da nuna musu cewa babba ne a bashi girman shi.
"Mommy bata dakin ki ne?"


Kallonta tayi sannan tace mata,
"Kamar ya bata dakina bayan ni nake tambayarki,"
"Toh ai bata dakina ne, dan ta shigo da asuba tana fita na farka"
Wani irin rawa Jikinta ya dauka bata san lokacin da ta nufi waje ba.
"Malam Idi bakuwar yarinyar nan tana iya?"
"Hajiya ai ta tafi, gashi wannan tace na bawa bakin jiya da suka shigo." Ya mika mata, fararra takardan, ganin har da tambarin Asibitin su yasa ta koma cikin gidan, ta duba jakarta. Samun nata tayi, jikinta a matukar sanyayye ta bude shi.


*_Assalamun Alaiki, Dr Zainab. Ina kara mika ta'aziya ta na rashin mijinki, na tausaya miki kamar yar da ta rasa mahaifinta Uwar da ta rasa mijinta. Allah yayi miki ni'imommin rayuwa ta ko ina, na gode da ƙaramcin ki a gare ni. Nagode sosai sai gashi ina tsaka da miki bayanin zan koma gida. Mohan Mamman Nasir ya zo min, don Allah ki taimaka min da rufe sirrina, kisan yadda tafiyar kaddara take, baka shirya mishi. Idan ya same ka haka zaka yi hakuri dashi, sannan kiyi hakuri na miki sata ban tab'a sata ba. WALLAHI ban tab'a zina ba. Kiyi hakuri ki rufa min asiri kodan rayuwar Yaranki nan Benazir da Yumnah. Suma mata ne idan kika boye nawa Allah zai boye naki da nasu, naso ace Mohan shi ya fara ta'adina amma sai gashi ƙaddara ta faɗa min. Ban sani ba ko iyayena dayan su ya tab'a wata ne ko yar wani ne ban sani ba, amma nasan zina Bashi ce. Idan kuma biya aka yi a kaina Ubangiji yasa haka ce mafi Alkhairi aka ina bashin ya tsaya haka kar ya cigaba da tab'a halina nagode sosai ina jinki kamar uwar da ta haife ni Maimunari I Umar Wodaadabe_


Kuka take kamar yanzun aka mata mutuwar mijinta. Wani irin kaunar yarinyar take ji har cikin ranta, ta kasa magana sai kuka kawai take tana karawa.


"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, Ubangiji, me yasa? Allah na tuba"


"Assalamu alaikum" Mohan da Dan Ba'are suka yi sallama.
"Wa'alaikimun salam!" Benazir ta amsa musu itama tana share kwalla, yarinyar tana da hakuri kamar mahaifinta tun rasuwar mahaifinta sai ta nutsu sosai,


Tun ba a gaya mishi abinda yake ba, jikin shi ya bashi Moonah ce tayi wani abu. Shiru yayi yana jin sautin kukanta har cikin kanshi, ya tsani yaga mace tana kuka komi kankantar ta kuwa.
"Meke faruwa?" Dan Ba'are ya tambaya,
"Sai ka tambaya ne? Moonah ta tafi?" Ya fada kamar baya son maganar. Kallon wai haka ne dan Ba'are yayiwa Benazir. Mika mishi takardan da Dr Zainab ta amsa a hannun Malam Idi, shi kuma ya mikawa Mohan.
"Ka karanta mana" inji dan Ba'are,
"A'a kai ka karanta" kallon shi yayi sannan yace mishi.
"Na yarda da kai ne"
*_Amincin Allah ya tabbata a gare ka ma'abocin tausayi da taimako ban sani ba ko zamu sake haduwa, amma dan darajar iyyenka karka nime Ni! Idan ka Kuskura ka tawo nima na. Zan tafi zan tafi zan tafi garin nisan nisa! Mohammed Mamman Nasir Mohan Aghali! Nasan kai waye nasan kai dan manya ne! Mohan nasan kana Sona! Amma kuma a yadda kake son ba zai mana amfani ba! Son ba zai mana rana ba, son ba zai amfane mu ba! Mohan ka duba mana yanayin mu! Ni yar talakawa ne futtik kai kuma ɗan shugaban kasa! Gaskiya kayi hakuri bamu dace da juna ba! Nagode sosai daga me kaunarka Maimunari_*


Sunkuyar da kai yayi, yana wani irin haki tare da dafe saitin zuciyar shi.
"Damagaram"
Ya mike dakyar ya nufa hanyar fita daga gidan. Kurawa Benazir ido yayi, sannan yace mata.
"Kingan shi nan? Yana kaunarki kimanin shekaru biyu da suka wuce. Dr Khalil mutumin kirki ne. Dr nayi Imani idan ya wulakantatta zan iya saka bindiga na harbe shi, amma ki saka a miki bincike sojan Nijar ne, kuma wallhi zan zame mata Dan uwa, na zan tab'a bari tayi kuka da Khalil ba. Don Allah Karki bari soyayya ta bashi wahala. Bai san wahala ba sai a kaina. Don Allah ki taimaka mishi da Kaunar Benazir yake kwana yake tashi!."


