Showing 84001 words to 87000 words out of 181864 words
kalle shi.
"Kace min congratulations"
"Ba zan fada ba"
"Toh kuwa zan fita a motar."
"Ok" ya faɗa bayan ya shiga.
A hankali na maida kai na jikin kujeran, ba yau ba ina son muyi magana da Hammah Mohan, ina son na gaya mishi gaskiyar kaina, ina son nayi rayuwa kamar kowa ina son Yancina. A dame na kalle shi.
"Hammah Mohan, ina son muyi magana da kai ban san yadda zaka dauka ba."
Kura min ido yayi sannan yace min.
"Idan ba zaka iya fada ba toh dole ne?"
"Eh dole ne"
Tab'e baki yayi na rasa gane yadda zan gaya mishi.
"Nifa lafiya ta lau, kuma yadda kake gani na ba haka nake ba."
"Dama na ce ina son sanin yadda kake mata maza"
"Hammah ka daina mai da zancen wasa mana"
"Ok na na mai da shi babba."
Baki daya ya ki saurarona, ni kuma ba kome bane yasa nake son gaya mishi halin da nake ciki ba sai fadar da muka yi da Hurayyah, ta kuma sha alwashin sai ta haɗa ni dashi. Toh ina son na gaya mishi amma da kuma abu me muhimmanci akai na.
Bayan mun isa gida na wuce dakin nayi abunda zanyi na fito, gabana ne ya fadi lokacin da naga sun zura min ido har da shi.
"WALLAHI tallahi Azim, mace ce Almamoon ba namiji bane." Kura min ido yayi tare da niman sanin ba'asi.
Ranshi ya kai kololowar baci, domin na kasa magana, jikina yana rawa.
"Yallabai shekaranjiya na shiga ban daki na ga audugar jinin, sannan na sami wannan bra din a ban dakin, idona idon Mamoon mace ce kuma idan nayi karya gata nan ka tambaye ta."
Kallona yayi tare da niman me zance,
"Meye gaskiyar abinda ta faɗa?"
"Hammah Mohan!"
"Gaskiya zaki gaya min?" Ya daka min tsawa.
"Abinda nake son gaya maka."
Bai saurarre ni ba, ya fita da wani e sauri, bin bayan shi nayi. Ko kafin na isa ya shiga mota tare da fita a haukace, haka nayi ta bin shi da mugun gudu. Na rasa gane dalilin da yasa yaji haushina.
Numfashi na sauke ina kallon motar, domin nasan ba zai tab'a saurarona ba.
Ina shiga cikin gidan naga ma'aikatan gidan suna min dariya, naji babu dad'i dan haka na koma daki na zauna ina nazarin su.
Sam ban san meye na tsare musu ba, baki daya sun tsane ni sun tsani alaƙar mu, karo na farko da naji bana mubaya'a da boye min jinsina da Innah take koma me zata yi ba zan cigaba da boye kaina ba.
..... Har dare ban ga Hammah ba,asalima kin shigowa yayi sai da yaga alamar nayi barci ya shigo. Haka ma washi gari yayi fucewar shi. Gashi ina son tafiya gida, dole tasa na hakura da abinda nake so na jira shi.
Haka kwanaki ya tafi babu shi babu alamar, karshe na tattara na koma gida.
Da tarin tambayoyi a bakina.
**
Niamey
Kallon shi Ɗan Ba'are yayi dariya ce ta cika mishi ciki, amma sanin bai da daraja yanzun zai kafta mishi rashin daraja yasa shi kura mishi ido. Yau kwana goma tunda yazo ya kasa gaya mishi gaskiyar abinda ya kawo shi sai dai ya zauna yayi ta busa shisha. Ya sha kamar ba gobe.
"Amma dai ƙasan ina da abun yi ka tarani a gaban ka kamar mai daukar darasi"
Ajiye bututun shishar yayi tare da saka hannun shi a tsakanin cibiyiar shi kamar mara gaskiya, ya sunkuyar dai kai.
"Mohan bana ciki da Bura Uba, zaka gaya min meye ke damun ka saka Ni a gaba kamar me niman gafara."
