Showing 9001 words to 12000 words out of 181864 words
katako ta bude cikin shi. Kudine babu iyaka. Suka zauna aka yi lissafin su tsaf.
"Innah har zai rage ma ai kuɗin."
"So nake na cigaba da tarawa, dan ba zaka yi karatu a makarantar gwamanti da babu kulawa ba, kai ma makarantan kudi zaka tafi." Murmushi yayi sannan yace mata.
"Insha Allah"
***
Haka suka share wata biyu sannan sakamakon su ya fito, haka Aminatu ta fasa asusun aka biya mishi kusan makudan kudade na makaranta, ranar da zai fara zuwa. Suka zauna dashi aka mishi nasiha, tare da mishi gargadi.
"Karka sake kayi wasa da karatunka, kayi hakuri da mutanen da zaku hadu makarantar yaran masu kudi ne dan haka karka bari a Kama ka da laifin da zai dame mu.
Haka suka gama mishi fada, sannan zai fita Malam Sanda tace mishi.
"Kin gaya mishi gaskiya akan" kallon shi tayi tare da cewa.
"Wannan sirrin shi ne, karka manta wata rana zai fahimci dalilin haka, kai dai ka hana shi mu'amala da maza da mata,"
Kallon su yayi kafin yace musu.
"Wani sirrin kuke boye min?"
"Babu wani sirrin da a ke boye maka"
"Toh shi kenan," ya faɗa tare da barin d'akin, shi da Baban shi.
A iya yanzun haka kawai take jin kamar sun tauye mishi hakkin shi da kuma yancin shi, sai dai kamar yadda Mijinta ya faɗa haka ne, baya son tarihi ta maimaita kanta ne akan shi, shi yasa ya zab'i hakan a matsayin babban al'amari akan.
Amma kuma tana ganin kamar haka ba hujja bane, kamar tauye hakkin shi ne, kai toh idan wani abu ya same shi fa? Gwara kawai a tafi a haka. Toh gaba kuma aka dawo aka samu akasi fa? Lallai bari malam ya dawo zasu yi magana domin ba zai tab'a yiwa ba, ka sayi kura da daddare da safe ka samu kare ne, haka ba zai tab'a yiwa ba..amma shi yaron ai bai san hujjar su na maida kome haka ba.
..... Bayan malam ya dawo ne ta kalle shi kafin tace mishi.
"Malam anya bamu so kan mu ba? Taya zamu bari har zuwa lokacin da."
"Ki bar kome a hannun, idan ta fara girma zamu fahimtar dashi kome, sannan zamu sauya mishi gari domin kar a samu matsala, karki yarda wani yasan wannan sirrin. Ya zauna a tsakanin mu."
Had'iye yawun tayi sannan tace mishi.
" Sai nake ganin kamar da cutarwa, a bar shi haka ba a gaya mishi dalilin da yasa yake raye a haka ba, sannan kuma. "
"Karki karaya mana, tsoron abinda ya faru shekaru goma sha daya nake kara ada Yaron nan ba wai dan wata manufa bane, kawai ki tayani boye maganar shi nan bana son kamar yadda iyayen shi suka mishi, shima ace ya fuskanci haka.
Duk da muna namu Allah yana shine gaskiya."
"Ko a ina Sama'ila yake oho?" Ta faɗa cikin sanyin murya, me ban tausayi. A hankali yake kwalla suka zubo mata, tana kallon kasa. Ya tafi ya manta da gida, ya tafi bai kuma waiwayar baya ba, me yasa ya tafi shima? Me yasa ya gaza tsayuwa ya fuskanci rayuwar abinda ya bari, babu kome, Allah yana nan zata rike yaron ta kuma boye mishi waye shi. Domin samun goben shi.
Amma Tabbas akwai sirri me girma ga rayuwar Almamoon.
****
Asalin labarin.
Fulanin Wodaadabe Bororo.
Wato sune Fulanin da basu zama kuma basu da mazauni daya, idan suka shekara anan yau gobe zasu kara shekara a wani garin. Sannan Allah yayi musu baiwar ilimin addinin Muslunci, musamman Alkur'ani.
