Showing 99001 words to 102000 words out of 181864 words
ta bar Yaran da Nanny saboda yanayin karatun Benazir, ashekaran zata fara jami'a. Suna dawowa ya nima mata Maryam Abatcha University. Kasancewar jami'ar ta Privat ce bata gwamanti bace. Yasa ya nima mata.
Duk da haka bai hana Zainab bin gari gari niman danginta da Na Sama'ila ba, suman jaririnta da bata san meye ta haifa ba, koda suke Faransa idan abin motsa mata har suma take, tayi kwana da kwanaki tana coma,. Shi yasa shima Dr Khalid bai tab'a kawowa zai rabata da soyayyar abinda ta haifa ba, dan ko lokacin da Mahaifiyar shi ta rasu, da suka zo sai da tayi ta bin dazuzzukar da Fulani suke, tana niman Danginta da Sama'ila, har ta isa Mali, babu su babu labarin su.
-----
Dawo labari...
Yadda take kuka ya d'aga musu hankali, tana kallon Benazir take tura baki.
"Mommy da shi abinda kika haifa damu wa kika fi so?" Ta tambayi uwar tana kallon ta,
"Shi" Khalid ya bata amsa, dan yasan abinda Zainab zata zab'e kenan, kwantar da kai Zainab tayi yana jin hawaye na zuba mata, Yumnah da tunda aka fara abun bata ce kome ba, Mik'ewa tayi ya zo gurin uwar ta kwanta a jikinta.
"Kiyi hakuri Mommy" ta faɗa kanta a kafad'ar uwar, abin tausayi.
Haka suka isa Maradi, bayan Zainab ta shiga d'akinta, zama tayi ta kuka, idan ta tuna Laifinta na baya. Tafuyar da tayi ta bar baya da kura yakan sata tsanar kanta da kanta, ji take bata yi deserved zama Uwa ba, domin ta gaza tausayin abinda ta haifa.
*
Can Niamey ana ta shirya ranar samun yancin kai, duk me ruwa da tsaki yana kan wannan shirin, kowa yana kan shiri musamman Primer Minister, sai bangaren Mohan wanda yake cikin damuwa sosai, amma yasa dan Ba'are ya shirya musu masu shirin.
....
Gidan Hammad H Dogo.
Murmushi Hajiya Karime tayi sannan ta kalli yar karamar Yarta.
Saura wata biyu da wani abu, ayi baikon ku, dan haka zan shiryawa Yaya Latifah, wancan maganin da aka kai mata, ita da kanta zata cinyar da danta maganin da zai rabu da ita, nan da kwanaki ƙalilan zai zo ya haukace ana yana niman ki, dan haka ki nutsu ki."
Yadda take shirya makircin ba zaka tab'a kawowa zata aikata ba, amma idan kayi dubi da halin dan Adam sai ka yarda zai iya aikata kome akan wanda ya yarda dashi, ita fa Hajiya Latifah hankalin danta take buƙatar a karkato mata ba wani abu can ba, amma baiwar Allah nan ta gwammace gwara ta rabu su da d'anta.
...
Tun bayan da yaji abinda Uwar shi take son aikatawa jikin shi yayi sanyi, dan haka ya tsiro daina cin abincin a dinning table, sai dai a kai mishi part din shi, idan aka kai mishi zai zubda ya dafa na shi, dan haka ya zuba mata ido, koda aka kwana biyu suna zaune take ce mishi
"Yaushe zaka je gurin Hanan"
"Ammyn yaushe kike son naje?" Ya tambaye ta, wani irin farin ciki ne ya lullube ta, dan ta tabbatar da dan ta ya dawo hanya tace mishi.
"Ya batun yarinyar nan da kake son?" Kallon mamaki yayi mata, kafin shima dan renin hankali ya yatsina fuska sannan yace mata.
"Wata Yarinya? Hanan dai nake so!" Ya gaya mata,
"Toh indai haka ne, toh idan kasamu lokaci kaje can ka duba ta"
"Insha Allah, zan fita zuwa gidan Umma Nuratu," tab'e baki tayi sannan tace mishi.
