Showing 3001 words to 6000 words out of 181864 words
gari suke."
Lumshe idanunta tayi sakamakon rungume nonuwarta da tayi har suna wani irin cika da tsirta da ruwa.
"Yaron yana bukatar ki sosai"
Kallon shi tayi cikin kuka tace mishi.
"Da fatan ba zaka tab'a juya mana baya ba, kar na dauko shi kuma kace ba haka ba, babu da Uwa bani da Uba, duk sun tafi sabida zanen ƙaddara ta, don Allah karka juya min baya, kai ne Ubana kai ne Uwata don Allah karka juya min baya."
"Insha Allah ba zan juya miki baya ba." Ya fada tare da murmushi domin karfafa mata gwiwar ta, a tare suka fito daga motar domin yara sun yanyaye motar suna kallon kansu da ihu.
"Laaa Abuh ce! Yaran suka fada tare da watsawa a gurin, a hankali take takawa, zuciyarta yana rawa, tsoro da tararradi ya zauna a fuskarta. Tana isa bukkar Sama'ila ta samu baya nan, juyawa tayi a kidime zata nufi gidan Kabo, wata dattijuwar mata tace mata.
"Ayya ita ƙaddara sau daya takan fada maka, amma zafinta sai ta shekara dubu tana bibiyar ka, da lokacin da kika haihu kin dauki abinki bakin ki alekun babu wanda zai kuma ganin ki sai tsananin rabo. A yanzun kuwa abu biyu suka haɗu a guri daya.
Tafiyar kaddara wacce baka iya tsayawa dole sai kayi, sai kuma akasin ƙaddara wacce idan ta same ka sai hakuri, ko minti talatin basu yi ba da barin garin nan sai wata rana." Dishi dishi, ta fara gani kafin ta ankara har ta zube a kasa, da gudu ya iso gare ta, bai tsaya ba wata dogon nazari ba ya dauke ta, suka bar garin baki daya. A mota yayi ta watsa mata ruwa bayan sun bar garin.
"Wayyo Allah na, wayyo Allah na wayyo na shiga uku, meye nayi ne haka? Meye na aikata da Ubangiji ya sab'a haduwar mu, meye yasa ban hakura na dauke shi ba, innalillahi wa'inna ilaihi rajioun Ubangiji na tuba Ubangiji, ina son jinjirina ina kaunar jinjirina, ya Allah na tuba ya Allah na tuba, na shiga uku me yasa nayi haka? Me yasa bani da zuciya na imani, Dr Khalid bani da tausayi na rasa Yarona na barshi a hannun mujirimi, ya rabani da Uwata ya Rabani da mijin aurena, ya rabani da Ubana ya kuma rabani da Yarona Wayyo Allah Ubangiji ka tsinewa Sama'ila, Ubangiji ka hana shi jin dadin rayuwar shi."
Kuka yake tana buga kanta tare da dukar cinyarta, duk hakurin ka sai ka zubda kwalla haka har suka iso garin Maradi, gidan Mahaifiyarshi ya kaita dama a can ya kaita. Kallon su tayi cikin tausayi tace mata.
"Kiyi hakuri Sama'ila yayi laifi amma laifin shi bai kai naki muni ba, da yayi miki sai kiyi hakuri da shi ki dauki d'anki ki dawo."
Dauko wata jaka tayi tare da mika mata.
"Wannan jakar Mero ta kawo ranar da abin ya faru, tace baffanki ya hana Sama'ila nisan zango dake ta hanyar da yayi amfani da ke, sai dai kabilar Bugaje basu cika zama ba suma, ba kamar Fulanin mu na yau da kullum ne ba, gashi dukiyar cikin shi sunce kiyi karatu kamar yadda kika so tunda har kinyi primary school da Secondry, since kiyi karatun da zaki amfani al'ummar Fulani, da wayar musu da kai. Domin sun tabbatar da zaki dawo, amma girman abin kunyar da ya faru dake ba zai iya sakawa su amshe ki ba, domin tunda suka ji labarin juna biyu gare ki, da shi Mijinki ya kai musu takardan sakin ki, shima yana cikin shi. Kiyi gudun abin kunya yasa suka tafi bawai basa kaunarki bane"
Wani irin kuka ta kuma fashewa da shi, tana yi tana karawa, tare da k'amk'ame jikinta, meye yasa aka fidda al'adun da basu da tushe? Me yasa ita ƙaddara bata zab'i kowa ba sai ita? Ji take kamar an cinnawa zuciyarta wuta yake ciki. Kuka take tana kuma wa, har yamma lokacin da aka juye ruwan wankan ta nonuwarta sun kuma cika da zubda ruwa.
