Showing 156001 words to 159000 words out of 181864 words
xan bukata na sati Uku, amma da ya tafi sai da ya share wata biyu, a lokacin na ga tashin hankali da damuwa, bani da kome sai da ta kai ina fita bakin hanya ina rokon abinda xan ci Ni da Yarinyana, sannan na kawo mana gida a girki.
Haka bai saka na samu sassaucin rayuwa ba, domin kuwa idan yarinya bata da lafiya, haka zan ta roko ina Bara."
Goge kwallar da yake zuba tayi sannan tace min.
"Ban rike shi ba, domin har lokacin ina mishi fatan sauki da salama, ina cikin wannan yanayin wata baturiyar London ita ta taimaka min na samu aiki a wani gurin girki, ban boye mata ba ina karatun likitanci, haka ta kuma nima min damar na koma makarantar, ita kuma Yarinyar da nake goyo ta gaya min na dinga kaita gidan reno, haka ce ta faru da dan albashin da nake samu nake rufa mana asiri, bayan wata biyu ya dawo, ashe ya kamawa matar wani gida mai kyau, dan haka sau daya yake leko ni, haka zai yi tafiyar shi ba tare da nasan yana yi ba, ana cikin wannan yanayin har muka shekara uku, yana zuwa min kullum da yamma, ko da safe. Benazir tana da shekara uku da rabi da watanin ranar yazo min a hargitse,. Yana kuka tare da niman yafiyana haka na yafe mishi. Bayan na yafe mishi muka koma kamar da.
Wai ashe fada suka yi da matarshi har ta kai shi ofishin yan sanda, ban gama kaduwa ba sai da naga yan sanda sun kawo sammacin shi nan na gane da gaske sun rabu, amma ban wani damu can ba, domin halin rayuwar da suka jefani dai Allah ne kawai ya sani.
Haka suka yi ta sintiri yana ƙoƙarin kare kanshi,kafin matar dai ta bar kasar sai da aka raba dukiyar shi gida biyu, aka bashi rabi,
Ke duk wanda ya yarda da Allah bazai tab'a tab'ewa ba, haka dai na zuba mishi ido, bayan haka yayi ta lallabani muka daidaita, amma ban tsira ba a gurin dangin shi, cewa suke nice na raba su.
Bani Mantawa bayan haka ya faru da wasu watanni muka zo bikin sallah, wallahi a ranar sai da nayi danasanin kasancewata a cikin su, domin kiri kiri suka yi ta zagina da cin mutuncina. Haka ya shigo gidan ya samu abinda suke min. A ranar na Allah ya dawo min da shi, domin birkice musu yayi tare da nuna musu ai duk aiken da yake musu daga Faransa, ba shi yake turowa ba,
Nice shine har suke cin mutumci na, yayi musu bori tare da alqawarin ba zai kuma musu alkhairi ba ya gaji, sannan a gaban mutane ya kira mayar matar shi da suka rabu aka yi magana. Ya gaya musu tunda muke dashi ban tab'a kai karan shi ba, duk da abinda zai min Baba fushi da kawo karan shi, amma ita yar uwar shi ta kai karan shi, wallahi sai da jikin su yayi sanyi sannan yayi alƙawarin ba zai kuma. Dawowa cikin su ba, ba zai kuma waiwayar su ba. Na sha wahala da dangin mijina, amma da yake Allah ba azzalumin sarki bane, sai gashi suna ganin mu, a raye amma babu yadda suka iya, koda ya rasu takardun shaida na filayen shi da wasu abubuwan shi da ta dangance su. Wallahi sun rike, sauran abubuwan kuwa suka matsa lallai sai da aka raba aka cire musu nasu, basu da gadon shi amma haka suka yi ruwa suka yi tsaki, Maimunari. Ina ji ina gani suka addabi rayuwata da na Yarana, zuwan Babanki na samu sauki domin gani suke dan abinda ya rage na hakkin su Yumnah kamar wata tsiya ce yau a kawo min korafin ana niman taimako gobe ma haka, hmm Allah ya taimaka asibitin da nake namu ne tare dashi muka gini badan haka da shima sai sun kwace.
