Showing 120001 words to 123000 words out of 181864 words
murmushi yayi yana kara jin wani irin dad'i a ranshi. Kwace Apple din Haddir yayi yana dariya.
"Salman don Allah kace ya bani kayana"
"Ka bashi"
Suka hada baki suka yi.
*
"Insha Allah, Mohan bai da matar da ta wuce ki, karki damu ina tare dake, karki gayawa Mahaifiyarki. Zan sami yarinyar na ci ubanta.". Share kwallar ta tai sannan tace mata.
"Babu kome Ammyn nagode" tana gurin har taga fitar yarinyar a cikin asibitin, sannan ta koma cikin asibitin. Tunda ta shiga cikin take cika tana batsewa, su kuwa yaran suka ajiye ta a gefe, domin dama babu wannan shakuwar a tare dasu.
**
Tunda muka shiga taxi na ajiye kaina a gefe, ina jin wani irin kuka nason zuwa min, amma ban iya yi ba, har muka isa gidan mu. Ina shiga daki na zube a bakin gado tare da sake kuka me ciwo. Na rasa gane meke min dad'i, mahaifin shi ya tafi ya sa nazo, amma ya tashi yana wulakanta ni, meye nayi mishi da zafi haka? Dama baya sona ne?ko dai ya fahimci abinda ya faru ne?"
Haka nayi ta kuka ina tambayar kaina, har na gaji nayi shiru, kafin na kwanta a d'akin, baki daya sai gashi na shiga wani irin kad'aici, bana son magana. Washi gari da na shirya da sunan zan tafi kotu, sai gashi na buge da nufar asibitin, har kofar dakin na isa amma na kasa koda budewa ne, haka na gama nazarin abinda zan yi kafin na leka yana rike da Alqur'ani, na jima ina kallon shi, kafin ba juya zan tafi muka yi kicibis da wata Nurse.
"Lafiya!"
"A'a babu kome!" Na juya na fita da sauri, bude kofar dakin yayi yana kallonta, kafin ya leka hanyar wajen.
"Kana niman wani abu ne?"
"A'a babu kome!" Ya fada yana dawowa dakin, itama kallon hanyar tayi tare da kallon d'akin.
"Kalaman su iri daya"
Shiga tayi ta bashi magani, yana sha ya nufi window ta waje, ya hangota tana mai juyawa bayan ta kalli window, kura mata ido yayi yaga yadda take share kwalla.
*Meye nayi miki da zafi? Kika juya min baya*
Tsare taxi nayi tare da shiga cikin ina dafe kaina, na juya na kalli window, yana tsaye. Sake labulen yayi tare da juya bayan shi.
_Baka min kome ba! Sai dai ƙaddara da ta had'a mu itace zata rabamu! Ni din wani namiji ya wuce iyakar ka ne! Kayi hakuri amma ina kaunarka_
Na fada a raina, tare da jingina kaina, muna isa kotun, biyan kudin nayi sannan na nufi cikin,ina isa Alkali yana fitowa da wasu abokan shi turawa.
"Bonjour Abie?"
"Lafiya lau, ya jikinki?"
"Da sauki Sosai" na gaya mishi. Tare da barin gurin su,
"Alkali amma Yarka ce ko?"
Dariya yayi yana faɗin..
"Maimunari a'a ba ita bace, amma a ofishina take aiki"
"Kai Amma kamar ku ta b'ace, gaskiya."
Murmushi yayi sannan ya raka su, suka tafi shi kuma ya dawo. Ya samu ina waya.
"Eh Hammah ban san dai me nayi mishi ba, indai akan abinda ya faru ne Allah ya bashi hakuri, a'a bani bace yanzun haka ina gurin aiki ban je asibiti ba."
"Toh shikenan" ajiyar zuciya na sauke. Lokacin da kwalla ya zubo min, kafin na fara aikin da yake gabana yana tsaye a bakin kofar. Duk abinda nake jikina na rawa, amsar takardun da suke ta watsewa yayi,tare da zaunar dani. A lokacin na samu damar kuka tun daga kasar zucuyata nake kuka.
"Abie me yasa kome yake zuwa min babu sauki? Me yasa ƙaddara ta take da zafi haka? Na zata ko."
"Kice Alhamdulillahi"
"Alhamdulillahi Ubangiji Nagode maka" na fada tare da zama ina shashekar kuka,ruwa ya mika min nasha.