Shiru yayi yana kallon Dan Ba'are, kafin ya kura mishi idanun shi da suke maiko alamar ruwa ce ta taru a cikin shi tace mishi.
"Kasan Yaron nan ya ninke mu ne baibai" Ya faɗa yana jin karin b'acin rai sama da na kullum, kafin yace mishi.
"Kamar Ya?"
"Kamar yadda ka sani!" Na fada a zafaffe,
"Toh Ni ban san kome ba?"
"Allah yasa karka san kome dan Ubanka, dan iska Yaron nan dai." Shiru yayi yana kallon shi. Ya ma rasa yadda zai da ranshi. Sai jingina kan shi yayi da jikin kujeran, kan shi yana kallon sama.
**
Damagaram.
Lokacin da na koma gida zunzurutun tsoron Allah da tsoron Innah kasa tambayar ta kome nayi, sai wani mugun shakkar ta ya kuma kama ni, dan haka na hadiye kome nayi shiru, har yanzun bani da zarran tunkarar Innah, har yau bani da kwarin gwiwar mata magana kai tsaye sai na nime taimakon Baba, shi yasa na ajiye batun bayyana kaina.
..haka nayi ta kome suku suku, na turawa Hammah Mohan sako yafi sau dari bai dawo min da shi ba, na kira shi bai kirani ba, karshe ma kin daukar kiran nawa yayi, na rasa meke min dad'i.
**
Yau ma kamar jiya yana son gaya mishi abinda ya faru amma ya saka bude baki.
"Wai kai dan iskan ina ne? Meye ya had'aka da Mamoon? Nayi imani da Allah da za a gwada jininka sai an samu ya kai dari uku meye yake damun ka haka."
Sake jan bargon yayi tare da lumshe idanun shi, yana kara jin takaici na murkusa shi.
Kasancewar likita ya zo har gidan ne yake duba shi, yasa Dan Ba'are rufe shi da masifa, bayan likitan ya gama auna shi, ya rubuta musu magani tare da mishi gargadin.
"Yallabai ka kula da kanka jininka yayi mugun hawa,.....
#Mai_Dambu
https://www.wattpad.com/1107772645?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=It8W%2FoFtRBNmtv626Ht7hoebrG%2FLVlSJZLNfj7SZVFb70I%2BU8R57oeYt0nQfprrru5On2xw2q9Wa9DKvsVlrhYzw3HNW938T6zol7nYvstpRTnu2EztkBZZewXp3wWvE
🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
BABI NA TALATIN DA D'AYA.
Dafe goshin sa yayi tare da lumshe manyan idanun shi, ya bude tar akan likitan.
"Karka bari iyayena su sani"
Ya fada yana me gyara kwanciyar shi a jikina matashin, yana jin kamar ta cire zuciyar shi ya huta. Ya gaji da damuwar Almamoon, allura likita yayi mishi wanda zai sanya shi barci. kuma anyi nasarar haka, domin yayi barci cike da mafarkin Mamoon tana sanye da wasu shegun kaya. Ga kai yake tare da mika mata hannu.
Amma sai wani ja mishi rai take tana wani yauki.
**
Kallon juna suka yi tare da Amincewa da bukatar su, kafin suka ce.
"Idan muka bar shi zai cigaba da kare Ubanshi, idan muka tab'a shi zai iya daukar kasadar tab'a mu, amma idan muka saka Ubanshi ya kashe shi wannan alfarma ne kuma samu.
Ranar da kasar mu ta samu yancin kai ranar zamu basu kyauta da ya dace dasu, daga dan har Uban zamu bashi kyautar da zasu iya daukar shi."
Sannan ya cigaba da tsara musu kome, cikin nutsuwa da sanin ya kamata, kafin ya mike kamar mutumin kirki, ya bar dakin da suke taron sirrin.
**
Yau kwana biyu.
"Wallahi Yaron nan mace ce ba namiji ba" inji Mohan.
"Kamar Ya?" Ya tambaye shi a rud'e.
