Showing 90001 words to 93000 words out of 181864 words

Chapter 31 - Bororoji Compelet Book Document by Mai Dambu .txt

29 Jan 2025

6266

gida ce, kawai kome ayi shi a cikin harkan arziki."
"Latifah kenan,gani nayi ba a haifi kowa da dukiya ba a duniya ya samu me yasa kike nuna son kan ki dayawa, me yasa baki tuna gobenki?"
Dariya da tayi sosai, kafin ta mike tana faɗin.
"Wallahi ina da buri akan Mohan, matar da Mohan zai aura ba karamar mace bace, matar da Mohan zai aura zata kasance mai nasaba wacce duk inda zan shiga da ita ce kyawawan tsaro zan hada shi da ita, wacce duk inda muka shiga za a gane yar babban gida ce kamar Hanan"


Abinda ya fahimta matar shi tayi nisa a don duniya, matar shi tana da mugun son kai, dan haka ta mike bai kulata ba ya barta tsaye tana bayanin abinda take son akan Mohan.


....
"Munmohan" ya kira sunanta a sanyayye,
"Na'am Hammah na" ta amsa a hankali, tare da jan hancinta alamar tana kuka, ko kukan yana son zuwa mata. A rud'e ya shiga tambayar ta.
"Babu kome, kawai dai ina hanyar Maradi ne na ma kusan shiga."
"A ina zaki sauka?"
"Gidan nan na kusa da Makarantar"
"A'a zan kira malam ya dauke ki." Ya fada can kuma yace.
"A'a ki kirani idan kin isa"
Baki daya ya rude, ya rasa gane wanda zai kira ya gayawa ya dauki mishi Moonah,
"Moonah! Insha Allah kome dare zan zo gare ki"
"Toh ina jiranka"
Kashe wayar yayi, tare da niman Dan Ba'are.
"Kai zoka kaini Maradi"
"Professor Ibrahim Dan Ba'are, idan ban kai ka ba zaka iya tsine min ne? Dan Ubanka a yanzun ne zamu tafi Maradin ko ce maka akayi Ni sallamamme ne.


"Kazo idan ba a sallame ka ba ai ni na sallame ka, dalla kazo muje ina jiranka"


"Mohan bana ciki da Iskanci, a wannan daren zamu fita?"
"Kayi hakuri" karon farko da Mohan ya bashi hakuri tabbas ba karamin abu bane. Cikin sanyin jiki yace mishi.
"Ina zuwa Insha Allah" domin tunda ya iya bashi hakuri yasan ba karamin abu bane, dan haka cikin wani irin yanayi, ya shiga had'a kayan shi.


Kafin dan Ba'are yazo har ya gama, koda yazo babu wanda yasan baya gidan dan sun fita daga cikin gidan.
**
Karfe tara na isa garin Maradi, dan ma mun tsaya a hanya, gidan da yake kusa da makarantar na isa, ina ganin kiran malam Ansar. Da kamar ba zan dauka ba sai na dauka.
"Kana ina ne?"
"Na shigo Maradi zan tafi gidana da yake kusa da makarantar, kuma Hammah Mohan zai iso an jima" na faɗa a sanyayye,
"Ok toh idan dai da wani abu ka min magana."
"Allah Sarki nagode sosai, Insha Allah idan da wani abu zan maka magana."
"Toh" ya faɗa min.
"Da fatan ba wani abu bane ya faru?"
"A'a babu kome" kiran Hammah Mohan ne na ga ya shigo min.
"Don Allah kashe zan dauki wani kiran."kashe wayar yayi na dauki kiran Hammah Mohan,
"Kina ina ne?"
"Hammah yanzun na shigo Maradi."


"Insha Allah zuwa sha biyu saura zan shigo kinji"


"Toh Allah ya kawo ka" na fada tare da tare abin hawa, ya kai ni har kofar gidan, na biya kudin sannan na shiga cikin gidan har yau da jami'an tsaro a kofar gidan.