Toh ban san meye baban ki ya gaya musu ba, amma naga sun shafa min lafiya, ban sani ba ko zama zai kuma had'a ku da Mohan, amma ki sani dole sai kinyi hakuri da mahaifiyar shi, sai kin dauke kanki daga kanta, matar da zai aura sai kinyi hakuri da ita, mutane sun kashi gida hudu ne.
Na farko babu ruwan su da kai idan kayi zasu zage ka, idan baka yi ba zasu zage ka, kuma babu me sauya musu ra'ayin su akan ka, kuma babu ruwan su da alkhairi ko sharrin ka. Dan haka dole ka yi hakuri da su domin can dama ba sa yinka kuma babu mai sauya musu alkiblan su akan ka. Sannan suna iya mu'amala da kai kota wani fuska,. musamman idan suka ji ana maganar baka da kirki zasu biyo ka su bincika basu son ka amma zasu duba wannan labarin da kuma waye kai.
Na biyu kuma suna sonka zasu zageka kuma da zasu ganka zasu makale maka, babu domin duk inda suka ganka kai nasu ne, da ka bada baya kai ne tsinannen su sannan idan b'taanci ya fito sune.masu yayyata shi da yadawa a duniya, sannan su addu'a suke Allah yasa kayi ka za domin duniya ta zageka. Babu ruwan su, da kai amma sun fi kowa yayyata sharrin ka, dan haka idan zaka kira makiyi toh su ba zaka kira su makiya ba, su ne ake kira mahassada, suna tare dakai amma basu kaunarka, suna ganin ka zasu ji ran su ya b'aci, ko magana kayi zasu juya zancen ka, ko dariya kai zasu juya shi. Irin wadannan idan kayi sallah biyar da ya wajaba akan ka toh alatilas ne ka saka su a cikin addu'arka wanda zaka hada da falaki da nasi. Sune asalin Original mahassada.
Na uku suka kaunar ka da zasu ga an tab'a ka sai inda karfin su ya kare, amma su suna iya kasancewa basu zama tare da kai, kuma ba ka san su ba. Su din masoya ne na hakika, kuma da wani abu zai had'a ka da su zasu biyar duk wani sharrin ka su fadi Alkhairin ka, irin su basu zama a jikin ka, koda zasu zauna a jikinka ba zasu tab'a fadar alkhairinka akan idanun ka ba, kar haka ya zame maka d'agawa sannan wani abinda baki sani ba irin su basu tab'a nuna miki suna yin ki akan idanun ki, sannan idan da zaki yi wani abu na kuskure baki sani ba, su zasu kare ki, idan da za ayi abu dan ranki ya b'aci su zasu hana shi isowa gare ki, su a cikin rayuwar ka baka san inda suke ba, da zaka yi kuskure zasu kiranka su gaya maka haka irin su suke, a duk inda suke suna maka kauna ce domin Allah da Manzonsa.
Sai mutane na hudu suna shigowa rayuwarka ce dan su amfana da baiwar ka, ko wani abin ka, sannan babu wani abinda zai saka su kaunaceka domin ba kaunar ce ta kawo su ba, dama sun zo ne domin ribantuwa da kai. Kuma suna gamawa zasu tattara ka su watsa gefe, ba iya a rubutu ba, ba iya a zamantakewar mu ba, ba iya a gurin ayyukan mu ba, a ko ina akwai irin su.
Kinga mutane na biyu da na hudu kiji tsoron Allah akansu, domin zasu iya kaika lahira da sawun ka kuma babu wanda ya isa ya dakatar dasu. Muna tare da su yau da kullum. Allah yasa mu dace...
👇🏻
Wannan labarin yana faruwa damu kuma muna tare da irin su ban saka dan kome ba, sai dai idan kana cikin masu irin wannan halin don Allah ka daina.