"Mace ce kamar yadda ka sani, taya hankalina ba zai tashi ba yaron ya gama cutar dani." Kasa magana yayi yana kallon Mohan,
"Ban san yadda zan yi ba, amma ina cikin tashin hankali" ya faɗa a sanyayye,
"Tashin hankalin Uban me? Malam kana son Yarinyar nan tun tana namiji, dan haka yanzun ya dace ka fidda abinda yake ranka, idan kuma ka b'oye toh wallahi damar da wasu suke nima kenan, ka tafi ka tambaye ta meye yasa ta boye kanta na tsawon lokaci haka? Yaron bai iya karya ba, sai dai idan bai dagamar fada ba, sannan ban ga abinda zaka daurawa kanka yawan jini ba, kana son ta sosai duk wanda yake tare da kai yasan kana son Yarinyar."
"A'a ba soyayya bane, kawai shakuwa ce. Na shaku da yaron kuma ina matukar tausayin shi. Ashe mara mutunci bai damu da yadda na damu dashi ba."
"Komo meye malam me taurin kai mun san kome, tunda har ka iya hana mu mishi magana yana namiji shine yanzun zaka kawo min gulma me ciwon soyayya kawai." Gyara kwanciyar shi yayi tare da Lumshe idanun shi, yana kara tabbatar da kanshi yanawa Almamoon wani irin mugun SO ne kuma shi kanshi bai san da me yake son Yaron ba, idan yace da zuciyar shi ce toh ba mamaki karya ne amma idan yace da ranshi ne wannan gaskiya ne. Dan haka ya cigaba da sauraron shawarar da Dan Ba'are yake bashi.
Murmushi yayi sannan ya mike da karfin shi, ban daki ya shiga yayi wanka sannan ya fito k'ugun shi daure da towel, hannun shi rike da wata karamar towel yana goge kanshi, murmushi ya sake irin gashi ga Mamoon suna cikin farin ciki.
Shiryawa yayi cikin jamfa da wando kaftani, sai wata hular dara wacce ya murza akan shi, yau yake jin shi kamar zai tafi zance. Dan haka ya shirya kai yadda yake shiryawa kamar ba shi ba, domin kuwa shi kan shi yasan yayi kyau. Privet jet zai bi domin idan ba shi ba zai isa Damagaram a kan lokaci ba. Kiran Dan Ba'are yayi ya gaya mishi. shi kuma ya kira sojojin da suke Damagaram akan ga Mohan nan zuwa.
Yana kashe wayar shi Ammyn na kiran shi.
"Ina ka shiga ne yau kwana biyu ina niman ka, toh duk da dai babu damuwa, kaje Hanan tazo kuyi magana da ita."
"Toh"
Ya fada tare da duba layinta ya ajiye ya a blacklist, koda zata kira shi ba zata sake shi ba.
Bai bi takan wata hanan ba, yayi fitar shi, anan Khalil ya bashi sakon da ya samu.
"Dama meye shirin ka?"
"Kyale su, haka nake bukata ka kula da kanka."
"Abbu da?" Khalil ya tambaye shi,
"Karka damu zan mishi bayani."
"Batun Hanan fa?"
Kallon shi yayi na wasu lokuta kafin ya mai da kallon shi bisa titin.
"Yarinyar ta cika tsani, sannan siririya ce tana da kyau amma ba Matsalata bane kyanta, ka duba yanayin su da yanayin Almamoon. Koda ban sonta matukar zata zauna dani nasan zan sami yara masu tarbiyya, ban sami soyayyar Uwa ba, sai gashi na samu soyayyar Mace da tausayina, dan haka ba zan iya auren Hanan ba domin daga uwarta har uwar da ta haife ni halin su daya, itama zata iya tashi da mugun halin su, Yarana su tashi a wahale, gwara wanda zan ajiye guri daya duk inda zanje zan dawo na ganta cikin Yayana, zata zame musu gata da jin kai. Ita kuma gata yayi mata yawa ba zata san hakkina da yake kanta ba."
Ya fada tare da lumshe idanun shi.
"Nima shekara daya da wani abu ne hadu da wata yarinya a Maradi, sai dai har yau ban kuma haduwa da ita ba, gashi Nanna ta matsa min na fidda matar da zan aura, wallahil ina cikin damuwa da soyayyar Yarinyar."
Dafa hannun shi yayi tare da cewa.
"Insha Allah zaka ganta, zaka same ta." Da wannan ya ajiye Mohan a airport, shi kuma ya koma gida ya cigaba da aikin su.