"Ka gaishe ta"
"Zata ji"
***
Lokacin da ya sami Umma Nuratu da abinda Mahaifiyar shi da Hajiya Karime suke mishi jikinta yayi mugun sanyi.
"Ka cigaba da addu'a, Insha Allah Ubangiji zai tsaya muku, su kuma Allah ya shirya su, nasan dai wannan ba halin Latifah bace barta da son gogaggayya da manyan mutane, amma wallahi ba halinta bane, kawai ƙaddara ce da son zuciya."
"Babu kome."
Haka yi mata sallama tare da barin gidan, tunda Dan Ba'are baya gari.. kullum zai yi waya da Moonah, sau uku sau hudu. wani lokacin yaji tana kuka wani lokacin kuma tayi ta mishi hira tana gaya mishi yadda take kewar shi. Tausayin ta yake kara cika zuciyar shi, idan ya nutsu sai yaga shi yana mata wani irin Mahaukacin SO ne, yayinda ita soyayyar da take mishi irin mai sanyin nan ne, yadda take son shi bata iya nuna mishi a gaban shi, amma shi yakan iya nuna mata a gaban kowa, sannan yasan Maimunari bawai ta bar gida bane sabida shi, a'a tabar gida ne sabida tana son zama mace. Wannan abun ya rike shi akan shi kamar hadda.
*
Tunda Hajiya Latifah ta gayawa Mahaifiyar Hanan kome ya fara kyau, suka shiga jifar Hajiya Lateefah kamar me, sai da suka samu ta dawo karkashin kulawar su, sannan hankalin su ya kwanta, a cikin sati biyu kacal suka gama birkita mata lissafi sai yadda suka yi da ita, Yaranta mata ma basu zaman gidan kasancewar Radiyah tana gidan Khausar da zama ita da gidan su sai hutu domin bakin cikin abinda Ammyn su take ne ya sa ta bar gidan, kuma Allah yasa mijin Khausar bai da matsala, dan kasuwa ne babba. Kuma ma'aikacin gwamnati, Nairah kan tana Faransa gurin Salman da yake shima yana da tashi iyalin kuma ya kama Kanwar shi ya rike duk sun watse mata sai Mohan din dai da ta addabi rayuwar shi.
Tsakanin Mohan da kanen shi akwai kyakkyawar fahimta, sannan. Sukan hadu da dandalin sadarwa ta Whatsp anan ya gabatar musu da Moonah, tare da gaya musu halin da ake ciki. Dukkan su, sunyi na'am da ita kuma suka bashi shawaran ya tsaya da kafar shi sai inda karfin shi ya ƙare, sannan itama yarinyar kar ya ce zai juya mata baya, suka yi ta rokon shi musamman Khausar da tace idan Moonah tazo Niamey ya kawo mata ita, anan yake kuma sanar musu da abinda Ammyn su tayi mishi na asirin da take mishi.
Sun tausaya mishi sosai, kafin suka yi ta turo mishi addu'o'in, da yadda zai nayi su, dake sun san halin uwar su da son nasaba.dan baka basu yi mamaki ba musanman da suka ji batun Yar Hajiya Karime, take suka nuna basu goyan bayan shi ya aure ta. Nan ya gaya musu nashi shirin da yake akan baikon.
Abin yayi mugun burge su, dan haka suka yi alkawarin zuwa dukkan su, dake lokacin an saka akan hutune.
Tun safe ya shirya bai gayawa kowa ba, sai Damagaram.
**
Kallon shi nayi kafin nayi kasa da kaina.
"Maimunari ki gaya min me yasa kika iya boye min wannan lamari? Na zata kin dauke ni a matsayin dan uwane? Sai jiya aka nuna min sakamakon ki an sauya miki suna daga Almamoon Isma'il Wodaadabe, ya koma Maimunari I Umar Wodaadabe, meye nayi miki da na cancanci wofantarwaki?"
"Ban san kome ba, duk abinda ka ga ya faru ba san kome ba Hammah Mohan ne yake min kome don Allah ka yi hakuri."
Na juya zan bar kofar gidan yayi maza ya riko hannuna, kallon shi nayi kafin na cire hannun nawa.
"WALLAHI har yau ina kaunarki, don Allah ki duba girman kaunar da nake miki, ki dawo gare ni. Amma idan kika ce baki sona ba zan miki dole ba."