*🤭 bari nayi wani Karambani, wata yar makotar kasar mu, ta tab'a niman Number na, sai aka ce mata wai mai_Dambun kike niman layinta? Matar da bata da mutunci a Media 🤣😂 Wallahi kusan shekara biyu kenan, lokacin ina rubutu masarautan Jordan, kawai sai tace musu eh ita nike nima, sai aka samu wata tace mata kinga ni babu ruwana da ita bana shiga harkan ta, kuma ina ganinta amma saboda ance bata da mutunci yasa bana kulata! Sai tace a bata Number na, maybe zata ji ni indai har yau tana tare dani, sai ta min sallama ba amsa, tace ga abinda take so nace mata to na tura mata MJ na cigaba da uzurina, Alhamdulillahi sai gashi ta kirani tace na ce ki bani book kin bani kuma baki tambaye ne kome ba, wallahi saboda yawan Jama'a yasa na manta ban tambaye ta ba, kuma wani abu anan sai da na kwana biyu ta kuma min magana don Allah taya zan ce mata bani kuɗin, sai nayi dariya nace mata ok bar kudin idan nayi wani book ki saya... Labarin na da tsawo, amma shi alkhairi jifa ce! Dan haka a ranar ban yi mamaki ba da ta gaya min haka. Kuma nayi godiya sai dai wani hukuncin Ubangiji na gama magana da ita, wata baiwar Allah ta min wani Alkhairin da bazan manta da shi ba. nagode sosai domin rayuwa ciken yake da jarabawa da kalubale sai an maka haka zaka san WHO Are You? Allah ka hada mu da masoyan Manzon Allah (S.A.W) domin sune babu tsatsa da lamba a zukartar su*
Taku har kullum
Ramlat abdulrahman manga
#Mai_Dambu...
[8/14, 10:44 AM] Joindah: https://www.wattpad.com/1115273030?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=%2FGBnJnXNijQUPspekfVSCvdwVvA67jfZnwBxxbrgfB3mZ707r2j51R%2BtHtXGLFFQhRnwEzTOFYN6wtlFDeefWMBEls9vr15DqQCkIJyDScb3H2il28oON918W3al4mnK
🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
Ana harin account ɗina fa, musamman wannan account ɗin... Wallahi 😓
BABI NA SITTIN DA BIYU.
Dan haka dole ki koyi mu'amalar irin mutanen wani lokaci ma sa masoyanka kake fada, sai ta kwab'e maka zaka Fahimci haka, sannan da gaske ne dole ki koyi hakuri, domin duk inda zaki zauna dole ki koyi hakurin nan shi yasa Allah madaukakin sarki yace masu hakuri yana tare dasu, dole ki koyi kawar da kai.(🌚🤣wallahi sai ina jin kunya idan na rubuta maganar hakurin nan 🙄domin ban da ita da rashin daraja ce zan iya fada akwai ta buhu buhu 🤨😒😏🌝🤸) mahaifiyar Mohan tana da zafi da fada, kuma irin su dole ka zama ruwan sanyi, sai a zauna lafiya. Bari na gaya miki wani abu, duk yadda aka kai da zaman aure dole ki samu positive and negative, dole cikin biyu ayi daya imma dangin miji su kauna ce ki bawa, umma miji yaki ki. idan aka yi dace kuma kika hada soyayyar dangin miji da namiji kin dace, idan kuma aka yi rashin dace uwar miji taki ki.
(Kuyi hakuri bawai babu Yaren Novel bane a labarin amma ina son ku fahimci wani abu ku mata ne! Kuma dole a gaya muku rayuwar wasu dangin mijin baka san da wanda Allah zai had'a ka dasu ba, amma yana da kyau mu fahimci kan rayuwa ba wai nace babu Sex bane a'a kawai labarin na gina shine akan wannan yanayin 🙄🤨 yan buta roro, idan aka barku da shugaban karamar hukumar wandon cinye shi zaku yi. Wallahi ba sex story bane labari ka fahimci sakon labarin shine damuwar, idan naso sai nayi labarin kamar Kwarkwarah 😂🤣 lami kenan a gaban Uban kowa ma za a karanta labarin babu jin kunya ko rufe fuska 👏🏼)
Ba wai na gaya miki mugun hali ne ko muguntatta ba, a'a tana da fada amma tana da kirki, kowani dan adam yana da kirki yana da banzan hali, idan Allah yaso halin kirkin ya danne banzan halin ka huta idan kuma halin banzan ya danne na kirki ka banu, domin duk wanda zai fadi wani magana akan ka toh halin banzan zai fada akanka. Ba zai tab'a duba tarin alkhairirronka ba, burin shi ya fadi wancan mugun halin."
