Showing 150001 words to 153000 words out of 181864 words
Khausar tayi cikin tausayawa ta kalli mahaifiyar tatta,
"Sannun Ammyn ya jikin naki?"
"Da sauki! Khausar kicewa Mohan, yaje Agadaz akwai yar kawu Shagari ya aurota!"
"Ammyn ki kyale Hammah Mohan,matukar kika nace zai auro ta amma zai sake ta."
"A'a ba zai sake ta ba" ta faɗa tana sauke numfashi.
"Assalamu alaikum" suka yi sallama shi da Khalil. Zubur ta mike tare da kallon su.
"Yawwa Khalil, gobe Insha Allah ku tafi Agadaz ku nimo auren Yar Kawu Shagari."
"Toh Allah ya kai mu"
"Mohan kayi ƙoƙari ka ga yarinyar tana da nutsuwa sosai."
"Toh" ya faɗa mishi.
"Khalil kaina ba yarinyar nan zaka auro ba ko?"
Shiru yayi sannan ya sunkuyar da kai.
"Me zaka yi da Zuri'ar su! Suna da mummunar nasaba."
"Ammyn ita yake so, kuma mahaifiyar shi da mahaifin shi sun amince ina ruwanki da bashi shawara? Iyayen shi sun san abinda ya dace da don Allah ki kashe matsalar mu da kika Kunno mana shi." Inji Radiyah da tafito daga cikin dakin su,
"Toh Allah ya baku hakuri, bani na hana Safwan aurenki ba, Allah ne ya nufa ba zai aure ki ba "
"A'a Ammyn kece sanadi da baki tozarta sirrin Maimunari ba da babu mamaki babu wanda zai ki auren mu, gashi ko makaranta ban isa na shiga ba, nuna Ni ake da yatsu."
"Toh dan an nuna ki laifi ne? Dama can kin fi karfin matsiyaci ke ba sa'ar shi bace!" Cikin jin haushi ta bar falon, domin zata iya yin abinda bai dace ba, baki daya yayunta sun zubawa Ammyn idanun, sai bakin mulki take da rayuwar su, tun ranar da taje aka kafta mata tijara a gidan su mijin Khausar take kwance ba lafiya.
"Ammyn zan tafi aiki domin yau aikin dare gare ni" ta shiga hada kayan aikinta ta saka a jaka.
"Toh ayi ta kwalliya dai domin ba zaki koma gidan da a san darajar ki ba! Gwara ki samo mijin kera sa'a, wanda zai nunawa Abdullahi yafi karfin shi"
"Ammyn nifa ina son mijina, kuma ban ga laifin mahaifiyar shi da tasa shi ya sake ni ba, dan haka babu namijin da zan kula wallahi mijina nake so, ni ba Hammah Mohan bane yaga zai iya, yanzun Salman da Haddir da basu tare damu ai hankalin su kwance domin zasu iya fuskar rayuwar da muke, shima Abbu naji yana niman aure, kuma ya ce min yarinya ce karama yar Sarkin Maradi"
Mikewa tayi zubur kamar zata tashi sama,
"Yarinya karama? Ya rasa abinda zai sai auren yarinya karama, ai budurwan zuciya ce!"
"Allah! Kina iya tozarta matar d'anki ma, balle matar da zan aura ranar juma'a daurin aure, ga katin nan"
Ya mika musu yana kallon su.
"Mohan naji ance kayanka zasu shigo ta kwatano, Allah ya taimaka."
"Amin Ya Allah"
"Yallabai don Allah ka saka baki yayi aure"
"A'a keda dan gwal dinki! Ai duk abinda kika zab'a mishi zai bi, yaro mai biyayya haka"
"Wallahi baya jin magana nace yaje Agadaz yaki min"
"Toh kai dan gwal kaji Maman ka"
"Insha Allah zan je"
Haka ya fita ya barsu, itama khausar ta tafi aikinta, suma suka wuce shashin Mohan, tunda ya kwanta, ya kurawa sama ido bai kuma magana ba.
"Khalil nasan kana sane da inda Maimunari take, amma kaki gaya min meye nayi da zafi ne?"
"Wallahi ban sani ba, muna chat da kome da Beenah amma bata gaya min ba, sai dai idan na tambaye ta zata ce min da sauki."