Haka ayi ta watsa mata ruwan idanunta a lumshe bata buɗe ba balle kayi tsammani bata jin zafin ruwan ne kuma tana ji har cikin ruhinta da gangan jikin ta.
***
Damagaram.
Anan suka fara yada zango, kuma sun ji dadin yanayin garin domin sun sayar da saniyar su, yar kudin ce, Sanda ya kama musu haya. Gidan da ya kama musu akwai mutane dayawa, musamman kabilu mabanbantar harsuna dabam dabam, yan kudin hannun su, dashi suka saka ledar tsakar daki, da kuma taburma, sai yar tukunyar da zasu amfani dashi, dan basu iya daukar wani shirgi ba, sabida fitar bata nutsuwa bace kuma ma basu san inda zasu fada ba.
Dan haka suka auno hatsi da zasu ci, dan ma sun shigo garin da yan dabbobin su. Ta watsa a tsakar gidan, bayan sun tambaya aka ce zasu iya saka kiwon su.
Wani abinda ya Kum burge su da gidan akwai rijiya da wata tsohuwar turmi, dan haka ta nemi Izni gurin daya daga cikin matan gidan zata yi daka. Cikin kallon tsoro ta nuna mata inda turmin yake, ta wanke hatsin sannan ta zuba ta fara dakawa, ta surfe shi tass, sannan ta kuma wankewa har ya tsane ta koma ta dake shi sai da ya zama gari, lokacin Sanda ya shigo, da sauri ya amshi Jaririn bayanta.
"Kabo bana son haka, taya zaki zo kina daka da goyon dan luɗi a bayanki, idan tabaryan ya fado daga hannunki fa?"
"Kayi hakuri mai gida" ta faɗa cikin wani irin farin cikin, sabida yadda ya nuna kulawa kan Al Mamoon, yayi mata dad'i. Haka ta gama dakar tazo dakin ta same shi.
"Ki dama mana kunu mana tunda na samo mana madarar Rakumi shi yafi yawa a garin nan" "toh me gida,"
Haka ta fito tana kallon yadda suke ta harkan gabansu.
"Iya isuhu kunyi bakin Bororoji ne?" Matar da aka kira Iyar isuhu tace.
"Eh wallahi, d'azun suka zo"
"Toh kuyi a hankali" matar ta faɗa dake tana saman katanga ne, jikin kabo ne yayi sanyi, ta koma daki.
"Maigida bari su gama nasu sabgar idan suka gama na fita nayi mana" dake shima yaji abinda aka fada, bai takura ba, haka suka zauna a dakin shiru, suna tarerayyar Almamoon.
Sai da suka ji tsakar gidan shiru ya fito ya fara kokarin niman abinda zata hada wuta, sai da tafita ta sayi itaccen tazo ta haɗa musu wuta aka daura kunun nono. Bayan ya gama ta wanke jikin tukunyar ta itaccen.
Komawa daki tayi, suka zauna tare da shan abin su. Tana jijjiga yaron su.
Hakuri yayi ta bata taɓa gaya mata abinda suke so, rayuwar Yaron shine kan gaba, dan haka ba zai yi kasa a gwiwa ba, Insha ALLAH sai yaron su ya taka muhimmiyar rawa a duniya...
**
Duk inda take tsammanin ganin Sama'ila da Aminatu bata same su ba,haka ta dauki kudin tai ta bin ƙauyuka da wanda suke iyakar Nijar da Najeriya, haka tayi ta b'atar da kudin ta, ta lalace sosai, bata da aiki sai na kuka, idan ta zauna kuka da kaunar danta take, yau ma tun sassafe take shirin fita Dr Khalid ya hana a barta ta fita. Yana sane da jininta yana yawan hawa.