Rike hannuna tayi sosai, tare da kallona.
"Jinki Allah ba zai tab'a jarabtarki ba? Ko yayi dake ne ba zai tab'a jarabtar rayuwarki ba? Maimunari idan har namiji zai dauke ni ranar aurena bayan an daura min aure da wani yaje yayi rayuwa dani meye yafi wannan muni da jarabta? Maimunari idan har zai tafi dani bai tab'a mu'amalata ta cikin nutsuwa ba meye yafi haka cin rai?" Damke hannunta nai hawaye na wasan tsare a fuskana, "kinsan me ya faru? Hatta rayuwar ki nice na lalata miki, domin ba zan manta ba bayan na gama tsine mishi, sai da nayi furucin da nasan shi yake dawainiya dake." Riƙe hannun juna muka yi, kwalla na zuba mana.
" Nice na jefa ki a ƙaddara, da a lokacin ban ce wani abu nakanki ba da yau rayuwarki bata cikin matsala. Kiyi hakuri da dangin shi da kuma Mahaifiyarshi."
"Mommy ba zan koma gare shi ba, shi daya yayi aure uku bayan Bana nan? Mommy wallahi ina son Mohan, Mommy kinji zuciya tab'a kiji yadda take bugawa, Mommy Mohan wani shashine na rayuwata, amma haka yayi watsi da ni, wallahi ina son shi. Mommy ban san yadda zan gaya miki yadda nake kishin sa ba, shi din mijina ne, Mommy ki min addu'a ko zan sami sauki a zuciyata. Mommy Mohan kamar zinari ne a cikin tsakiyar taku.
Shi din Kamar ruwa ce min a zafin sahara, kyauta ne da na samu bayan na rasa kome na, Taya ba zanyi kuka ba, amma nagode zan koyi hakuri zan kuma koyi dauke kai, amma Tabbas ba zan iya hakuri a min irin abinda aka miki ba, ba zan iya dauke kai a cutar dani ba, wallahi zan yi magana, kuma idan ka takani zan rama, sai dai idan ba zan iya ba."
Dariya yayi tare da isowa gurin mu.
"Yar Baba gaya mata dai ke ba irinta bace, zaki iya yaki dan kwatar kanki. Karki yarda wani ya taka ki, kina da Uban da zai tsaya miki, ko ita uwar Mohan kyaleta nayi sabida Mohan amma da na mata abinda zata nime ki da kanta, amma bana son haka domin xan fi son ki sami soyayyarta da zuciyar ta, shi kuma Mohan ba yadda kike tunani bane, Yaron yana sonki"
Mikewa nayi ina kunkuni.
"Haka kawai ai da ya damu da Ni, ba zai zauna ba sai ya nimo ni amma bai zo ba yana can ina soyayyar shi da yan mata dama ai nasan nice na takura mishi toh na fita a rayuwar shi. Allah ya bashi hakuri ya cigaba da zama da Kanwa dan Ba'are, Allah zai saka min"
Na fada ina kuka.
Su kansu dariya na basu domin ba dage sai faɗa nake, zaunar da Ni Abie yayi ya mika min ruwan addu'o'in da kullum yake bani, nasha sannan na sauke ajiyar zuciya.
"Kiyi hakuri" kallon shi nayi kafin, nayi kwafa.
"Wallahi da zan ganshi sai na sashi ya dauki cikin shi nima na gaji, tunda bai da."