Takowa nayi gaban shi, sannan na kalle shi.
"Mohammed Mamman Nasir Aghali, shine muradina. Shi din mafarkina ne, domin ina ji a jikina gobe na yana tare da shi ne, shi son shi nake, kai kuma shakuwa ce me had'e da cutarwa don Allah ka hakura dani, kabarni na zauna da abinda nake so. Idan ka dage zaka sani jin tsanarka har karshen rayuwata. Mohan nake SO! Akan shi nasan meye SO! Akan shi nasan dadin SO. Kai kuma a malamina na dauke kuma abokin shawara na, idan ta kama."
Daga nesa yake kallon yadda take magana, ranshi yayi mugun ɓaci, har yau parking idanun sa na kansu. Bai yi yunkurin juyawa ba, amma ya fito daga motar ya tsaya yana kallon su.
"Ki yarda dani ba zan tab'a zarginki ba, ina mugun sonki da ba zan iya juya miki baya ba, amma idan kika ce min na hakura wallhi zan hakura." Kallon shi nayi domin ya bani tausayi kawai nace mishi.
"Ka hakura" sannan na juya zan koma cikin gidan dan nasa Mohan yana hanya, hango shi nayi yana ta latsa wayar shi, gabana ne ya fadi, dan haka na nufe shi, had'iye yawun tsoro nayi.
"Barka da zuwa ya hanya?"
"Hmm" yace min yana kallon agogon hannun shi.
"Ina jiranki"
Ya fada min, haka na shiga cikin gidan, na samu Innah na gaya mata zan tafi.
"Mohammed yazo ko? Ban isa ya shigo ya gaishe ni bane?"
"A'a zai shigo mana" na fada da sauri,idan na gaya muku ina cikin gidan nan ne amma sam bana jin dadin zaman shi, wallahi Innah ta azabtar dani ta hanyar da ban zata ba, amma da nayi hakuri gashi zan tafi samun horona.
Mikewa nayi zan fita tace min.
"A'a Saurayi yafi iyayen riko, dan haka zaki iya tafiya a dai tuna da akwai Allah kar a sake da namiji dan ya iya samun damar shiga jikin mace, ba iya nan ba sau daya ake hada shimfid'a da wasu. Magana ya ƙare, daga nan dai yawun da amai"
Murmushi nayi mata sannan nace mata.
"Da zanyi wannan yanayin da tuni nayi tun ina amsar sunan mata maza, amma kuma nagode Ubangiji ya baki ladar rikeni da kika yi, ai kin min gata, kin gama min kome. Tunda kika iya rike ni na tsawon shekaru ashirin haka." Na mike tare da nufar dakina na kwashi duk wani abuna me muhimmanci, ko haya na kama a Maradi na dauko Baba Mari ta zauna dani, amma ba zan kuma dawowa gurin Innah. Har zan fita na kuma dawowa dakin ta.
"Innah don Allah me yasa iyayena suka tafi suka Barni?" Wani shegen dariya ta saka tare da nuna ni da yatsa tace min.
"Idan kika sani haƙa rami zaki yi ko binne kanki,. Idan kika san abin da ya faru. Wuka zaki saka ki datse wuyarki ko jijjiyar hannunki, ga wannan wukar ki ajiye sabida amfanin gaba, ko ki kashe iyayenki ko, ko kashe kanki"
"Wannan wani irin abu ne? Meye tayi miki da zafi? Idan Ni ne baki so zan barta amma da na fahimci itace baki son ta amsa sunanta na mace ya sani jin dud duniya bani da matar da nake so bayan ita. Insha Allah nan da wata biyu daga fadar shugaban kasa zai zo shi da kanshi ya nima min aurenta idan yaso kiyi duk abinda yayi miki."
Ya durkusa tare da d'ago ni, ina kallon Innah kamar gumki, kaina ne ya sara, na fara jin jiri, yana rungume dani, haka ya fitar dani bayan ya saka Ni a motar shi ya koma ya kwaso min kayana. Sannan ya shiga cikin gidan ya ce mata.