Da gudu beenah ta haura sama, bata kuma dawowa kasa ba, Dr Zainab kan hawayen ta ne ya tsaya cak. Wani irin gata Allah yayi mata haka ne? Har gida ana niman soyayyar d'an babban gida, Family Ba'are da yake Agadaz. Masu rike da Wazircin garin. Kwalla ne ya zubo mata.
" Sai na yi nazari!" Daga haka ta mike tare da bin bayan beenah.


Lokacin da ta shiga dakin ta sami yarinyar a tsakiyar gado, ta cusa kanta a tsakanin cinyoyinta, tana kuka. Zafi biyu ko na ce uku ne ya hadu mata, zama tayi tare da janyo yarinyar a jikinta.
"Beenah! Baki son shi ne?"
"Mommy. Bi yarinya ce fa, kuma Daddy yace nayi karatu akan me zan yi aure? Ina tsoron shi kar yayi ta."
"Kinga kamar ba zai yi haka ba, yan uwan Daddyn ku, tun da na dawo suka watse babu wanda ya zauna min, Nanny ma ta tafi. Beenah bani da kowa sai ke da Yumnah. Bani da dangi, Beenah ki duba idan bai miki ba, ba zan tab'a miki dole ba, abinda kike so shi nake so."


"Nagode sosai Mommy"
Insha Allah zan duba." Ta fada tana share kwallarta, tun da suka haɗu a airport, ta manta shi ashe shi yana sane da ita, yana nan yana niman ta a ranshi, lumshe idanun ta yi.
"Mommy ba zan tab'a yin aure ba, bana son na tafi na barki kina kewar Daddy." Kwalla ce ta zubo mata, turo kofar dakin Yumnah tayi wacce tashinta kenan daga barci.
"Mommy ina Addah Munah!"
"Ta tafi"
"Mommy me yasa baki barta ba? Muna sonta muma tazo ta zauna."
"Gashi bani da number ta."
"Ina dashi, ranar da wayarta ya fadi a bayan gado ta samin Number na kirata, ina da shi."


Da sauri ta fara duba wayar, amma bata samu ba.
"Mommy ashe banyi saving ba"
"Kara dubawa da karfe nawa kika kira?"
"Kamar da dare ne"
"Toh duba mugani"
Can kuwa ta hango shi kasa can, kiran wayar tayi. Kamar ba za a dauka bata, sai kuma aka dauka.
"Addah Munah! Me yasa?"
Amsar wayar Mommy tayi.
"Na zata ina da iko dake ashe ke yar kanki ce? Me yasa ba zaki gaya min ba zaki tafi?"


"Kiyi hakuri."
Daga haka ta kashe wayar baki daya, sake kiran suka yi yaki shiga. Shiru suka yi. Haka kawai ta shiga kallon rubutun Maimunari, Wodaadabe? Gabanta ne ya fadi.
.
Bai tab'a shiga b'acin rai da bakin cikin rayuwa ba irin yau, daga shi har Khalil babu me iya magana, kowannen su da abinda yake damun shi. Har suka bar Maradi.


. Karfe biyu na rana muka shiga garin Damagaram, ban isa gida ba, sai da na shiga kasuwa na sayi kayan maza, na tsaya a gidan wanka na sauya sannan na nufi gidan mu da kayan, sallama nayi. Ina tana daki, a hankali na nufi dakin da jakata, ina shiga na zube akan gwiwata, kwalla na zuba min, bata da lafiya ta rame sosai, a hankali na rarrafa na isa gaban ta, ina zuwa na kwanta akan cinyarta, ajiyar zuciya ta sauke. Kafin tace min.
"Nayi laifi babba na boye ki, amma yau da kika dawo min kina kuka sai nake ganin kamar nice silar kukanki? " Komawa nayi jikinta na kwanta, ina shashekar kuka.
"Nayi ta ja miki jafa'i da masifa bayan wanda kike ciki, na ja miki tashin hankali da damuwa bayan wanda kike ciki, nayi fushi na gaya miki magana, wai dan karki juya. Toh ya za ayi kaddarar mu ce tazo a haka. Mun yi tunanin tunda Allah bai bamu Haihuwa ba, sai mu mayar dake namiji domin gudun ƙaddara, nayi tsammanin dan kina sufar maza ba zaki tab'a jin namiji ya burge ki ba! Ashe gudun ƙaddara."


