Showing 180001 words to 181864 words out of 181864 words
First Love." Inji Mommy
Daka tsalle nayi na rungume Hammah Mohan, abinda Mommy ta faɗa.
"Ai dukkan su munanan ne, kace karshen kyau!" Inji Abie.
Kuka na fashe da shi, ina kara rungumar Hammah Mohan, murna nake ji yadda iyayena suke nuna min. Kamar zan shige jikin Mommy
Sai dare muka koma domin an kawo abinci daga gida, na gaji sosai.
"Yan mata ya kama ta kiyi wani abu dan wallahi ina son ganin ki da ciki."
Dariya nayi na gyara kwanciya ta a jikin shi.
"Kayi wani abu"
"Ai ina kan yi ko kin sha maganin hana haihuwa ne?" Da sauri na tashi zaune tare da cewa.
"Wallahi ban sha kome ba, hutu ne kawai."
"Gaskiya bana son hutun nan ya isa haka."
Gyada mishi kai nayi sannan na ce mishi.
"Toh Hammah na, Allah ya kawo mai Albarka."
** Sai da Mommy tayi sati biyu sannan aka yi suna Bayan sunan inda aka sanyawa yaran Mariya da Mustapha,
Inda muke kiran Mustapha da Aneen Mafiya kuma muna kiranta da Anam.
Bayan sunan nima na fara nawa. Laulayin kamar yadda Hammah Mohan yaso.
Bayan wata tara Allah ya nufa ba sauke katon Yarona namiji, wanda tare muka yi nakudan da Hammah Mohan.
Aka saka mishi sunan Abbu muna kiran shi Abul Khair,
***
Bayan wasu shekaru.
Mun fito makarantar su Yumnah, anyi bikin yaye su, Aneen da Anam suna fada, gefen su Widad ne, tana kallon su. Bata musu magana ba, na shigo motar.
"Ummin Abul Khair, Kinga Aneen tana ce min dan lukuti" ya fada idanun shi na cika da kwalla.
"Ummi wannan kawu Aneen din bai da kirki zaginta yayi wai munafuka." Inji Widad da take kallon su.
"Toh ya isa haka ko na hada mu da Appa yayi min maganin ku"
Bubbuga glass din motar aka yi na kalli wanda yake wajen motar tare gabana ya fadi na kuma saka key tare da kiran Mohan, yayi ta buga motar yana ihu, can sai ga Hammah Mohan.
Kwallon da Hisham wanda ya dawo Mahaukaci karfi da yaji, sannan aka janye Hammah Mohan, yazo ya fito dani, ya rike hannun.
"Mata ta! Maimunari Isma'il Wodaadabe, tana dauke da cikina na hudu a jikinta, inuwarta ka kuma rab'a sai na kashe ka." Sannan ya juya muka bar gurin.
*
Koda muka dawo gida na razana ba iya ni ba hatta yaran tsoron Baban su, suke sai da na shiga ban daki jini ya tsinke min dole muka nufi asibitin, sai da aka bani hutun wata biyu, yaran suka koma gidan Beenah, dake Su Aneen da Anam sun koma gidan mu gurin Mommy, Allah sarki Abie da kanshi ya haɗa min maganin da na sha cikin ya koma ya zauna, sati na ɗaya aka sallame ni.
Mohan ya dauke min kome, haka na cigaba da kula da cikina..
Anyi bikin Radiyah dan sai yanzun Uwar Safwan ta amince sakamakon rashin dadin da matar da ta aura mishi take fuskanta a gurin shi, ita da kanta ta roki Umman shi ta aura mishi Radiyah.
Jalilah itama tayi aure a can Saudiya kanin mijin Muslimah ya aure ta, beenah ma Yaranta uku.
Mace mai suna na, sai Mai sunan Umman su, sai Mai sunan Baban su da baban shi, ana kiran shi Hanif, mai sunan Umma kuwa ana kiranta Walidah. Sai Jewanah.
Nairah itama anyi bikinta ta auri dan Sarkin Kano, an sha biki sosai mune manyan yayyu.
***
Cikina yana wata bakwai, Allah yayiwa Matar Salman rasuwa, gurin haihuwa, mugun tsoro ya kamani, babu shiri na shiga nakudar wata bakwai, haka na haifi yarinyar yar karama da ita, aka saka ta a kwalba. Khausar ce a kan mu.