"Iyayen ki suna ina ne?"
"Damagaram!" Kura min ido yayi na wani lokaci, kafin yace min.
"Kinji abinda bakina suka ce min? Wai muna kama dake?" Da sauri na d'ago kai ina kallon shi. murmushi yai min sannan yace min.
"Tashi muje!"
"Toh aikin fa?"
"Karki damu zan dauki hutun yau baki daya akwai shari'ar da bani zan yi ba. Yau ina son nayi shi da ke ne ko baki son fita yawo dani ne?"
"Zan je"
Fita muka yi da shi, a hankali driven shi yake jan mu, yana yawo damu. Idan naga abu nace ina so zai tsayar da driven na saya na dawo, haka ya zama duk inda muka je babu abinda bai saya min ba, sai da muka dauko hanyar dawowa gida nayi mamakin da ya kawo ni har gida, da zan fita yace min.
"Yau da na fita dake, na sami nutsuwa ya dauke min damuwar da nake da ita. Allah yayi miki albarka ya daidaita ku da saurayinki" sunkuyar da kai nayi ina wasa da laida kayan hannuna, sannan nace mishi amin,sannan na shiga cikin gidan.
Sai da ya ga na shiga cikin gidan, sannan ya juya tare da barin unguwar shi da driven shi suna nufi office yayi abinda zai yi ya wuce gida.
.
"Karka musanta min mana tazo har nan fa! Kuma na ganta a tsaye taga lokacin da na sake labulen kan me yasa zaka kace a ita bace, bayan na ganta da idona."
"Kai Hammah sai kace wacce aka sace ta, kawai kayi fatan kasami lafiya domin Ammyn tana shirya maka aiki na musamman. Ta dawo da baikon ku nan da sati daya." Inji Salman yana kallon Mohan,
"Kuma da alamun ana baikon ba zai dauki lokaci ba a azayi bikin" inji Radiyah da take mika mishi ruwa.
"Allah ya bata sa'a"
"Bro me ka shirya mata."
Lumshe idanun shi yayi tare da kwanciyar shi,yaki magana. Dan Ba'are ne ya yi amfani da shirun shi ya gaya musu shirin sa.
"Amma baku da kirki! Wa Ammyn zamu watsawa kasa a idanu? Zan so naga yadda haka zai faru!" Inji Khausar tana dariyar mugunta ,dukkan su sun yarda akan bawa dan uwansu baya, kuma sun amince da abinda ya shirya musu, kawai abinda suke son gani mahaifiyar su ta amshi abin. Shigowar Primer minister yasa dakin ya kara armashi aka shiga hira.
A hankali Nairah da Radiyah suka fitar da wani gown Peach color, suka nuna mishi.
"Yayi kyau, amma ba zai mata kyau ba" ya faɗa yana shan kunun gyada da Khausar ta kawo mishi.
"Hammah ga wani ja ne?" Mika mishi Tap din suka yi yana dubawa yana kallon kayan a hankali ya tab'a wani tare da mika musu.
"Hanan fa?" Khausar ta tambaye shi daidai shigowar Ammynsu.
"Tun wancan satin na ba Ammyn kudin gown ɗinta bansan ya aka yi ba"
"Eh mun sayo mata Royal blue ne"
"Amma Ammyn ita" wani kallon banza ta watsawa Nairah tayi shiru tana tura baki gaba.
"Haba a tashi a ba mutum abinda bai mishi ba, sam bata da wani fasali idan ka cire farin fata mutum sai kace 1"
Tsaki tai cikin fada da hargagi Ammyn tace mata.
"Zan fasa bakinki nan idan kece zaki zauna mishi da ita! Mohan wai baka sonta?" Ta tambaye shi ranta a b'ace.."ina sonta mana" ya faɗa yana hararan Nairah. Haka suka shiga watsewa har dan Ba'are, suka bar mata dakin, nan ta ga shima ya kwanta kamar zai yi barci. Ta dauko magani a cikin jakarta zata saka mishi yana kallonta, tana gama saka maganin a cikin flast din tace mishi.
"Kayi barci ne! Bari naje na dawo" tana fita ya mike tare da tausayin mahaifiyar shi, wacce irin masifa ce haka? Bai tab'a ba sai da dan Ba'are ya shigo ya gaya mishi ya shiga ya zubda har kunun yayi wani irin farau a idanu, yana zubdawa ya wanke sannan ya zauna yana bawa Mohan hakuri.