"Innah ki yafe min, don Allah ki yafe min. Wallahi ko wuta kika ce na zauna Innah zan zauna, Innah idan irin rayuwar da kike so ne nayi zan yi don Allah karki kuma barina na tafi wani gurin na hakura da karatun ma."


"Mohan da?" Tambaye ni, tashi nayi ina kallonta, zuciyata ta na bugawa da sauri da sauri. Zare hular kaina nayi, taga kwandila tass na kwashe gashin. Cikin sanyin jiki tace min.
"Me yasa?"
"Bai dace dani ba, iyayen shi masu kudin gaske ne kuma manyan mutane ne, sun zab'a mishi wacce ta dace da shi, idan na cigaba da kula shi akwai matsala ne kawai na hakura."


Rike hannun tayi cikin kulawa.
" A soyayyar gaskiya ana samun fada da zage zage, amma ba a tab'a rabuwa ba, yayi miki wani abu ne?"
"A'a bai tab'a kallona da nufin zina ba!"
"Soyayyar gaskiya ce a kwayar idanun shi, kaunar gaskiya ce a jinin shi.yasan kin tawo?"
"Na bada sako a bashi."
"Tabbas zai zo! Tafiyar Ƙaddara ba a shirya mishi, zai zo domin zai biyo sawunki, zai zo yana biye dake kamar inuwarki."


"Innah Ni fa bana son shi" na fada mata kaina a sunkuye.
"D'ago ki kalle ni!" Kasa d'ago kai nayi ina wasa da hannuna.
"Har yau kina son Mohan"
"Nifa bana son shi "
"Hmm"
Tace min, da sauri na d'ago kai ina kuka nace mata.
"WALLAHI bana son shi"
"Toh Allah ya kyauta," tace min.


Sallah muka yi na kwanta a jikinta, ina jin wani sanyi, sai bani labarin irin taimakon da Ansar yake musu,kuma ba ga haka tun daga cimmar mu, fada tayi min akan askin da nayi, bayan la'asar ta kalle ni.
"Ki saka kayan matanki, kin fi kyau da shigar matanki kinji Uwata."


"Toh." Na sauya kayana na dauki katin bankina, na nufi bank naje na cire kudi, na yi mana sayayya kafin na dawo,ina sauka a napep na hango motar Hammah Mohan. Shiga cikin gidan nayi, tare da sallama yayi wani irin zama kamar Almajiri, abin tausayi. Dauke kai nayi tare da gaida Khalil sannan na wuce dakin Innah na zuba kayan abincin na dawo na wuce d'akina.
"Uwata kizo" inji Baba da yake zaune. a hankali na zauna ina kallon shi.
"Uwata ga Mohan, meye yayi miki da zafi?"
"Bana! Na gaya maka gaskiya!"
"Shi nakeson ji"
"WALLAHI bana son shi ne! Yayi hakuri bana son shi" a hankali ya d'ago kai yana kallonta, kafin ya sunkuyar da kai.
"Meye nayi miki? Meye nayi miki da zafi?"
"Ka gane mana kawai bana sonka ne, idan kuma ka matsa min zan bar garin nan na gaya maka ba zaka tab'a gane inda nake ba" dafe kan shi da yake sarawa yayi, tare da kura mata ido.
"Ki gaya min meye ya faru?"
"Kai dan Shugabanan kasa!"
"Naci kaniyar shugabancin kasar meye matsalar shugabancin kasar da soyayyar mu?ke kiga ya meye nayi miki da zafi?"


"Toh Malam an tab'a soyayya Dole ne? Tunda tace bata yi a sake mata mara tayi fitsari mana. Kazo ka saka yarinya karama a gaba da ido kamar cutar haukar ta motsa,." Rintsa idanuna nayi sabida naji ciwon maganar shi, amma ga Hammah Mohan bai kula shi ba, dawowa gabana yayi tare da riko hannuna, yace min.
"Gaya min don Allah, meye nayi miki?"
"Baka min kome ba, Ni da kai ne kamar bamu dace da juna ba, idan da zaka yi hakuri haka zai fi ace ana takura junan mu nan, Kayi hakuri kana da zafin kishi. Ni kuma mutum ce da Allah ya halicce ni da kaddarorrin mabanbanta,. Ban san yadda zaka dauki kowacce ƙaddara ta ba, soyayyar fatar baki zata iya gushewa daga zaran ka fahimci ƙaddara da yake yawo a kaina, don Allah kayi tafiyarka zan Nime mutum daidai dani."


"Maimunari kowacce irin ƙaddara take zagaye dake zan iya zama dake a haka kai koda kuwa ace a gidan karuwai na tsinto ki, toh wallahi zan zauna dake a haka, fatana ki yarda da Ansar Yusuf yana sonki"


"Hisham Waadi ANSAR!!!" Ya fada da mugun karfi, tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login