Sai da muka yi wata biyu asibitin aka sallame mu, itama ta koma gidan mijinta sai dai Ammyn ce da Allah ya daura mata jinya sosai, kullum ta ganni sai tayi kuka da niman gafarana. Ga Small Mom itama yaranta biyu, Armaya'u da Areeshah.
Bayan shekara daya, idan ka ga yarinya na ba zaka dauka yar wata bakwai bane, wacce muka saka mata sunan Ammyn muna kiran ta, Khairat.
Zirga zirga muke domin bikin Yumnah da Abie ya bawa Salman ita, bata son shi amma sabida biyayya yarinyar nan ta amshe shi hannu bibbiyu..
Haka muka sha bikin su, dake ya dawo gida da aiki, aka kai ta gidan shi da yake Maradi. Muma haka kawai Mohan ya saka mu muka koma Maradi.
Bayan bikin da wata uku aka mai da mata yaran Salman ɗin.
Rayuwa cike da kaddarorrin masu kyau da marasa kyau mun amshe su, na cigaba da shiga daji ina wayar da kan al'umma Fulani musamman Bororoji babban burin Baba Mari, ya'yanta da suka b'ace. Su dawo amma babu labarin su. Alhamdulillahi domin duk inda muka samu labarin su muka kai musu kayan tallafi da kulawa. Har da musu burtsaitsai sai makaranta ya'yan makiyaya.
Wannan gudunmawar da nake badawa yasa Hukumar Majalisar Dinkin Duniya, suka bani lambar yabo, tare da bani matsayin na musamman inda ake biya na da dallar Amurka, shi wannan kawai ya ishe ni nayi hidimar al'umma.
Ganin yadda nake son dakatar da muguwar dabi'ar Hammah Mohan da kanshi ya tafi asibiti da ni, aka dakatar da haihuwar mu, yace min.
"Ki bautawa Allah, sannan ki tuna da Al'ummar Annabi, karki manta da igiyar aurena akanki na yarda dake ki shiga ki wayar da kan al'ummar Bororoji."
Nayi kuka nayi farin ciki, sannan na cigaba da abinda ya sani. Kuma na yarda da Allah, yana tare da mu.
Gefe guda kuwa Hisham yana ganin Cigaban bakin cikin yadda yake ma ya ishe shi, uban shi ya mutu mutuwar wulakancin, sai a anan aka samo gawar mahaifiyar Hisham din da ya tsafeta yana aikin sabo da ita, shi yasa ake son ka gina Alkhairi zaka same shi a gaba.
**
Shafa wuyana yayi tare da cewa.
"Radiyah ta haihu, baki samu zuwa ba, Nairah kan tace na.miki godiya sako ya isa."
"Radiyah Beenah ta je mana amma Insha Allah zamu je da Yaran."
"Toh Allah ya kai mu"
***
Washi gari
Muka je gidan tare da Alkhairi, dan muna hira wata rana, ta tab'a ganin wata mota tace tana so, dan haka ya saya mata motar, na sami yan uwan mijin suna mata dariya, dan Uwar mijin ta mata bawa Uwargidan ta kyauta kujeran Umra, da muka shiga gidan suna mata wannan tsiyar gani na yasa kowa ya shiga hankalin shi, haka tayi ta gaya min abinda suke mata.
Mika mata key motar ta nayi, ta fito da guda tana ihu, ai babu shiri suka fito, kowa ganin motar ta sai da jikin shi yayi sanyi, dan haka na nuna mata karta damu, bayan mun koma gida na gaya mishi yayi mata Alkhairi akai mata domin haka zai saka dangin mijin su d'aga mata kafa,. Har sauran yan uwan ta, suna kokarin share mata kuka. Sai gashi hatta mijin shima binta yake yi.
......
Mommy tun daga Yan biyu tace ta yafe a kai kasuwa, sai dai mu yaranta, Yumnah ma da ta haihu ba laifi aka yi hidima. Ta samu ya mace aka saka sunan Mommy.
Bayan wani lokaci mai tsawo na ajiye aikin inda na tubure zan kuma haihuwa bai Musa min ba, muka je aka cire min abinda aka saka min a hannu na.
Wata na zuwa kuwa Sai ga cikin nayi ta addu'a Allah yasa na samu takwaran Innnah.