Bayan sallah isha Umman Dan Ba'are da Hajiya Karime suka zo, duk da ba tafiya daya bace amma kuma a tare suka shigo dakin a cika.
Nima shigowa nayi daga bakin kofar nake kallon shi, ta jinin kofar dake akwai glass, d'ago kai yayi, muka yi ido biyu.
"Khalil Maimunari tazo ka tabbatar ka hanata tafiya, idan aka watse ina son ganinta,"
Da sauri ya fita tare da tsare ta, tana kokarin tare abin hawa.
"Mss Mamman Nasir Aghali, ina za a tafi haka? Muje can ki zauna" ya nuna min guri muka zauna ina rike da kulata, kaina a sunkuye.
"Gashi ka bashi ka tabbatar yaci abincin ya sha magani"
"Toh amma ai shi romeo yace na tabbatar kin jira baki sun tafi na kaiki cikin dakin shi."
"A'a Hammah zan tafi kawai bana jin dadin jikina ne"
Saka wayar shi yayi a kunnen shi, yana faɗin.
"Zata tafi fa"
"Bata wayar"
Mika min wayar yayi, na masa a sanyayye, sannan na saka wayar a kunnena.
"Zaki iya tafiya idan kin so, bakin cikin ki bai kashe ni ba, Kinga kuwa tafiyar ki ba zai kashe ni ba, sai an jima" sannan ya kashe wayar, shiru nayi ina kallon wayar.
Kallon Hammah Khalil nayi, sannan na sunkuyar da kaina, ina faɗin.
"Zan jira shi"
"Me yasa kika bashi wahala?"
"Hammah Mohan yana da zafin kishi! Idan yana tare dani zai tsane ni wata rana"
" Bazai tsane ki ba" haka ya shiga bani hakuri, har suka fito sannan ya amshi kular yana gaba ina baya har muka shiga d'akin, yana kwance yana waya, yadda yake magana a gadarance ya tabbatar min shi da Hanan ce.
Dan haka na sunkuyar da kaina, ina tsaye, ina jin wani abu a raina.
"Toh kasha maganin kwari ki mutu!" Kome ta gaya mishi ya caka mata Bakar magana haka oho.
"Kina shan wine ai sabida gyaran jiki da gashin ki me zai hana kisha zai saka ki barci!" Kashe wayar yayi tare da sakawa a kasan pillow.
"Khalil kasan yarinyar nan tana shan beer! Wallahi na zata sharri ne, Radiyah tayi mata sai d'azun da Nairah take nuna min wani video ɗinta, ina ga ita kanta bata san Nairah ta dauka ba, duba fa kimanin dubu dari uku ake sayar da wannan kwalbar, da na tambaye ta sai ce min tayi ai ba wani babu bane yana taimakawa fatarta da kuma gashin kanta! Don Allah matar da zan aura na ajiyewa Yarana."
"Toh kayi hakuri mana, baka kan shirin ka ba, Angon mata biyu" inji dan Ba'are ya zoyale shi.
"Zanci Ubanka dan iska, ina wasa da kai ne, mace daya ta ishe ni."
"Hanan ko Maimunari?"
"Mitsww! " Yaja tsaki,fita Dan Ba'are yayi ya barsu. Saukowa yayi daga gadon, ya tako gabanta, d'ago kai nayi ina kallon shi. Ina matsawa da baya. Har muka kure bangon dakin. Yayi maza Yasaka hannun shi akan karfen da maso buga kaina.
"Meye ya kawo ki"
"Ba gurinka nazo ba, nazo ganin Khausar ce"
"Toh amma kuma shine kike lekena bakin ce baki sona ba?"
"Eh... Eh... Amma ai ba gurinka nazo ba"
"Toh gurin wa kika zo? Naga dai baki da mara lafiya nan asibitin."
"Eh na sani" na fada ina kawar da kaina.
"Toh meye kika kawo a kular?" Ya amsa yana budewa. Kamshin kayan miya da kayan kamshi ya daki hancin shi.
"Ai kin kawowa mara lafiyar ki ne?" Kokarin kwace kwanon nake amma ina ya kwace abin shi.
"Idan kika nace zan baki wahala" kyale shi nayi ina kallon shi, karshe na koma bakin kujeran na zauna ina kallon shi,
Mikewa yayi ya wanke hannun shi, ya cinye gurasar da na kaso mishi da miya.