Ina shiga cikin gidan wanka nai tare da salallolin da suke kaina, babban addu'a ta, Allah ya sanyayya min zuciyar Innah, amma ban ji dadin yadda tayi ta min miyagun kalamai ba, ko babu kome Innah ce ta reneni, ita ta min kome, Innah ta min gatar da babu wanda zai min bayan shi. Dan haka na zauna nayi kuka nayi kuka har sai da kai na ya fara sarawa ban san ya akayi ba wani irin jiri ya kwashe ni a sallayar na zube.....kuyi hakuri wallahi na gaji ne....
*Nagode sosai Maman Humairah da kawo min ziyara Allah ya bar zumunci 😍💃💞 Ubangiji ya bawa Humairah lafiya Nagode sosai*
#Mai_Dambu..
[8/7, 10:03 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1108262550?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=cavWiGGyBrCAo%2BWqCLglY3Gs%2BgN1rFoDPpKB0zWz6PoxIH7kodf8pwkn%2Bapj%2BNu2jcr3lLRQ1jZyx3x0Y0w3eVNqEUJhy%2FQFfQ%2FqU6I47IboRfk%2Fq6JpeUV04y6Fe%2BIf


🐂🐂BOROROJI🫀🫀


~The Journey of Destiny💔~


Mai_Dambu


Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....


BABI NA TALATIN DA UKU.


Ban tashi sanin inda kaina yake ba sai a gadon asibiti, a hankali na bude idanuna. Da nake ganin dishi dishi, d'aga hannu nayi kamar zan yi wani abu. Naji ana magana kamar daga can nisa, maganar ma amo take min kamar yadda nake tsammanin amsakuwa na saka.


A hankali naji an kuma tsikara min allura, nace.
"Wash" daga haka ban kuma sanin inda kaina yake ba, sai washi gari da safe. Na bude idanuna na hango Baba yana zaune.


Kokarin tashi nake, Baba Mari ta mai dani.
"Koma ki kwanta yar nan Sannun ai kin auna arziki, tunda gashi kin farka da kanki." Kallonta nake tare da kuma kallon dakin.


"Sannun Maimunari, Allah ya baki lafiya yasa Zakkar jiki ne, inji Innarki wai a gaishe ki" inji Baba, na san ya fada ne kawai amma bawai dan Innah ta saka shi bane, dan haka na mike dakyar na nufi ban daki. Da taimkawar Baba Mari nayi wanka da alola. Sannan ta mika min doguwar riga na saka, kafin ta kuma taimaka min na fito waje.


Sallah nayi da wanda yake kaina, ina cikin yi Hammah Mohan suka shigo tare da dan Ba'are. Gaida Baba yayi fuskar shi a daure tam, sai harara ta yake. Yaki min magana.


Tea ya hada min sannan ya mikawa Baba Mari, ta fara kokarin ganin na sha, ture tea din nayi. Tare da kallon shi, takaici ne ya kuma kama shi. Ya mike tare da zuba hannun shi dukka biyu aljuhun rigar shi.


"Me yasa ba zaka min magana ba?" Kura min ido yayi sannan yace min.
"Duk abinda zan yi a rayuwa ina niman albarkan iyaye ne me yasa da tace bata son alaƙar mu kika dage?" Ya tambaye ni, tare da zuba min ido, wanda suke cike da b'acin rai.


"A'a Hammah Mohan, kai ne nake ganin zan samu nutsuwa da kai kace zaka d'aga min hankali? Sai na wuce diffa, kuma wallahi gurin Malam Ansar zan tafi" na gaya mishi ina kuka.
"Sai me? Ki wuce diffa ki tafi duk inda yayi miki. Ina can ina faffutikar rayuwar da zamu yi saboda ke zaki b'allo min wata tashin hankali,


Toh ki sani da kinyi kuskuren tafiya diffa da har abada kin rasani kenan, dan haka zaki tashi kibi Baba Damagaram, kuma kika sake ki kayi wani shirme."


Mikewa nayi akan Abin sallah, na tako gaban shi ina kallon shi.
"Idan ka sani na koma can toh na rantse maka da Allah zaku nime ni ku rasa." Na gaya mishi,
Kasa magana yayi sabida yadda na kafe shi da ido, ina ƙoƙarin ganin ya yarda da abinda zan aikata. Kasa magana yayi sannan ya juya tare da cewa.
"Nag."
"Mohammed ka kyaleta ta zauna a nan Maradi tunda ga Iya Mari, ina ga idan ta zauna a nan hankalinta zai kwanta, itama Innarta hankalin ta zai kwanta. Babu amfanin a maida ita gida dole, tunda ga shi akwai inda zata zauna babu wani abu."