Ai kuwa Allah cikin ikon shi, na samu cikin, aka nuna mana namiji ne, haka ya kashe min jiki, bayan watanni da na dauka Allah ya sauke Ni lafiya, na samu da namiji ne, aka saka sunan Abie, muka kiran shi Adeel.
Watan shi tara na samu ciki. Na sha bakar wahala kamar zan mutu, kafin na haifi yarana biyu mata, Aka saka musu Ummul Khairi sunan kakan Mohan, sai fatar sunan Innah ana kiranta da Meenat.
Naga gata da soyayyar mijina, kuma har yau ina alfahari da mijina, domin ya d'aga darajata daga cikin mutane masu yawa,
***
Bayan shekara goma sha biyar.
Arziki yaci Uban da, na kara kankaro daraja ta, Ammyn kuwa bata moruwa, a cikin shekarun nan muka ji labarin mutuwar Hajiya Karime.
Addu'ar barci na tofa musu, sannan na rufe dakin na nufi namu dakin.
Karfi da yaji ana niman lalata min miji wai ta fito ta karar siyasa, abinda had'a mu kenan. muke rigima, ina shigowa ya riko hannuna.
"Na janye kudirina na bawarwa dan Uwansa Ahmad Bala Raees, daga karamin mataki har zuwa shugaban kasa zan mara mishi baya."
"Shima ce maka akayi Halimah Ishrat zata yarda mijinta yayi ta yawo da Gantali irin na yan siyasa? Salon yaje ya hadu da wasu manta su lalata mishi rayuwa?"
" A'a karki ce min kema zaki fara kishi a tsakanin zubda jini?"
Cikin fushi na ture shi zan wuce.
"Mohan mijin mace daya ce kuma ke ce matar shi a duniya da lahira. Kuma nasan shima Ahmad!"
"Wai ina ka bar Sheikh Zunnur Bin Jonah(Alhubbuh Fihi Mararatun) da kanin shi Yunus Zunnun bin Jonah? Ko ka manta da Arshan ne(Ruwa a jallo) toh idan ka manta su ka bude idanun ka kaga Malam barci nake ji"
Bakin shi a sake yace min.
"Nasan Ashraf,.nasan Mehran, nasan Aliyu Asadullah, nasan Malik da Maheer, nasan Dr Yohanna Chibok! Nasan Ahmad Halwani! Toh na kuma san Aalim da Aamil sai wane?"
"Yunus mai Nasara tare da Ahmad Roma da Amaan Mandara idan ka manta bari na tuna maka su! Da alamu ka manta Jikar Innah wuro, Sadeeq da Aminin shi Imran"
Daukata yayi cak yana faɗin.
"Gaya min sirrin Labarin Addah Ramlat!"
"Eh toh da zaka ce Dambujebuje da zan fi tuna maka kome, cikin nutsuwa."
*Alhamdulillahi Ubangiji Nagode maka sosai da ka bani damar kammala labarin nan akan lokaci kuyi hakuri wallahi bani da lokacin kaina kuma yau ina da zuwa ganin likita amma na tsaya na karasa labarin nan,kuyi hakuri da yadda na kawo shi karshe wallahi ina da uzurirruka masu yawa! Kuyi hakuri! Koda hidimar Muwaddah da Walid aka Barka kasan an baka aiki, balle kuma gana gida ga na miji! And ku ma'abota hankali ne ku duba yanayin, rubutu babu sauki amma Nagode sosai da kuka bani haɗin kai dari bisa dari*
Insha Allah October 10! Zan sake muku sabon Free Book dina Alhubbuh Fihi Mararatun! Free ne sabida kaunarku da yake raina. Sai wanda zan yi na kuɗi amma shi babu rana wallahi Ruwa a jallo!!!.....
INSHA ALLAH
Upcoming books.
ALHUBBUH fihi Mararatun!!
RUWA A JALLO!!(WANTED)
Now
Mu hadu a Kishi a tsakanin zubda jini (Ana kan FREE Pages) ga masu bukata zasu biya ta nan 0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank sai su min magana ta Whatsp 08130269641....300₦ ko katin mtn.
Kufito kwanku da kwarkwatarku kuzo ku sayi kishi a tsakanin zubda jini, ko kuma nayi ta bori rashin daraja,🙄😭😭😒😏 bari na ga Masoyan asali.
#Mai_Dambu