Zunzurutun baiwar da Allah yayi musu kasancewar su bakakken Fulani masu jajjen shanu, yasa zaka sami yaro karami an daura shi a saman saniya yana tafe yana karatun Alqur'ani, kuma ya tafi da saniyar har wata tafiya.
Yanayin shigar su ba kamar na sauran Fulanin bane, domin suna sanye da wata hafaffera, riga ce Armless, har gwiwar su rigar take, sai wandon yadi ce baka kowa wata kala, suna saka hular malafa akan su, matan su, suna tara gashi a gaban goshin su, me shegen yawa kuma suna saka bakakken kaya har kasa kamar riga da zabi ko doguwar riga.
Suna shigowa gari da matan su, tallar maganin mata ko maganin gashi, suna bin gida gida suna tallar shi, zaku gan su dogaye ne matan. Kyakyawa bakakke...
Duk da ana samun fararren su, amma bakakken sunfi yawa, suna da Albarka na dabbobi, sannan kuma suna da matukar kyakyamin abinda ya shigo musu, musamman abinda ya kasance sabon abu.
BOROROJI suna da wata muguwar dabi'a wacce take salwantar da rayukan mata da yan mata, mace kome girman mata idan har tsautsayi ya faɗa akanki shikenan.
Ismail Mohammed Wodaadabe.
Shine cikakken sunan Sama'ila, yana da kanwa daya tal a duniya Aminatu.
Dayawa abokan shi sun sha mishi barazana zasu dauke Kanwar shi, amma bai tab'a damuwa da haka ba, sabida yasan abinda ya shiryawa, wani mugun hali da yake dashi. Shine yawancin matasan bororo suna zuwa mishi yayi musu aiki, kuma idan yayi kamar yankar wuka taci.
Umar sanda shine cikakken sunan abokin shi saurayin Kanwar shi Aminatu. Zaune suke a kasar bishiya.
"Ila, shin da gaske zaka babu kanwarka dan naga baku da dangi ko daya a wannan rigar kace suna can mali"
Mik'ewa yayi bayan ya kad'e jikin shi ya rufe Alqur'anin shi. Yana faɗin.
"Duk cikin abokaina kai ne kawai kace min kana son auren Aminatu sauran kuwa cewa suke zasu yi *CIRENTA* shi yasa na amince ka nemi aurenta kai ma ai ba dangin ne da kai ba."
"Toh meye na bakar magana? Daga tambaya sai bakar magana ta biyo baya." Kallon shi yayi da wutsiyar ido, yace mishi.
"Ba bakar magana ba ce farar magana ce."
"Ai kaji ka mutumin banza kawai"
"Idan ni mutumin banza ne toh Sannun na Allah" ya faɗa yana kad'a kan shanun shi.
"Ban da ina girmama Aminatu da ba zan tab'a yarda na bi ka ba"
"Idan baka bini ba sai na fadi na mutu dan ka ki bina"
"Wai kan Ila bakinka baya mutuwa ne?"
"Sai ranar da kasa ta rufe min ido" ya faɗa abin shi haka bai dame shi ba, sai ma kara hada kan dabbobin shi yake suka bar gurin kiwon, ba tare da ya gayawa Sanda ba, ranar juma'a, Sanda ya shiga gari juma'a aka daura auren Aminatu,
[7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Littafi na D'aya...
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Idris
I'm on Instagram as @s.square_fashion_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=gorfmwut2x22&utm_content=cgl6gfx
```Zaku iya samun kayan mu daga turaren zamani na wuta, shu'umar humra, dambun nama na mata, tsumin. Da sauran su kayan mu ba irin nasu bane sai an gwada akan san na kwarai..... Akwai haɗin kayan amare da na uwargida...🗣️🗣️Friday Promo!!! Buy 13pcs @15k only : Turaren wuta 5pcs, humra 3pcs, Turaren tsugunno, shu'umar humra, mopping and toilet perfume, curtains and carpet parfume &kasko💃🏻💃🏻```
Zuciyar Mutum..!