"Baba nawa Moonah take da zata bawa mutane zab'i? Ita wacece da zata bawa mutane zab'i?" Ya fada a sanyayye, abinda na lura nice yake Zafaffa min murya amma duk wanda ya fishi yana ƙoƙarin gaya mishi kowacce kalma cikin sanyi da nutsuwa.


"Bance dole ka zauna dani ba,
duniya tana da fad'i zaka iya tafiya akwai Dubun ka da suke buƙatar rayuwa dani, ka gane" na fada ina ninke kayan da nayi sallah dashi, a yanzun da nake jin haushin kowa, wallahil billahi azim duk wanda ya kuskura ya tab'a Ni zai ji magana me tsada.


Fisgo ni yayi tare da fitar dani a dakin yana zuwa gurin motar shi ya wulla ni cikin motar, sannan ya zaga ya shiga cikin motar, ya bata wuta. Muka bar asibitin, kaina yana gefe.


Tunda ya saka ni yaga ina kallon waje, kuma ina kuka. Haka yayi ta gudu, bai tsaya ba sai da muka isa doso, anan ya nima min abinci ya bani, bayan ya tafi masalaci.


Wayar shi ya dauko tare da kiran Dan Ba'are, gaya mishi zai kai ni gidan su, gurin Umman Dan Ba'are, idan ya barni a Maradi wallahi yasan wancan jakin zai iya daukar nauyin wannan gangancin ba. Ina jin shi yana fadan haka na juya ina kallon shi, dan haka ya maida Baba Damagaram, Iya Mari a maida ita gidan ta.


Ina kallon shi ban yi mamaki ba, amma nasan ranshi a b'ace yake dan haka nima na had'e raina ina jin lallai ba zan tab'a yarda ya rena min hankali ba. Bayan mun gama abinda zamu yi , muka wuce Niamey.


Mun isa ana sallah magarib, gidan su Dan Ba'are ya wuce dani, ana sallah. Masalaci ya wuce bayan ya kai ni babban falon gidan. Yayi tafiyar shi, basu san na shigo ba, sai bayan da suka idar da sallah, suka fito. Da mamaki suke kallona kanen shi.


Amma Ummar shi tasan da zuwa na, komawa cikin dakin kanen shi suka yi tare da gaya mata ga bakuwa. Tana fitowa ta amshi ni hannu bibbiyu. A d'akinta nayi sallah aka kawo min abinci naki ci, kuka ne kawai yazo min, dan haka na cusa kaina a tsakanin cinyoyina, na shiga kuka. Bata hanani ba, sai ma barina da tayi nayi kukan.


Kallon tausayi ta mana, domin indai ba wani ikon Allah ba, tayi Imani da Allah yar uwarta ba zata tab'a yarda ayi wannan al'amarin ba. Amma ta yarda da al'amarin Ubangiji shine mai kowa me kome, zai iya shirya kome yadda yaso, ya kuma had'a al'amarin shi babu shawaran kowa.
*
Kwana na uku da zuwa gidan ya dauke kafar shi babu shi babu alamar shi, kai ko waya bana samun shi, abin ya bani mamaki sosai. Dan haka na sami Umman Dan Ba'are a kitchen tana aiki, na rasa inda zan saka damuwa ta.


"Sannun da aiki Umma, dame zan tayaki?" Juyowa tayi tare da murmushi.
"Zaki iya fere dankali?"
"Eh" ta bani kayan feran, na fara ban jima ba kuwa na fere cikin hannuna.
"Kai daga aiki?"
"Laa babu kome umma bari na wanke na saka magani." Haka na wanke hannun, ina me dangwala magani, sannan na manna plastic, na dawo zan cigaba da aikin ta hanani, bayan takira Nazirah yarinyar da take mata aiki ta amsa.