"Khalid me yasa ka hana Musa ya barni na fita?" Kallonta yayi sannan yace mata.
"Sabida ina son na kilace ki daga fita ko ina, so nake na kuma sabunta rokon ki akan na baya. Ina son aurenki, kuma ba wasa nake miki ba, wancan ranar da kika tawo har kika kwanta a kasar bishiya, ba dan Allah ya nufa zan tafi niman ko zan ganki ba me kika san zai faru dake? Don Allah ki taimaka min aurenki zanyi ba wani abu ba, idan muka zauna a inuwa daya Insha Allah Ubangiji zai kuma baki wani Yaron ki duba lamirina."
Hawaye na zuba mata ta kura mishi ido, tun lokacin da suke shigowa gari da nono yake Bin ta yana Sonta amma take gaya mishi ita tana da wanda zata aura, zama tayi dab'as tare da fashewa da kuka. Ta rarrafa gaban shi tare da rike kafarshi.
"Don Allah karka manta ka tayani niman Yarona wallahi ina son shi"
.d'ago ta yayi tare da cewa.
"Insha Allah zan tayaki niman Yaronki Insha Allah."
Da wannan shawaran ya sami mahaifiyar shi, dake itama dattijuwar arziki ce mai kaunar Ƴaƴan wasu da nata, tace mishi.
"Allah ya tabbatar da alkhairi"
Dan haka a cikin satin aka daura auren Zainab Hamza Bugaje, tare da Dr Khalid Agla, akan sadaki CF dubu arba'in da biyar.
***
A hankali zaman garin Damagaram yake niman fin karfin su, kasancewar yadda mutane suke tsoron su. Yasa suke dan fuskar halin rayuwa.
"Iyar Mamoon, naga kin iya surfe da daka ko zaki mana mu biya ki"
"Kai Iyar isuhu zan yi mana," ta faɗa tare da amsar hatsin, kafin awa daya tayi musu daka cass, ta kuma daka musu. Ta tankad'e musu. Sannan ta basu,
"Laaa. Iyar isuhu kiga yadda yayi laushi. Nima Iyar Mamoon zaki min" take mata suka shiga kawo mata surfe, matan maraya suna da banbanci da matan karkara, sabida matan karkara suna juran aiki, matan maraya kuwa basa iya juran ire iran wannan aikin.
Shi yasa har makota kawo mata surfe suke, tare da bata aikin.
Aminatu tana da mugun hakuri, ga dauke kai akan abubuwan da suke faruwa, idan yaron ta yana kuka zata goge shi. Du buga surfen su.
***
Tunda aka daura auren kawai yasan da auren ne amma babu wani abu na auren sai yawan rikicin da take mishi dan haka ya shawarci mahaifiyar shi zasu bar kasar. Bata ki ba tayi musu addu'a, dan haka ya haɗa mata kaya suka nufi Faransa,. Zuciyar ta cike da kewar D'anta. Ranar da zasu bar garin Maradi, kuka tayi ta yi tana kallon yadda tayiwa kanta iyaka da D'anta ko iyayenta basu dame ta ba karma yadda tayiwa kanta iyaka da D'anta.
Wannan shine sanadin Kenan da ta bar garin Nijar.
***
2011/August/04
Idan kace rayuwa tabbas Aminatu da Sanda sun ganshi,kuma suna kan ganin shi. Duk wani abin da zasu yi domin amfanin Almamoon suna yi, kuma Alhamdulillahi.
Yaron ta taso babu tashin hankali, sai dai idan ka tsokane shine fa bai iya fada ba kamar kurma.
Shi yasa yaran da suke gida daya dasu basa fada dashi sai dai idan an fi karfin su, shine zai shigar musu. A wannan yanayin har suka saka shi a makarantar boko, da arabiyya dan ma yana karatun Alqur'ani a gaban Baban shi Sanda yayi nisa.
Almamoon Allah yayi mishi baiwar Ilimi, tun yana shekara biyar ya fara shiga musabaka, kuma yana lashewa, gashi da wani banzan hali shine karka nuna mishi ka damu dashi domin da wannan yanayin yake iya saka damuwa, idan kace kana son shi da abota, wayyo Allah..ka shiga uku domin zai ta baka wahala ne, yana share ka.