Tashi yayi zaune, tare da kallon shi sannan yace mishi.
"Don Allah ka mata magana ta turo min hoton Matana mana"
"Toh bari na dubata."
Yana bude data ya fara duba ko tana online, aikuwa ya hango ta, ta daura hoton Maimunari,
Mika mishi wayar yayi yana kallon ta, sanye take da doguwar riga, ta yane kanta da farin mayafi.
"Ya Allah! Kai kasan dalilin cusa min kaunarta a raina! Ubangiji ka tabbatar da zama na har abada a rayuwar mu"
"Amin Ya Allah Mohan" inji dan Ba'are, kwanciya yayi yana kallon fuskarta, cikin sabon kaunar matar shi.
"Yar budurburdu dina"
"Toh toh ya hakuri bani wayar na yi magana da yar kwailata"
"Dan iska"
Ya cilla mishi wayar ya cigaba da kwanciyar shi, idanun shi a rufe, yayi tare da tuno daren da ya tsaya mishi a rai, yarinyar ta bashi hadin kai sama da kome a rayuwar shi, ta yi hakuri da shi a daren kuma ta dauke laluran shi, tun daga ranar bai kuma jin wani sha'awa na mace ba, bai kuma kallon mace da sunan bukata ba, mace daya ya so a rayuwar shi bayan ita kuma Allah na tuba ba zai kuma jin dadin wata ba.
***
Haka Ammyn ta sashi dole ya tafi niman auren Farisa, cikin girmamawa aka yi bikin, ranar da aka kawo mishi amarya Mohan ya mika mata takardan sakinta cikin mutuntaka, sannan ya shure kama yayi tafiyar shi Dubai, sai da yayi sati Uku me kyau sanan ya dawo. Ya sha masifa babu iyaka, nan ma yace mata.
"Idan akwai wata yarinyar ki hadani da ita zan aureta."
"Ni na haɗaka da wata ka je ka sake ta, ai na yafewa Maimunari kai ka jira dai duk ranar da ta bayyana sai ka je ka zauna da ita."
***
Zuwan Mommy ya rage min damuwa, abinka da likita babba, ita tayi ta daura ni akan magani. Matsowar bikin Benazir da Khalil ne yasa, hankalin su yaso rabuwa biyu, dan haka Abie da dan uwan Baban su, suka tsayar da magana akan ayi hakuri na sauka lafiya, lokacin Itama Beenah din zuwa lokacin ta gama karatun ta.
Sosai Iyayen shi suka amince, Kum basu wani d'aga hankalin su ba, haka aka Cigaba da shirya jiran haihuwata.
... Matsa min kafa take, a hankali. Tana bin karatun Alqur'ani karatun Shaikh Jafar Mahmud Adam Marigayi, a hankali take bin shi a cikin suratul Rahama, lokacin da tazo akan wata ta goma, inda Allah yace shin mai dan adam yake bukata wanda Allah bai bashi ba.
"Ya bani Uwa ya bani Uba, ya bani kane, ya bani rai da lafiya.....
🤭Kuyi hakuri kunji.... Raina ne ya sosu, Insha Allah ba zan kuma ba🌚🌝 saura Page daya na tafi hutu 👏🏼 Don Allah ina bawa mutanen grp din Kishi INSHA Allah ina gama wannan zaku ji ni 😏🤸 kwana biyu ban kafta rashin daraja ba, wallahi har kaikayi nake ji😂🤣
#Mai_Dambu.
[8/14, 8:18 AM] +234 815 778 5691: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
BABI NA HAMSIN DA TAKWAS.
Kura mata ido yayi yana mamakin yadda Allah ya daura mata son kanta, sunkuyar da kai yayi yana kallon shaddar jikin shi.
"Zan nima maka maganin ko kurwanka ta kama ta sake maka shi, Insha Allah wannan masifar da me yayi kama."
Bai ce mata kome ba, haka dai ta gama masifar ta, yayi mata sallama ya bar gurin. A cikin kwanakin bai da lokacin kanshi domin tun da ya rabu da Maimunari ya ajiye aikin soja, sai ya koma kasuwanci, kuma dama yana kasuwancin bai mai da hankali bane. Amma yanzun da ya mai da hankali yana ganin Cigaba sosai.