"Insha Allah, sai ta zame miki inuwar gajimare, sai ta zame miki Alkhairi a rayuwar ki, Innah kina raye zaki ganni da Maimunari, Ban san wani irin son zuciya yake dawainiya dake ba, amma tabbas zaki gani abinda kika mata sai kin gani akwaryan cin tuwonki"
Daga haka ya fita bai kuma bin kanta ba.
"An fada sai ta kashe kanta, kuma sai me duk ihun da kake iyayen ka bazasu Barka ka auri Yar da aka haifa da auren wani ba, Shegiya ce ho Shegiya ce bata hanyar aure aka same ta ba, wannan tambarin shi zai kashe ta ko kashe iyayen ta. Munafuki" haka tai ta faɗa tana fadar abubuwan da ya faru.
***
Tunda ya kwantar dani, nake dunkule a jikin kujeran.
"Hammah ta gaya maka wacece Ni?"
Banza yayi da ita domin yau baki daya an b'ata mishi rai, sai da suka yi kamar zasu dambatu da Ansar ya tafi, sannan ya shiga cikin gidan ya kuma samun na Innah tana buga nata isar, bai san meye Moonah tagayawa Ansar ba, amma kuma abinda Ansar ya gaya mishi yayi mishi ciwo.
_Kai a tunanin ka ta zan rabu da Munnah ce? A'a na barta ta huta ne a da sabida ba zan mata dole bane, a yanzun kuwa! WALLAHI idan ina numfashi toh sai na haddasa gaba me zafi a tsakanin ku. Idan ina numfashi kana ji kana gani zata haramta maka kayi fatan na mutu domin shine rufin asirin ka kamar yadda ka rabani da ita sai na rabaka da ita ka zuba ido ka yi kallo akan idanun zan yi kome By now let US started the Game idan nayi nasara zan dauke ta nayi tafiya da ita! Amma kasani idan kayi nasara zan so ka saka bindiga ka harbe ni,. Mohammed Mamman Nasir Aghali idan ka cika cikakken Buzu Bugaje me nasara da Zarra ka amince da game din mu! Kuma zan baka damar choice din shaidu. Ni na zabi abokina Mutallab! Kai kuma ina jiranka idan ka cika da namiji ba lusari ba muyi tsayayya magana ayi wasan rai da mutuwa akan Munnah idan ka gama shawara ga katina zan biyo ka har Niamey mu kulla yarjejeniyar idan muka ba isa namiji ba zaka share. Gani ga kai Ga Munnah Allah ya bamu sa'a sai naji kiranka_
🙄 Kunji watsassse munahiki meye nufin ka? Shashancin kawai! Amma da gaske game din zai badda citta wallahi🤣🤫 ina team din wanda yayi nasara... Bana team din loser 💃 all the best Ansar Yusuf Abzin. Duk wannan Chakwakiyyar a free book 🙄😠😩 ina laifin da Book ɗin kudi ne 😭 Alqur'an kamar yadda kuka karanta book din nan haka zaku karanta Na kuɗi na kuma ku saya ko na kafta muku rahin daraja 🙆🏾♂️😩
#Mai_Dambu
[8/7, 10:03 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1109328405?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=f4DtUHMnMYkq7YQxK69EHXzYx4qdYjE9KB3IVp12Bnb%2BzEoaanjkzsPH8vAt9jgM2j%2Blswb6qNSSL7B8%2FPrpejrjetMFg5iT6eRxuTuhL2RSdvHxFf9zphNfPityAhJD
🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
_Allah Nagode maka!🙆🏾♂️ Tunda Jannart ta da Malik suka mutu na shiga hannun mutane 😭 nace muku zan kashe wani ne?😩_
BABI NA TALATIN DA BAKWAI.
Idan na fahimci Innalillahi tana nufin, keb'ewa da nake da Hammah Mohan ba haka kawai bane ina barshi yana wani abu dani? Hmm tashi nayi tare da kallon shi.
"Tsaya a can zan sayi abu!" Na gaya mishi. Tsayawa yayi bakin hanya daidai kofar wani shagon sayar da maganin, sauka nayi tare da ɗaukar kudi a jakata, ban san nawa bane kawai ina zuwa shagon nace mishi.