"Ai ke kika da hankali tunda gashi zaki sauke mishi cikin ya dauka, rigimammiya kawai" Mommy ta zungure min goshi.
Cikin sabon bakin ciki na kuma fashewa da kuka.
"Abie ka ganta ko? Ni aka yiwa laifi amma ita haushina take ji, wallahi sai na rama akan Mohan duk abinda aka min tunda ya cuce ni"
"Kyale ta, Uwata haka take bata da kirki, kinji babu wanda zai kuma sa min ke kuka kina da Jarumin Uba irina, ko na miki kiranye Mohan din ne duk inda yake ya sussuce ya fito niman ki"
"A'a!" Na fada,
"Yawwa Yar albarka Ubangiji yayi miki albarka Insha Allah zaki yi kyakkyawan karshe da kyakyawan sakamakon hakurin ki."
Gyada mishi kai nayi, tare da mik'ewa a hankali. Wato lallabani da Abie yake kamar wata kwai, amma ba zai hana idan nayi rashin hankali ya taka min birki ba. Ashe Benazir ta haukacewa Khalil. Allah Sarki baki daya ta nuna ba zata aure shi ba. Babu wanda ya sani.
***
Niger.
Baki daya ya Surkukurce idan ka ganshi ba zaka dauka Khalil din da ka sani ba zaka yarda shine ba.
"Mohan yarinyar taki fahimtar ba da gayya aka hada auren ba, wallahi duk yadda naso na mata bayani taki, yanzun haka ta yi ta rufe Ni a WhatsApp ɗinta. Mohan ban san inda take ba balle na je."
Wallahi duk sai ya bashi tausayi, ya rasa yadda zai yi dashi.
"Khalil ban san me zance maka ba, domin kuwa nima ina cikin yanayin da kake ciki, kuma nasan maganar baki ba zata wadatar ba, dole sai da rarrashi. Kayi hakuri Insha Allah zaku dai-dai ta."
"Ba zata yarda ba, wallahi ba zata yarda ba, duk yadda na bata hakuri taki asalima cewa tayi ba zata aure ni ba, ni da zasu amince da sun duba alamarina "
"Zasu amince mana." Inji Mohan,
"A'a na hakura da ita, sabida itama Umma Umarnin Nahnah take bi, sabida soyayyata ba zan hana Mahaifiyata yiwa nata Mahaifiyarta biyayya ba, Allah ya zab'a min wacce ta fita, akan dangina ba zan zab'e ta, dukda ina kaunar ta, amma na zabi Mahaifiyata na barta"
Wani irin sanyi jikin Mohan tare da kallon Khalil, wani irin Tausayin Khalil yayi wani irin mutum ne shi da yake cike da sonka kowa ya zauna dashi sai tayi rashi mai girma, duk wanda ya rab'a sai ya rasa wani na jikin shi yanzun Khalil ya rasa yarinyar da yake matukar kauna. A hankali ya mike tare da barin gidan su, tunda ya shiga cikin gidan su. Ya sami mahaifiyar shi tana fada da Radiyah, zama yayi tare da daura kanshi a zaman gwiwar Hajiyar shi.
"Ammyn na amince zan auri Jalilah!"
"Haba? Lallai ka kyauta min, Nagode kuma kaga ta samu tarbiyya na gari"
"Ammyn don Allah ki so Maimunari mana! Don Allah ki kaunace ta, wallahi zan miki biyayya"
"Koda zaka dawo da ita, sai naga yadda ka zauna da ita ta kuma samu kwanciyar hankali a rayuwar ku zan duba yadda zaku zauna."
Lumshe idanun shi yayi tare da sauke ajiyar zuciya, a kai akai yana kuma kara jin kamar ya gama rasata kenan, tabbas ba ji bane ya rasata baki daya, domin yasan ya rasa ta baki daya. Kwallar da yake danne shi, a hankali yake jan numfashi, sabida yadda yake jin kirjin shi tayi nauyi, Yana ji yana gani ya rasa yarinyar da ya kaunata.
"Ammyn me kike so nayi domin ki Huce!"
"Ka hakura