Showing 36001 words to 39000 words out of 181864 words

Chapter 13 - Bororoji Compelet Book Document by Mai Dambu .txt

29 Jan 2025

6260

sauya musu tsarin su yake, Ashari'a kuwa yasha babu iyaka da Tsinuwar su akan ya sauya musu alkibla....
Please if you read hope me sharing to family and friends😭😭😭 karku manta da komens da bote, ko muje hutun kwana uku 😛😁😜🙄😩
#Mai_Dambu...
[7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: *🐂🐂BOROROJI🫀🫀*

~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
BOOK ONE
https://www.instagram.com/batool_spices
Fatima Batool enterprise
Yaji
Ginger and garlic
Onion powder
Pepper soup
Curry
Biryani spices
Mixed spices
Indian spices
Arab spices
Chai masala
Baharat blend
Tandoori blend
Thai masala
Garam masala
Provence
Tea spice
Zobo powder
Gu garzaya Domin samun kayan kamshi na fatima Batool Enterprise. Domin samun yajin suyar na naman layya 😋


Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azi_zat


*Gaisuwar ce wannan shafin Aunty Safiya Jos, Ummi Ilham Gombe, Mom Sayeed Kano, Mrs Faruq matar kakana Nagode sosai*


Sai da rai....
BABI NA SHA BIYU.
Da'go kai yayi tare da kallon su, cikin nutsuwa da yanayin shi na cin Uban kowa ya kwana lafiya, yace musu.
"Matukar wanda zai kula da ya iya kome dukkan ku barin gidan nan zaku yi domin ban yarda da fuskar ku ba. Ku b'ace min da gani marasa mutunci"


Rabil da Hurayyah suka wuce kitchen, Bilal da Moussa suka wuce gurin wanki, Sarah da Nouhu suka wuce bayan dakin da ake ajuye kayan aikin cikin gidan.


Hurayyah da Rabil girki suke, Bilal da Moussa, wankin da guga suke. Sarah da Nouhu sharan gidan suke da goge goge. Kusan idan ya cire Hurayyah itace Mohan ya kawo ta da kanshi sauran kuwa. Daga can fadar gwamnati aka kawo su. Kuma yana kyautatta zaton Hajiya Safiya ce. Ya tsani matar nan kamar me.
***
Niamey.


Shige take da fice, tana hango yadda Hajiya Latifah ta harde ana mika mata wasu takardu, zata saka hannu. Murmushi tayi sannan tace.
"Da Sannun zan ruguza ki, tunda nai babban nasara kawar da wanda ya tsaya muku"


Fitowa tayi cikin shigar Alfarmar ta nufi gurin da Hajiya Latifah take.
"Barka da hutawa ranki shi dade"
Sai da ta b'ata lokaci kamar ba zata amsa ba kafin tace mata.
"Hmm"
Ta cigaba da aikin ta, kamar bata san da tsayuwarta a gurin ba.
"Hmm, dama ranki shi dade akan batun matsalar Mohan"


Ta faɗa tana kallon yanayin da Hajiya Latifah ta shiga, ganin yadda Jikinta yake rawa yasata sake murmushin mugunta, sannan ta cigaba da cewa.
"Dama naga"
"Kije bana son jin sunan shi tashi ki bar min nan"
Ta daka mata wani irin tsawa, wanda yasata mikewar dole, domin babu karya ta razana. Bayan tabar gurin kan Hajiya Latifah ya shiga sara mata kamar zai rabe biyu.


Tsaki tayi tare da mik'ewa, ta nufi cikin gidan, koda ta shiga har ta manta kome akan shi. Itama Hajiya Safiyar dadi ya sata bata kuma bin wani abu akan Mohan din, sai dai tana da kudirin jibi Insha Allah zata dira a Maradi ta cirewa dan Ba'are rashin mutuncin da yake kan shi.


Kuma wallahi ta isa sai ta ganawa Mohan azaba, dan duk cikin Yaran Hajiya Latifah ta tsani Mohan sama da kowannen su,, shi yasa bata yi kasa a gwiwar gurin tsayawa sai da kome ya faru dashi kafin hankalinta ya kwanta. Shima dan Ba'are sabida ba haka kawai yake ba da ta jijjiga shi da karfin ta. Ta kuma nuna mishi Allah daya ne.