"Nasan wannan girkin Kawar mu ce" ban kula shi ba,yana gamawa ya wanke hannun shi, sannan ya dawo ya durkusa a gabana.
"Kina nan akan bakarki ko kin zo niman sulhu ne?"
"Don Allah kyale Ni" na fada ina niman hanyar mik'ewa, shima mik'ewa yayi kamar zan fad'i, ya saka hannun shi a k'uguna, a hankali ya d'ago ni.
"Idan kika ga kin fadi ina raye, Allah ne ya nufa zaki fadi matukar ina raye, rayuwarki zan bawa kariya da tawa" a hankali na janye jikina ina dauke numfashina.
Daga Ni har shi muna tsaye rike da juna, kamar ba zamu rabu ba, kafin na janye hannuna na amshi kular na saka a laidar, waya yayi can sai ga Hammah Khalil.
"Ka zauna anan zan kaita gida"
"Wannan wani irin Iskanci ne? Niman Beenah nake a social media amma ban dace ba!"
"Benazir kake nufi?"
"Eh man" ya faɗa a fusace, kallon Hammah Mohan nayi ina wasa da hannuna.
"Nawa zaka bani na baka Number ta,"
"Kai Maimunarin Hammah Mohan!" Mika mishi wayar nayi, ina kallon shi ya dauki Number ta, sannan ya koma bakin gadon ya zauna, yana kad'a kafar shi.
"Zaka iya tafiya kawai zan ji da kome"
Ya wurga mishi key,tunda muka fita escort suke bibiyar shi, sabida bashi tsaro, asali ma a bakin ward din suna tsaye, ciki ne dai basu shiga ba.
Hannuna ya lalluba ya hada yana tuki dashi.
"Kin razana ni a cikin sati biyu zuwa uku, sabida ban san laifina ba. Kuma ana ta bani wahala."
"Ni ban baka wahala ba, Kishin da yake zagaye da ranka shi zai kaika ya baro ka, amma ni kam bani da burin cutar da kai."
Juyawa yayi tare da kallona.
"Me yasa, kika so juya min baya?"
" Ba za a bar maganar ya wuce ba?" Na tambaye shi ina kallon gefen hanya.
"Shi kenan" ya fada min, koda muka zo apartment din mu, shima zuba min ido yayi, na wani lokaci. Kafin ya ce min.
"Nagode da kulawa?"
"Allah ya baka lafiya" na saka kai zan fita, yace min.
"An saka ranar baikona" gabana ne ya fadi sosai, kafin na juya na sake mishi wadatacciyar murmushi nace mishi.
"Allah ya tabbatar da Alkhairi! Yanzun kan dole mu hakura da juna,"
"Sabida me yasa? Kika sani ko kizo a Matana na biyu" ya faɗa yana zolaya na."
"Hmm"
"Allah ya kiyayye ko?"
"A'a kawai gani nayi kawai bamu dace."
Bakin shi naji a saman hannuna, yayi matukar sanyi bakin shi, a hankali ya d'ago bakin shi.
"Next time kika Kuskura kika fadi wani abu a kan soyayyar mu bakin ki zan kaiwa hari, domin shine tanadina na gaba" maza nayi na rufe bakin, yana murmushin mugunta,.hararan shi nayi bayan na fita.
"Allah ya shirya ka" na fada ina dariya, haka shima dariya yake tare da cewa.
"Tsaya don Allah na nuna miki shiriyar da Allah yayi min yarinya da kin fadi gaskiyar ki"
"Ba dani ba gad'a a hurumi."
Sai da yaga shiga na sannan ya juya abinshi.
... Ina shiga Auta ta fashe da dariya, tana faɗin.
"Munafukai kun shirya kenan da alamun shi ya kawo ki"
Dage mata gira nayi, sannan na wuce d'akina. Ina bata labarin baikon shi da Hanan, ban san me yasa ba kodan abinda ya faru dani ne haka kawai nake jin na hakura da Mohan, na cire shi a rayuwata, baki daya sai na rasa meke min dad'i. Har Abie ya fahimci irin halin da nake ciki da kanshi yake bani hakuri har ya bani addu'o'in da zan nayi idan akwai Alkhairi a soyayyar mu, karshe abinda ya gaya min ya sani jin sauƙin Al'amarin.