BABI NA HUDU
Koda Sanda ya dawo aka bashi labari, mamaki ya bashi yadda aka daura.
"Nagode sosai Abokina" duk ya rasa yadda zai mishi godiya, sai ga kuka.
"Ji sakarai."
Ya fada yana murmushi,
"Nagode"
"Abinda nake so ka rike min ita da Amana, shine abinda zaka min tsakani na da kai"
"Insha Allah zan rike ta, da amana Insha Allah ba zaka tab'a samu na da laifi ba."
Ba iya shi ba hatta sauran abokan su, sunyi matukar mamaki da abinda Ila yayi, sai ma dai kawai matsalar da aka samu wani abokin su da ya tab'a niman Aminatu har suka sami matsala da Sama'ila, shine kawai yayi barazanar dauke ta.
Dan haka shima Sama'ila da ta shi, bai tsaya ba dan ya san halin su na Fulani da aikata abinda suka fada, sai yayi maza ya kad'a hankalin mutumin yayi gaba, haka ya saka suka zauna lafiya.
Bayan shekara daya da auren su, Ado wani abokin Sama'ila ya gayyaci Sama'ila bikin shad'i na wani abokin shi a rugar Alu, suka tafi tare, dan sun tafiya da Sanda yace ba zai sami zuwa ba.
**
Malam Hamza Ja'e Bugaje, babban malami ne a cikin rugar kowa yasan shi da mutunci da kamala, dattijon arziki. Haka yasa ake daraja shi. Kuma abin burgewa Ardo Mustapha babban Aminin shine dan har sunyi baikon yaran su, Zainab Abuh da Kabiru Almustapha, sai dai Zainab tana karatun ta na sankadire, kasancewar Malam Ja'e yayi cuɗanya da mutane, yasa ya saka yar shi karama a makarantar boko, duk da ana ganin kamar yazo da bidi'a amma haka bai saka ya fasa abinda yayi niyya ba.
Tsakanin Kabiru da Zainab akwai soyayya mai karfi sosai, wanda ya saka kowa yake ganin kamar bai zama dole su mallaki juna ba, amma sun dauki haka a matsayin kaunar suce. Zainab tana kai kindirmo cikin gari, kuma a duk lokacin da ta tafi makarantar boko take tafiya da nonon, idan ta ajiye a Office din shugaban makarantar, sai ta wuce aji ana tashi zata dauki kayan ta ta nufi Asibitin Aminci da yake cikin garin Maradi. Ana take sayar da nonon.
Dr Khalid.
Matashi ne dan kabilar Buzaye, kyakyawa ne, ajin farko dogo me cikar halittar jiki. Idan ka ganshi zaka Fahimci namiji ne, mutum ne mai yawan fara'a da barkwace, haka haduwar shi da Zainab, da zolaya ya fara cewa yau yaga Yar Fulani da unifoam. Kamar da wasa aka fara.
Wata uku yana dakon sonta, bai gaya mata ba, sai ana gobe zata daina kawo nono sun gama makaranta, tana da shekara goma sha bakwai.
"Dr daga yau na daina kawo nono, sabida zanyi aure kuma."
"Kamar Ya? Wallahi ina sonki na kasa gaya miki ne, toh Allah ya sanya Alkhairi, amma Allah ya gani ina kaunarki da aure."
Murmushi tayi sannan tace mishi.
"Kayi hakuri koda baka gaya min ba, ina da mijin da zan aura shi yasa na gaya maka ma yanzun Nagode da kaunar da kayi min."
Haka suka rabu ita kam bata ji kome ba, sabida zuciyar ta yana ga mijin da zata aura....
***
Tunda aka fara shirin bikin nan kowa yake murna, dan haka zasu fita bikin shad'i idan aka yi kuma, zasu saka abu a fuskar su, tafi ta ta nuna musu mijinta a cikin su. Dan haka aka gayyace matasan fulani daga rugagge masu yawa.
Kafin a fara wasan sun fita da yan mata, bakin wata rijiya suka zauna, suna hira shiru tayi tana kallon su.
"Abuh meke damunki tun jiya"
Murmushi tayi sannan tace musu.