"Bani maganin mura" na ajiye mishi kudin, yana gani ya shiga dibo min su, ya tara min, sunan su nake bi, zuba min yayi a laida. Sannan na dauki daya na bude take na shanye a gurin, na ajiye mishi kwalbar, na dauki sauran zuwa motar, tunda na shiga na zauna na juya mishi baya, haka nayi ya shan maganin nan bai tashi sanin abinda nake aikatawa ba sai da na kwalbe Kwalba uku, da na farko biyar yaji karan zuɓewar kwalabe a kasa, wani taka birki yayi tare da birkito ni.
Ganin saura Kwalba biyu ina bude ɗaya yayi maza ya gangara bakin hanya, ya kalle ni. Ranshi yayi mugun b'aci, kifa kai nayi sabida maganin ya fara tasiri a jikina.
"Ka gaya min me yasa duniyar take shirin juya min? Innah tace kana samun damar kwanciya dani zaka gudu kabarni, Ansar Yace min kana kwanciya dani zaka gudu kabarni me yasa tunanin su yayi daya ne?"
Jan numfashi nayi, sannan ba cire hijab dina nace mishi.
"Ka tab'a ganin mace a tube? Toh yau zaka ganin ni full naked." Na shiga cire kayana ina faɗin.
"Kawai zan baka kaina a wuce gurin, idan nayi haka zamu fi samun nutsuwa daga ni har su."
Raba rigar jikina nayi gida biyu, kafin na juya na kalle shi. Kwantar da kujeran nayi baya, kafin na shiga ƙoƙarin cire zanin jikina. Komawa nayi na kwanta, sabida na kasa cire zanin sai na shiga ƙoƙarin cire bra din, anan idanun shi ya sauka akan dukiyar fulanina. Da na fitar da dayan shi. Dayan yana cikin rigar shi. Tausayin ta ya kuma ninka sama da baya, cire rigar shi yayi ya lullube ta, sannan ya motso da fuskar shi, yana kallon yadda take mutsu mutsu da bakinta, kunnen shi ya kai yaji tana faɗin.
"Ba zan tab'a kashe iyayena ba, Innah amma zan iya sadaukar da rayuwata domin shafe tarihina, ina son Hammah Mohan!" Gyara mata kwanciya yayi, sannan ya tadda motar tare da barin gurin da gudu, ina son ya isa Niamey akan lokaci.
*
Damagaram.
Shigowa malam yayi ya same Innah tana fadar abubuwan da suka faru, akan rayuwar Moonah, kasakai yayi da bakin shi yana kallonta.
"Me ya faru?" Ya tambaye ta,
"Waye ban da wadannan lalatattun, yazo ya dauke ta har yana gaya min maganar banza ashe na cancanci wofantarwa Maimuna?" Ta fashe da kuka tana kallon shi.
"Baki cancanci haka ba, amma kuma daga ke har Sama'ila kun so kanku dayawa, ai dama na gaya muku dole gaskiya zata bayyana kanta. Ai ba yau aka fara ba. Ai ba yau Sama'ila ya fara ba, ba kuma sabon abu bane.
Dan haka ki ha bakin ki kiyi shiru, kiyi addu'a kawai Allah ya takaita hakkin iyaye akan ku. Kin zata yaran da ya raba da iyayen su, hakkin su zai tafi a banza ne? Ba zai tafi ba. Shima gudun tafiyar Ƙaddara yasa shi bai tab'a tunanin aure ba, da ya kuskura yayi auren da yaji yadda ake yinta na gaji da halin ki Allah ya gani, yar dan Uwanki? Zaki wulakanta ta, kamar ba jinin ki. Ai ko da Sama'ila yace ki rike ta karta tab'a bayyana kanta sai ya dawo ce miki akayi zaku yiwa Allah yawo? Ai baba Nasiru yayi gaskiya, dalilin soyayya ta bayyana kanta, yau dalilin SOYAYYA yarinya karama tana kuka. Ki barta ta rayu da abinda take so abu ya ci tura, toh Ni dake muzuba mu gani Allah yabawa mai rabo Sa'a."
Daga haka ya juya ya bar gidan ranshi yana soya, sabida zunzurutun bakincikin, ita kanta sai da tayi al'ajabi da abinda malam