Yana isa jirgin yana tashi da shi sai Damagaram.
.
Kawai a raina nake son kuka dan haka ina tashi ban tsaya ba, nayi ficewa ta, domin Innah tana barci tun ranar da Hammah ya daki Shago na samu hutu a cikin Unguwar mu, kowa mutuntani yake.
A hankali nake tafiya so nake na bar cikin unguwar baki daya, motar sojoji ne ya tsaya a gefen Hanyar.
"Dan saurayi? Don Allah kasan gidan su Almamoon" kallon shi nayi yana cikin Hilux, a hankali na sunkuyar da kai tare da jan hancina.
Hular kaina na cire bayan na gyara tsayuwa ta, na warware mayafin da yake jikin hular tare da baza gashina har ƙafadana.
"Eh nasan dai gidan su Maimunari Isma'il Wodaadabe" na fada tare da rike k'uguna.
"Toh ya shigo zance ko ta shigo"
"Anya yanzun duniya babu yarda da fatan ba harbe ni za ayi ba." Saukowa yayi tare da takowa gaba na.
Sai na ganni yar cakwai, a gaban shi. Bude min kofar yayi na shiga, sannan ya shiga shima. Kallona yake kawai ina gyara mayafin kaina.
"Dama nasan da wannan, amma me yasa" murmushi nayi sannan na cigaba da wasa da hannuna.
Riko hannun yayi yana faɗin.
"Moonah kin min adalci?" Sunkuyar da kai nayi ina gyara zaman mayafina.
"Ba haka bane, naso nayi maka bayani amma baka saurare ni ba, ka mai da batuna shirme."
"Moonah!"
"Na'am Hammah na."
"Me kike ji a kaina?"
Kallon shi nayi kafin na mai da hankali na, kan yatsuna.
"Alkalamin ƙaddara ta zana kaddarar mu tare, sai Yau da nake tare da kai sai nake ga kamar nayi shishigi da son kaina dayawa, na zake dayawa. Sam na manta da akwai irin wannan lokacin, gani nake kamar ni din Yar kaina ce, sai yanzun da gari ya waye na Fahimci wacece ni."
Na kai hannu zan bude kofar motar, rike ni yayi yana kallona.
"Me yasa kike son kawo wani damuwa kuma?"
Juyawa nayi na kalli hannun shi da yake rike da hannuna. Wani irin kallo na mishi wanda yasa shi saurin sake mayafin. Murmushi nayi domin ya burge ni yadda yayi saurin fahimtar yanzun ba da bane.
"Ni da kai muna da banbanci fa, Kai dan Shugabanan kasa ne, ni kuma ko dagaci Ubana bai rike ba, dan haka yana da kai ka fahimci wani abu, kawai alaƙar mu a iya abota ne bayan haka bana jin akwai wani abu da za...."
"Bana son jin haka!" Ya fada da karfi,
"Kin san yadda maganarnki yake kona min rai?"
A hankali na bude motar na fito, ina kallon waje, shima fitowa yayi tare da zuba hannun shi cikin aljuhun wando shi. Sai yanzun na kare mishi kallo ya hadu sama da kullum. Dauke kai anyi ina wasa da hannuna.
"Me yasa?"
"Ban sani ba, amma koma meye ai suna da hujjar bani abinda ya dace, koma meye suna da ikon sauya min ra'ayina."
"Amma basu da ikon sauya miki ƙaddaran ki, basu da ikon sauya miki goben ki, ki tsaya a matsayin mace kamar arziki ne" murmushi nayi sannan nace mishi .
"Gobe na? Ƙaddara ta? Yau nake dashi gobe bani da kome sai abinda Allah ya bani." Rike hannuna yayi sabida ya lura tafiya zan yi, juyawa nayi tare da zame hannuna cikin nashi.
"Ka gane yanzun da baya akwai banbancin, idan da shaidan bai samu galaba akan mu ba, a yanzun da muka san kan mu zai iya samun damar shiga rayuwar mu."
"Har ila yau ba ki faɗa min me kike ji a kaina ba" murmushi nayi sannan na juya ina faɗin.