"Babu kome kawai ina kewar kune" murmushi suka yi. Matasa ne samari suka nufi gindin rigiyar zasu sha ruwa, watsewa yan matan suka yi, ya rage sai ita. Su dake suna zaman gida sun san su waye matasan, shi yasa suka gudu Ita kuwa bata ma tab'a jin ko labarin su ba, tana dai kallon su, suka gama shan ruwa, sau daya ta d'ago kai ta kalli Sama'ila, bata kuma kara kallon shi ba, har ya juya zai tafi yace mata.
"Baki ga yan uwanki sun gudu bane ke gaki yar taurin kai?"
Sauke numfashi tayi sannan tace mishi.
"Toh meye zan guduwa? Ko mutuwa ai ba a gudunta, dan haka kuyi tafiyar ku, anan kuka same ni."
Tab'e baki yayi tare da bin abokan shi suka tafi, dayawa abokan shi,sun san yana taimaka musu gurin samun mata, amma basu tab'a jin yace yana son wata mace ba, duk da kuwa yan mata dayawa suna kawo mishi kansu ya aura Amma yake ki. Dan ce musu yake matar da zai zauna da ita yana son wacce take tankawa ne ba wacce take tsoron shi ba.
Haka yasa yake nan shirgegen tuzuru, shi baya ma niman yan matan, sau dari idan zai hadu da su dauke kanshi yaƙe, sabida baya son damuwa. Yana ganin yadda abokan shi suke kawo karan matayen su.
"Ila yarinyar tayi maka ne?"
"Ta cika kyau da farin fata".kuma haka ne, duk cikin rugar Alu babu ta biyun Zainabu kyakyawa ce fara kuma me kyau, doguwar ma'abociyar gashi da cikar kamala, kamar mahaifinta. Mahaifiyar ta tabiyo dan bafulatanar Libya ce ko nace balarabiyar Libya, haka take fara kal da ita.
Shi yasa duk cikin rugar aka musu lakabi da, Fulanijo. Sabida basu yi kama da Fulanin asali ba.
Dan haka yana tafiya gizo take mishi, itace mace ta farko da ya fara gani kuma tayi mishi, dan haka yana tafiya be amma bawai yana cikin nutsuwar shi bane. Bai kuma shiga dimuwa ba, sai da aka fara wasan ya ganta itace zata zab'i Kabiru kai tsaye bai iya boye abu a ranshi ba yace mata.
"Bai dace dake ba, zan shiga shaɗin ni na dace dake"
"Allah yayi min tsari, koda mazan rugar Alu sun kare wallahi na fi karfin zuwa a matsayin matar ka, balle ka duba da kyau ka ganshi, mijin aurena ne a can"
"Lallai ina sonki da aure ki hakura dashi a daura auren da ni"
"Ba zan tab'a koda ana mutuwa a dawo." Ta faɗa tare da juyawa ta zab'i mijinta a gurin, tana zaban shi ta gaya mishi abinda Sama'ila yake gaya mata, ai kuwa fada ya rikice a tsakanin su, dakyar aka tashi taron dan sabida faɗar da aka yi,
---
Tunda ya koma gida, yake sintiri a dakin shi, yana huci sabida tsirta mishi yawu da tayi a fuskar shi. Takaici ne ya kama shi ya ciro kayan shi ya fara aikin shi da sunanta. Sai yaga haske me ƙarfi ya lalata nashi aikin. Karshe haka ya fita ya yanka tunkiyar shi ya fara aikin da ita, bai kai ga idarwa ba, yaga nashi aikin ya rufe na hasken. Har goshin asuba, kafin ya kammala. Yana idar da sallah bai tsaya ba sai rugar Alu, yana isa ana daura auren Zainab Hamza Bugaje da Kabiru Almustapha Bugaje. Yana zuwa bai kai ga musu magana ba ya shiga cikin gidan Malam Hamza Ja'e ya dauko amarya a gaba yayi tafiyar shi da ita, sai da ya bar gurin aka samu damar ihu ko kafin abi bayan shi sun b'ata babu shi babu ita.