"Idan kina son Mohan zan iya kama miki shi yadda duk duniya babu wanda ya isa ya raba shi dake, amma kuma meye ribarki? Meye zaki samu bayan soyayya kike nima? Gashi nan dai kin samu idan babu kwanciyar hankali fa, kiyi hakuri ki fuskanci ƙaddarar ki, Allah zai baki abinda kike bukata."
Da wannan yanayin na hakura tare da cire raina akan shi baki daya.
***
A kwanakin da suka gabata an sallami Mohan, inda aka shiga hidimar baikon shi. Da kanshi ya kawo min kayan da zan saka ranar amma naki sai da muka yi faɗa kafin ya ajiye min yayi tafiyar shi....
Zata fashe.....
Gaskiya ina jin tashin daraja🤔🙄 idan kuma kayi dace na kafta toh bi ma'ana da Yaren Larabci ba zan yi typing gobe ba, haka kawai nake jin haka💓
#Mai_Dambu
[8/8, 10:02 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1112247835?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=QQEFDfGekFSRJARqCuAgczdBfyHHQPoGIoXw1TaQOoLLncl9SQq3Zn4Oggvn2k4IOQsrOsZ3SiMt1bhI1OjgktiAuZVMV8ZakJtY1sLTSD8fi3CxlBeppdQp3axJbI3j
🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
BABI NA ARBA'IN DA BAKWAI.
_SANNUN MUTANE 🤡🙋🏾♂️ INA GAISUWA MUSAMMAN MUTANE ANSAR DA HAJIYA LATEEFAH DA HAJIYA KARIME 💓😘 ANA TARE 🤝_
Kallon gown din nayi ina Kuma juya shi.
"Amma ai wannan bai yi kama da gayyatar ki yayi ba, sabida."
Kallonta nayi domin bana jin a raina ba gayyatatta yayi ba. Watsar da kayan nayi tare da kwanciya ina jin babu dadi.
"Na tsane shi!"
"Da gaske"
"Allah ina gaya miki na tsani Hammah Mohan!" Na kuma fadar haka ina kallon kayan,
"Zan yarda kina jin haushinsa amma banda tsana, meye laifin shi? Dan kawai za ayi baikon shi da wata mace?" Tashi nayi zaune na kuma kallonta.
"Amma dai...."
Shiru nayi tare da komawa na kwanta, ina jin daci a raina, tsaki nayi tare da juya mata baya, raina na kara b'aci, ina zan iya samun kamar shi, sai dai nasan na rasa shi kenan har abada.
Da haka na tsunduma cikin tunani.
**
Diffa.
Sanye yake da irin kayan sakin nan, yana zaune a kujeran guragu. Ya saka hoton Maimunari a gaba yana kallon ta.
"Appa!" Watsar da abubuwan da suke gaban shi yayi, cikin fushi da damuwa.
"Yarinyar kawai nake bukata! Amma ka gaza niman soyayyarta, meye amfanin kiranka da sunan D'ana soyayyarta ma ta gaggare ka! Dan ina nakashe" ya faɗa da karfi. Sai da mutanen gidan suka fito.
Zuɓewa yayi a gaban shi. Ya rsa yadda zai mahaifin shi ya fahimci abinda yake faruwa.
"Yarinyar da tun tana namiji yace min nata sona, duk lokacin da na shirya mata wani abu bata tab'a faduwa sai nasara, yarinyar ta rike Allah sama da yadda kake tunani, Appa Munnah ba gama garin mutane bace domin yar baiwa ce tana da tawwakali don Allah kayi hakuri, idan tana rabon mu zata shigo cikin gidan nan, tunda itace kake bukata zan kawo maka ita indai zaka yi nasara a rayuwar ka."
Sanarwan baikon Mohan da Hanan ne ya katse mishi sauran bayanin, murmushi yayi sannan ya ciro wayar shi zai kira Munnah sai ya fasa, dan haka ya shiga garin ciki babu iyaka. Dan haka yake jin yanzun zai iya tura mata sakon da zai saka ta amince da shi ta wata fuskar,dan haka ya tura mata da wata wayar.
**
Da Asuba bayan na idar da sallah, ina kwance na janyo wayata na kunna, bayan na bude data. Na duba Internet, abu daya ne wato sake hotonan Hanan da Mohan, babu karya babu hassada sun