"Bana jin kome a raina akanka, asalima sai yanzun na fahimci kai Mutum ne mai matukar gundura da hawa kai"
Cafko ni yayi tare da sake dariya, yana mai d'aga ni sama, dariya nake kamar zan zauce.
"Tun ba yau ba na gaya miki yadda nake jin ki a rayuwata Me yasa ba zaki gaya min yadda kike jina ba?" Sauke ni yayi yana kallon yadda nake wani jijjiga, tare da mai da kaina kamar mazari na nakasa rayuwa guri daya.
"Idan na gaya maka yadda nake jin ka me zaka bani?" Na hada index fingers dina ina buga su.
"Kawai zan tafi gidan tv na basu labarin kaunar da nake miki ne"
" A wannan shekarun naka?" Na tambaye shi ina wani hararan shi.
"Ayya kuma ta nan kika ɓullo min? Me kika fito yi toh" Ya tambaye ni,
Tab'e baki nayi ina kallon shi, kafin na yatsina fuska ina faɗin.
" Kuka na fito yi, amma da na ganka sai na ji na hakura. Ban cika damuwa da kome bane kaje idan na san me nake ji zan kira ka na gaya maka."
Shiru muka yi tare da kallon juna, kafin ya juya tare da shiga motar yana faɗin.
"Ubangiji yasa karki gaya min, aikin banza aikin wofi" ya buga motar. Dariya ya bani, san haka ina kallon suka bar unguwar gyara zaman mayafina nayi tare da saka hula, na nufi gida.
Lokacin da na shiga cikin gidan, Innah tana kallona ganin na shigo da walwala yasa tace min.
"Me ka samu?"
"Babu" na wuce dakin.
"Mamoon!" Da sauri na fito,
"Meke damunka?"
"Babu"
"Zo ka gaya min?"
Cikin tsoro da abinda zan tambaye ta, yasa Ni zare ido. Kirjina yana mugun bugawa kamar zai b'alle,
"Me yasa ka damuwa?"
Shiru nayi ina kallon ta, kafin ba ce mata.
"Innah me yasa?" Shiru nayi,
"Me yasa me? Ina jinka ?"
"Innah ai ni ba namiji bane? Me yasa na."
"Mutumin nan shi yazo da motar sojoji ko?" Ta tambaye ni tana murmushi. Girgiza mata kai nayi jikina yana rawa,
"Kin Fara soyayya ko Maimunari? Maimunari gaya min soyayya ko? Da nace ki rabu dashi baki rabu dashi ba? Toh bari na gaya miki ba sonki yake ba jikinki yake bukata, idan ta gama dake ba zai kuma kula ki ba, Yaran masu kudi haka suke."
"A'a Innah Mohan ba haka yake ba?" Dukar bakina tayi tare da cewa.
"Baki isa ba wallahi"
Cikin fushi na mike tare da cewa.
"Na isa na gaji..... Wayyo Allah na Nepa suna wahalar da mu fa😭😭 wallahil babu wuta.
#Mai_Dambu
[8/7, 10:03 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1107772645?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=It8W%2FoFtRBNmtv626Ht7hoebrG%2FLVlSJZLNfj7SZVFb70I%2BU8R57oeYt0nQfprrru5On2xw2q9Wa9DKvsVlrhYzw3HNW938T6zol7nYvstpRTnu2EztkBZZewXp3wWvE
🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
BABI NA TALATIN DA D'AYA.
Dafe goshin sa yayi tare da lumshe manyan idanun shi, ya bude tar akan likitan.
"Karka bari iyayena su sani"
Ya fada yana me gyara kwanciyar shi a jikina matashin, yana jin kamar ta cire zuciyar shi ya huta. Ya gaji da damuwar Almamoon, allura likita yayi mishi wanda zai sanya shi barci. kuma anyi nasarar haka, domin yayi barci cike da mafarkin Mamoon tana sanye da wasu shegun kaya. Ga kai yake tare da mika mata hannu.
Amma sai wani ja mishi rai take tana wani yauki.
**
Kallon juna suka yi tare da Amincewa da bukatar su, kafin suka ce.
"Idan muka bar shi zai cigaba da kare Ubanshi, idan muka tab'a shi zai iya daukar kasadar tab'a mu, amma