Yau da la'asar ya shirya zuwa duba Maimunari, yana isa da kayan marmari da ya kawo mata,ya samu basu asibitin. Ya tambaya aka ce ba. A san inda suka tafi ba,bai kuma tabbatar da ya rasa Maimunari ba sai da yake gidan Abie ya samu a rufe nan ya gane cewa sun tafi da ita wani gurin ne, haka ya kira Khalil ya gaya Mishi. Amma babu wani labari, da ya sami Abbu da zancen cewa yayi.
"Ban san inda suka tafi ba, amma koma yayya ne ai Mahaifiyarka ta bukaci haka, dan haka idan na isa kuma na haife ka ka kyale musu yar su ta huta, ita ba matar ka bace Yanzun sannan kuma ba zai yiwu uwarka tana tozarta su ba, dan haka na gargade ka da ka fita hanyar ta, ko kuma na sab'a maka."
"Amma Abbu!" D'aga Mishi hannu yayi tare da cewa.
"Itama iyayenta suna SONTA, kuma babu wanda zai yarda ayi ta wulakanta Mishi d'a. Dan haka ka tafi ka zauna da uwarka ita ka barta da nata iyayen, saboda kai ta saka su a kotu, saboda kai ta wulakanta su, duk sabida soyayyar ka. Indai har zata aikata haka saboda tana son ta dawo rayuwarka amma uwarka taki meye yasa ba zaka kyale ta ba? Me yasa ba zaka hakura da ita ba? Tayi kokari tayi kokari. Don Allah ka kyale ta ta huta Ubangiji ya bata wanda ya Fika kai ma Ubangiji ya baka wacce ta fita."
Jikinsa ne yayi mugun sanyi, sannan ya mike a hankali tare da nufar hanyar waje.
"Insha Allah na hakura da ita, Nagode sosai Abie"
Tun daga ranar yayi wani irin sanyi, magana ma bata dame shi ba, baya harka da kowa sai Khalil shima sai yana gari,.ana cikin wannan yanayin me niman auren Radiyah, suka turo har an gama magana, amma mahaifiyar yaron ta tawo da kanta, har gurin Hajiya Latifah.
Bayan sun gaisa tace mata.
"Hajiya Lateefah nice Mahaifiyar Safwan kawai jiya Mahaifin shi yace min sun zo nima Mishi auren yarinyar da yake nima bai gaya min ba sai da suka gama magana. Toh gani nan nazo na gaya miki gaskiya. Bana son had'a zuri'a dake! Ba dan kome ba sai dan mijinki shege ne bai da asali"
"Keke!"
"Ke yi kasa da muryanki! Indai har uwa irinki zata kashe auren danta ranar da ya kwanta da matar shi, meye laifina dan nazo akan a fasa auren dana da Yarki a? Dan haka ita da kika saka ta wulakanta iyayenta. Kin ga ina son kaina da arziki ba zan so dan da na haifa ya maka ni a kotu saboda yar ki ba.
A takaice dai ba zan tab'a barin shi ya auri yar ki ba, da ya auri Yarki wallahi gwara ya mutu bai yi aure ba, balle kuma ga mata kaca kaca."
Ta mike tana kad'a keyn motar ta, tare da ɗaukar jakarta, har zata fita tace mata.
"Wallahi kamar yadda kika saka iyayen Maimunari kuka haka zaki yi kuka ga yara mata gasu nan a gabanki"
Sannan ta fita, yadda kuka san gumki haka ta koma, tana cikin wannan yanayin, Khausar ta shigo dauke da jakar kayanta, niki niki. Idanunta cike da kwalla,
"Lafiya!" Ta tambaye ta, zama tayi cikin shashekar kuka, tace.
"Hajiyarsu Abdullahi tasa ya sake ni" ta faɗa hawaye na zuba mata, daidai lokacin da Radiyah take shigowa da nata kayan, kallon su uwar take cike da mamaki.
"Akan me?" Ta tambaya bakinta na rawa.
"Ban sani ba." Mikewa tayi tare da fita. Dake dama an ce wanzab bai son jarfa, sai gata har gidan Surukar Khausar, ta samu ma suna magana akan Khausar ne.ta shiga cikin gidan.
"Hajiya Marwanatu lafiya Abdullahi ya sake Khausar?"