Koda ya dauko ta daure musu hanya yayi yadda bazasu sake su nime shi ba, ya nufi Mali da ita.
Tunda ya tafi da ita suka yi tafiyar kwanaki kusan goma, sannan suka isa inda garin su yake, cikin wani ƙauye can, anan ya ajiye ta. Bawan Allah nan bai d'aga mata kafa ba, sai da ya rabata da kimarta, sannan ya cigaba da azabarta da ita, duk da tana kallon shi amma bata tab'a tunanin meye ya haɗa da shi ba, tana zaune dashi ne har tsawon wata biyar, sannan ya daukota ya dawo da ita, rugar Bako.
Bayan tafiyar shi iyayen ta, sun tafi har rugar. Suka samu bayanan bai ma zo garin ba ita ba, abinda ya ya saka mahaifinta komawa kenan, duk bayan sati daya sai yazo, jin labarin ko sun dawo mishi da iya. Babu su babu labarin su.
Har kusan wata biyar sannan ta dawo da ita. Ranar da ya dawo da ita, aka yi ta rigima da shi a rugar Bako. Ya kafe akan matar shi ce har itama yasa ta cewa mijinta ne, koda iyayenta suka zo yarinyar nan taki yarda akan iyayen tane, haka suka tafi suna kuka. Kuma abinka da jini sai sun tafi tayi ta kuka tana da nasani.
A wannan yanayin ta samu ciki, haka tayi ta wahala, gashi mutanen garin sun tsangwame ta, shima yayi mata wulakancin.
Mahaifinta duk da abin ya dame shi bai fasa niyyar shi ba, dan sai da yayi kokarin lalata abinda yayi mata, yana b'oyewa ne amma tun ranar da abin ya faru, mahaifin Kabiru ya kawo mishi takardan sakin, abinda tun daga lokacin ya fara kokarin ganin ya bar garin sabida abin kunyar da ya faru da diyar shi. Bai kuma gigita ba sai da Mahaifiyar Zainab ta je yaga halin da take ciki na laulayi, wannan dalilin yasa ka suka tattara suka tafi abun su, Kabiru ne yayi taurin kai yazo ya samu Sama'ila akan lallai ya sake mata matar shi. Shi kuma ya dake shi a kanshi karshe a anan aka sami gawar shi kuma babu wanda ya isa yayiwa Sama'ila magana, suma iyayen Kabiru sun bar garin da suke, rugar ta watsa babu kowa. Lokacin da Zainab ta ji labarin tayi bakin ciki amma bata iya magana ba, domin tana buɗe bakinta zata ji wani abu ya tsaya mata a wuya. Gashi duk abinda yayi da izza yake gaya mata, dan so yana matukar kaunar ta, amma matsalar idan ya tuna yadda ta wulakantashi a gaban jama'a, abin zafi yake mishi, shi yasa koda abokan shi suka zuga shi bai hakura ba sai da ya dauke ta ranar aurenta, da mijin. Wannan kawai ya saka shi ya Huce takaicin shi. Amma kuma lokacin da yaga cikin shi na d'agawa daga maranta ya daura musu kaunar duniyar nan ita da abin cikin domin har ya daina hulda da ita burin shi idan ta haihu a warware wancan auran a daura dashi. Sau dayawa yana ganin k'iyayyar shi a kwayar idanun ta, bai tab'a zaton zata girma haka ba.
Tsawon Wata goma sha biyar ana wannan yanayin, har ranar da ta haifi abin cikin ta, wanda ko fuskar shi bata kalla ba, tayi tafiyar ta, wannan abin yayi masifar mishi ciwo, yasan muguwar al'adun sun na cire mace daga gidan mijinta a tafi da ita shi ya lalata mishi kome na shi. Tunda ta tafi ya kasa koda fahimtar kanshi da zuciyar shi, yasan ita yake so, amma bai san yadda aka yi ya iya cutar da ita da soyayyar shi ba.
Yayi kuka yayi danasanin, ya ji a ranshi ya zalince ta, musamman abinda ya haifa, wannan abin ya saka shi