Shiru ne ya ratsa kitchen ɗin, kafin na yanke shirun da tambayar ta.
"Umma ina Hammah Khalil?" Murmushi tayi sannan tace min.
"Yana can da Mohan a part din shi"
"Dama Hammah Mohan yana nan ne?"
"Eh yana nan" shiru nayi dan bana son na fidda damuwa ta, dan haka na shiga taimaka mata da shirya wasu abubuwan. Shigowar Jalilah Kanwar Dan Ba'are yasa ni matsa mata, domin yarinyar bata da mutunci.

"Umma me kike dafa mana ne Hanan zata zo" ta faɗa tana kallon inda nake, fuskarta dauke da murmushi.
"Waye ya saki kiran Hanan? Wato kin zama munafuka ko? Kin gaya mata Mohan ya kawo yarinyar da yake so ko? Hmm zaki hadu da shi indai Mohan ne"


"Umma ina ruwa na? Babu abinda ya shafe ni, kawai tace zata zo ne" marin bakin ta tayi. Tare da kallonta cikin zafin rai.
"Karki gaya min maganar banza, yanzun nakira Khalil yayi min kwallon dake munafukar banza, Allah yasa wani abu ya faru sai na baki mamaki."


Ta fada tare da nuna mata hanyar ta, tana zuwa bata yi wata wata ba, ta bangaje ni. Sai akan idanun Hammah Mohan shi da Hammah Khalil. Ashe suna jin abinda Umma take faɗa. Ganin su a tare ba karamin firgitatta yayi ba, a tsora ce tayi gefe zata wuce.
"Idan na miki wani abu kamar na sayawa Moonah k'iyayyar kuce, amma Insha Allah ba zata kuma zama a cikin gidan nan ba, ai na zata idan na kawo mahaukaci nace ina so a kula dashi ke mai bashi kulawa ce ashe ba haka bane, munafuka ce ke har kina." Kasa magana yayi domin bakar zuciya ce dashi.


"Karka yarda ka fitar da ita daga gidan nan kaji ko" juyawa yayi a fusace, shi kuwa Khalil ya bi ta da kafa zai tokare ta.
"Kiyi hakuri kinji"
"Babu kome"
Na gaya mata, haka muka gama aikin sannan na nufi dakin nayi wanka da sallah azhar, ina zaune sai ga su tare da wata kyakyawan Yarinya irinta ba ita daya bane su uku ne, Hanan,Jalilah , Hilal. A tare suka shigo d'akin. Suna kallona, wayata na dauka tare da turawa Hammah sako, sai naga babu amfanin haka tunda akan shine gwara na tsaya na cigaba da fada akan shi.


"Jaliy wai ba kin ce min guduwa tayi daga gaban iyayenta ba ta biyo saurayi?" Kallon ta nayi kamar yadda yake kallona.
"Eh mana, an ga dan masu kudi an haukace da baki kamar zunubin" inji Hilal.


Ban yi musu magana ba, sai ma cigaba da nayi da amfani da wayar hannuna, abu na farko fada ba nawa bane, amma dole na koma gida, duk abinda za ayi zan fi samun damar kwatar kaina. Ban da anan dan haka suka gama cin zarafina ban tanka musu ba. Sai da zasu tafi Hanan tace min.
"Karuwai ke bin maza har cikin gidan su, matar da tasan ciwon kanta nima mata miji iyayen ta suke."


"Tabbas haka ne, amma macen da ta isa da kanta namiji baya kin ta, walo kyakyawa ce ko mummunan ce, sannan idan mace ta isa mace tayi karya a tallatawa namiji Ita sai dai namiji yayi ta haukar niman ta, dan haka ki tambayi waye Almamoon a gurin Mohan? Idan ya gaya miki ni kuma Moonah zan gaya miki girman furashin kaunar da yake min. Koda zai aure ki, sai dai ya aura kawai amma nice rayuwar shi."


Na fada mata ina me shiga ban daki, na rufe bayan na bude pampo na fashe da kuka, ashe suna fita ta kira mahaifiyarta, Hajiya Karime bata dauka ba. Dan haka suka yi ta shirya tsiyar su kafin su had'a da iyayen su.