"Zauna mana Hajiya Lateefah,ai abin ba na tashin hankali bane"
"Akan me zan zauna"
"Toh ita Yar gidan Babban alkalin bata da zuciya ne? Ko ba haihuwarta aka yi ba? Kinga indai har ke zaki iya sakawa dan gwal irin d'anki ya sake yar mutane bayan kuma kuna da abin kunyar meye a cikin dan nace dana ba zai zauna da yar da aka haifi Ubanta shege ba?"
"Wallahi karya ne, sharri aka mishi."
"Malama fita mana a gida, domin duk nan babu mahaukaci irinki,.dan haka maza a tafi a nimawa yaran ya'yan asali masu kyakyawan nasaba"
Asalin koran wulakancin suka mata tare da gaya mata ai ko mata sun kare babu wanda zai auri yar yaranta, taje itama yaji yadda iyayen yarinyan da ta wulakanta take ji!"
"Wai dan akan Maimunari kuke wulakanta Ni?" Ta tambaya kamar zata fashe da kuka.
"Kai kunna mata wayar nan ta gani"
Muryanta ne ya fito fili lokacin da take cin mutuncin Maimunari a asibiti.
"Wallahi na rantse da Allah matukar ina raye babu ke babu Mohan. Yar karuwa ribar dadiro. Yar matsiyata an ce miki arzikin iyayenki zai saka na hakura ki zauna d'ana ne? Ko ance miki cikin da yake jikin zan yarda na d'ana ne? Toh ai bari na gaya miki tun wuri gwara ki nemi uban cikin jikinki, yar matsiyata jinin kazamta."
"Kai kashe min idan ina jin wannan abin ji nake kamar na tattara yaran da Abdullahi da Khausar suka haifa kamar a watsar da su mota ya bi ta kansu" inji Surukar Dr Khausar,
Wani irin abu taji a kirjinta zuwa kanta, dakyar ta d'aga kafarta cikin tashin hankali tace.
"Hajiya Marwanatu, don Allah karki wulakanta jikokinki"
"Ke kika iya wulakanta abin cikin yar mutane! Bayan d'anki ya yarda na shine? Toh ai dan mu ba jahilai bane da mun baki abinda ya dace, dan haka fitar mana a gida Allah ya wadaranki"
Kasa magana tayi ta fita, dakyar ta shiga mota aka fita da ita, baki daya ta rasa fahimtar mene faru, a cikin yan kwanaki ƙalilan kome ya lalace mata. Ji take kamar tayi ta zuba ihu, amma babu hali.
**
Tunda suka isa Geneva, wato Zurich, Abie bai da lokacin kan shi sai na sintiri zuwa asibiti. Kuma Alhamdulillahi domin wannan karon ma ya kuma gayyato likitan da ya dubata, shi ya kuma dubata. Amma wannan karon an yi mata aiki a zuciyarta, dan ma damuwar ya hadu da laluran ciki ne. Haka yayi aikin cikin nasara.
Bayan kwana uku masu kyau, ta fara motsi, a hankali kuma ta farka baki daya, sai dai tun daga ranar. Abie yake mata addu'o'in yana bata a ruwan zam-zam tana sha, abinda ya haifar mata da komawa tayi sanyi. Magana ma sai kayi da gaske take yin shi. Sai nasiha, tare da bata tarihin magabata,
Sannan ya kawo mata irin daukaka ta Khalid bin Walid, wanda Allah ya mishi kirari da saifullahi Ma'asum, sabida yadda yayi adawa da musulunci, sannan ya dawo yayiwa Musulunci hidima yayi adawa da kafirci, tare da kawo mata misalai dasu Nusaiba, Rabi'atul adaweyya, irin su Ummul Salma, karewa ya kafa mata suratul Maryam har dasu mujadala, da yadda mata suka yi gwagwarmaya a musulunci, sai ga Maimunari tana kuka tana rike hannun shi yace mata.
"Lokacin khalifancin Umar, Allah ya yarda dashi, yace an taba zuwa yaki aka kamo bayi aka kawo su, yace yana tsaye sai ga wata mata a cikin su, an daure kafarta da hannunta da Sarka na karfe, yace dan matar ne ya b'ata, bata iya tashi tayi tafiya rarrafe take tare da ciro mamarta duk inda ta ga yara na wasa sai da durkusa ta nemi D'anta, wasu malamai ma sunce an ce matar bata gani, haka tayi ta niman D'anta. Balle ke da dukkan mu mun san mun yi miki laifi, mune iyayenki mun baki hakuri amma bamu tsira ba, haba Uwata ai bawa baya wuce ƙaddarar shi."