Gashi da farin jini idan turawa yan yawon bude ido suka shiga makarantar su, har rige rigen daukar hoto ake dashi sabida bakin fatar shi, wanda idan ya shiga rana har wani kyali yake, idan ka cire kwayar idanun shi da hakoran shi sune fararre tass a jikin shi sai harshen shi ja, bayan nan babu wani abu da zaka ce fari ne a tare da shi..
Yanayin fatar shi ta janyo mishi soyayyar mutane, sai dai abu daya yake mugun bawa kowa haushi a tare shi a yanzun yana da shekara goma a duniya idan ya yab'a maka bakar magana sau ka rasa inda zaka saka kanka.
A yanzun haka yana tare da wasu yan ajin sune. Amadu Bukar sai Salihu Muhmuda jarabawar suke ta gama primary.
"Mamoon don Allah taimaka min da amsar nan mana?" Inji Amadu Bukar, Banza yayi dashi. Can Salihu Muhmuda ya taba shi.
"Don Allah taimaka mana abokin mu"
"Ai kusan ni na kawo ku makaranta shi yasa zan baku satar amsa," ya faɗa mu....
[7/14, 1:05 PM] RamlatArManga: I'm on Instagram as @s.square_fashion_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=gorfmwut2x22&utm_content=cgl6gfx
```Zaku iya samun kayan mu daga turaren zamani na wuta, shu'umar humra, dambun nama na mata, tsumin. Da sauran su kayan mu ba irin nasu bane sai an gwada akan san na kwarai..... Akwai haɗin kayan amare da na uwargida...🗣️🗣️Friday Promo!!! Buy 13pcs @15k only : Turaren wuta 5pcs, humra 3pcs, Turaren tsugunno, shu'umar humra, mopping and toilet perfume, curtains and carpet parfume &kasko💃🏻💃🏻```
🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Littafi na D'aya...
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Idris
_🙄 Daga farawa naga yadda kuke sakawa Dan baki namu ido fa😛🤭 Wallahi ko hmm_
BABI NA UKU.
Wata tafiyar.
Sake baki Salihu Muhmuda yayi tare da Amadu.
"Amma zamu haɗu" suka fada mishi,.mik'ewa yayi cikin rashin tsoro yace musu.
"Idan muka hadu abinda kuka bani ku hanani" ya faɗa yana fita daga kujeran,
"Mara mutunci"
"Lokacin da aka zo rabon shi bana nan"
"Mugu"
"Eh gadon shi nayi"
"Dan iska kawai"
"A'a sai dai guguwa"
Ya fada tare da barin tabirin su, kamar zasu fasa jarabawar, karshe haka suka mike zasu kai, sai a lokacin Amadu ya kai idanun shi kasar tabirin su ya lura da rubutun da Almamoon yayi ya ajiye musu. Da sauri suka dauka. Murna kuwa baki yaki rufuwa.
Koda suka gama, fitowa suka yi. Tare da samun shi a kasar bishiya ya zauna yana ta rubutu, idan ka ga hancin shi har baki, daga gefen fuskar shi kuwa saje ce ya kwanta gwanin ban sha'awa.
"Kai mara mutunci" banza yayi musu.
"Mun gode"
" Da aka yi me?"
"Da bamu amsar da kayi"
Kallon su yayi sannan yace musu.
"Ai ina mamakin yadda Uwayen ku suke kashewa jakuna kudin makaranta." Ya fada tare da mik'ewa.
"Wawa kawai dan baki duna"
"Eh toh ta yiwu ni bakin ne, amma kuma ina takaicin haduwa da katon jaki" ya faɗa tare da nufar hanyar ajin su.
"Almamoon dan me gadi"
Cak ya tsaya tare da juyawa ya sake murmushi, kafin tace mishi.
"Eh toh dukda haka yafi cirani" da Yaron ya ji abinda ya gaya mishi fasa ihu yayi tare da burgima, an zage mishi uba an can dan cirani.
Haka yayi ta kuka har Malamin su ya shigo tare da tambayar su meye ya haɗa su.