***
Washi gari
Kamar ba zan shirya ba, amma sabida irin yadda Malam Ansar yake bina da idanun yasa ni hada kayana, na raba biyu. Na saka rabi a cikin wata jaka, rabi kuma na barshi a dakin Baba Mari, sanan na tsaya tare da cewa.
"Baba idan aikin da sauki zan na zuwa duba ki, Insha Allah."


"Allah yayi miki albarka, ya kuma kare ki daga sharrin shaidanun mutane da shaidanun Aljanu, karka yi wasa da ambaton Allah a duk inda kike, gurin da zaka shiga haka kawai nake ji a jikina akwai babban Al'amari a gurin. Dan haka a rike Allah babu wasa sallah nafilla, walaha da duk wani sallah bayan sallah farillah, ba ayi da La'asar da magarib, amma ana yin shafa'i da wutiri, karka manta Alhamis da Litinin kayi azumi ka nemi dacewar Ubangiji.."


Rike hannu na tayi tana kallon fuskana tace min.
"Wallahi nayi mafarkin inda zaka cike yake da ƙaya masu matukar hatsari, shi yasa na mike da nima maka kariya, Insha Allah zaka yi nasara amma karka manta gaskiya tafi kome tasiri kar manta da karatun Alqur'ani domin itama haske ce s duk inda mutum yaƙe."
Wato matar nan jinta nake kamar ita ta haifi Innata, zunzurutun kulawa. Sannan ta bani addu'o'in.
"Baba zamu tafi makara muke"


"Allah yayi muku albarka" ta faɗa tare da juya mana baya, mu kuma muka fita, ina lura da take taken shi magana yake son min, amma na wani b'ata rai, sai da muka fita daga gidan ya rufe Kofar gidan sannan ya tako har zuwa inda nake, ya bude motar ya shiga. Shiru ne ya gifta tsakanin mu. Kamar ba zai yi magana ba.


"Ina rokonka don Allah don sonka da Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, ka kame kanka, tunda kasan yanayinka ba irin tamu bace, yanayi biyu ne a tare da kai don Allah karka yarda wani ya fahimci halin da kake cikin har yayi kokarin cutar da kai, Wallahi idan wani abu ya same ka, kashe kaina zanyi da bakin ciki,"


"Ai makabarta bata cika ba, dan haka Allah ya jikan musulmai wanda ya kashe kanshi kuma Ubangiji ya san yadda zai yi dashi" (hali a jikin rai yaƙe Bakar magana) kallon shi Malam Ansar yayi tare da cewa.


"Wai meye nayi maka ne ka bi ka tsane ni haka?" Ya tambaye shi kamar zai yi kuka,
Wani banzan kallo na mishi, kafin nace mishi.
"Kawai naji a raina na yi ta kafta maka rashin arziki ne" ya bashi amsa.
"Indai akan dan rungumo ka da nayi jiya ne Allah ya baka hakuri." Dauke kai nayi kamar ba dani yake ba, gidan shugaban makaranta muka nufa, daga nan shima ya koro min jawabin shi da abinda zamu yi kallon shi nayi kafin nace mishi.
""Toh" sanan muka bar gidan, ina ji kamar na rufe su da dukka, kiran dan Ba'are yayi ya gaya mishi gamu nan mun iso amma akwai jami'an tsaro sosai.


Bayan kamar minti goma sai gashi ya zo da kanshi, suka yi magana kafin ya leko cikin motar ya kalle ni.
"Kai fito" ya faɗa babu wasa a fuskar shi. Ganin shi dirkeke, ga fuskar nan babu sassauci ya sani fitowa ina kamkame jakata.kallon na yayi sannan yace min.
"Koma cikin motar"
Komawa nayi, sai lokacin na lura da fuskar malam Ansar, ya b'ata rai ainun. Fuskarshi har wani ja yayi.
"Malam Ya naga yaron kamar mace?"
"Almamoon namiji ne, haka kowa yake gani kamar mace amma namiji ne"
"Toh ince bai da matsala, irin dauke dauke da sauran su?"
A wannan gaɓar kamar malam Ansar ya daka mishi mari, amma ya rarrashi kanshi yana kallon shugaban jami'ar.