"Abie kayi hakuri." Iya abinda na iya fada kenan na kwanta,.ina kuka mai mugun cin rai, amma a sanyayye.
"Kina kukan kin rasa Mohan ne ko kina kukan abinda muka miki ne?"
"Dukka Abie"
Na fada mishi haka, fita yayi tare da gayawa Baba Mari ta tsaya dani.
....
Sai da nayi sati biyar asibitin sannan aka sallame ni, koda na dawo gida ma, gasu Benazir da Abie ya mai da ta makaranta, Yumnah ma haka, idan suka dawo kuma shi yake karantar damu a gidan, a hankali na Fahimci iyayena suna min wata irin soyayya da yasa basu iya tsawata min, musamman Mommy bawai bata fada bane a'a kawai tausayina ne yasa kullum sai ta kirani a waya,kuma koda na dauka daga Sannun sai Sannun da ya jiki da sauki, shikenan. Babu abinda yake hada ni da ita, kuma zata b'ata lokaci tana saurarona, bawai bana son iyayena bane, kawai ni dai ina da yakinin sun tafi sun barni babu wanda ya damu dani sai yanzun da na girma suka damu dani, idan ta ga nayi shiru, tayi min magana nace mata hmm! Sai ta kashe wayar ta kira Benazir ta turo ta d'akina.
Duk da halin da nake ciki ban tab'a tsanar su Benazir ba, asalima jin su nake kamar mun fi haka kusanci, bana son naga Beenah tana rab'ewa idan ta ganni da Abie muna zaune, sai naji kamar sabida Ni aka raba su da Mahaifiyar su.
Yanzun haka ta shigo dakin tana waya da Mommy, zama tayi tana kallona.
"Mommy gata nan dai tana karatu ne"
"Toh Toh kyale ta, karki dame ta, amma ya Babyn ku? Yana lafiya?" Dariya ta saka tare da cewa.
"Lafiyan shi lau, Mommy baki ga Yadda Adda Munah ta koma ba, zan dauka miki hotonta."
Kashe wayar tayi tare da zuwa zata dauke ni na buge wayar ya fadi can, kallona tai tare da juyawa ta dauki wayarta, ta ga ya tsage.
"Addah Munah! Ba laifi bane idan kinyi fushi da Mommy, amma kuskure ne babba wulaknta Uwa. ciki ne a jikinki, kuma zaki so idan kina haife shi ya mutunttaki ko? Wallahi da ace Daddy ne ya saya min wayar nan ba zan tab'a miki magana ba, Amma wannan wayar Mommy ce ta bani ranar da na cika shekara sha takwas, ko da wasa ban tab'a barin shi ya fadi haka ba, sabida ina son Uwata duk abinda zai fito daga gare ta mai kyau ne,"
Fita tayi daga dakin can ta dawo tare da wata jaka, ta shiga zazzage min shi baki daya a gabana, tana kuka.
"Dairy ɗinta ne baki daya, labarinta ne a nan baki daya, soyayyarki ce a nan baki daya. Zaki tozarta mana mahaifiyar mu, idan baki sonta Kice baki kaunar ganin mu, yau zamu bar miki gidan Abien ki, domin ba zan cigaba da kallon ki, kina tozarta min mahaifiyar ba."
Tana fadar haka ta juya ta fita daga d'akin, tana kuka.
Da Abie suka haɗu. Ya riko hannunta har falo ya zauna da ita, goran ruwa yasa aka kawo mishi ya mika mata tasha. Tana shashekar kuka.
"Abie ita me yasa bata farin ciki? Allah ya bar mata Mommy da kai! Mu kuma Allah ya dauke Daddyn mu!"
Wani irin lumshe idanun yayi, tare da bude su akanta.
"Abie a duniya akwai na biyun uwa?"
"Babu!"
"Toh meye yasa take wulaknta Uwa?"
"Sabida laifin da muka aikata? Kuma har yau Mommynku bata zauna da ita ba, kuma tana bukatar