***
Tunda ya bar gidan ran shi yake b'ace, dan haka bai dawo ba sai yamma, ina zaune ya turo min sako.
_ki fito ina jiranki_
Allah yasa wayar tana hannuna, na sha kuka har nagodewa Allah, na saka mayafi a saman abayar jikina na fito a hankali, hango shi nayi a sabuwar motar shi. A hankali na isa gurin shi. fitowa yayi tare da bude min motar lokacin su Hanan sun fito suma, sannan ya zaga ya zauna, yaja motar muka fita.
"Me yasa ki kuka?"
"Ina son zuwa gurin Innata ne?"
"Ok Insha Allah gobe zaki tafi, sun fitar da inda zaki yi horon aiki." Kallon shi nayi kafin nace mishi.
"A ina suka kai Ni?"
"Maradi suka barki amma na dawo dake Niamey hedkwatar kasar Niger."


Kallon shi nayi kafin nace mishi.
"A ina kenan?"
"Babban Kotun kasar nan, zaki yi aikin wata shida ne, sauran zaku koma makarantar kuyi karatun wata shida, sannan a kammala jami'a, sai maganar auren mu" kallon shi nayi kafin na dauke kaina daga gare shi.
"Moonah kina fushi da ni ko? Nima ina jin babu dadi, karki kuma barin gida saboda ni, duk abinda Innah zata miki kiyi hakuri zai wuce, kuma kiyi ta addu'a, domin shine makamin mumini, Moonah ina sonki dayawa, amma bana son kiyo abinda zai rabaki da danginki, bana son a goranta miki, ina son ganin ki cikin farin ciki."


"Zan baka rayuwata da kome da na mallaka, idan har ka d'aga darajata, zan kare ka na zame maka garkuwa, Hammah Mohan ina jin kamar bazan yi nisan kwana ba, ina ji kamar akwai babban abinda zai saka ni mutuwa lokacina bai yi ba, Hammah idan haka ya faru, don Allah karka manta da Ni, idan wani abu yafi to nawa mara kyau karka guje ni, Amma ina jin tsoron lokacin da zaka juya min baya, ina jin tsoron lokacin da ƙaddara zata shiga tsakanin mu, ina tsoron tafiyar ƙaddara. Ina tsoron b'ankad'o wani shashi na rayuwata da zata zaka kowa ya guje ni. Hammah haka kawai nake ji bani da kyakyawan background haka kawai nake ji akan ka soyayyar ka zan iya zab'an ka na bar tawa rayuwar, Hammah idan nace bana sonka nayi karya, idan nace ina sonka nayi karya Amma kullum zuciyata da kai take bugawa, Hammah wata rana zaka tuna da na gaya maka haka."


Na fada tare da fashewa da kuka, d'ago kaina nayi tare da kallon shi.
"Kasan me? Da Malam Ansar yake fadar wasu abubuwan dan ina cikin jinsin mata maza na zata kawai iya shine mai wannan yanayin halin, amma da Innata ya bude bani ta fadi cewa Ni bakar ƙaddara ce sai naji duniya ta yi min dabaibayi, Hammah Mohan ina son jan numfashi m, sai na tokare kirjina da matashi, idan ina son kuka sai na ta dukar gefen zuciyata. Hammah tausayin kaina nake ji, ban san kome ba sai soyayyar ka, me yasa soyayyar ka yazo min a bazata? Me yasa soyayyar ka ta zame min kamar guba. Hammah Mohan don Allah ka tsaya a gefen titi ka rungume ni, ina son naji dumin wani a kusa dani ina son dumin uwa ko Uba a kusa dani, kai kuma kamar Dan uwana ne nake jin ka, don Allah just hug me" a hankali ya sauka a gefen titin, ya fito tare da bude kofar da nake ya mikar dani, sannan ya kai hannun shi baki daya ya rungume ni, kaina na saka a kirjin shi ina jan kuka na, kuka nake sosai yana bubbuga bayana.
"Insha Allah ba zan tab'a juya miki baya ba, ba zan tab'a rabuwa dake ba, Maimoon ina tare dake har karshen rayuwata, Kece

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login