"Yaron bai da matsala, kuma ban tab'a jin malam Ansar ya fadi wani abu akan shi ba, ko abokan karatun shi basu tab'a koraafin yayi musu ta'adi ba."


"Toh Shikenan, kuje dashi Insha Allah gobe idan ya taso makarantar yazo Insha Allah kafin lokacin an gama mishi kome nashi na gidan domin babu me tsallake wancan shingen babu alamar kai ɗaya ne daga cikin gidan."


"Mun gode" d'aga musu hannu yayi tare da juyawa ya bar gurin su.
"Gaskiya ban da dole da Almamoon ya hakura da wannan aikin kawai raina bai kwanta da wannan gida me cike da murɗa murɗan maza ba"
Inji malam Ansar, jin haka shugaban Jami'ar ya lullube shi da faɗa, har suka isa makarantar. Kamar zai ajiye Almamoon sai ya dawo dashi gidan. Sannan ya nufi makaranta domin fushi yake sosai kuma ba kome ke damun shi ba sai kishin bala'i da ya daurawa kanshi akan Yaron. Dan shi har kwanan gobe kallon da Yakewa Almamoon ba na wasa bane.


....
Bayan tafiyar su, ya koma cikin gidan. Zama yayi yana hasashen fuskar Almamoon, haka kawai yaji yaron yayi mishi kuma ya kwanta mishi, bai da nutsuwa da wata shirme irin n yaran yanzun,


Kallon Mohan yayi tare da cewa.
"Bana son barin ragamar rayuwarka a hannun mutane da suke kewaye da kai ne" shiru yayi sannan ya cigaba da shafa kanshi yana jin tsannanin tausayin halin da Aminin shi yake ciki. A hankali ya mike bayan ya nufi inda ya ajiye kome ya fara shirin shi da yasaka a ranshi, yayi ta aiki yana connect din na'ura a cikin gidan. Bayan nan ya fito.


Akwai wani yardadden Yaron Mohan mai Suna Malik, har yau bai tab'a jin Malik yace mishi ga wani abu na Mohan ba, dan haka lokacin da Mohan ya fara jinya da zai zuba jami'an tsaron Malik ya bawa rikon su. Dan haka ya fita tare da kiran shi suka nufi lambu. Zama Dan Ba'are yayi yana me kallon Malik da ya sara mishi.


"Gobe Insha Allah yaron da zai kula da Mohan zai zo, kasan me ina son ka zuba ido akan Yaron! Daga yau zan mai da kula da gidan a hannun Fahad, kai kuma ka zauna a cikin gidan kana taimaka mishi da wasu abubuwan. Akwai abinda nake zargi a cikin gidan amma ban tabbatar ba, don haka zaka ajiye unifoam. Nasan kai ɗaya ne kasan kome akan Mohan har da abinda ya shafi dukiyar shi, naji dad'i da ka zama mutum mai Amana da gaskiya, Insha Allah zaka ga sakayya a gurin Ubangiji. Gashi nan wannan key motar da zai na kai shi makaranta ne, wannan kuma duk wata zana cire CF dubu dari bakwai kana bashi katin bankin shi na kamfanin shi da yake doso ce, babu abinda zai yi da izinin Ubangiji. Don Allah ka zama me amana da na san ka dashi, bayan ku duk mutumin da ya nemi shigowa gidan nan"


Jan hannun shi yayi kamar wanda ya ke jan bindiga ya dauke kamar yayi harbi, "ku gama dashi, idan ka fahimci Yaron yana da dauke dauke ka kira Ni ka gaya min zan zo na mai dashi, sannan duk bayan sati biyu kana ciwo mishi dubu hamsin kana bashi, sabida kashe wasu kannan bukatar shi. Idan kaga wani sauyi kai min magana, idan na samu lokaci Insha Allah zan zo na kai shi sokoto gurin kana na"


Gyada kai yayi sannan yace.
"Insha Allah"
Daga nan ya bar gurin dan ya sallame shi, zuwa yayi inda motar da zai na kai Almamoon makaranta, yake ya duba yaga BMW ne, jinjina kai yayi sannan ya nufi sansanin su, ya saka sunan wani daga cikin su aka kira shi. Ko minti biyar ba ayi ba. Ya shigo tare da sara mishi.
"Gashi daga yau aikin ka shine kai yaron da zai na kula da lafiyar Yallabai Mohan makaranta da duk inda yake buƙata."