"Zagina yayi na bashi hakuri" inji Almamoon,
" Karya yake cewa yayi Ubana dan cirani"
Tsaki malamin yayi sannan yayi musu fada.
... Bayan sun gama jarabawar suna nufi hanyar gida, yau ya shirya musu tsiya shi yasa bai kula su ba.
"Yau idan muka je gida zan samu anyi mana abinci me dad'i?" Suna son yayi magana amma dake yayi shiru basu kuma takalo shi ba.
Haduwa da wasu yan samarin unguwar su, suka tsaya tare da make su, amma ban da Almamoon, wuce su yayi. Sai da suka bar gurin.
"Mamoon kai wani irin mugun mutum ne ka ga sun tsare mu ba tsaya ba."
"Me ya faru daku?" Ya tambaye su, kamar bai ga abinda ya faru ba.
"A'a babu"
"Nima naga alama" ya ga musu tare da wuce su, matasan nan ba kome yasa suka make su Amadu Bukar da Salihu Muhmuda ba, sai dan tsokanar su da suka yi, kuma akan idanun shi suka tsokane su. Shi kuma baya tab'a bin bayan karya.
Haka suka isa gida idan suka gaya mishi maganar banza ya gaya musu wacce tafi tasu muni.
"Dan banza munafuki wanda baya yarda yayi wanka a gaban mutane." Wannan maganar tayi mishi zafi, da gaske ne baya tab'a wanka a gaban mutane, kuka kamar yadda babba zai shiga ban daki yayi wanka, haka shima yake. Rasa amsar basu yayi har suka isa cikin gidan, zasu nufi dakunan iyayen su yacewa Salihu..
"Ka tambayi Iyakar me yasa bata wanka a waje"
Ya gaya mishi sannan ya shiga dakin su. Samun Innar shi yayi tana ta daman cura fura da aka kawo mata aikin shi take.
"Sannun Innata"
"Sannun D'an albarka, dauki abincin ka yau Allah ya taimaka malam ya samu dan albashi ya sayo maka shinkafa aka dafa, duba ka gani har da nama."
Kallonta yayi sannan yace mata.
"Innah hala ko cin namar baki yi ba daga ke har Baba." Ya fada idanun shi na cika da kwalla.
"Mun ci mana"
Ta faɗa tare da maida hankalinta kan aikinta, bude kwanon yayi ya ga Bama kusan ya lullube abincin, sai ganye da aka zuba a saman namar, ture abincin yayi tare da cewa.
"Ba zan ci ba"
"Yi hakuri Bawan Allah, sanyin idaniyar Innar, Dan da aka haifa tsiya na barci, Kasan yadda nake kokarin kyautata maka, toh maza ci sai ba baka labarin wani mafarkin da na jima ina yi akanka"
"Wallahi ba zan ci ba sai dai muce tare"
Shafa kanshi yayi tare da cire mishi hular kanshi, gashin kanshi irinta Bororoji yana nan daga tsakiyar kanshi anyi Mishi wata irin kitso me hawa biyu, doka sai wasu kanana da aka saka musu wuri wato braid, gashin nan baki suddin har gadon bayan shi, wuyar shi a daure yake da guru da azurfa, murmushi yayi sannan yace mata.
"Gobe za a fara shadi a rugar Baima, zamu je don Allah Innah ki bar ni naje" kura mishi ido tayi cike da tsoro.
"A'a ba zaka je ba"
"Don Allah nace Innata..."
"Iyar Mamoon! Wallahi nakawo miki dokaciya, kiyiwa Mamoon fada da irin maganar da yake zarowa nan."
"Toh Allah yayi min baƙi bari nayi shiru kar kayi Magana"
Rufe mishi baki Innar shi tayi.
"Kiyi hakuri Iyar Salihu."
"Ina dalili yaro sai kace mace gurin zaro magana, na kara jin yacewa Salihu me yasa bana wanka a gaban su."
"Toh ai dalilin da nasa nima bana wanka a gaban jama'a kenan" ya faɗa tare da kallon Innar shi, kamar zai yi kuka.
"Iyar Mamoon"
"Toh kiyi hakuri"