"Insha Allah" ya sara mishi, tare da juyawa ya fita..daga nan shima Malik ya haɗa kayan shi yayiwa Fahad magana, gyada kai yayi tare da rungume shi yana faɗin.
"Allah ya baka sa'a"
"Amin Abokina Nagode" suka tafa sannan suka bar gurin.


***
Sake shirya kayana nayi, sannan na kalli Malam Ansar da yayi ciki ciki da fuska.
"Wallahi karka sake abin duniya ya rinjaye ka"
"Toh ai kai ma da abin duniyar ka janyo ni" na fada tare da gimtse fuskana,


"Baba wannan Yaron ya rena ni, duk abinda nayi dan na kare shi nake amma ban da kwashe min albarka babu abin da yake." Ya gayawa Baba,
"Almamoon bana son rashin kunya mana, me yasa ka rena malamin ka? Dan ya taimaka maka sai yayi laifi? Toh kul bana son haka, idan ka sake na kuma jin haka sai na sab'a maka"
"Kiyi hakuri, kayi hakuri ba zan kuma ba" ya faɗa kamar zai fasa ihu, wuni ranar har dare suna manne a dakin baba.


Washi gari da ya tafi makarantar, ya samu zasu fara jarabawa yayi rashin test da wasu abubuwan, dole zai maimaita wannan zangon da haka dake karatun a ranshi yake nan ya amince tare da yarda yayi duk abin da zai yi, yana tashi daga makaranta, ya nufi gida. Malam Ansar da kanshi yazo ya dauke shi suka nufi can gidan.


Karfe biyu da rabi yayi mana. Kofar get din farko, dan haka ya kira mutumin , ko minti goma ba ayi ba sai gashi sun fito tare, da wani mutum, suna zuwa shi mutumin jiya yana sanye da kayan sojoji, sai jar hular da yake kanshi, yana zuwa ya mikawa malam Ansar hannu suka gaisa, sannan ya leka Ni.
"Ban rike sunan shi ba"
"Almamoon Isma'il Wodaadabe"
"Ai kace Bororo ne?"
"Eh haka nake tsammanin" inji malam Ansar,
Bude min kofar suka yi na fito a hankali, ina kallon su.
"Don Allah ku saka ido akan shi yaro ne, dan har yanzun bai cika sha tara ba, don Allah kar wani abu mara dadi ya same shi. Sannan Insha Allah zan ina zuwa duba shi"
"Malik bashi Number ka, idan kazo ka kira shi, Insha Allah har cikin zai kai ka, Mamoon kai kuma mu wuce."
.kasa tafiya nayi na tsaya a gaban shi, kwalla na cika daga idanuna.
Riko hannuna yayi tare da kallon yadda nake kuka.
"Baka son rabuwa da ni ne?"
Gyada mishi kai nayi.
"Me yasa?"
"Babu" na fada ina jan dogon hancina.
"Maza wuce Allah ya bada sa'a" ya faɗa min, kuka ne ya zo min na toshe bakina, haka suka sani a tsakiyar su, muka nufi inda wata mota take, wanda aka kira Malik ya bude min baya, juyawa nayi ina kallon Malam Ansar har. Na shiga motar, leken shi nake ta bayan motar, kwalla na zuba min. Kawai sabon da nayi dashi ne yasa haka, a hankali muka bar gurin ina kallon jami'an tsaron da aka girka a kofar gidan kafin ka shiga gidan ma tukun, Ashe ba karamin tafiya bace idan da kafa ne, kallon gidan nake me dauke da aljannar duniya duk inda muka wuce sake baki nake har muka isa cikin gidan sosai.


Tun ban shiga gidan ba gabana yake faduwa, har muka shiga cikin gidan, a hankali suka shiga gaba. Ina bin su a baya har muka fada wata babban falo. Hoton wani soja ne yayi mana mara ba da zuwa gidan, ina d'aga ido na kalli hoton. Kamar wanda aka daki kahon zuciyata, wani irin bugu yake duk wani dakika jin shi nake kamar zai fasa kirjina, dafe kirjin nayi tare da saurin dauke idanuna akan hoton ba mamaki kodan kwarjinin da hoton yayi min me yasa na ji wannan yanayin a raina. Har muka fara haurawa sama, sake juyowa nayi na kalli hoton naga ya kura min ido, da sauri na bi bayan su da gudu, har suna juyowa.
"Lafiya Mamoon?"
Dakyar numfashina ya dai-dai ta, na girgiza musu kai.
"Toh muje" haka suka kai Ni falon sama, sannan suka ce na tsaya. Suna shiga can sai gasu tare da mutumin hoton nan ne,


Zuba mishi ido nayi, abu biyu naji a lokaci guda, wani mugun tsoron shi da kwarjin da yaji min, sai wani abu da na hango a tattare dashi, yadda ya kafe ni da ido ya sani sunkuyar da kai na kasa, jikin yana kerma sakamakon hango shi da nayi cikin fararren kayan barci.


Zama yayi sannan ya kalle su, bai ma san me ke faruwa ba.
"Yawwa Almamoon ga shi nan mara lafiyar mu, shi yake bukatar kulawa, wannan shine Malik zai taimaka maka a duk lokacin haka." Gyada musu kai nayi, domin ban san me zanyi musu bayan haka ba.


"Kayi hakuri nasan kai dalibi ne ka iya abinci, sabida zan amshi kula da abincin shi a hannun masu yi na dawo dashi hannun ka ne?"
"Na iya"na fada ina kallon kasa,
"Shi kenan, and ka kula da lafiyar shi don Allah duk sauran bayanin yana gurin Malik. Shi zai taimaka maka"


Haka ya mike tare da mika min hannu, kasa karb'a nayi sau da ya kuma min alama na mika mishi a karon farko a rayuwata da nayi haka dan ko da nake makarantar ban tab'a yarda ba, amma yau nayi. Sai naji kunya ya addabi ni, har ya fita sannan Malik yayi mishi rakiya.


"Ka ciro kudi ka kai shi ya zab'i kayan da ya dace da shi, wancan kayan da ya saka sai kace wani Bugaje,. Ka nima mishi kananun kaya masu kyau da tsada, sauran kuma a hada mishi da takalmi da duk wani abun da zai fito dashi gari. Zaka iya tambayar shi dai ka sayo mishi.


Haka suka tafi suna tattaunawar...
Baya bata da kaɗan.
Wato suna barin gurin, kaina a sunkuye, ba zan iya fahimtar yadda abin ya faru ba, amma tabbas sai dai nake kamar ba a duniyar mutane nake ba, domin wata irin shaƙa da Mutumin yayi min, ya sani fara ganin wata duniya na daban.
Gashi ya danne ni akan kujeran, kamar zai kashe ni. Wutsul wutsul nake, kafin Allah ya bani nasarar buga mushi kararrawan sadarwan shi, zuɓewa yayi a kaina tare da dauke wuta. A lokaci guda muke kallon idanun juna, lumshe idanun shi yayi tare sake jikin shi alamar ya suma a jikina, wallahi gashi kaman gumgumemmen dutse, kasa motsi nayi.. a hankali na kuma kallon fuskar shi, naga yana lumshe sai kwalla da take bin fuskar a hankali yana diga a daidai saitin zuciyata. Kasa jan numfashi nayi, tare da jin wani abu ya cika min wuyana.


A hankali na shiga janye jikina, amma kamar bana kome, gaskiya mutumin nan kato ne, dakyar na iya d'aga hannun shi da kanshi, shigowar Malik yaga yadda nake kiciniya sai da ya tintsire dariya, har yana nuna ni.
"Sannun Kaji, da fatan bai maka kome ba?"
"Da yanzun sai dai wani ba ni ba domin shake ni yayi zai kashe ni." Na fada kwalla na zubo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login